Showing 36001 words to 39000 words out of 113443 words
gwiwa yasa kai ya shiga gidan bakinsa ɗauke da sallama, kasancewar ba wani samun wutar nefa suke sosai ba a unguwar yasa ya zaro wayarsa ya kunna fitila ya haska ƙofar ɗakin.
Sosai Ya Azeez yaji gwiwarsa tayi sanyi sakamakon tozali da yayi da ƙaton kwaɗon dake garƙame a jikin ƙofar ɗakin, cikin mamaki yace "Kenan yarinyar nan yau ma sai data saka ƙafa ta sake fita daga cikin gidan nan..toh ina kuma taje ita da bata da lafiya...?" Ya faɗa a fili cike da al'ajabi lokaci ɗaya yana zama kan wani ƙaramin dutsen siminti dake ajiye a bakin ƙofar ɗakin nasu ya yi tagumi.
Gefe guda a ransa kuwa faɗi yake "Ya Allah kaji ƙaina ka tausaya min ka yafe min laifukan da nayi maka wanda na sani da ma wanda ban sani ba, Ya Allah kaga zuciyata kaga abinda ke cikinta Allah ka dubeni ka yaye min abinda nake ji a zuciyata ka musanya min da mafi alkhairi..."
Yake faɗa lokaci ɗaya yana jin tsiyayowar wasu hawaye masu ɗumi da raɗaɗi saman kumatunsa.
*******
Fadwa kuwa a dai-dai wannan lokacin tana can gaba gaba a tsakiyar filin rawa tana ta cashewa abunta hankalinta kwance, ko ajikinta babu abinda ya dameta dan ko tunanin gida ba tayi kawai sha'anin gabanta take.
Ta zage sai kwasar rawa take har da kaiwa ƙasa, ƙawayenta kuwa duk sun baibayeta suna ta mata ɓarin sababbin kuɗi ƴan dubu dubu, ita kuwa ta dage sai juyi take tana ta wani kakkarya jiki kamar zata karye.
Sai gurin ƙarfe 11:30pm dai-dai sannan aka tashi daga Dinnern mutane suka soma fitowa daga hall ɗin kowa yana nufar inda motarsa take fake, a hankali a hankali duk mutanen suka fara watsewa da haka kowa ya kama gabbansa harabar gurin ta zamo ba kowa sai iya security ɗin dake aiki a gurin.
A hankali Hajiya Labiba ke jan motar tana tuƙi cikin ƙwarewa da natsuwa yayinda Fadwa ke zaune a gefenta tana kallon hanya suna taɓa hirar yadda Dinnern ta kasance sama sama suna shewa cike da nishaɗi, da haka har suka shigo unguwarsu Fadwan.
Dai-dai lokacin Ya Azeez ya dawo daga gidan bulon da yake kai ajiyar kekensa ya iske motar Hajiya Labiban fake a ƙofar gidan nasu yayinda suka buɗe duka ƙofofin motar lokaci ɗaya suna ƙoƙarin fitowa, abunka da dare gaba ɗaya muryar Fadwa duk ta karaɗe layin inda take ta kwasar dariya cike da nishaɗi tana faɗin "Ai wallahi ji nayi kamar kar a tashi Dinnern nan yanzu ƙawata, abun yayi masifar yi min daɗi ji nayi dama a kwana anayi wallahi bazan gaji ba, kai harkar arziki tayi ina tsiya ta ga rana ai talauci babbar masifa ce, shiyasa Annabi yace mu nemi tsari da talauci..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana fitowa daga motar tare da rataya jakarta a gefen kafaɗarta.
Hajiya Labiba data fito daga motar itama tana kallonta cikin dariya tace "Ai biki ma ba'a fara ba tukunna ƙawata, ƙila har sai kin gaji da zirga zirga kin daina zuwa kinsan biki indai na gidansu Lubna Sambo ne saika gaji da zaryar zuwa party dan akwaisu da son raƙashewa..kamar ƴaƴan dujal...."
Fadwa ta saki dariyar jin daɗi tana faɗin "Tabɗi aiko bazan taɓa gajiya ba ƙawata kema kinsani indai irin wannan harkar ce mu ne kan gaba gaba dan bama taɓa bata kunya..."
