Showing 54001 words to 57000 words out of 113443 words
faɗa a shagwaɓe tana marairaice fuskarta.
Ɗago kansa yayi ya kalleta fuskarsa ɗauke da wani kyakkyawan murmushi wanda ya sake fito da zallar dattako da hutunsa, a hankali ya miƙa mata hannunsa cikin nuna ƙauna irinta ɗa da mahaifi ya riƙo nata, bayan ya amsa mata sallamar tata cikin nuna tsantsar kulawarsa da jin daɗin ganinta da yayi yace "Zo nan kusa dani uwata maganin kukana..." Ya faɗa tare da ɗagota ya zaunar da ita a kusa dashi, duƙar da kanta ƙasa tayi tana ɗan murmushi take faɗin "Na gode Abbie na..." Ta faɗa tare da ɗagowa ta watsawa Zahra harara.
Saurin ɗauke kanta tayi gefe tana zumɓuro baki kafin tace "Yauwa Aunty Shatu dama fa ke nake ta jira ki fito, ki ɗan bani aron wayarki in kira Ya Abdul in sanar masa mun sauka gida lafiya...dan kar yaji mu shiru ya ɗauka ko wani abun ne ya faru damu...ko ba haka ba Ummi...?"
Ta ƙarashe maganar da sigar tambaya tana kallon Ummi dake ƙoƙarin shirya abinci akan dinning, juyowa Ummin tayi ta kalli Shatu data wani haɗe rai tana hararar Zahra tace "Gaskiya kam kinyi tunani mai kyau auta ya kamata ku kirasa ku sanar dashi kun sauka lafiya, saboda yaron yayi muku abun alkhairi bai kamata ku manta dashi da wuri haka ba..."
Abbie wanda yaji zancen nasu daga sama sam bai gane inda suka dosa ba, juyowa yayi ya dubi Ummi cikin rashin fahimta yace "Wai waye ake cewa za'a kira ɗin ne..me kuma yayi musu...?"
Dama kamar jira Zahra take tayi tsagal tace "Wani bawan Allah ne mai kirki a Kaduna yake Abbie. Jiya shi ya dinga ɗawainiya damu ya k..." Katseta Shatu tayi a fusace da faɗin "Dalla rufewa mutane baki mai shegen surutun tsiya kawai, faɗi ba'a tambayeki ba kin saki baki kina wani zaro zance sai kace wata mai bada lectures...." Ta faɗa cike da jin haushin Zahran tana harararta.
Baki kawai Abbie da Ummi suka saki suna kallon ikon Allah, kafin Abbie yace "To ke uwata gaya min abinda ya faru tunda kin hana auta ta faɗa min...."
Ɗif Shatu tayi ta ɗukar da kanta ƙasa ta kasa cewa komai, ganin yadda ta yin ne kuma yasa Abbie ya juya yana kallon Zahra da tai zaune tsumu tsumu yana faɗin "To ke gaya min auta wanene Ya Abdul ɗin kuma tunda ita uwata ta kasa min bayani...."
Juyowa Shatu tayi da sauri tana faɗin "Allah zan gaya maka Abbie, jira nake dama sai mun gama ci abinci tukunna...." Ta faɗa fuskarta a haɗe babu alamar fara'a, dariya Abbie yayi irin tasu ta manya kana yace "To wai me yake faruwa ne nifa ban gane ba...ko dai suruki aka samo min ne a Kadunan uwata shine ake jin kunyata ba'a so in sani, domin na lura bakin nan na auta akwai daddaɗan labari da akeson fesa min....?" Ya faɗa tare da kallon Shatu data miƙe da sauri ta nufi hanyar dinning area inda Ummi ta gama jera musu abinci saman makeken tebur ɗin dake gurin taja kujera ta zauna lokaci ɗaya tana turo baki tace "Abbie nidai dan Allah ku taso muci abinci wallahi yunwa nake ji sosai..." Ta faɗa a shagwaɓe tana ƙoƙarin buɗe kular farfesun dake gabanta.
Tasowa sukayi dukkansu suka nufo dinning area ɗin kowannen su yaja kujera ya zauna kana Shatu ta miƙe ta fara zuzzubawa kowa nasa, tuwon shinkafa ne miyar taushe wacce taji naman rago da kayan miya sai tashin ƙamshi take, gefe guda kuma ga farfesun kayan cikin rago da sassanyan kunun aya wanda yaji madara da kayan ƙamshi, turawa kowannen su abincin tayi gabansa, kana itama ta zuba nata taja kujera ta zauna a kusa da Ummi bayan sunyi bismillah kowa ya fara cin na gabansa.
