Showing 102001 words to 105000 words out of 113443 words

Chapter 35 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7581

had'u lokacin da za'aje dinner, Ya Azeez kusan zaucewa yay sakamakon kyaun da yaga Shatu tayi masa sosai, idanu kawai ya zuba mata acikin motar, amma baiyi gigin ko kama ɗan yatsarta ba, saboda yasan bazai taɓa iya jure hakan ba.
Shatu ma a nata ɓangaren gani tayi Habibyn nata ya canza mata sosai ya ƙara mata wani masifar kyau, lokaci ɗaya ya sake tafiya da imaninta, gefe guda kuwa sai take ganin tamkar yafi ƙarfinta, kawai ta tsinci dami akala ne, amma ba sa'anta bane.
Bayan anyi dinner lafiya an tashi, Ya Azeez kasa zaune da tsaye yayi sabida yadda haɗuwar Eishatunsa da ƙamshinta suka gigita masa tunani, ai kuwa ranan ya addabeta da kira dan kusan raba dare sukayi suna hira.
Haka ya kwana a falo kasancewar Abban Fadwa ya iso shima tunda rana, wanda kuma a nan ɓangaran Ya Azeez ɗin ya sauka shiyasa ya keɓe kansa a wani guri daban yana ta waya da Eishatunsa.


Washegari kuwa misalin 11am.
Dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren ABDULAZEEZ NASEER ABDULLAH ARABI da amaryarsa AISHA BELLO ƊAN ƘWARAI akan sadaki mafi daraja.
Sosai ɗaurin auren ya samu halartar manyan mutane, kama daga kan ƴan kasuwa, ƴan siyasa, manyan Malamai da sauran masu faɗa aji dake garin Kanon duk halarci taron ɗaurin auren.


Faɗar irin tsananin farin cikin da Abban Fadwa yake ciki kuwa a wannan lokacin ɓata baki ne.
Sai faman washe baki yake yana ta gaggaisawa da mutane, ga manyan manyan ƴan kasuwa kota ko'ina, har da ma waɗanda bai taɓa tunanin zai gansu ido da ido ba a wannan ranar duk sai da ya gansu.
Inda kuma ana gama ɗaurin auren aka tafi walimar cin abinci wani katafaren babban hotel aka gabatar da liyafar, wanda sai abinda ranka yake so shi zaka ci.
Kusan kuma duk wanda yake jigo a gurin amarya da angon sai daya halarci liyafar.
Zahra kuwa ba zama sai kai da kawowa take, ga tawagar ƙawayenta itama data gayyato sai hidima take dasu.
Farin ciki kuwa a fuskar Ya Azeez kasa ɓoyuwa yayi, sai faman doka murmushi yake zuciyarsa tai fari tas tass tamkar bai taɓa shiga wata damuwa ko tashin hankali ba a rayuwarsa.


Haka dai akayi yinin biki na kece raini, Masha Allah anci ansha biki yayi a duk yadda akeson ganin bikin ƴaƴan gata, biki yayi armashi sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya.


Wanda kuma anan gidansu Shatun bayan an ɗaura aure, da yamma Ummi tai nata bikin tare da ƙawayenta, sai kuma amarya da aka fito da ita filin walimar inda aka ɗauko wata shahararriyar Malama da aka ɗauko tun daga garin Bauchi tana gabatar da wa'azi akan zaman takewar aure.


A wannan lokacin kuwa babu wanda zai yiwa Shatu kallo ɗaya ya iya ɗauke idonsa akanta, saboda tsananin kyawun da tayi.
Farin lashi ne tass a jikinta mai zanen golding, da alkyabba golding colour mai kyau da ɗaukar ido.
Ana cikin wa'azin ne kuma Umma ta shigo gurin tare dasu Mami da Imaan da wasu daga cikin danginsu Ya Azeez ɗin na Babura.
Ummi da kanta ta miƙe ta tarbosu ta basu gurin zama na musamman a inda take zaune tare da tawagarta.
Sosai Umma ta dinga jin wani irin girma da tsananin daɗi da farin ciki yana mamaye zuciyarta, tana ta kallon Shatu wacce a lokaci guda taji ta shiga ranta, wanda kuma a gefen Shatun itama hakan ce ta kasance, dan tana ganin Umman taji gabaki ɗaya matar ta gama kwanta mata arai.
Saboda daga ganinta tasan bata da matsala.


Sai wajen ƙarfe 5pm. Aka tashi bayan kuma an rufe taron da addu'a ne aka shiga rabon takeaways, masu cike da kayan daɗi, sai kuma wata jaka mai kyau dake ɗauke da hotunan amarya da ango da aka zuba abubuwa kala kala a ciki.