Hajiya Labiba ta buɗe baki kenan zatayi magana Azeez dake tsaye daga can gefensu yana sauraren su ya ɗaga murya yana faɗin "Muje ki buɗe min ƙofar ɗakin tukunna sai ki juya ku koma inda kuka fito kuje ku ci gaba daga inda kuka tsaya..." Da sauri dukkansu suka juyo suna kallonsa ganin irin banzan kallon da yake binsu dashi ne yasa gaba ɗayansu suka ɗauke kai cikin wani irin yanayi, Hajiya Labiba ta kama murfin motarta ta buɗe kana ta waigo tana faɗin "Toh ƙawata kuje ki buɗe mai ƙofar, sai mun sake haɗuwa goben, Allah ya huta gajiya..." Tana gama faɗin haka ta juya ta watsa mai harara kana ta shige motarta ta zauna ta kunna tayi ribas ta fice daga layin a guje ta barsu nan tsaye suna kallon kallo.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad:Aishaalto09*
1️⃣5️⃣
Ya Azeez daya daskare a tsaye kawai kallon Fadwa yake cikin mamaki da al'ajabinta dan tunda sukayi aure zai iya cewa wannan shine karo na farko da ta taɓa irin wannan fitar ta kuma kai har wannan lokacin haka a waje dan haka abun yayi bala'in ɗaure masa kai da mamaki.
A hankali ya matso kusa da ita lokaci ɗaya yana ƙare mata kallon sama da ƙasa kafin cikin sanyin muryarsa yace "Yanzu tsakaninki da Allah Fadwa abinda kike yi kin kyautawa kanki kenan..? Yanzu wannan itace irin rayuwar da kika zaɓarwa kanki a matsayinki na matar aure...? Wannan wace irin fitina ce haka kika ɗorawa kanki..ko an gaya miki talauci hauka ne da zaki bi ki takura rayuwarki ki hana kanki sukuni da kwanciyar hankali a banza da wofi...? Yanzu ke hakan da kike yi yayi miki dai-dai kenan a matsayinki na matar aure ace ki saka ƙafa ki fita ki bar gidanki bada sanin mijinki ba tun da sauran safiya ki tafi gidan ƙawaye kije ki miƙe ƙafa ki ta zama kina zubarwa da kanki mutunci kamar wacce bata da mafaɗi...Yanzu ke hakan shine dai-dai a gareki...?"
Ya faɗa lokaci ɗaya yana ƙureta da ido, gaba ɗaya Fadwa sai taji gwiwarta tayi sanyi ta ɗago kai tana dubansa cikin wani yanayi tace "Meya faru kuma daga dawowata da tsohon daren nan zaka tsareni da wasu kalar maganganu marasa tushe ballantana makama...ko nayi maka wani laifin ne...ko kuma gidajen ƙawayen nawa da kake ta nacin maimaita ina zuwa naka ne ko na wasu ƴan gidanku da abun zai dameka...?" Ta faɗa kai tsaye tana aika masa da wani mugun kallo cike da jin haushinsa, kafin ta saki tsaki lokaci ɗaya tana faɗin "Idan naka ne ko na wani daga cikin danginku daga yau don girman Allah Ya Azeez ka hanani zuwa, ko kasa idan naje su wulaƙanta ni suyi min korar kare suce kar in sake zuwa kaji....?" Tana gama faɗin haka kawai taja wani dogon tsaki ta wuce tana harararsa.
Har ta kusa shiga gidan ya tafi da sauri ya sha gabanta ya tsaya yana watsa mata wani mugun kallo kafin ya fizgi hannunta da ƙarfi a fusace ya jata ƙiiii kamar kayan wanki suka shige cikin gidan, Fadwa data cika da mamakinsa ta zaro ido waje cike da tsoro ta shiga ƙoƙarin ƙwacewa a hannunsa tana ta tittirjewa amma yaƙi sakinta har sai daya sadata da tsakar gidan sannan yayi wurgi da ita can gefe guda ya watsar har sai da kanta ya gwaru da bango ta saki ihun azaba lokaci ɗaya ta dafe kanta cike da tsoro dan ba ƙaramin buguwa kan nata yayi ba.
