Showing 21001 words to 24000 words out of 113443 words

Chapter 8 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7574

cika suka kunna, sai murna take bakinta yaƙi rufuwa.
Da rawar jiki ta ɓare sabon layinta na MTN data siya tun a kasuwa ta saka kana ta zaro tsohuwar wayarta ƙirar Aitel a cikin handbag ɗinta ta buɗe ta zare tsohon layinta na Airtel a ciki ta saka a sabuwar wayar, sai data jira layukan duka suka gama hawa kana ta kwalawa Rabi kira tazo ta miƙa mata tsohuwar wayar tace "Gashi nan kema sai kije ki gyara kya ƙarasa ta..."


Cike da murna kuwa ta ƙarba tana ta zuba godiya har da duƙawa lokaci ɗaya kamar zata kifa ƙasa saboda farin ciki, domin ta daɗe dama tana ƙaunar waya ƴar dangwale amma tsabar maƙo da son abun duniya ya hanata siya saboda bazata iya cire maƙudan kuɗaɗe ta siya waya ba, duk ko da irin kuɗaɗen da Hajiya Labiba take biyanta duk wata naira dubu talatin bata jin zata iya cire ko rabi ne ta siya waya, shiyasa take ta fama da ƴar ƙaramar nokia ɗinta mai touch light, amma yanzu tunda ta samu an bata zata iya ƙuru ta cire kuɗi ta bada a gyara mata.




Sai da komai na wayar ya gama saituwa kana nan take Hajiya Labiba ta ɗauki wayarta tai mata vtu transfer na dubu uku direct daga bankinta ta siyan mata data na wata ɗaya, ba ɓata lokaci ta buɗe mata Facebook da WhatsApp da Instagram dake dama duka tana yin abun ta tun kafin tayi aure.
Sai data gama yi mata saitin komai dan har a group ɗinsu na Isassun mata wanda nasu ne yasu yasu class mates ɗin juna waɗanda sukayi karatu tare, sai da ta yiwa admin ɗin magana kana ta maidata saboda dama tana ciki da aka buɗe mata sabon WhatsApp ɗin ne sai tayi left a group ɗin.


Komai na gama saituwa Hajiya Labiba ta miƙa mata wayar lokaci ɗaya tana faɗin "Barka My Ƙawa an dawo online..sai chat kuma, dama kowa sai tambayarki yake ina kika shiga kwana biyu ba'a ganinki a online....?"


Cikin sauri Fadwa ta gimtse fuskarta tana faɗin "Amma dai baki ce musu wayata ce ta lalace ba ko...dan kar su rainani...?"
Ta faɗa tana wani tsatstsareta da ido.


Tsareta da nata idanun itama Hajiya Labiban tayi tana kallonta kafin ta girgiza kai lokaci ɗaya tana faɗin "A'a ban gaya musu ba, kawai cewa nayi kin gaji da chatting din ne shiyasa kika daina hawa sai kin huta..."


Ta ƙarashe maganar da murmushi akan fuskarta tana kallonta, sai a lokacin Fadwa ta saki murmushin itama kafin tace "Ai dama nasan bazaki taɓa gaya musu ba saboda ke ƴar amanata ce, da dai waccan zaƙwai akuyar Zulai ɗin ce Lubna nasan tsaf zata gaya musu tace wayata ce ta lalace, ta zubar min da kima da mutuncina a gurinsu suji daɗin rainani...."


Kai tsaye Hajiya Labiba tace "Tsaf kuwa indai Lubna ce kaɗan daga aikinta ne wannan tsaf zata iya...."
Ta faɗa tana dariya, itama Fadwan dariyar tayi kafin daga haka suka ci gaba da hirar group ɗin nasu.






Suna nan zaune har ƙarfe 6pm. Ta buga amma Fadwa bata da niyyar tashi ta tafi gidanta, sai ma sake gyara zama da tayi ta cigaba da chatting din da suke a group tana kwasar dariyar labarin da wata ƙawarsu Azima ke basu akan mijinta, daga ƙarshe da abun yayi mata daɗi ma bata san har lokaci ya wuce haka ba, dan har an idar da sallar magriba duk bata sani ba.
Sai da Hajiya Labiba ta taɓa ta ta nuna mata lokaci a wayarta sannan ta farga ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi akan kujera tana jan tsaki lokaci ɗaya tana faɗin "Kai wallahi hirar tayi min daɗi sosai, shegiya Azima ashe itama haka ta iya tsiya...?"


Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara fashewa da dariya kafin ta sake ɗaukar wayar zata ci gaba da chatting ɗinta hankali kwance, fizge wayar Hajiya Labiba tayi a hannunta tana faɗin "Kin kuwa ga time Fadwa...fast 8pm fa yanzu..? Ya kamata gaskiya ki tashi kiyi shirin tafiya gidanki dan kila zuwa yanzu mijinki ya daɗe da dawowa ke kina nan...."




Cikin ɓacin rai da takaici Fadwa ta kalleta kafin ta miƙe ta ɗauki jakarta da gyalenta lokaci ɗaya tana faɗin "Wallahi na tsani takura a rayuwata, ba dan ba dan ba da babu abinda zai hanani kwana yau a gidan nan Allah na rantse..." Ta ƙarashe maganar tana jan tsaki.




Jinjina kai Hajiya Labiba tayi kafin tace "Kisha kuruminki ai wata rana dole zaki kwanan tunda gashi an kusa fara bikin ƙanwar Hajiya Lubna, kinga ai dole zai barki ki zo nan ki kwana biyu har sai an gama biki sannan ki koma gida..."


Cike da jin daɗi Fadwa ta washe baki tana faɗin "Allah ya kaimu ya nuna mana, ai wallahi ko bai amince ba sai na taho..."


Ta faɗa tana yin gaba yayinda Hajiya Labiba ta miƙe itama tabi bayanta don yi mata rakiya, dan yau bata jin zata samu damar kaita gida, saboda tasan mijinta yanzu haka yana kan hanyar dawowa gida tunda yau ma anan gidanta yake, kuma ita bata son duk abinda zai hanata bawa mijinta cikakkiyar kulawa ɗari bisa ɗari a kwanaki biyun da yake zuwa yana yi a gidanta, saboda ta sani tana da kishiya ba ita kaɗai bace shiyasa take kiyaye duk abinda zaisa ta shiga hakkin mijinta ballantana har ya hanata bashi kulawar da ta dace.




















*Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya🤲*
*WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*






9️⃣


Ƙarfe 9pm dai-dai mai keke napep ɗin daya ɗaukota daga gidan Hajiya Labiba ya sauketa a ƙofar gidanta bayan ta biyasa kuɗinsa ta juya ba tare da fargaban komai ba ta nufi gidan, tun kafin ta ƙarasa ta hango ƙofar gidan nata a buɗe an wangale ƙofar saɓanin a rufe da kwaɗo kamar yadda ta barshi ɗazu lokacin da zata fita, cike da mamaki ta ƙarasa bata ko bi ta kan tsohuwar mashin ɗin da ta gani fake a ƙofar gidan ba ta shige tana tambayar kanta ko dai ɓarayi ne suka shigo musu gida suka kwashe mata kaya, wannan tunanin daya bijiro mata ne yasa da sauri ta afka ta yaye labulen ɗakin kai tsaye kafin a fili ta furta "Aiko dana shiga uku na lalace..dan na gama yawo na tashi aiki...." Ta faɗa cikin tashin hankali tana zare ido.




Kamar daga sama ta jiyo muryar mahaifinta daga cikin ɗakin yana faɗin "Baki shiga uku ba tukunna Fadwa, tunda abinda kika zaɓarwa kanki kenan..."




Wani matsanancin faɗuwa gabanta yayi kafin da sauri ta saki labulen a tsorace tana dafe ƙirjinta cikin zaro ido tana faɗin "Na shiga ukuna...ashe Abba ne..to yaushe yazo gidan...?"




Daga cikin ɗakin ta sake jiyo muryarsa a karo na biyu cikin bada umarni yana faɗin "Shigo ciki..."


Ɗaga ƙafarta tayi cikin sanyin jiki ta fara ja da baya da baya tana dafe bakinta lokaci ɗaya tana girgiza kanta kafin ta juya da sauri jiki na rawa zata fice daga gidan, dan tabbas in da tasan cewa mahaifinta yana cikin gidan da babu abinda zai sata tayi sha'awar shigowa sai dai tayi ta tsayuwarta a waje har ya gama zamansa ya fito ya tafi, dan tafi kowa sanin halinsa kaɗan ne daga cikin aikinsa ya zage ya gurjeta yay mata shegen duka kuma babu mai iya ƙwatarta a hannunsa.




