Showing 63001 words to 66000 words out of 113443 words
masa kai tare kuma da sunkuyar da kansa ƙasa yana faɗin "Insha Allahu Abba..."
Sake kallonsa Abban yayi da kyau yana ƙara nazarinsa, kana kuma cikin tausasa murya yace "Akwai wasu sabbin shaguna na guda huɗu dake kasuwar Kurmi, sannan akwai guda biyu kuma dake kasuwar Kwari, ka haɗa duka na mallaka maka su halak malak sun zama mallakinka, kuma koda bayan raina zan faɗa kuma zan barshi a rubuce babu su a cikin lissafin dukiyata, wannan naka ne nine na baka su kyauta, dama kuma na gama ordern komai da za'a buƙata a shagunan, kuma insha Allahu ƙarshen watan nan kayan da nayi ordern zasu iso Nigeria dan haka ka zauna cikin shiri, sannan zan saka a ƙara gyara muku gidan motocina dake cikin gari, dan inaso zan ƙara muku jari kai da Fahad ku riƙa shigo da motocin kwatano da China, kamar yadda muka din gayi da mahaifinka lokacin da yana raye...."
A razane Ya Azeez ya ɗago kai yana kallonsa, kafin ya juya da sauri ya kalli Fahad dake ta washe baki cike da farin ciki yana faɗin "Aboki kaji abinda Abba yake faɗa kuwa...?" Ya faɗa cike da matsanancin mamaki da al'ajabi yana kallonsa.
Cike da tsananin farin ciki kuwa Fahad yace "Naji mana aboki ina matuƙar tayaka murna..." Ya faɗa fuskarsa ɗauke da tsananin farin ciki da jin daɗi.
Ya Azeez kuwa gaba ɗaya rasa abun cewa yayi saboda tsabar farin ciki, wai yau shine ake maganar yi masa kyautar shaguna ɗai ɗai ɗai har guda shida sukutum a cikin garin Kano, kuma hakan duk bai isa ba har sai da aka ƙara masa da jarin motoci da gidan motocin kansa ɗungurungum duk dan ya ƙara inganta rayuwarsa.
Kawai sai ya samu kansa da jin saukar wasu zafafan hawaye masu matuƙar ɗumi daga cikin idanunsa suna kwaranyowa saman kyakkyawar fuskarsa, da sauri Abba ya kallesa yana girgiza masa kai kafin yace "Da kasan irin tarin abun alkhairin da mahaifinka yayi min a rayuwa AbdulAzeez da bakayi mamakin duk abinda zanyi maka ko in mallaka maka ba, saboda duk wani arziki da zan samu yanzu ko in samesa a nan gaba to mahaifinka shine sanadi..domin shine ya koya min harkar kasuwanci sannan kuma ya nuna min yadda zan juya biyar ta zama goma, ashirin ta zama hamsin, a haka har na mallaki manyan shaguna na tara abun duniya fiye da zato da tunanin mai tunani.
Amma duk da hakan dai-dai da rana ɗaya bai taɓa gwada min baƙin ciki ko hassada ba, haka zalika bai taɓa min gori ko ya nemi wani abu a gurina ba.
To ni kuwa taya zan iya manta halaccin wannan bawan Allah a gareni..? Taya zan iya mantawa da iyalinsa har in gaza tallafawa rayuwarsu alhalin kuma suna neman taimakona...?"
Wani irin miƙewa Ya Azeez yayi da sauri ya faɗa jikin Abba ya rungumesa ƙam ƙam tare da fashewa da wani matsanancin kuka lokaci ɗaya yana faɗin "Wallahi nama rasa bakin magana Abba, bansan da wane irin baki zan iya gode tarin alkhairanka a garemu nida mahaifiyata da ƙanwata ba, kai mutumin kirki ne Abba..kai mutumin kirki ne..." Yake faɗa yana ƙara fashewa da kuka.
A hankali Abba yake bubbuga bayansa alamar lallashi, kafin kuma ya ɗagosa daga jikinsa yana share masa hawayen fuskarsa cikin tsananin nuna ƙauna da kulawa yake faɗin "Ya isa..ya isa ka daina kukan haka nan dan Allah, nidai fatana shine Allah ya tayaka ruƙo ya kuma baka damar kula da al'amuran kasuwancinka yadda ya kamata..."