Koda aka tashi daga gurin walimar kuwa sai data sake wani sabon wankan sannan aka tsantsara mata kwalliya, sosai tayi masifar kyau sai haskawa take, gashi ta sha jan lalle ɗau daya zanu ya ƙara fito da kyakkyawar farar fatarta tamkar domin ita kaɗai aka ƙerosa.


Sai da aka gama yi mata hotuna da iyayenta daƴan uwanta kafin nan aka shiga da ita ɓangaren Abbien ta, Ummi tayi mata faɗa sosai kana shima Abbie ya ɗora mata da nasa.
Koda suka fito daga ɓangaren Abbien kuwa kwance tai akan cinyar Ummi tana ta hawaye, sai a lokacin ta fara jin wani tsananin kewar Ummin da Zahra, wanda kuma tunda aka fara bikin bata yi tunanin zataji tana missing ɗinsu irin haka ba.
Bama kamar Zahra da ƙawarta Husna Baita, da kuma Umminta da Abbien ta, domin duk nasihar da Ummin ke mata na tayi biyayya wa mijinta ne, ta kuma bishi sau da ƙafa.
Daga ƙarshe dai Ummi ta ƙarashe da yi mata bankwana itama tana nata hawaye.




Misalin ƙarfe 6:30pm.
Bayan an idar da sallar magriba Abban Fadwa da Abban Fahad da Abbie, su suka ɗauki Shatu a sabuwar motarta da Abbien ta ya bata ba tare da ɗan rakiya ko ɗaya ba.
Wanda kuma daman tuni Abban Fahad yace Ya Azeez da Fahad ɗin suje can sabon gidan Ya Azeez ɗin da ya ƙera a unguwar.
Tarauni G.R.A su jirasu.
Ƙerarren gini ne irin na zamani wanda yaji ababen more rayuwar duk wani jin daɗin duniya, babu ce kawai ba'a saka ba acikin gidan.
Bayan sun kaita ne sukai musu nasiha mai ratsa jiki da addu'ar zama lafiya, kana suka miƙe sukayi musu sallama suka tafi.
Fahad shima yayi musu nasiha mai ratsa jiki da zuciya sosai kana daga bisani kuma yaja Ya Azeez ɗin suka fita inda aka bar Shatu da Basma matar Fahad ɗin da ƙawarsu Husna, nan suka tashi suma suka shisshiga ko'ina a cikin gidan suka zazzagaya suna ta yaba kyawu da tsaruwarsa.
A hankali Shatu ke biye dasu suna ƙara ƙarewa gidan kallo, yayinda su kuma suke ta ƙara kutsawa ko'ina suna kuma ƙara yaba tsantsar haɗuwa da tsaruwar da gidan yayi.
Dai-dai sun iso wani gefe daga tsakiyar gidan ne kuma idanunta suka sauka akan wani madaidaicin swimming pool mai kyau wanda aka ƙawatasa da wani irin nau'in ruwa mai kalar blue mai kyau da ban sha'awa, sosai gurin yayi mata mugun kyau.
Daga can gefen swimming pool ɗin kuwa wasu kyawawan furanni ne masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, wanda aka kewaye gefe da gefensu da wani kalar wuta mai fidda kala kalan haske mai kyau da burgewa.
Ita kam bata ma san dame zata iya tsara haɗuwa da tsaruwar da kuma tsantsar kyawun gidan ba.
Haka suka gama zagaye ko'ina a cikin gidan, kana suka dawo falon da shima ya gaji da tsaruwa ya amsa sunansa falo, wanda aka narka uban dukiya mai tarin yawa a cikinsa, suka zauna suna ƙara yabawa tsantsar ƙoƙarin da Ya Azeez ɗin yayi.


Su Ya Azeez da Fahad kuwa basu dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i suka shigo da manyan ledoji masu ɗauke da gasassun kaji masu zafi sai su fresh milk masu sanyi da sauransu.
Nan Husna da Basma suka ce bazasu bar amarya ba sai anyi siyan baki dole Fahad da Ya Azeez suka siya baki, inda da ƙyar suka yarda suka karɓi dubu ɗari da hamsin, wai tayi musu kaɗan.


Daga ƙarshe dai Fahad kama hannun matarsa yayi suka fita, Husna ta bisu itama domin su sauketa a gidansu dan bada motarta tazo, bayan duk sun fice ne aka bar Ya Azeez kawai da Eishatunsa a cikin gidan.


