Showing 93001 words to 96000 words out of 113443 words
damesu, waya kuwa a rana sai suyi ta yafi sau ashirin, har wata shaƙuwa suka ƙara yi ta musamman a tsakaninsu, domin basu iya yin awa ɗaya ba tare da sunji muryoyin junansu ba.
Yayinda gefe guda kuma ga harkar kasuwancinsu Ya Azeez ɗin da zuwa yanzu komai yake ƙara haɓɓaka, wata bakwai gidan motocin su yayi da buɗewa, amma lokaci kaɗan ya yiwa sauran zarra wanda kuma dama Ya Azeez haka yake komai ya sakawa hannu sai abun yayi albarka.
Wanda kafin kuma wannan watannin Abba da Fahad na matuƙar alfahari da samun Ya Azeez ɗin saboda tsantsar maida hankalinsa akan kasuwancin nasu.
Haka ma Ummansa dan zuwa wannan lokacin tuni ya siyan mata wani haɗaɗɗen gida mai kyau a cikin unguwar Mashi Road, sannan ya zuba mata ababen more rayuwar duk wani jin daɗin duniya, da motar hawa mai kyau da tsada sannan ya ɗaukan musu direba saboda zirga zirgan kai Imaan makaranta da ɗaukota, sai kuma idan Umma zata fita unguwa itama ya kaita kuma ya dawo da ita, sannan duk wata yake biyasa.
Haka Abban Fadwa shima sha tara ta arziki Ya Azeez yake masa, wanda bama shi kaɗai ba kaf dangin su da suka rage na Babura suna matuƙar alfahari da samun Ya Azeez, saboda shi kwata kwata bashi da burin tara wani abun duniya, burinsa kawai shine ya yiwa jama'a hidima ya kuma kyautata musu tamkar yadda mahaifinsa ya dinga taimakawa mutane yana tallafawa rayuwarsu kafin rasuwarsa.
Sannu a hankali abubuwa suka gama daidaita a tsakanin Shatu da Ya Azeez ɗinta, dan ta kai yanzu har Abba ya samu Abbie da kansa yayi masa magana, inda kuma kai tsaye Abbien ya basu dama yace su turo, sosai Abba yayi matuƙar farin ciki.
Inda kuma yana komawa gida ya samu Ya Azeez ɗin ya sanar masa da duk yadda sukayi da mahaifin Shatun.
Sosai shima Ya Azeez ɗin yayi farin ciki matuƙa, dan har sai daya kasa ɓoye farin cikin da yake ciki a gaban Abban, wanda kuma da kansa ya kira Ummansa ya sanar da ita abinda ke faruwa, sannan kuma yace ta gayawa Abba Fadwa jibi zai turo direbansa da mota yazo ya ɗaukesa domin su haɗu da Abban Fahad aje nema mai auren Shatun, saboda yana so cikin lokaci kaɗan ayi komai a gama.
Inda kuma anan ne Umman ta sako masa zancen Fadwa, wanda shi har ga Allah ma tuni ya daɗe da shafe babinta a rayuwarsa, dan tun daya samu Shatu kuma bai tunanin akwai wata mace da zai iya so ko yaji tana burgesa a duniyarsa, balle kuma daya fahimci cewa Shatu na da tsananin kishi a kansa gashi ta tsani ayi mata zancen kishiya ballantana ace ya taɓa aure, ranar ta dinga fushi dashi kenan tana ɓata rai, sai yay ta aikin lallashi da ban baki sannan yake iya shawo kanta.
Shiyasa koda Umma tayi masa zancen yace ta ɗan bashi lokaci zasu yi maganar daga baya, tun daga haka kuwa bai ƙara tada mata zancen ba, itama kuma Umman tun da taga haka sai bata ƙara tunkararsa da maganar ba ta zuba mai ido kawai tana so taga iya gudun ruwansa.
Kwana biyu da maganar kuwa Ya Azeez ya tura direbansa Kaduna yaje ya ɗauko Abban Fadwa, nan suka haɗu gabaki ɗaya dasu Abba da Fahad da wani abokin Abban sukaje gidansu Shatu inda suka samu Abbie da ƙaninsa Baffan su Shatu da yazo daga Yola suka yanke magana inda akayi komai a mutunce da girmama juna Abba ya bada komai da ake buƙata kana aka tsaida rana wata ɗaya kacal, dan a cewar Abban gwara ayi komai a gama cikin lokaci saboda azumi dake gabatowa.
Nan dai suka haɗu suka gama tsara komai cikin mutunta juna, suka yanke shawarar yadda abubuwan zasu kasance.