A hankali dukkansu suka amsa da "Ameen ya Allah Abba..." Suka faɗa a tare suna murmushi, kafin Fahad ya ƙara matsowa gabansu yana faɗin "Abba muna godiya sosai Allah ya saka da mafificin alkhairi ya ƙara girma da nisan kwana..."
A hankali Abba dake murmushi irin nasu na manya ya masa da "Ameen ya Rabbi..sai a kula sosai, Allah yayi muku albarka yasa kuma a gama lafiya..."
"Ameen Ameen..." Suka ce kana daga haka kuma suka ɗora da hirar kasuwanci.
Sun daɗe dashi a falon suna tattaunawa, dan sai gurin ƙarfe 11:45pm. Sannan suka bar ɓangaren Abban, sukayi mai sai da safe suka wuce ɗakin Fahad, koda suka shiga basu wani tsaya komai ba sakamakon dukkansu dama kowanne jallabiyar da yayi sallah ce a jikinsa, dan haka kawai suka haye gado kowa ya nemi gurin bacci suka kwanta.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:19 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
2️⃣5️⃣
Washegari 9am. Dai-dai gabaki ɗayansu zaune suke akan makeken dinning table ɗin gidan suna breakfast, Abbie, Ummi, Shatu, sai auta Zahra.
A hankali kowa ke cin abincin dake gabansa cike da natsuwa, amma ban da Shatu wacce tunda ta zauna a gurin babu abinda ta iya ɗauka ta kai bakinta, gaba ɗaya ta rasa abinda ke damunta tunda ta tashi ta rasa gane kanta, sai faman jujjuya cokalin dake hannunta kawai take tana ɗan satar kallon Zahra dake zaune a kusa da Ummi tana cin abincinta hankali kwance babu abinda ya dameta.
******
A ɓangaren su Ya Azeez kuma dai-dai lokacin fitowarsu kenan daga ɗakin Fahad, cikin shirinsu tsaf, inda suke sanye da wata dakakkiyar farar shaddar gezner mai maiƙo da yarari a jikinsu ɗinkin samarin zamani masu ji da kansu.
Kansu sanye da hular zanna bukar mai kalar brown irin zaren aikin dake jikin shaddar, sai agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannuwansu shima na kamfanin Rolex ne, ƙafafuwansu kuma duka sanye suke da rufaffen takalmin fata.
Sai dai a kallon farko idan kayi musu zaka fahimci tsantsar kyau na musamman da shigar tafi yiwa Ya Azeez sosai, gashi dai komai anko suka saka domin ɗinkin da Fahad ɗin ne yayi musu wanda zasu saka ranar taron bikin, amma idan ka kallesu a lokaci guda zaka hango tsantsar zati da haibarsa uwa uba kyau da nasabarsa ga kuma wani kwarjini na musamman, fuskarsa na ta fitar da wani annurin farin ciki wanda yake jin yana taso masa tun daga can ƙasan zuciyarsa a hankali kuma yana mamaye illahirin ƙirjinsa.
A hankali suka ƙarasa saukowa cikin falon inda suka iske Abba da Mami da Ibrahim zaune a dinning suna karyawa, cikin natsuwa suka ƙarasa suma kowanne yaja kujera suka zazzauna.
Inda cikin tsananin kulawa Mami dake kallonsu fuskarta ɗauke da murmushi tace "Masha Allah tagwayen Abba da Mami, kunsha kyau abinku kun fito sak angwaye sai zuba ƙamshi kuke..."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙarewa shigar tasu kallo kafin ta juya ta kalli Abba dake riƙe da kofin kunun tsamiya a hannunsa yana sha tace "Alhaji baka ga angwaye bane..banji kace komai ba...?" Ta faɗa still fuskarta ɗauke da wani ƙayataccen murmushi tana kallonsa.
Murmushi Abban yayi shima kafin ya ajiye kofin dake hannunsa yana faɗin "Ai ni tun kafin ma su fito naji gabaki ɗaya falon ya gauraye da ƙamshi mai daɗi, baki ga har wani haske da walwali ko'ina ya ƙara ɗauka ba sai wani shaining muke muma mun samu tabarrakin sabbin angwaye...?" Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya cike da zolaya yana murmushi.
Nan ma dukkansu murmushin suka sake yi kafin kuma Ibrahim ya kallesu a tare yana faɗin "Gaskiya kunyi kyau sosai my brothers, idan Aunty's ɗina suka ganku yau na tabbata sai sun ƙara ruɗewa sosai a kanku..."