A hankali ya ƙara matsawa kusa da ita sosai kana ya kai hannu cikin natsuwa ya ɗaga mayafinta, hawaye yaga suna sakko mata domin ji tai gaba ɗaya duk wata murna da farin ciki da take tuni ya kau a zuciyarta, saboda sai yanzu ne ta gane cewa tabbas ta rabu da kowa nata ta koma sabuwar rayuwa, idanunsa ya tsura mata yana ta kallon kyakkyawar fuskarta da ta sha kwalliya, hawaye sai zubo mata suke babu ƙaƙƙautawa, gani yayi ayau ɗin tafi masa kyau fiye da kullum da ko yaushe ma, domin har wani annuri da haiba yaga take saboda tsabar tsananin kyaun da tayi.


"Masha Allah..."
Ya furta yana ƙara kallon yadda Ubangijin talikai ya ƙera mata tsantsar kyawu gwanin ban sha'awa da burgewa, kuka take ɗan ƙaramin bakinta kuwa sai rawa yake yana wani irin shacking da motsi kamar tana son yin magana.
Matsawa ya ƙara yi kusa da ita sosai ya yaye mayafin gaba ɗaya ya rungumeta.


A hankali yake yi mata raɗa a kunnenta, cikin wani irin tattausan lafazi yake faɗin.
"Nasan dole zakiyi kukan rabuwa da Ummi da Abbie, amma bai kamata kiyi kuka a irin wannan ranar mai cike da ɗimbin tarihi da farin ciki a garemu ba, ranar da mutane da dama suke fatan gani a rayuwarsu amma Allah bai basu damar hakan ba, ranar yau rana ce mai matuƙar muhimmanci a rayuwar mu, pls na roƙeki karki ɓata mana ita da ƙunci kiyi mana giɓin farin cikinmu..."


Ƙara lafewa tai sosai a jikinsa ta kwantar da kanta a saman faffaɗan ƙirjinsa dake ta tashin ƙamshin daddaɗan turarensa mai matuƙar daɗi da sanyaya zuciya.
A take kuma taji kukan ya yanke mata ɗif, sai wani matsanancin farin ciki dake neman mamaye ilahirin ruhi da gangar jikinta.
Hannunsa ya kai ya kamo nata tattausan hannun daya sha jan lalle ya riƙe gam a nasa yana kallon ƴan siraran yatsunta da sukai wani irin mugun kyau da jan lallen ya ƙara musu.
A hankali yake wasa dasu yayinda kuma yake ta shafa bayanta da ɗayan hannunsa.
"Yau fa ke ƴar gata ce, matsayinki ya ƙaru sosai akan wanda kike dashi, daga yau za'a dinga ruɓanya miki ladanki saboda aikin ladan da zaki riƙa yi koda yaushe...ai nasan kina so ko...?"
Ya faɗa a hankali cikin wata iriyar kasalalliyar murya data sake kashe mata jiki da zuciya lokaci ɗaya ta saukar mata da kasala.
A hankali ta kaɗa kanta tana faɗin "Alhamdulillahi na gode Allah..."


Kyakkyawan murmushinsa yay mai kyau daya ƙara bayyana tsantsar kyawu da haibarsa, a hankali ya ɗago kanta daga saman ƙirjinsa yana ƙara kallon kyakkyawar fuskarta dake ƙara dilmiya zuciyarsa a tafkin ƙaunarta.
A hankali ya fara matso da fuskarsa kusa da tata a tunaninta ɗan gutun hawayen da suka rage zai share mata, hakan yasa ta saki jikinta, kawai sai ji tayi ya haɗe bakinsu waje ɗaya lokaci ɗaya kuma ya kama tausasan laɓɓanta yana tsotsa a hankali, kana ya saka hannayensa duka biyu ya riƙe ƙugunta ƙam ta yadda bazata iya zamewa a jikinsa ba.
Abunka kuma da an daɗe ba'a haɗu ba, sai gashi tun yana yi a hankali a hankali har ya zage yana ta tsotsar bakin nata da zafi zafi yana sauke zafafan numfarfashi haɗi da ajiyar zuciya.
Ƙoƙarin ƙwatar kanta take amma ina ta kasa, sai mutsu mutsu take amma yaƙi sakinta, har sai daya gaji dan kansa sannan ya janye bakinsa a nata ya ɗago fuskarsa yana kallon tata fuskar data kwaɓe cikin shagwaɓa da sangarta tana shirin yin kuka.
Saurin matsawa gefe tayi tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tana faɗin "Habiby bacci nake ji..."
Yana jin haka ya miƙe da sauri yana kallonta cike da tsananin sonta da begenta yace "A'a ki bari sai muci abinci munyi sallah tukunna sai mu kwanta..."
Kai Shatu ta girgiza kana kuma cikin sanyin murya tace "A'a na ƙoshi kuma munyi sallahn magriba da isha'i tun ɗazu dasu Basma..."
Murmushi kawai yayi ya matso dab da ita ya zura hannunsa ya fara zirya da yatsunsa a wuyanta yana sauke wasu irin tagwayen numfarfashi a hankali cikin kunnenta yana kuma kallon gefen wuyanta inda wasu ƙananun gashi masu laushi suka kwanta luf luf gwanin sha'awa.
"Yanzu ki shiga toilet kiyi alwala, idan mukayi sallah muka ci abinci sai mu kwanta..ko ƴan matana...?"
Ya faɗa cikin wata iriyar kasalalliyar murya, kana kuma yana ci gaba da shafa wuyanta da yatsunsa.
Saurin janye jikinta tayi tana turo baki kafin tace "Ina da alwalata tunda nayi sallar isha'i bata karye ba..."
Murmushi yayi kafin yace "A'a shiga dai ki sake wata..dan wannan kam da ƙyar in bata karye ɗin ba..."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana ɗan kama gefen kunnenta ya ɗan ciza kaɗan, kana kuma yayi kissing ɗin wuyanta, sannan ya ɗago yana kallonta da idanuwansa da suka koma kamar na mai jin bacci.