Koda suka kammala cin abincin Zahra ce ta fara miƙewa ta tattare kayan da suka ɓata ɗin ta kai kichin, kana Abbie, Ummi da Shatu suma duk suka tashi suka koma cikin falo suka zauna, ita kuwa Zahra koda ta kai kayan kichin bata barsu haka ba sai data tsaya ta wanke su tsaf ta maida kowanne ma'ajiyarsa kana ta dawo tazo ta goge kan dinning table ɗin sannan ta koma falon inda ta iske Abbie da Ummi suna ta hira yayinda Shatu kuma ke zaune a gefe guda riƙe da wayarta tana chatting.
Zama tayi a kusa da Ummi tana faɗin "Barkanku da hutawa Ummina da Abbiena..." Ta faɗa tare da jingina kanta a kafaɗar Ummin, ɗan shafa kanta Ummin tayi kana tace "Yauwa autar Ummi sannu da ƙoƙari Allah yayi muku albarka...." Da Ameen suka amsa dukkansu kana Abbie ya dubi Zahra dake faman satar kallon Shatu ta gefen ido yana faɗin "Auta kefa nake ta saurare dan na lura bakin nan naki akwai kyakkyawan labari mai daɗi da akeson a labarta min, shiyasa duk na ƙosa nima inji ko mene ne..."
Kamar dama kuwa jira Zahra take ta shiga zayyane masa komai daya faru a Kaduna da irin taimakon da Ya Azeez yayi musu har zuwa kawo su tasha da yayi suka hau mota babu abinda bata zayyane ba sai wanda ta manta.
Shatu kuwa tunda ta fara zayyane labarin ta tsaya tsam ta bar abinda take yi ta zuba mata ido kawai tana aikin kallonta, gaba ɗaya lamarin Zahra yanzu bala'in takaici yake bata, ita a nata ganin bata ga dalilin da zaisa a damu da yayata labarin wannan mutumin ba. Kawai dan saboda ya taimaka musu shikenan za'a wani damesu da maganarsa sai kace wanda suka ɓata ya tsintosu ya dawo dasu gida.
Mamaki da takaicin Zahran bai gama sakinta ba ta tsinkayi muryar Abbie yana faɗin "Ina numbern tasa take auta maza jeki ɗauko wayata a ɗaki ki saka min in kirasa ayi masa godiya, wannan ai bai kamata a kyalesa haka ba tare da mun yaba masa mun nuna masa farin cikinmu kan abun arzikin da yayi mana ba, maza maza tashi kije ki ɗauko wayar ki saka min numbern in kirasa kar dare ya ƙara yi...."
Ko kafin ma ya gama rufe baki Zahra ta miƙe da sauri ta nufi bedroom ɗinsa, Shatu kuwa gaba ɗaya ji tayi kamar ta tashi ta bita ta rufeta da duka saboda tsabar takaicinta.
*******
A ɓangaren Ya Azeez kuwa koda ya koma gida kasa aiwatar da komai yayi duk jikinsa a sanyaye yake gaba ɗaya al'amuran Fadwa sun gama hargitsa masa tunani, dama ɗan zaman da yayi ne a gidan Ummansa yasa duk wata damuwa da baƙin cikin zuciyarsa suka kau, amma tunda ya dawo ya shigo cikin gidan ya fara jin komai yana dawo masa sabo kamar yanzu ne Fadwan ke sanar dashi cewa tana Abuja sai nan da kwana huɗu ko biyar sannan zata dawo, a hankali ya sake yin juyi akan shimfiɗarsa yayi rigingine ya tsurawa saman silin ɗin dake ɗakin idanu, yanzu fa shikenan haka zai zuba idanu yana kallon Fadwa tana abinda takeso amma babu damar ya kwaɓa mata..?
Yana cikin wannan tunanin wayarsa ta ɗauki ƙara, cike da mamaki yayi saurin tashi zaune ya lalubo wayar dake aje gefen filonsa, kallon fuskar wayar yayi a hankali ganin baƙuwar special numbern da ake kiransa da ita ne yasa ya ƙara cika da matsanancin mamaki, to shi wa yake dashi da zai kirasa a wannan daren..? Idan Ummansa ce ai numbernta ya kamata ya gani.