Dariya duk sukayi yayinda Abba yace "Ina zakuje ne haka da akasha irin wannan haɗaɗɗen wankan...?"
Ya faɗa cike da yanayin barkwancin daya saba musu yana kallonsu.
Ɗan juyawa sukayi suka kalli juna kafin daga bisani Ya Azeez yace "Gurin amaryarmu zamuje Abba amma bazamu daɗe ba insha Allahu yanzu zamu dawo..."
Kai kawai Abban ya jinjina ba tare kuma da ya sake cewa komai ba, ya ci gaba da shan kununsa, kana suma suka soma cin soyayyen plantain da dankalin da Mami ta saka musu kana kuma suna haɗawa da tea.
Bayan sun kammala ɗin ne Ibrahim ya miƙe ya wuce ɗakinsa domin yayi shirin tafiya makaranta, saboda yau yana da lecture ƙarfe 11am.
Inda su kuma gaba ɗayansu suka miƙe suka koma cikin falo yayinda Abba da Mami kuma suka wuce sama inda ɗakin Abban yake.
Suna nan zaune sai ga Abban ya sauko yayinda Mamin ke biye dashi a baya tana riƙe da brief case ɗinsa a hannunta, da sauri duk suka miƙe yayinda Ya Azeez ya matsa kusa da ita ya karɓi jakar hannunta, kana suka juya atare suka fice daga falon.
Suna tsaye a farfajiyar gidan Abba ya fito ya samesu, suna ganinsa da sauri suka buɗe masa bayan motarsa ya shiga ya zauna, yayinda direbansa kuma ya taso da sauri yazo ya shiga gaban motar, ya kunna suna ɗaga masa hannu yaja, maigadi ya wangale musu gate suka fice daga gidan.
Sai da suka ga fitarsu daga gidan kana suma suka ƙarasa inda motar Fahad ke fake daga gefe suka shisshiga inda Ya Azeez yaja motar a hankali suka fice suma daga cikin gidan.
*******
Acan ɓangaren Shatu kuwa gaba ɗaya ta rasa meke mata daɗi, haka kawai take jin kanta cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, a haka har kowa ya gama breakfast ɗinsa duk suka miƙe, yayinda Abba ya wuce falonsa, Ummi da Zahra kuma suka wuce kichin, aka barta ita kaɗai ƙwal a dinning area ɗin, tayi zaune zuru ta tasa abinci a gaba, amma ta kasa kai koda loma ɗaya ne bakinta.
Ganin duk sun tashi sun barta ita kaɗai ne yasa haka nan ta daure ta ɗan tsakuri dankali da kwai kaɗan taci, tasha ruwa kana ta miƙe ta tattare kayan ta kai kichin inda ta iske Ummi na ƙoƙarin ɗora girkin rana yayinda Zahra kuma ke gefe tana wanke wanken kwanukan da suka gama cin abinci suna taɓa hira sama sama.
A hankali ta ƙarasa shiga cikin kichin ɗin ta ajiye filet da kofin dake hannunta, kana ta matsa gurin Ummin bayan ta yi mata sannu, ta fara ƙoƙarin tayata aikin da take yi.
Ganin yanayinta ne yasa Ummin ta ɗan kalleta cikin nazari, kafin tace "Wai me yake damunki ne yau naga duk kinyi wani iri dake kamar mara lafiya, ko akwai abinda yake damunki ne dan tun ɗazu nake lura da yanayin ki, kwata kwata yau bakya cikin walwala, ko akwai inda ke miki ciwo ne...?"
Jin abinda Ummin ta faɗa ne yasa tai rau rau da idanu kamar zata yi kuka kafin tace "Wallahi nima haka kawai nake jina wani iri Ummi, kamar bani da lafiya amma kuma babu inda ke min ciwo, daga ƙirjina ne dai kawai nake jin wani irin nauyi mara daɗi kamar wani abu zai sameni..."