Bai sake cewa komai ba ya miƙe tsaye ya saka hannayensa ya ɗauketa cak ya ɗagata sama, da sauri ta saka hannayenta ta zagaye bayan wuyansa kana ta kwantar da kanta saman faffaɗan ƙirjinsa tana murmushi.
Murmushin shima yayi yana sakar mata kiss a saman idanunta, kafin ya nufi saman bene da ita, ya tura ƙofar haɗaɗɗen bedroom ɗinsu suka ratsa har cikin toilet ya kaita sannan ya direta a gaban fanfo.
Kallon kanta tayi ta cikin madubin dake toilet ɗin, a hankali ya matso ta bayanta ya tsaya, kana ya zuro hannuwansa ta saman ƙirjinta ya ƙara matso da ita sosai jikinsa ya haɗa bayanta da ƙirjinsa.
A hankali ya saka hannu ya cire mata ƴar siririyar sakar gwal ɗin dake wuyanta tare da kissing ɗin bayan wuyanta da gefe da gefen kunnuwanta, kana kuma a hankali ya saka yatsun hannunsa biyu ya ɗago kanta suna fuskantar juna ta cikin madubin.
A hankali kuma cikin murya ƙasa ƙasa yace "Yanzu kiyi alwala sai nima inyi muje muyi sallah ko...?"
Gabanta taji ya faɗi, lokaci ɗaya tsoro ya kamata, ganin haka yasa ya ƙara matsowa a kunnenta ya raɗa mata "Kar kiji tsorona kinji...?"
Ya faɗa tare da zura hannu ya kunna fanfon, shiru tayi bata ce komai ba.


A haka dai sukayi alwalar kana suka fito daga cikin toilet ɗin, yana riƙe da babbar rigar tsadaddiyar farar shaddarsa, ya ɗorata saman makeken gadon daya kusan mayaye ɗakin, sannan ya nufi tafkeken wardrobe ɗin dake ɗakin ya buɗe ya ɗauko mata wani dogon hijabi ya kawo mata, sai data ƙarba ta saka, sannan ya ɗauki darduma ya shimfiɗa musu kana suka daidaita tsaiwarsu cikin natsuwa suka tayar da sallah.
Bayan sun sallame yay musu addu'a sannan ya juyo ya kama kanta ya riƙe ya shiga karanto mata addu'a, kamar yadda Annabi S.A.W ya koyar damu.


Shatu dai gaba ɗaya gabanta sai faɗuwa yake, dan haka nan take ganin take takensa kamar ba zai ɗaga mata ƙafa ba a yau ɗin.
Sai daya gama mata tambayoyi ta bashi cikakkiyar amsa yadda ya dace, sannan ya tashi ya nufi falo yaje ya ɗauko ledojin da suka shigo dasu ya kawo gabanta ya ajiye, kana ya sake sauka ya shiga kichin ya ɗauko filet da kofuna guda biyu ya dawo ɗakin, da kansa ya zuba komai ya matsa kusa da ita ya ajiye.
A hankali ya gutsuro naman ya kai bakinta, kasa buɗe bakin tai ta ƙarɓa saboda haka nan kawai take jin fargaba da tsoro sun cika mata zuciya.


