Showing 69001 words to 72000 words out of 113443 words
dasa kai da sauri ta fice daga falon.
Tana fita harabar gidan kuwa direban su dake zaune akan benci ya taso da sauri ya ƙaraso ya buɗe mata wata farar mota ƙirar Vibe dake fake a harabar gidan ta shiga ta zauna kana ya mayar da ƙofar ya rufe, ya zagaya shima ya shiga mazaunin direba ya tada motar, maigadi ya wangale musu gate lokaci guda ya silala motar suka fice daga cikin gidan.
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:19 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
2️⃣7️⃣
Ƙarfe 2pm. Dai-dai Ya Azeez suka shigo garin Kaduna, direct gidan Ummansa suka nufa kamar yadda ya kwatantawa direban.
Suna isa ƙofar gidan direban kuwa yayi parking, Ya Azeez ya buɗe motar a hankali ya fito, kafin cikin natsuwa ya juya ya kalli direban dake ƙoƙarin tayar da motar ya wuce yace "Ba dai nufinka tafiya zakayi ba tare daka tsaya ko ruwa ne ka ɗan sha ba...?"
A hankali direban ya jinjina masa kai yana faɗin "Eh yallaɓai so nake in koma da wuri, saboda bana so inyi tafiyar dare, shiyasa nake so in juya da kafin duhu yayi saboda hanyar ba kyau..."
Ɗan kwaɓe fuska Ya Azeez ɗin yayi yana faɗin "Aiko baka isa ba saika tsaya kasha ruwa ka huta kafin ka wuce..."
Murmushi Nuhu direban yayi kana ya buɗe motar ya fito yana faɗin "Toh yallaɓai..." Ya faɗa tare da ɗaukar jakar Ya Azeez ɗin kai tsaye suka nufi cikin gidan a tare bakinsu ɗauke da sallama suka shiga.
Umma ce zaune akan tabarma ita kaɗai a tsakar gidan yayinda take riƙe da littafin Husnul Muslim a hannunta tana karantawa, jin sallamarsu ne yasa ta ɗagowa da sauri fuskarta ɗauke da murmushi take faɗin "Waalaikums salamu, maraba da baƙin Kano..yanzu kuke tafe da ranan nan...?"
Ta faɗa cike da kulawa tare da ajiye littafin dake hannunta, ta miƙe lokaci ɗaya tana ƙara yi musu barka da zuwa tace "Ku zauna mana..." Ta faɗa tana wucewa ta shiga cikin ɗaki da sauri ta ɗauko wani sabon kofin jug da ƙananan kofinansa guda biyu, ta fito taje ta ɗebo musu ruwan randa mai sanyi ta kawo gabansu ta ajiye, kana ta ƙara komawa cikin ɗakin ta ɗauko wata ƴar madaidaiciyar kula da suke zuba abinci, ta haɗo dasu filet da cokula ta kawo musu.
Sai data zuzzuba musu kana ta koma gefen tabarman ta zauna suna ƙara gaisawa, yayinda take tambayar ya suka baro su Abba da Mami, suka amsa mata da lafiya ƙalau sunce ma agaisheta.
Har Nuhu direba ya kammala cin abincinsa yasha ruwa, amma Ya Azeez shi ko taɓa cokalinsa bai yi ba, ganin haka yasa Umma juyawa ta kallesa, kafin cikin kulawa tace "Kaci abincin mana karya huce, idan ya huce bazai maka daɗin ci ba..."
A hankali ya kalleta kafin yace "Zanci Umma, so nake in ɗan ƙara hutawa tukunna..."
Kaɗa kai kawai Umman tayi ba tare da tace komai ba, yayinda shi kuma Nuhu direba ya miƙe yana faɗin "Yallaɓai zan wuce..kar dare yayi min a hanya..."
Ya faɗa tare da ɗan duƙawa yana yiwa Umma sallama, bayan tayi masa fatan alkhairi da addu'ar sauka lafiya ne kuma ta ƙara yi masa godiya kana tace ya gaishe mata dasu Mami da Abba dasu Fahad da Ibrahim, ya amsa mata da Toh, kana Ya Azeez ya miƙe domin yi masa rakiya suka fice daga gidan.
Ya Azeez kuwa sai da yaga tafiyarsa kafin ya dawo cikin gidan, kusan Umma ya ƙaraso ya zauna yana sauke numfashi.
Ɗagowa Umman tai ta kallesa kafin kuma cikin kulawa tace "Ya hanya, ya ka baro mutanan gidan...fatan anyi biki an ƙare lafiya...?"