Fadwa kuwa dama ita yasan babu abinda zaisa ta kirasa haka kawai ballantana yayi tunanin ganin kiranta a dai-dai wannan lokacin, alhalin yana da tabbacin ta riga ta gama gaya masa duk abinda take da niyyar gaya masan, dan haka yake da yakinin babu abinda zaisa ta kuma kiransa.
Agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakin ya kalla ƙarfe 9:20pm ya gani dan haka yayi ta maza kawai ya daure ya kawar da al'ajabinsa ya ɗaga kiran lokaci ɗaya ya kai wayar kunnensa cike da ƙoƙarin ɓoye damuwarsa duk da bai san waye takamaiman me kiran nasa ba yace "Assalamu alaikum..."
Daga can ɓangaren kuwa Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai yayi saurin saka wayar a handfree bayan ya amsa masa sallamar kafin ya ɗora da faɗin "Barka da dare Abdul..."
Wani banbarakwai haka Ya Azeez yaji sunan a kunnensa, dan haka yayi shiru bai amsa ba.
Ɗan murmushi Alhaji Bello yayi daga can ɓangaren kana yace "Ko ba da AbdulAzeez nake magana ba ne....?"
Ajiyar zuciya ya sauke a natse kafin yace "Nine inaji, ina wuni...?" Ya faɗa tare da ɗan yin jim kaɗan cikin nazari.
Daga can ɓangaren kuwa Alhaji Bello juyawa yayi ya kalli Zahra da tai wani zaman dirshan a gabansa ta tanƙwashe ƙafafuwa ta zubo masa idanu tana faman washe baki.
Ɗan murmushi yayi kafin yace "Nasan baka gane mai kiranka ba ko..? To sunana Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai kuma nine mahaifin Zahra da Aisha ƴan matan daka taimakawa jiya da daddare a garin Kaduna..."
Cikin tsananin mamaki Ya Azeez ya waro kyawawan idanuwansa waje yana kaɗa kai, kafin ya sauke numfashi cike da kunya yace "Barka da dare Alhaji...ina wuni..fatan sun sauka gida lafiya...?" Ya faɗa lokaci ɗaya yana duƙar da kansa kamar yana gabansa.
Ƴar dariya Alhaji Bello yayi kafin yace "Bakanmu dai yaron kirki, Alhamdulillahi wallahi sun dawo gida lafiya mun gode Allah, dama na kiraka ne domin inyi maka godiya bisa ga irin taimakon da kayi mana saboda ba dan Allah ya kiyaye kuma ya haɗaka dasu ba, da bamu san abinda zai faru a jiyan nan ba, sakamakon dukkan mu babu wanda yasan lokacin da suka ɗauki mota suka fita daga gidan nan, sai dai kawai dubawa akayi sama ko ƙasa akaga babu su babu alamar su a gidan wai sun tafi Abuja. Nidai babu abinda zan ce maka sai godiya da fatan alkhairi, Allah ya biyaka ya rabaka da iyayenka lafiya..."
Cikin tsananin jin daɗin addu'ar tasa Ya Azeez ya amsa da Ameen Ameen, kana daga nan suka yi sallama bayan yace agaishe dasu Zahra da Shatu da sauran mutanen gida.
Wanda basu sauke wayar ba har sai da Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai ya cewa Ya Azeez ɗin yayi saving numbernsa shima zaiyi saving ɗin tasa a wayarsa domin su riƙa gaisawa, kana daga haka suka yanke wayar.
Ajiye wayar Ya Azeez yayi ya koma ya kwanta kana yaja ɗan yalolon bargonsa ya rufe ƙafafuwansa lokaci ɗaya yana gyara kwanciyarsa cikin tarin nazari da tunanin rayuwa.
Cikin haka bacci mai daɗi ya kwashesa ba tare da ya bar zuciyarsa ta samu sukunin tuna wata aba can Fadwa ba.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
2️⃣2️⃣
Tunda suka fara wayar Shatu ta tashi tsam ta bar falon, kai tsaye ɗakinsu ta wuce tana shiga ta tuɓe kayan jikinta ta ɗaura tawul ta wuce toilet, a gurguje ta ƙara watso ruwa domin taji daɗin jikinta, bata jima a toilet ɗin ba ta fito ƙirjinta ɗaure da tawul kai tsaye gaban wardrobe ɗinta ta nufa ta saka hannu ta buɗe ɓangaren inda kayan bacci suke gasu nan kala kala a jere gwanin sha'awa da burgewa.