Cikin sauri Zahra ta bar abinda take yi ta juyo lokaci ɗaya tana kallonsu, kafin ta ɗan saki murmushi tace "Toh Allah yasa dai alkhairi ne Aunty Shatu, kuma ina fatan idan ma alkhairin ne Allah yasa haɗuwarki ne da tsantsareren saurayi wanda zai kasance mijinki abin alfaharinki a nan gaba, dan naga ko a novel ɗin hausa irin wannan yanayin da kikace kina ji, ake cewa anaji idan za'a haɗu da haɗaɗɗen saurayi mai kyau na nunawa a cikin taro ko Ummi...?" Ta faɗa da dukkan gaskiyata tana kallon Ummi data saki baki galala tana kallonta, kafin ta juya ta kalli Shatu data wani haɗe rai tana watsa mata harara tace "A'a a'a ni kam babu ruwana ban taɓa karanta littafin hausa na ci karo da hakan ba...." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana dariya.
Zahra itama dariyar tayi tana faɗin "Allah kuwa Ummi haka ne, kinsan ance idan abun alkhairi zai sameka kana ji a jikinka, haka idan sharri nema, shiyasa akoda yaushe akeso ka dinga yiwa kanka addu'ar Allah ya haɗaka da dukkan alkhairin duniya da lahira..."
Gyaɗa kai Ummin tayi cike da gamsuwa tana cewa "Ƙwarai kuwa uwata, haka maganarki take, to Allah ya haɗamu da dukkan alkhairinsa duniya da lahira..."
Da Ameen duk suka amsa mata, kana Shatu ta ɗauki tumatur ɗin da Ummin ta fito dashi daga cikin fridge ta matsa gaban sink ta kunna fanfo ta fara wankewa a hankali, yayinda kuma a lokaci guda maganganun Zahra suke ta kai kawo a zuciyarta.
*********
A dai-dai wannan lokacin kuma Ya Azeez ne da Fahad zaune a cikin wani ƙayataccen falo na gani a bada labari, dake cikin wani haɗaɗɗen gida mai rai da lafiya, gabansu kuwa wani ɗan madaidaicin ƙaramin teburi ne mai kyau da aka cikasa da abubuwan ciye ciye da juices masu sanyi kala kala.
A hankali wata kyakkyawar budurwa da bazata wuce shekaru talati ba ta shigo falon yayinda a bayanta kuma wata matashiyar budurwa ce ke biye da ita ɗauke da wani babban farati a hannunta, wanda da ganinsu kasan cewa ƴaƴan manyan mutane ne, cikin natsuwa dukkansu suka ƙaraso cikin falon, inda direct babbar ta nufi gurin Fahad dake hakimce akan kujera ya zubo mata ido, cikin wani irin takun salo da iyayi irin na sangartattun ƴaƴan gata ta isa gabansa tana faɗin "Your welcome love, barkanku da zuwa..." Ta faɗa tare da zama a kusa dashi lokaci ɗaya tana sakin wani ƙayataccen murmushi.
Basma Jada kenan kyakkyawar budurwa kuma ƴar gata a gurin iyayenta.
Murmushin jin daɗi Fahad yayi tare da yi mata wani sassanyan kallo yace "Nagode amaryata..." Ya faɗa cikin nuna tsananin jin daɗi yana murmushi, kafin kuma ya juya ɓarayin da Ya Azeez ke zaune yana latsa wayarsa yace "Aboki ga fa amarya tamu ta iso..." Sai a lokacin ne Ya Azeez ɗin ya ɗago kai ya kallesu kafin kuma ya juya lokaci ɗaya ya harari ɗayar budurwar da tun da suka shigo falon ta tsura masa idanu ƙirr tana ta ƙare masa tun daga saman kansa har zuwa ƙasan ƙafarsa kamar zata cinyesa ɗanye, watsa mata harara yayi a fakaice kafin ya ɗan ja tsaki ƙasa ƙasa yana faɗin "Nifa na tsani kallon ƙurulla a rayuwata, haba mutum sai kace maye..." Ya faɗa cike da tsantsar takaici yana harararta.
Karaf kuwa sai a kunnenta, aiko take taji wata masifaffiyar kunya gaba ɗaya ta dabaibayeta, da sauri ta miƙe tsaye bayan ta ajiye farantin data shigo dashi, ta juya da sauri cikin hanzari ta fice, kamar zata kifa.
Wata muguwar harara ya rakata da ita har ta ƙarasa ficewa daga falon, kafin ya saki tsaki, kana ya juyo lokaci ɗaya yana kallon Fahad da amaryarsa da gaba ɗaya suka zubo masa idanu suna kallonsa, ɗan taɓe bakinsa yayi shima ya kallesu kana kuma ya saki ƙaramin murmushi yana faɗin "Barka da fitowa amaryar mu, ya taro kuma..." Ya faɗa tare da watsawa Fahad daya kasa ɗauke idanunsa daga kanta harara yace "Toh maye ai sai ka barta haka kuma da wannan mayataccen kallon naka, ka barta ta huta..."