Cikin sanyin muryarsa yace "Alhamdulillahi su Mami duk suna gaisheki, Abba ma yace a gaisheku da Imaan..."
Ya ƙarshe maganar lokaci ɗaya yana jayo filet ɗin abincin da Umman ta rufe masa ya buɗe, ya ɗauki cokalin ya soma cin abincin a nutse hankalinsa kwance, yayinda gefe guda kuma suke taɓa ƴar hira a tsakaninsu.
Suna tsaka da hirar tasu ne kuma aka kira la'asar, dan haka ya miƙe ya ɗauki buta, yaje ya ɗauro alwala ya fice zuwa masallaci, koda ya dawo ya iske Umma itama har ta idar da tata sallar tana zaune akan tabarma jikinta sanye da hijabin da tayi sallah.
Dan haka yana zama suka cigaba da hira, inda a nan ne kuma Ya Azeez ɗin ke gaya mata irin kyautar abun arzikin da Abba yayi masa, har kawo jarin da yace zai ƙara musu shida Fahad su haɗa hannu gurin ƙara yalwata harkar kasuwancinsu, da yace ya basu gidan motocinsa su dinga saro motoci daga Kwatano da China suna shigowa dasu gida Nigeria.
Umma kuwa tun kafin ya ƙarashe bayanin da yake mata idanuwanta suka cika taf da hawayen farin ciki, dama ashe akwai ranar da farin cikinsu zai dawo garesu..? Ashe akwai wanda zai tallafi rayuwarsu ya agaji maraicin ƴaƴanta..? Lallai wannan mutumin kirki ne, ita kam bata san da wane irin baki zata iya gode tarin alkhairansa a garesu ita da ƴaƴanta ba.
Da mamaki tace "Yanzu duk wannan abun alkhairin wa kai kaɗai bawan Allahn nan yayi su Yayan Imaan...?"
Ta faɗa cike da tsananin farin ciki da mamaki tana kallonsa.
Ɗauko jakarsa yayi tare da buɗewa ya zaro wata ɓaƙar leda a ciki ya miƙa mata yana faɗin "Gashi wannan ma ke yace in kawowa..."
Zaro idanu tayi da mamaki tana ƙara kallon ledar, kafin tasa hannu ta ƙarɓa ta warware tana faɗin "Allah sarki shidai baya taɓa gajiya da abun arziki...mun gode..mun gode Allah ya saka masa da mafificin alkhairi ya ƙara masa buɗi..."
Ta faɗa tare da warware ledar tasa hannu tana ƙoƙarin fito da abinda ke ciki, baki ta buɗe sakamakon ganin kuɗi ne rafar ƴan ɗari biyar biyar sababbi fil fil har guda huɗu a ciki, ware ido tayi cike da tsananin mamaki tana faɗin "Ikon Allah, kaga ashe kuɗi ne aciki..."
Ta faɗa cike da tsantsar mamaki tana nuna masa kuɗin, zaro ido yayi cike da mamaki dan shima karan kansa bai san kuɗi ne a ciki ba, dan yadda ya bashi a kanannaɗe a leda haka ya saka a jakarsa ba tare daya buɗe yaga ko mene ne a ciki ba, dan shi irin mutanen nan ne waɗanda basu iya shisshigi ba kwata kwata, kuma basa so ayi musu.
Da sauri yasa hannu ya karɓi kuɗin ya jujjuya a hannunsa, kafin ya saki murmushi yana faɗin "Allah sarki Abba, wallahi Umma mutumin nan akwai kirki, har dubu ɗari biyu fa..? Wannan ai sai dai kija jari kawai kita kasuwanci abinki..."
Gyaɗa kai kawai tayi ba tare da tace komai ba, ranta fari tas kyautar naira dubu ɗari biyu ƙyal ba tare da aikin komai ba, itako dame zata iya biyan wannan bawan Allah..?
Sosai bakin Umma yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki, dan rabonta da riƙe kuɗi irin haka tun kafin karayar arzikin mijinta, dan tunda komai nasu ya ƙare bata taɓa tunanin ko a mafarkin zata riƙe dubu hamsin nata na kanta bane a lokacin, ballantana kuma a nan gaba.