Wani kallon banza ya wurga mata ba tare da yace komai ba ya fara matsawa gabanta, tana ganin haka ta ƙara gigicewa jikinta ya ɗauki rawa da kakkarwa, a gigice ta soma matsawa tana ja da baya da baya a tsorace tana faɗin "Dan girman Allah Ya Azeez kayi haƙuri..wallahi tallahi gurin bikin ƙanwar Hajiya Lubna mukaje daga can muke..na rantse da Allah ba yawo naje ba idan kuma baka yarda ba ka kira Hajiya Labiba ma ka tambayeta kaji wallahi duk muna tare dasu acan..." Ta ƙarashe maganar cike da tsoro tana kallonsa, gaba ɗaya yanzu yanayinsa tsoro yake bata, tun abinda yayi mata jiya ta ƙara shiga taitayinta take kuma ƙara jin tsanarsa a ranta, Ballantana kuma yanzu da taga ya bala'in fusata, sai take ji a ranta kamar rufeta kawai zaiyi da masifaffen duka.
Dan haka ta samu hantar cikinta da kaɗawa ga wani tsananin tsoron muguntarsa da firgicin da suka ziyarci zuciyarta lokaci guda, a ruɗe ta ja da baya da sauri ta matsa gefe.
Sake ɗaure fuskarsa yayi tamau kamar wanda bai taɓa dariya ba yace "Amma kin tambayeni lokacin da zaki fitan, ko kin taɓa gaya min zakije bikin ƙanwar ƙawarki...?"
Bakinta na rawa tace "A'i nasan kona tambayeka bazaka taɓa barina inje ba ne, shiyasa nayi tafiya ta..." Ta faɗa cike da gadara haɗe da tsoro tana harararsa ƙasa ƙasa, dan Allah ya gani al'amarin nasa ya fara bata haushi, ta ya zai wani tasota gaba ya tsareta da wasu shegun koɗaɗɗun tambayoyinsa kamar wani alƙali.
Duk yana kallonta amma bai ce komai ba ya kaɗa kansa kawai ya juya cikin raɗaɗin zuciya yana faɗin "Ok hakan yayi dai-dai, muje ki buɗe min ƙofar ɗakin dan Allah inaso zanyi wanka..."
Ya faɗa cike da takaici wanda da gani kasan ransa a matuƙar ɓace yake, wata irin dakiya taji tazo mata ta wani kallesa tun daga sama har ƙasa a wulaƙance kafin ta fashe da wata irin dariya wacce kana jinta kasan ta tsantsar rainin wayau ce da son turawa mutum haushi tace "Uhmmm Ya Azeez kenan nida zaka taimaka min ma kayi min adalci ka sahale min wannan ƙaddararren auren naka mara amfani wallahi daka gama min komai ka taimaki rayuwata dan Allah ya gani kamar ina zaune ne akan ƙaya haka nake jina..wai muje ki buɗe min ƙofar ɗakin inaso zanyi wanka, sai kace wani ɗakin azo a gani ko wanda yake da haɗaɗɗen toilet ɗin wanka a ciki ni wallahi wani lokacin ma dariya kake bani idan naga kana wannan taƙamar da wani nuna isa da gadara sai kace wanda ya isa da gidansa ya kuma mallaki komai na jin daɗin rayuwa...nan ko hotiho ne fankan fayau..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana sake fashewa da dariya kana ta miƙe ta ɗauki jakarta da tayi wurgi da ita can gefe ta zura hannu ta lalubo ɗan makullin ta bi bayansa, yana nan tsaye a bakin ƙofar ɗakin ta raɓa ta gefensa ta tsaya sai data kallesa ta wani taɓe baki sannan ta zura makullin ta buɗe ta tura ƙyauren lokaci ɗaya ƙofar ta buɗe kana ta matsa gefe ta bashi hanya tana faɗin "Na buɗe ranka ya daɗe..."
Ta faɗa tana ƙara sakin wani shu'umin murmushi.
Ko kallonta bai yi ba ballantana tasa ran zai tanka mata haka yasa kai ya shigewarsa cikin ɗakin ya barta nan tsaye tana hararar bayansa.
Ɗaga kafaɗarta tayi alamar ko a jikinta kana tabi bayansa ta shige ɗakin itama, tsaye yake a tsakar ɗakin yana ƙoƙarin tuɓe kayan jikinsa ta shigo ta wucesa ta shige uwar ɗaka, har ya ɗaga rigar jikinsa zai cire ya tuna da ledar fura dasu fruit ɗin daya siyo mata tun ɗazu suna tsakar gidan ya manta dasu, ya juya da sauri ya fice yaje ya ɗauko mata furar kuwa har ta gama saki salaf ba sanyin ko kaɗan saɓanin lokacin daya siyota ƙarara dan har da ƙanƙara aka saka a ciki, ya dawo ɗakin hakimar tana zaune a bakin gado ya shiga uwar ɗakan ya dire mata ledojin a gabanta ba tare da yace mata komai ba ya sake juyawa ya koma falo.