Kafin daga bisani suna gamawa kuma Abban Fadwa yayi musu sallama dan yace a yau ɗin yake son komawa Kaduna, dan haka yake so ya koma da wuri saboda bayaso dare yayi musu akan hanya.
Daga nan kuwa ko gidan Abban bai koma ba dan ko Ya Azeez ɗin ma ta waya ya kirasa sukayi sallama, kafin ya shiga mota direban Ya Azeez yaja suka ɗauki hanyar komawa Kaduna.
Inda kuma a daren ranar ne bayan Abban ya dawo gida da daddare bayan sallar isha'i iyayen Alhaji Zailani suka zo tambayar auren Fadwa, wanda kuma sai a ranar ne ma Abban yasan da zancen cewa Alhaji Zailanin yana nemanta, saboda duk abubuwan dake faruwa a gidan ko kaɗan Mama bata taɓa gaya masa ba, haka kuma itama kanta Fadwan bata taɓa yi masa maganar ba.
Amma duk da haka Abban bai nuna musu komai ba ya karɓe su hannu bibbiyu suka gama magana, bayan kuma sun bada sadaki da komai da komai ne.
Kuma suka sanarwa da Abba cewa
angon da kansa ya riga da ya tsaida rana sati biyu kacal saboda yace baya so aja wani lokaci mai tsawo dan yana so ana gama biki zai ɗauketa su wuce Saudiya, nan take kuwa Abba yace hakan yayi dai-dai babu wani abu, Allah ya kaimu lokacin lafiya, daga haka kuwa sukayi sallama suka rabu a mutunce.
Abba na shiga gida kuwa ya zubewa Mama kuɗin da iyayen Alhaji Zailanin suka kawo, kana kuma ya sanar da ita lokacin bikin kamar yadda angon ya tsara.
Sosai kuwa Mama da Fadwa sukayi farin ciki, dan Fadwa har ji ta yi kamar sati biyun da aka saka ɗin sunyi mata nisa, dan ita ba ta ƙi ma ace yau ɗin ne aka ɗaura auren ba.
Shi dai Abba kawai kallonsu yake da ido ba tare da yace musu komai ba, na shi kawai ido ne, kuma su ɗin ya saka musu.
Tun washegarin ranar kuwa Fadwa da Mama suka soma shirye shiryen biki kota ko'ina balle da suka ji zancen ana gama biki Fadwa da angon nata zasu wuce Saudiya.
Kan kace me kuwa tuni Mama ta fara yayatawa ƴan unguwarsu cewa Fadwa zata auri shugaban majalisa kuma ana gama biki zasu tafi Saudiya.
Ƙawayen Fadwa kuwa koda sukaji labarin zata auri mai kuɗi sosai suka tayata farin ciki, dan a cewar masu zuciya da hali irin nata sai yanzu ne ta samu dai-dai da ita.
Nan suka hau shirye shiryen biki ba kama hannun yaro, ankon dinner kuwa leshi mai tsada suka fitar na kece raini sannan ga event kala kusan biyar da suka shirya yi.
Tun ana saura sati ɗaya biki kuwa gidansu Fadwa ya soma cika maƙil da mutane ta ɓangaren Mama, amma a ɓangaren Abba babu wanda yazo domin babu wanda ya gayawa, dan ko dangin su dake Babura babu wanda yasan da labarin auren Fadwan a karo na biyu ballantana kuma Umma da kwata kwata ma bata san abinda ke faruwa ba.
Mama kuwa sai kaiwa da kawowa take tana ta fankama tana hura hanci ita a dole ga surukar shugaban majalisa sukutum da guda.
Fadwa kuwa tana jin yadda ƴan uwan Mama ke ta labarin haɗuwar gidanta da Alhaji Zailani ya aiko da mota aka kaisu sukaje suka gani, sai yabawa suke suna faɗar irin gyaran da yayi mata da yadda ya zuba mata abubuwan more rayuwar jin daɗi da hutu, Mama sai saka masa albarka take tana kwararo mai addu'oi, saboda dama yace baya buƙatar komai gashi ya zuba mata komai da ake buƙata har fiye da yadda ake zato.
Sai dai wani abu dake ƙara ba Fadwan tsananin mamaki da takaici tun da aka fara zancen auren nasu sau ɗaya kawai Alhaji Zailanin yazo gurinta suka haɗu dashi, shima kuma ranar wayar hannunta yazo ya karɓa yace zai sake mata sabuwa, kuma tun daga ranar sai bai sake zuwa ba gashi kuma babu wayar da zata kirasa, wayar Mama kuwa ko ta kirasa da ita ma bata shiga.