Cikin kayan baccin ta zaɓo wasu riga da wando farare tas masu taushi da tsari ta zura a jikinta, kana ta ɗauki wata hular net baƙa ta zura akanta, matsawa tayi gaban madubin dake ɗakin ta ɗauki turarenta mai sanyin ƙamshi ta fesa kaɗan a jikinta kafin ta bar gaban madubin ta wuce ta haye saman gado ta kwanta lokaci ɗaya taja tattausan bargon dake ajiye a gefen gadon ta lulluɓe rabin jikinta dashi tai luf ta lafe tare da lumshe idonta tana jin wani irin yanayi a tattare da ita.
Rabin hankalinta gaba ɗaya yana can falo inda ta rasa dalilin zuciyarta na azalzala mata da son ƙara jin muryarsa, tsaki ta saki ta ƙara ƙudundune kanta a cikin bargon ta runtse idonta da ƙarfi a ƙoƙarinta na son barci ya ɗauketa koda da ƙarfin tsiya ne, saboda bata jin zata iya biyewa zuciyarta akan gurguwar shawarar da take son bata na ta tashi ta koma falon.
A ɓangaren Zahra kuwa bata shigo ɗakin ba sai gurin ƙarfe 10pm kuma har lokacin Shatu idonta biyu ta kasa bacci sai faman juyi take tana tunane tunane marasa tushe ballantana makama, a haka Zahra ta shigo ɗakin ta isketa inda tana jin motsin shigowar Zahran ta lumshe idonta da sauri kamar mai bacci, wanda abinda bata sani ba Zahran na lura da ita tuni ta gama ganowa idonta biyu ba baccin take ba. Kallonta tayi tana mamakinta dan ita duk a zatonta yau idan tazo kwanciya mai rabata da ita sai Allah, saboda tasan halinta farin sani ba'a taɓa cin bashinta sai an biya, amma yau abun mamaki sai ta ga saɓanin haka.
Taɓe bakinta tayi a hankali tana sauke numfashi kafin ta shiga tuɓe kayan jikinta ta wuce toilet direct itama taje ta watso ruwa a gurguje ta fito, gaban ɗayan wardrobe ɗin dake ɗakin ta ƙarasa ta buɗe, wasu kayan bacci ne masu kalar ruwan madara ta zaro da sauri ta zura a jikinta kana ta ɗan fesa turare, ta lallaɓa ta haye gado kusa da Shatu ta kwanta kana taja bargo a hankali ta rufe ƙafafuwanta zuwa cikinta, ganin kamar bacci ya ɗauketa ne yasa ta ƙara matsawa kusa da ita sosai tana karanto musu addu'ar bacci ta shafa kafin ta shafawa Shatun a jikinta itama, sannan ta koma ta kwanta ta ƙudundune lokaci ɗaya tana runtse idanuwanta masu cike da baccin gajiya.
Wanda a ɓangaren Shatun itama hakan ce ta kasance da ita bayan Zahra ta shafa mata addu'ar baccin dama kamar jira take wani daddaɗan bacci mai cike da wasu irin mafarkai masu tsananin daɗi yayi awon gaba da ita.
*********
Washegari
Misalin ƙarfe 1:20pm Shatu ce tsaye cikin wasu tausasan riga da wandon Palazzo masu bala'in kyau da sheƙi.
Inda riga da wandon suka kasance kalar royal blue da ɗigon fari fari a jiki, sai rigar kimono data ɗora akai fara itama mai ɗan zane zanen fari da yarfin royal blue ɗin a jiki wacce bata wuce gwiwarta ba, sosai shigar tayi mata masifar kyau ta kuma fito da zallar wayewarta da kalar fatarta mai kyau da ɗaukar hankali, ta zura tsadadden half cover ɗinta fari ƙirar kamfanin Italy, kana ta ƙaraso gaban madubi ta ɗauki turaren Smart Black cikin jerin tsadaddun turarukanta dake gaban madubin ta fesa wanda ya haɗu da ƙamshin body mist ɗinta na white mist suka bada wani daddaɗan ƙamshi mai sanyi da sanyaya rai.