Ko kallonsa ba tayi ba ballantana ta kalli ledar daya ajiye matan, haka ta miƙe ta tsallake su tana sakin tsaki ta fara ƙoƙarin cire kayan jikinta, sai data cire sarka da ƴan kunnen da Hajiya Labiba ta ara mata da awarwarayenta tsaf ta zuba mata a cikin jaka sannan ta tuɓe kayan jikinta ta janyo zani ta ɗaura ta haye gado ta kwanta lokaci ɗaya ta lumshe idanunta tana sauke numfashi.
Tana nan kwance ya shigo cikin ɗakin ya ɗauki soson wanka da gajeren wandonsa ya sake ficewa, zuwa can kuma har bacci ya soma ɗaukarta sama sama ta jiyo motsinsa a falo ta miƙe da sauri ta sauka daga kan gadon ta ɗaga labule ta ɗan leƙa.
Hangosa tayi yana ƙoƙarin shimfiɗa tabarma a tsakar ɗakin, da sauri ta ƙarasa gabansa tana faɗin "A'a Ya Azeez ya haka ba dai nufinka a nan zaka kwana ba...?"
Ko ɗaga kai bai yi ya kalleta ba yace "Haka nake nufi Fadwa yau anan nake sha'awar kwana..."
Ya faɗa kai tsaye ba tare daya kalleta ba, ya ƙarasa shimfiɗa tabarman kana ya juya ya koma cikin ɗakin yaje ya ɗauko wani ƙaramin bargonsa da Ummansa ta bashi tun lokacin yana karatu a BUK yazo ya shimfiɗa akan tabarman ya haye yayi kwanciyarsa abunsa ya juya mata baya, kallonsa kawai Fadwa take yi cike da mamaki kafin ta saki tsaki tana hararar bayansa ta juya tayi komarta cikin ɗaki ta haye gado tayi kwanciyarta hankalinta kwance taja bargo ta lulluɓe jikinta ta ƙudundune tana faɗin "Ni dama Allah zaisa kayi zuciya ka sawwaƙe min wannan munafukin ƙaddararren auren naka daka taimakeni wallahi, sai inje in duƙufa da yi maka addu'a ina roƙon Allah ya haɗaka da dai-dai kai wacce zata dace da yanayin talaucinka dan ni dai kam ai nayi maka nisa kowa ya sani kawai an shiga hakkina ne babu yadda zanyi...." Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana jan tsaki kana ta sake lafewa a gadon ta lumshe idanuwanta wanda suke cike da baccin gajiya, dan har wani lumshewa suke yi suna mata wani yaji yaji saboda tsabar rashin samun isasshen baccin da bata yi ba, ga kuma gajiyar da tayi tuɓus gaba ɗaya jikinta a sake yake kamar wacce aka yiwa shegen duka ƙafarta kuwa har wani ɗib ɗib take mata saboda tsabar taku da raye rayen da ta sha yau.
Bata jima da kwanciyar ba, wani daddaɗan bacci mai cike da zallar natsuwa da jin daɗi yayi awon gaba da ita.
Ya Azeez kuwa ya daɗe idonsa biyu ya kasa bacci yana ta juye juye da tunane tunanen rayuwa zuciyarsa kamar zatayi bindiga saboda tsabar baƙin ciki da takaicin Fadwa, gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idanuwansa sai wani irin tafasa da ƙuna zuciyarsa take yi. Ganin tunanin yana neman hanasa sukuni da natsuwar zuciya ne a banza yasa ya tashi ya ɗauki buta bayan ya kunna glove ɗin ɗakin haske ya gauraye ko'ina kasancewar akwai wutar nefa da suka kawo tun ƙarfe 12:30am. Basu ɗauke ba ya fita tsakar gida yaje ya ɗauro alwala ya dawo ɗakin ya shimfiɗa darduma ya hau ya daidaita tsaiwarsa ya tada sallah.
Ya daɗe a sujjadarsa ta ƙarshe yana kai kukansa ga rabbil izzati cikin ƙasƙantar da kai da nuna tsantsar tawakali da tsoron Allah, kafin ya ɗago daga sujjadar yana mai ƙara miƙa dukkan lamuransa ga Sarkin sarakuna mai ji kuma mai gani wanda yake shi kaɗai bashi da wani abokin tarayya. Ya daɗe zaune akan darduman yana ta yiwa Allah kirari kafin ya ɗora da salatin Annabi (SAW) daga nan ya shiga kwararo addu'oi kan Allah ya zaɓa musu dukkan abinda yafi zama alkhairi a tsakaninsa da Fadwa sannan ya tashi ya shiga cikin ɗakin ya ɗauko Alkur'ani da cashaba ya dawo ya zauna ya fara karatu a hankali cikin daddaɗar muryarsa mai sanyi da sanyaya zuciya da saukar da shauki ga duk wanda ya saurara.