Sai dai kusan kullum ya aiko direbansa yace yana gaisheta.
Ranar yau ta kama Asabar ranar da ake ɗaurin auren Fadwa, gaba ɗaya gida ya kacame sai hidimar biki ake kota ko'ina a cikin gidan, Mama da ƴan uwanta da wasu daga cikin makwabtan su da a yanzu suke matuƙar ganin girmanta da kimarta, sune suke ta kai kawo a tsakar gidan suna aikace aikace, yayinda su Ilham da Amatullah waɗanda suka sha ankon su na wata atamfa mai kyau suma suke ta nasu kai kawon a cikin gidam.
A ɓangaren uwar gayya Fadwa kuwa tana can cikin ɗakin Mama ita da gogaggun ƙawayenta dukkansu sun sha kwalliya ta kece raini suna ta tasu hidimar.
Ƙarfe 2pm. Dai-dai kuwa aka ɗaura auren a masallacin dake bakin layinsu, inda kuma ana gama ɗaurawa ango yace yana buƙatar a bashi amaryarsa ya tafi da ita, saboda a yau ɗin yake so su kammala shirin tafiyarsu.
Aiko Abba da kansa ya shiga har cikin gidan ya sanarwa da Mama cewa maza Fadwa ta fito mijinta naso zai tafi da ita gidanta da kansa.
Nan ko Mama tai tsalle ta dire tace ba tasan zancen ba, dole yayi haƙuri sai dare kamar yadda ake kai kowacce amarya itama akawo motoci na kece raini akaita.
Abba dai bai sake tanka mata ba yasa kai ya fice daga gidan ya koma kasuwa abinsa, inda a nan gida kuwa Mama itama bata sake bi takan zancen Abban ba suka cigaba da hidimarsu.
Bayan sallar magriba kuwa lokacin gidan ya ƙara cika da mutane maƙil ƴan zuwa kai amarya, inda kuma kowa burinsa shine kawai yaje yaga gidan da za'a kai Fadwa domin ya ƙaras da bada labari.
A lokacin da aka sanar da cewa motar ɗaukar amarya ta iso ne kuwa mutanen suka dinga fita bakin titin unguwar domin samun motar shiga.
Fadwa kuwa tana can tare dasu Hajiya Labiba dasu Hajiya Zalika da Hajiya Lubna da wasu sauran ƙawayensu da Mama da itama ta shirya ta saka hijabi tace dole da ita za'a tafi kai amaryan.
Fitowa sukayi a hankali yayinda hannun Mama ke riƙe dana Fadwa, tafiya suke Mama nata faman washe baki cike da tsantsar farin ciki, jama'ar unguwar na biye dasu da sauran ƴan biki suna ta shewa suna guɗa, Fadwa kuwa sai wata dariyar farin ciki take da nishaɗi tana jin daɗi.
A dai-dai lokacin suka isa bakin titi, nan take kuma kallo ya koma sama Mama ta hau waige waige tana zare ido, da mamaki ta saki hannun Fadwa ta ƙarasa inda wata mota ƙirar 207 ke fake ta tsaya tana tambayar wani dattijo dake tsaye a gurin tace "Malam ina motocin ƴan kai amaryar suke ne...?"
Ta tambaya cike da tsananin mamaki tana kallonsa.
Ɗan kallonta dattijon yayi kafin yace "Ga dai nan motar da amaryar zata shiga nan domin ita kaɗai akace in ɗauko..."
Ya faɗa tare da nuna mata motar da ya jingina da ita ɗin.
A take kallo ya ƙara komawa sama, dan ba Mama ba hatta Fadwa da sauran ƴan biki sai da suka shiga tsananin shock da mamakin kalaman mutumin, ba ma kamar Fadwa da take ganin kamar mafarki take ba gaskiya ba, wayar hannun Hajiya Lubna ta ƙarɓa da sauri ta kunna fitila ta ƙarasa gaban mutumin ta haska fuskarsa, ganin kuma mutumin da Zailani ke aikosa wajenta ne yasa ta sakin wani ƙaramin murmushi lokaci ɗaya tana sauke numfashi, kafin ta juya gurin Mama tana faɗin "Kai Mama ashe fa Baba Salahu ne direban Alhaji shine baki ganesa ba, dama kinsan yace ana gama ɗaura auren ranar zamu wuce Saudiya, ƙila tafiyar dare ce zamuyi ne shiyasa..."