Tana ƙoƙarin yafa ɗan siririn farin gyale a kanta Zahra ta shigo ɗakin itama cikin shirinta na wata pink ɗin atamfa ɗinkin riga da siket wanda suka dace da jikinta da kalar fatarta, ta yana ɗan madaidaicin ƙaramin gyale itama akanta, ta nufo inda take gaban madubin ta tsaya tare da dubanta tun daga sama har ƙasa tana faɗin "Masha Allah ƴan matan Ummi, kin ganki kuwa..? Gaskiya kinyi kyau sosai ba ƙarya wallahi..."
Ido Shatu ta lumshe tare da sakin ƙaramin murmushi kana tace "Amma ai ban kai autar Ummi kyau ba ko, domin ita komai tasa a jikinta kyau yake mata...?"
Ɗan shagwaɓe fuska Zahra tayi tare da juyar da kanta gefe tana faɗin "A'a nidai ba ruwana ki daina wani haɗa kanki dani saboda kin fini kyau da komai da komai nesa ba kusa ba, amma sai ki wani dinga yaudarata kina cewa wai na fiki kyau, ko a ina ne na fiki kyau ɗin oho..." Ta ƙarashe maganar a shagwaɓe tana ɓata fuska.
Wani ƙayataccen murmushi Shatu ta saki tana cewa "To na daina Aunty Zahra shikenan ko...?"
Murmusawa kawai tayi ba tare data kuma cewa komai ba ta ƙarasa gaban madubin ta sake gyara kwalliyar fuskarta kana ta juyo tana duban Shatu tace "Ni kam na gama shiryawa ke kawai nake jira..."
Wayarta kawai ta ɗauka da Atm card ɗinta ta saka cikin wata ƴar madaidaiciyar handbag fara ta saƙala a hannunta tayi gaba Zahra na biye da ita a baya suka fito, kai tsaye cikin babban falon gidan suka nufa, Shatu na gaba, Zahra na biye da ita tana lallatsa wayar dake hannunta. Shigowar su cikin falon ce tasa Ummi dake fitowa daga kichin hannuta riƙe da wani babban farati ta saki wani lallausan murmushi dake bayyana tsantsar ƙaunarta ga ƴaƴan nata, tace "Masha Allah my baby's gaskiya kunyi kyau sosai tubarakallah, amma ya kamata ku bari muci abincin rana dai kafin ku tafi shopping ɗin nan, tunda na gama girkin tun ɗazu..."
Ta faɗa tana wucewa kai tsaye dinning area ɗin ta ajiye farantin, kafin ta shiga jera abincin lokaci ɗaya tana faɗin "Maza kuzo kuci sai ku wuce, saboda nasan idan na biye muku baci zakuyi ba, sai dai kuyi ta min hanya hanya tunda dama can abincin ba wani damunku yayi ba, dan haka idan na kyaleku ba ci zakuyi ba..."
Jin abinda tace ɗin ne yasa dukkansu sukayi ƴar dariya kana suka wuce zuwa dinning area ɗin kai tsaye.
Bayan sun zazzauna ne Ummi tayi sarving ɗinsu, inda ta zuba musu farar shinkafa da miyar kaji zuƙu zuƙu da tayi, sai haɗin coslow da pepper chicken data sakawa kowannen su a wani ɗan ƙaramin bowl, ta turawa kowa filet ɗin gabansa, kana taja kujera itama ta zauna tana faɗin "Maza kuyi ku kammala ku tafi, kafin rana ta ƙara kwallewa kuje ku kwaso zafi ku dawo min gida a galabaice kuce kuma kai na ciwo..."
Ta faɗa tare da ɗaukar cinyar kaza ta kai bakinta ta soma ci, ɗago kai Shatu tayi ta kalleta kafin ta ɗan turo baki a shagwaɓe tana faɗin "Wai ina Abbie ni ban ganshi ba ko har ya fitan ne...?"
Kai Ummi ta gyaɗa kana tace "Ya fita tun ɗazu, saboda yau suna da ɗaurin auren yaron wani abokinsa Alhaji Sale Musawa da za'ayi a Kundila shiyasa ya fita tunda wuri, saboda ya samu ya halacci ɗaurin auren, amma yace ba zai jima ba ana gama ɗaurawa zai dawo gida..."
Jinjina kai Shatu tayi kana tace "Allah ya sanya alkhairi ya dawo dashi lafiya..."
A hankali Ummin ta amsa da "Ameen ya Allah..." Kana daga haka suka ci gaba da cin