A haka cikin dabara ya samu ya ciyar da ita da ƙyar, wanda duk da haka bata ci wani abun kirki ba tace ta ƙoshi, ya bata fresh milk itama tasha kaɗan, kana kuma shima ya samu ya ɗan ci naman kaɗan yasha fresh milk ɗin.
Bayan sun gama ne kuma
Shatu ta miƙe ta shiga toilet ta wanko bakinta ta fito, kana shima ya shiga ya wanko bakinsa ya fito.
Shatu idanu ta zuba masa ganin yana ƙoƙarin cire rigar shaddar dake jikinsa.
"Meza kayi kuma zaka cire riga...?"
Ta tambaya jikinta na tsuma.
"Kayan bacci zan saka, kema ki cire naki sai in saka miki..."
Ya bata amsa yana ɗan sakin ƙaramin murmushi.
Shatu idanunta ta runtse ganin ya cire rigar jikinsa gaba ɗaya surar jikinsa ta bayyana, murmushi yayi ya saka rigar baccinsa kana ya canza wandon shaddar ya saka na bacci, kana ya taka ya isa inda makunnar wutan ɗakin yake ya kashe ya kunna wata kala mai kyau mara haske sosai.
Jin motsinsa ta bayanta yana ƙoƙarin cire mata riga yasa tsoro ya ƙara cika mata zuciya.
Wata shegiyar rigar bacci mai masifar kyau ya ɗauko ya saka mata wacce bata ɓoye komai na jikinta, luff tai a jikinsa tana ƙara shaƙar daddaɗan ƙamshinsa mai sanyaya zuciya, jin yana ƙoƙarin saka hannunsa cikin rigar baccinta ne yasa ta fara ƙoƙarin zamewa daga jikinsa tana riƙe mai hannu.


Jikinsa na rawa ya ɗagata cak ya shimfiɗeta a saman tamfatsetsen gadon baccinsu, daya sha shimfiɗa da wani lallausan zanin gado fari ƙal mai kyau da ɗaukar hankali.
Shatu kuwa duk ilahirin jikinta ɓari yake yi, jin Ya Azeez ya rungumeta ƙam ajikinsa ne yana ƙoƙarin cire mata riga yasa ta riƙe masa hannu a tsorace tana girgiza mai kai.
Bata gama tsorataba sai da taji yana lasar fuskarta zuwa wuyanta, yana yawo da hannuwansa a sassan jikinta, lokaci ɗaya kuma yana mata raɗa tare da gaya mata kalaman soyayya masu daɗi da kashe jiki.
Jikinta banda tsuma babu abinda yake.
Baki ta buɗe da zummar magana yayi maza ya haɗe bakinsu waje ɗaya.
Ya dinga wasa da harshensa a cikin bakinta yana mata wata irin tsotsa cikin fitar hayyaci.


Shatu banda hawaye ba abinda take, jin irin yadda Ya Azeez yake sarrafata yana juyata ne, ga wani irin wasa da yake da ƙirjinta wanda tun bata jin abun har ta fara jin daɗin yanayin amman tsoro ya hanata ta nuna jin daɗinta a zahiri. A zafafe yake kissing ɗinta yana shafa bayanta sai wani yarrrr yarrr take ji tana jin wani baƙon al'amari na kusantar sabuwar duniyarta, ya jima yana tsotsar bakinta kafin ya janye ya tashi zaune yana ƙoƙarin cire rigar baccin jikinsa, sai daya cire sannan ya koma ya kwanta lokaci ɗaya yana ƙara jawota jikinsa ya rungumeta yana shafa bayanta tare da jan hannunta ya kai kan fuskarsa yana shafawa a hankali a hankali har ya sauko dashi kan faffaɗan ƙirjinsa da taji babu riga.
A hankali ya kai hannunsa yana ɗan shafa gefen fuskarta yana wani lumshe ido, shiru tai tana jin duk abinda yake mata amma bata da ikon hanasa saboda yadda ya gama kashe mata jiki da salonsa, mai cike da tafiyar da tunani.


Hakan yasa ta sakar mai jiki sosai saboda tana jin daɗin abubuwan da yake mata, duk a tunaninta kuma iya hakan za'a tsaya sai ta ƙara sakin jiki ta lafe tana karɓan sakwannin da yake aika mata dasu cikin tsantsar kulawa da ƙwarewa.
Sai daya gama shagaltar da ita da wasanninsa masu matuƙar tsayawa a zuciya, sannan ya soma ƙoƙarin isar da kansa gareta, cikin shauki haɗe da muradi mai girma.
A lokacin ne ta ƙara tsorata ta hau rirriƙesa tana kuka.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lumshe idanuwansa ya kai laɓɓansa saman goshinta ya manna mata wani sassanyan kiss, sannan ya gangaro da bakinsa kusa da kunnenta a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login