Ta faɗa cikin ƙoƙarin danne tashin hankalin da take jin yana bijiro mata, kafin kuma ta buɗe bayan motar kai tsaye ta shiga ta zauna sannan ta yafito Mama dake tsaye har lokacin jikinta a sanyaye tace "Mama ku shigo kuyi mana rakiya koda zuwa airport ne keda Hajiya Labiba, daga can sai a dawo daku gida..." Ta faɗa tana matsawa Maman ta shigo ta zauna, kana itama ƙawarta Hajiya Labiban ta shiga wanda itama tsantsar mamaki da al'ajabi suka kusa kasheta.
Haka sauran dandazon mutanen suka tsaya suna gani aka ja motar dasu Mama da Fadwa da Hajiya Labiba kaɗai ke ciki aka wuce.
Nan fa unguwa ta ƙara ɗauka Fadwa ta auri hamshaƙin mai kuɗi an tafi Saudiya har dasu Mamanta, wasu nata faɗin dama rabon auren mai arzikin ne ya rabota da auren Ya Azeez, wasu kuma suce Allah yasa dai na ƙwarai ne, wasu kuwa har da ƙari akan abinda basu sani ba.
Mama dai kam gaba ɗaya cikinta ya gama ɗurar ruwa, kwata kwata ta rasa wane irin tunani zata fara yi, ita dai gata a cikin motar ana ta tafiya da ita amma gabaki ɗaya ba tasan inda aka nufa dasu ba.
Hajiya Labiba kuwa kawai miƙa wuya take ta cikin motar tana ƙarewa layukan da suke ta wucewa kallo, wanda kuma tunda take a garin Kaduna bata taɓa sanin akwai irin waɗannan jagwalallun unguwannin ba, wai kuma da sunan mutane ne ke rayuwa a cikinsu.
A haka har suka shigo cikin wata kwaraɓaɓɓiyar tsohuwar unguwa wacce kai da ganinta kaga tantagaryar unguwar talakawa futuk, wanda kuma duk a zaton Fadwa dasu Hajiya Labiban wucewa za'ayi ba tsayawa ba, basu ankara ba kuwa suka ga yaci burki a gaban wani ruɓaɓɓen gida mai gajeruwar katanga da kwata faca faca kota ko'ina.
*Ina matuƙar godiya masoyana🙌*
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:20 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
3️⃣5️⃣
Wani irin kallon yagalgalallen gidan suke cikin tsananin mamaki da al'ajabi, kafin Hajiya Labiba tayi ƙarfin halin buɗe baki cikin tarin mamaki tace "Kai Malam gidan Alhaji Muhammad Al'ameen Zailani fa zaka kaimu shugaban majalisa, ya kuma ka kawo mu nan...?"
Ta faɗa lokaci ɗaya tare da buɗe ƙofar motar ta fito tana ƙara ƙarewa gidan kallo.
Buɗe motar yayi ya fito shima yana faɗin "Nan ne gidan nasa ai Hajiya..."
"Nan ne gidan fa kace...?" Hajiya Labiba ta tambayesa cikin tsananin mamaki da al'ajabi tana kallonsa.
Daga cikin motar kuwa Mama da Fadwa gaba ɗayansu kallon kallo suka hau yiwa juna, kafin daga bisani Mama tayi ƙarfin halin buɗe ƙofar motar ta fito itama cikin sanyin jiki tana faɗin "Wai ina ne gidan ne daka zo ka wani tsunburemu anan sai kace wasu marasa galihu, kodai motar ce ta lalace ne...? Toh ka kira Alhajin mana ya turo da wata motar kar mu ɓata musu lokaci har jirgin ya tashi bamu isa airport ɗin akan lokaci ba..."
Mama ta faɗa tana fitowa daga motar.
"Munzo ai nan ne gidan Baaba..." Mutumin ya faɗa kai tsaye yana kallonta.
Wani irin zaro ido Mama tayi tare da dafe ƙirjinta, kafin tace "Nan ne gidan wa ɗin..? Wannan kufan ne gidan Alhaji Zailanin kome kake nufi ne..? Ban gane maganarka kai tsaye ba yi min gwari gwari ta yadda zan gane..."
Ta faɗa cikin tsananin tashin hankali tana kallonsa.