Dariya Fahad ɗin yayi yana faɗin "Ina ruwanka sa'idawa idan ma cinyeta nayi ai tawa ce ko Baby...?"
Gyaɗa mai kai tayi a hankali tana murmushi, kafin kuma cikin nuna tsantsar wayewarta tace "Daga gani dai ba sai na tambaya ba wannan shine, amininka Azeez Arabi da kake ta bani labari na Kaduna ko...?"
Da sauri Fahad ya gyaɗa mata kai yana faɗin "Shine kuwa Baby kin canka dai-dai..."
Murmushi kawai tayi ba tare data sake cewa komai ba, suna cikin haka ne kuma wayar Ya Azeez ɗin ta ɗauki ƙara, da sauri ya zarota daga cikin aljihun wandonsa ya duba, ganin da yayi Ummansa ke kira ne yasa ya miƙe da sauri ya nufi hanyar waje tare da barin kiran nata ba tare daya ɗauka ba, har ya katse, sannan ya sake bin bayan kiran.
Sun daɗe sosai a gidan dan sai gurin ƙarfe 11am. Sannan suka fito bayan sun shiga cikin gidan sun ƙara gaishe da iyayenta da sauran baƙinsu da basu gama tafiya ba, kana suka fito ta rakosu har gurin motarsu kafin suka yi mata sallama suka wuce.
Tafe suke a hankali suna hirar abinda ya shafesu, inda anan ne Ya Azeez ke tambayar Fahad dalilinsa na matsawa a ɗaura masa aure ba tare da biki ba, kamar wanda ya auri bazawara alhalin kuma shi da kansa ya gaya masa cewa Basman budurwa ce ba bazawara ba.
Idanu Fahad ɗin ya ɗan runtse a hankali kafin ya juyo gaba ɗaya yana fuskantarsa yace "Wallahi babu yadda na iya ne Aboki, ban san yadda zanyi da yarinyar nan ba. Inda dan ta nine wallahi da tun jiya a gidana zata kwana amma bani da yadda zanyi ne kawai saboda anfi ƙarfina, kuma tun farko da aka buƙaci hakan a gurina ban yi wani tunani ba na amince, shiyasa dole na cika alkawarin dana ɗauka, amma ka sani wallahi bada son raina bane hakan ta kasance, saboda ina matuƙar son Basma kawai dai babu yadda na iya ne..."
"Ban gane ba, kamar ya babu yadda ka iya...?"
Ya Azeez ya tambayesa cike da rashin fahimtar inda zancen nasa ya dosa.
Fahad Yace "Wallahi nida kaina bansan haka abun zai zama ba aboki da tun farko ban amince da tsarinsu ba, amma gaba ɗaya nine da laifi, kuma ban san haka abun zai zo ya dameni ba daga baya da ko kwatanta yi ma banyi ba..."
Fahad ɗin ya faɗa cikin tsananin damuwa da tashin hankali, dan gaba ɗaya sai yanzu ne yake daya sanin abinda yayi.
Cikin rashin fahimta Ya Azeez ya sake cewa "Kai nifa duk ban gane nufinka ba har yanzu, ka fito fili kayi min bayanin abinda ke faruwa dalla dalla, dan in fi ganewa sosai da sosai..."
Fahad kuwa da yaji gaba ɗaya har ya fara muzanta a gaban abokin nasa yace "Wallahi nine nayi sakaci aboki har hakan ta faru, da tun farko da iyayenta suka ce sai ta gama karatu sannan zasu aurar da ita inda nayi haƙuri da duk hakan bata faru ba, amma yanzu dana nace ai kaga gashi nan ina ji ina gani za'a mayar dani sauna kullum inta jerangiya a titi ina gararanban zuwa wajenta kuma wai da sunan tana a matsayin matata kuma amarya amma tana gidansu, har sai ta kammala karatunta sannan za'ayi biki ta tare a gidana, wannan wace irin lukutar masifa ce...?"
Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya cike da damuwa yana kallon Ya Azeez daya wani taka burki da sauri ya gangara gefen titi ya tsaya kawai, yana kallonsa cike da tsantsar takaici yana ji kamar ya rufesa da masifaffen duka saboda