Sun daɗe suna tattaunawa akan kuɗin, tare da yanke shawarar abinda ya kamata Umman tayi dasu. Inda Ya Azeez yace ta cigaba da saro atamfofi da lesuka ta dinga saidawa kafin kuma aga abinda Allah zaiyi, kuma itama tayi na'am da wannan shawarar sosai, dan haka tace washegari da kanta zata shiga kasuwa ta samu shagon ƴan sari inda zata dinga zuwa da kanta tana saro kayanta.
Haka Imaan ta dawo ta samu wannan kyakkyawan labarin, tayi matuƙar murna sosai itama, kuma ta bada goyon baya ɗari bisa ɗari akan shawarar da Ya Azeez ɗin nata ya kawo.
Nan ya kusan raba dare suna ta hirar duniya, dan sai gurin ƙarfe 11pm. Sannan yayi musu sai da safe ya tashi ya wuce gida.
Washegari kuwa tun ƙarfe 10am Umma ta shirya ta tafi kasuwa, inda akayi mata kwatancen shagon Ɗan Fulani wani mai sayar da atamfofi da lesuka akan farashi mai sauƙi da rahusa, direct aka rakata har shagonsa inda tayi sa'a kwanansa biyu kenan da dawowa daga Lagos ya kawo kaya sosai.
Nan ta zage ta zaɓa aka haɗa mata komai da komai, sannan ya bata akan farashi mai sauƙi yadda idan ta siyar itama zata samu nata akai.
Koda ta dawo daga kasuwar da kanta ta shisshiga gidajen maƙotansu ta kai musu kayan ta gaya musu duk mai so tana saidawa, kuma komai mutum yake so ya faɗa ko menene idan bata dashi ma zata ɗauko masa.
Kan kace me, tuni kasuwanci ya fara haɓɓaka dan ta kai yanzu kome ake so tana gida daga zaune zata kira ɗan fulanin a waya ta gaya masa duk abinda takeso, ya haɗa komai yaba yaron shagonsa ya kawo mata har gida.
******** *********
A ɓangaren Fadwa kuwa yau kimanin satinta biyu kenan cif a garin Abuja, kuma duk wannan tsawon kwanakin bata taɓa koda kiran Ya Azeez a waya bane, haka kuma shima tun ranar da suka tafi data kirasa bai ƙara koda kwatanta kiran layinta bane har yau tsawon kwana goma sha biyar.
Wanda ita Fadwa anata ɓangaren tun ranar data kirasa ta sanar mai da tafiyar tata bata ƙara kunna wayarta ba har yau, ballantana tayi tunanin kiransa ta bashi haƙurin jinta shiru da yayi bata dawo ba har tsawon kwanaki da yawa haka.
Gararin gabanta kawai take yi babu abinda ya dameta, shima kuma ana shi ɓangaren haka ne, dan ko kaɗan bai taɓa ɗorawa kansa damuwar rashin dawowar tata ba har lokacin, wanda shi a nashi ganin ma gwara ya zuba mata idanu kawai yaga iyakar gudun ruwanta.
Wanda kuma ko kaɗan rashin jin ɗuriyar tasa da batayi bai taɓa damunta ba, abinda taso taga dama kawai shi take yi abinta.
Sashe guda aka ware musu a cikin rantsatstsen gidan suke zaune su kaɗai abinsu, gashi kullum rana ta duniya sai direba ya kwashesu sun fita yawon zaga gari, duk wani gurin shaƙatawa sai sun leƙa shopping mall kuwa iri iri babu wanda basu shiga
sunyo siyayyan kaya ba.
Fadwa an samu abinda akeso dan haka ko maganar komawa gida bata so ayi mata, shiyasa koda Hajiya Labiba da Hajiya Zalika suka shirya komawa Kaduna tun washegarin da aka kai amaryar cikinsu babu wanda yabi ta kanta balle suyi mata maganar komawa gida, kuma itama bata yi musu ba.
Haka kuwa tana kallo suka gama shiryawa, abin takaicin kuma har da ita a ƴan rakiyarsu zuwa airport, tana kallo kuma suka shiga jirgi dan komawa amma ko ajikinta, sai ma ɗaga musu hannu da ta dinga yi tana faɗin "Allah ya tsare ya saukeku lafiya ƙawata, sai mun dawo muma agaidasu Alhajin..."
Hajiya Lubna dai kawai da ido take binta, dan ita zuwa yanzu al'amarin Fadwa gaba ɗaya ya daina bata mamaki, tsoro yake bata.
Kamar kullum yau ma tunda safe suna gama karyawa direba ya kwashesu suka fice, yau ɗin wani haɗaɗɗen gurin shaƙatawa sukaje, daga can kuma suka wuce Sahad Store inda suka danƙaro siyayyarsu.