Ganin yadda Mama tayi ne kuma yasa Fadwa buɗe motar itama ta fito tana kallonsu, wanda kuma ganin Fadwan ne yasa Mama saurin matsawa gabanta ta riƙo hannuwanta cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa tana faɗin "Ke Fadwa dama wai wannan shine gidan da Alhaji Zailanin yace zai ajiyeki, nan ne kuma gidan da ƴan uwana sukaje suka gani har suka koma suna yabawa...?"
Numfashin Fadwa ne ya soma rawa yayinda kuma zuciyarta ta hau dokawa tana tsalle tamkar zata faso ƙirjinta ta fito waje saboda tsantsar tashin hankali da ɗimuwa.
Sake girgizatan da Mama ne tayi tana ƙara tambayarta yasa ta dawo daga duniyar tunanin data lula.
A hankali ta girgiza kai kafin tace "A'a Mama ba wannan bane, wancan a Millonion City yake ya taɓa kaini na gani..."
Ta faɗa tare da juyawa tana kallon mutumin daya kawo sun kafin tace "Wai Baba Salahu ya haka ne, ya zaka kawo mu nan ka zube sai kace wasu dabbobi, ina shi Alhajin yake...?
Wanda ta kira da Baba Salahu yace "Hajiya ai nan ne gidan naki, kuma Alhaji yana nan zuwa ya tsaya ne ya ƙarasa sallamar baƙinsa, amma yace ki shiga ciki ki jirasa yanzun nan zai ƙaraso..."
Jada baya da sauri Fadwa tayi tana girgiza kai kafin tace "Wannan wace irin magana ce kake yi haka Baba Salahu, nan ne fa gidana kace shi wancan gidan kuma daya taɓa kaini na gani fa na waye shi ina yake...?" Ta faɗa cike da tashin hankali tana kallonsa.
Ɗan ɗaga kafaɗarsa Baba Salahun yayi kafin yace "Ki dai shiga daga ciki Hajiya, idan yazo da kansa zaiyi miki bayanin komai..."
Fadwa taja da baya da sauri tana riƙe da hannun Mama tace "A'a ba dai wannan gidan zan shiga ba Baba Salahu, ka dai sake kiransa kaji, amma ba dai nan gidan ba..."
Yace "Hajiya nan ne gidan fa..."
Mama ta watsa masa wani mugun kallo tana faɗin "A'a kaiko bawan Allah taya zakace mutum mai tarin arziki kamar Alhaji Zailani zai ajiye amaryarsa a irin wannan matsiyacin gidan, ka dai sake kiransa ɗin kaji, amma wannan zancen naka yayi kama da ƙanzon kurege..." Ta faɗa cikin ƙara tabbatar da zancen nata, domin ita a ganinta bazai taɓa yiwuwa ace mutum kamar Alhaji Zailani mai tarin dukiya da manyan motoci ya aje matarsa a wannan ruɓaɓɓen gidan ba, mutumin da yake shugabantar majalisa sukutum da guda taya za'a ce ma yasan irin wannan tsinanniyar unguwar balle ace wannan gidansa ne.
Ita dai Hajiya Labiba tana tsaye daga gefe tana ta kallonsu, amma gaba ɗaya jikinta ya gama yin sanyi da lamarin.
Fadwa kuwa wani irin tsantsar tashin hankali ta tsinci kanta a ciki, ita fa sai yanzu ne ma take son yiwa kanta wasu tarin tambayoyi da tun a baya ta gaza yiwa kanta su sakamakon rufewar da idanuwanta sukayi a lokacin.
Sai data gama kallon ƙazantar bolar da kwatamin dake ƙofar gidan, sannan ta juya cikin sanyin jiki tana kallon Mama da faɗar irin tsananin tashin hankalin da take ciki itama ɓata baki ne, domin abun yayi matuƙar gigita tunaninta har yana neman fitar da ita daga hayyacinta.
"Mama ya zanyi ne..ta ina zan fara fuskantar wannan ƙasƙantacciyar rayuwar...? Nifa gaba ɗaya kaina ya kulle..."
Fadwa ta faɗa cikin tsananin tashin hankali tana duban Maman da itama ta zuba mata ido tana kallonta, sai a lokacin ne kuma Hajiya Labiba ta ƙaraso garesu ta dafa Fadwa da zuwa lokacin take ji tamkar ta ɗora hannu bibbiyu akai ta fashe da ihu tana dukan kanta saboda tsantsar damuwa da tashin hankalin da take ciki.
Juyowa Fadwan tayi ta kalleta kafin tace "Dan Allah ki tasheni daga wannan mummunan mafarkin da nake yi kice dani ƙarya ne ba gaskiya bane abinda Baba Salahu yake faɗa, dan Allah kice