Yana nan akan darduman bai tashi ba har 4:30am. Na asuba dai-dai ta buga a alarm ɗin daya saka cikin wayarsa domin ya riƙa tadashi, sai da yayi addu'a ya shafa kana ya miƙe cikin kuzari da wani irin farin ciki da yake ji tun daga can ƙasan zuciyarsa yana taso masa wanda baya rasa nasaba da addu'oin da yayi, linke darduman yayi ya ajiye akan tabarman daya shimfiɗa sannan ya mayar da Alkur'anin uwar ɗaka ya ajiye a inda ya ɗaukosa, kana ya fita daga ɗakin yaje ya buɗe ɗan kichin ɗinsu ya ɗauko murhun gawayi ya fito dashi tsakar gida sannan ya koma ya ɗauko ƙaramar tukunyar da suke dafa ruwan wanka da tsintsiya ya fito, sai daya haɗa gawayin wanda ya samu da ƙyar ya rure har ya kama sannan ya zuba ruwa a tukunyar ya ɗora ya rufe, kana ya ɗauki tsintsinya ya hau sharan tsakar gidan kamar yadda ya saba.
Sai daya share ko'ina yayi fes fes gwanin sha'awa ya kwashe sharar ya zuba a abin zuba shara kana ya ɗauki manyan bokitan da yake zuwa ɗebo ruwa dasu ya fita, sai daya ciccika ko'ina kamar yadda ya saba duk bayan kwana uku, koda ya gama lokacin ruwan daya ɗora yayi zafi sosai ya juye a bokiti ya sake zuba wani ya ɗora sannan ya sirka wanda ya juye ya shiga cikin ɗakin ya ɗauko kwandon soso ya fito ya ɗauki ruwan ya shiga banɗaki, bai wani jima sosai ba yayo wanka ya fito ya zuba ruwa a buta ya ɗaura alwala kana ya koma ɗaki har lokacin gimbiyar na nan a ƙudundune tana sharar bacci, bai ko bi ta kanta ba ya buɗe jakarsa ya ɗauki riga da wandonsa na wani farin yadi mai sauƙin kuɗi ya saka sannan ya shafa mai sama sama kana cikin sauri ya fesa turare a gurguje ya ɗauki casbahansa ya fice ya zura takalmansa ya nufi masallaci dan lokacin har ƙarfe 5am tayi da ƴan mintuna dan har wasu masallatan ma sun tada sallah.
Yau bai wani zauna a masallacin ba ana idar da sallah ya fito ya nufo gidan yana zuwa ya iske ruwan daya ɗorawa Fadwa yayi zafi sosai har yana shirin tafasa bai sauke ba ya shiga ɗakin direct ya wuce uwar ɗaka, bai yi wani mamaki ba ganin har lokacin tana nan kwance tana ta sharar bacci bata tashi ba, kaɗa kai kawai yayi ya ɗauki makullin keke napep ɗinsa dake ajiye a saman jakarsa kana ya ɗauko wandon daya cire ya laluba aljihun ya zaro kuɗi ya ciri ɗari biyar ya ajiye a kusa da ita sannan ya zura sauran cikin aljihun wandon da ke jikinsa, har ya juya zai fice daga ɗakin sai yayi wani tunani ya fasa ya dawo da baya ya tsaya a kanta yana kiran sunanta a hankali yake faɗin "Ke Fadwa...Fadwa..." Ya faɗa cikin sanyin muryarsa lokaci ɗaya yana ɗan dukan ƙafarta.
Kamar a mafarki Fadwa taji muryarsa a sama yana kiran sunanta, cike da takaici ta saki tsaki kafin ta juya tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta da suke cike da bacci har lokacin.
A hankali har ta gama waresu fes a kansa yana tsaye kyakkyawar fuskar nan tasa a haɗe tamau kamar wanda bai taɓa dariya ba, sai ta ga ya ƙara mata wani kwarjini na musamman ya cika mata idanu, kayan daya saka sun karɓi