Sai yamma liƙis suka nufo gida.
Washegari kuma tunda sassafe suka tashi da shirin komawa gida, dan haka yau tunda Fadwa ta tashi take ta wani kumbure kumburen fuska da baki.
Hajiya Lubna kuwa duk tana lura da ita kuma taga take takenta amma ko kaɗan bata tanka mata ba, dan ta fahimceta so take kafin su bar garin su raba abun faɗe a gaban ƙanwarta da mijinta, haka kawai tasa ta barwa kanta abun gori, shiyasa tayi banza da ita taƙi kulata, har tai ta gama ba tabi ta kanta ba.
Ƙarfe 3pm. Dai-dai suka gama shiryawa direba ya kwashesu zuwa airport.
*********
Ƙarfe 6pm. Dai-dai dawowarsa kenan daga cikin garin inda ya faka napep ɗinsa a ƙofar gida ya fito ya nufi cikin gidan, yau ɗin a gajiye yake tuɓus, dan haka ya tashi aikin tunda wuri ya nufo gida dan ya samu ya ɗan watsa ruwa ajikinsa ko zaiji daɗi, ɗaki ya shiga ya ɗauko bokitin wanka ya ɗebi ruwa ya fito ya shige banɗaki.
Koda ya fito jallabiyarsa kawai ya zura ya ɗan fesa turare, ya ɗauki casbahansa da wayarsa ya fito, yana ƙoƙarin kulle ƙofar ɗakin ne ya juya ya kalli tsakar gidan, wanda ya haɗa uban ƙura ko'ina yayi bututu saboda rashin samun gyara kwana biyu da baiyi ba, dan yanzu kullum idan ya tashi tunda sassafe ya gama ƴan aikace aikacen da yake yi irinsu gyaran ɗaki da ɗebo ruwa, baya samun tsayawa yin sharar tsakar gidan yake ficewa, kuma baya dawowa gidan sai dare, shiyasa baya samun lokaci sosai saboda abubuwa sunyi masa yawa, ga kuma shirye shiryen tafiyarsu China shida Fahad sai ƙara matsowa take.
Sosai yau yake ƙara jin tsananin takaici da baƙin cikin rashin Fadwa a cikin gidan, dan ko babu komai mutum ma rahama ne, koda kuwa bazai yi maka aikin komai ba, idan kana jin motsinsa zaka dinga jin daɗi.
Ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yayi kamar yadda take bunne a zuciyarsa, amma Fadwa kam ta gama kaishi bango, kuma dole zai ɗauki mataki akanta.
Haka har ya gama kulle ƙofar ɗakin ya fita zuwa masallacin dake kusa dasu zuciyarsa tafasa take.
Koda aka idar da sallar magriban bai fito daga masallacin ba, har sai da aka kira isha'i yayi sannan ya fito riƙe da casbahansa a hannu ya nufo gidan, yayinda yake tasbihi a zuciyarsa.
A hankali ya shiga layin nasu wanda kuma yana shanyo kwana tun kafin ya kai ga isa ƙofar gidan ya hangi wata tsaleliyar farar mota fake a ƙofar gidan, cak ya tsaya daga ɗan nesa kaɗan yana kallon motar, yayinda a zuciyarsa kuwa mamaki yake da tambayar kansa, waye yazo yayi masa banzan parking haka ya rufe masa ƙofar gida ruf..? To ta ina zai shiga gidan kenan..?
Ganin an buɗe gidan baya ne an zuro ƙafa mai ɗauke da haɗaɗɗen takalmi mai tsini ana ƙoƙarin fitowa yasa da sauri ya ƙaraso gurin yana kallon wacce ke ƙoƙarin fitowar, wanda ta cikin motar itama take ƙare masa kallon tsaf, kafin kuma ta ƙarasa fitowa cike da gadara tana wani irin yatsine fuska a wulaƙance tana kallonsa.
Ganin yadda yake mata wani ƙasƙantaccen kallo ne yasa tasha jinin jikinta sosai, amma ta dake bata nuna ba, sai ma juyawa da tayi cike da yanga ta zura kanta cikin motar ta ɗauko jakarta da ɗan madaidaicin akwatinta sai wata ƙatuwar farar leda dake cike da tarkacen siyayyarta, kana ta matsa tana yiwa direban sai da safe, kafin kuma ta juya cikin takunta na isa da taƙama ta raɓa ta gefensa ta nufi cikin gidan.
Wanda yana ganin haka shima ya rufa mata baya da sauri yana faɗin "Karki sake ki shigan min ɗaki, kizo ki koma inda kika fito...."
Ya faɗa da kakkausar murya yana nuna mata ƙofar gidan.
Juyowa tayi tana watsa masa wani mugun kallo kafin tace "Kamar ya in zo in koma inda na fito, ban gane nufinka bane....?"
Ta faɗa cikin tsantsar rainin hankali tana watsa masa harara.
Bata gama rufe baki ba, ya sake daka mata wata uwar tsawar data gigitata lokaci ɗaya ta zaburar da ita, ta juyo da hanzari tana kallonsa, a fusace ya watsa mata wani ƙasƙantaccen kallo yana faɗin "Nace karki sake ki shigar min ɗaki, ki koma inda kika fito Fadwa bana buƙatar ganinki acikin gidana ki fita ki tafi...." Ya faɗa a zafafe yana nuna mata ƙofa.
Wani wulaƙantaccen kallo ta aika masa tana ƙara haɗe fuskarta kafin tace "Sai me dan ka hanani shiga wannan ruɓaɓɓen ɗakin naka, wanda babu komai a cikinsa sai tarkacen komatsai kamar zauren Almajirai, nace sai me AbdulAzeez...!?"
Ta faɗa tana huci haɗe da zafga masa harara, kafin kuma ta juya lokaci ɗaya tana ƙoƙarin tura ƙofar ɗakin.
Wani ɓacin rai ne mai tsananin zafi ya tokare zuciyar Ya Azeez, idanuwansa sun rufe gabaki ɗaya ko gani baya iya yi, a harzuƙe ya damƙota, sai ji tayi ƙiiiii ya jawota baya da ƙarfi ya fizgota kamar wata tsumma ya hankaɗeta tayo baya a tsorace tayi taga taga zata kifa, da sauri ta kama kyauren ƙofar ɗakin ta riƙe.
Cike da tsananin mamaki da al'ajabi take binsa da kallo kafin tace "Wai me yake damunka ne haka AbdulAzeez...?" Ta faɗa a tsorace tana binsa da kallo, bai kulata ba illa sake nuna mata ƙofa da yayi yana faɗin "Nace ki bar min gidana bana buƙatar ki a cikinsa, ki koma inda kika fito kije kici gaba da duk abinda kika ga dama babu abinda ya dameni..amma gidana kam kin bar ƙara ko kwana ɗaya ne a cikinsa, yau ba sai gobe ba zaki bar min gida ki kama gabanki..."
Baki kawai Fadwa ta buɗe galala tana kallonsa kafin ta saki tsaki tace "Toh wai sai me idan na bar gidan naka, sai kace wani gidan arziki daka damu mutane da abar maka gidanka, abar maka gidanka sai kace gidanka kona uban...."
Bata ƙarasa ba taji saukar wasu zafafan maruka har biyu masu azabar raɗaɗi da zugi Ya Azeez ya wanke fuskarta dasu dama da hagu, lokaci guda kamar gilmawar walƙiya haka taji saukar marukan akan fuskarta.
Wanda saboda tsabar azaba bata san lokacin data faɗi zaune a tsakar gidan ba ta dafe kumatunta dake mata mugun raɗaɗin azaba, tana bin Ya Azeez ɗin da kallo mai cike da tsantsar tsoro yayinda kuma hawaye ke shatata a fuskarta kamar an buɗe famfo.
_______________________
#Barkan mu da juma'a hajji babbar rana, Allah ya sadamu da dukkan alkhairin dake cikin wannan rana, ya kuma karemu ya kiyaye mu daga sharrin dake cikinta..
________________
*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
2️⃣8️⃣
Ko bi takan kukan da take bai yi ba, ya ƙara matsawa gabanta lokaci ɗaya yana nuna ta da yatsa yace "Wannan shine na farko kuma na ƙarshe Fadwa, duk abinda zakiyi karki sake gigin sako iyayena a ciki, kuma ko wace irin rashin kunya ce akanki ki dinga taunata kafin ki yarda ta fito daga bakinki kice zaki furtata, ni nan da kike gani ba lusarin namiji bane da zaki maidani shashasha mara tunani, duk abinda kikeyi ina sane kawai ƙyaleki nake yi, ba kuma wai dan ina tsoronki bane yasa nake ɗaga miki ƙafa kawai ina miki haka ne saboda darajar mahaifinki, amma ke kanki kin sani bayan shi baki da wani