Ji tayi an fizgota ta baya da mugun ƙarfi an wancakalar da ita gefe guda, a zafafe ta ɗago tana huci lokaci ɗaya tana ƙoƙarin miƙewa, ganinsa tsaye a kanta yana watsa mata wani irin mugun kallo ne yasa ta zabura da sauri ta miƙe tsaye tana aika mai da wani banzan kallo sama da ƙasa kafin cike da masifa tace "Wannan wane irin iskanci ne da wulaƙanci da zaka wani fizgoni ka watsar dani sai kace wata mage...wannan ai tsabar mugunta ce da mugun hali salon kaje ka karya ni ka illata ni ka kashe min rayuwa tunda baka da asara ai...."




Marin da aka ɗauketa dashi ne ya hanata ƙarasa maganar da tayi niyyar faɗa, da sauri ta dafe kuncinta ta ɗago tana kallonsa, kafin ta farga idanunta ya gama buɗewa ta samu gano wanda ya maretan ta sake jin saukar wani zazzafan marin wanda har yafi na farkon azaba haɗe da raɗaɗi a karo na biyu.


Matsawa baya tayi da sauri tana sosa kumatunta da yayi mata wani irin cik saboda mugun shigarta da marukan sukayi, kafin ta duƙe a gurin cikin rawar jiki har lokacin kuma tana tallabe da kumatunta dake mata mugun raɗaɗi sakamakon marin da mahaifin nata yayi mata wanda yasa gaba ɗaya fuskarta ta ɗauki zugin azaba.




Kyakkyawan farin Dattijo ne da shekarunsa a ƙalla zasu iya kaiwa 65 tsaye a gefen Ya Azeez fuskarsa ɗauke da matsanancin ɓacin rai yake dubanta kafin ya juya yana duban Ya Azeez wanda ya duƙar da kansa, cikin nutsatstsiyar muryarsa mai cike da tarin kamala da dattako haɗe da ɓacin rai yace "Kana tsaye kana kallonta take gaggaya maka irin waɗannan maganganun amma ka kasa yi mata komai...? Wannan wace irin zuciya ce gareka da bazata iya baka shawarar hukunta iyalinka idan tayi maka ba dai-dai ba...? Kenan nufinka kafi son ta cigaba da duk abinda takeso kana kallonta ko...?"


Ya faɗa yana tsaresa da ido, da sauri ya girgiza kansa yana faɗin "A'a Abba ba haka bane...."




"To idan ba haka bane yaya ne....?" Ya faɗa yana ƙara kafesa da idanu.


Rusunawa yayi cike da girmamawa kafin yace "Wallahi Abba ina mata faɗa sosai idan naga tayi ba dai-dai ba kum...."


Saurin katsesa yayi da faɗin "Kana mata faɗa idan kaga tayi ba dai-dai ba amma kuma take cigaba da aikata ba dai-dai ba ɗin...baka tunanin cewa har yanzun baka mata irin hukuncin daya dace da irin laifin da take aikatawa bane....?"


Ƙwarjinin dattijon ne yasa ya kasa magana kawai ya duƙar da kansa ƙasa yana kallon Fadwa wacce ta takure a guri guda ta matse kafafunta tana matsar ƙwalla.




Wata uwar tsawa ya buga mata wacce tasa jikinta ya sake ɗaukar rawa da kakkarwa ta zaburo babu shiri ta matso gabansa da rarrafe cikin rawar murya take faɗin "Ab..ba...dan Allah kayi hakuri wallahi tallahi bazan sake ba...dan girman Allah wallahi daga yau zan dinga jin maganar Ya Azeez na rantse da Allah bazan sake fita ko nan da can ba sai da izininsa...."


Ta ƙarashe faɗa cikin rawar jiki tana matsar ƙwalla.


Wani murmushin takaici kawai Ya Azeez ya saki kafin ya kaɗa kai a zuciyarsa kuwa cewa yayi zaki gane baki da wayau ne yarinya ba dai kince bakya jin magana ba, zamu zuba nida ke aga wanda zai ci riba.


Fadwa kuwa sosai take shassheƙar kuka tana matsar ƙwalla kamar gaske, shi dai Ya Azeez kawai girgiza kansa yake yana kallonta, dan yasan babu wani kukan da take kawai tsabar bariki ce da iya kwarewa a munafunci yasa take haka.




Shi kuwa Malam Jabir kallon Fadwa wacce ke zube a gabansa tana kuka yayi kafin ya ɗauke kansa lokaci ɗaya yana kallon Ya Azeez wanda ya duƙar da kansa yana faɗin "Ayi mata haƙuri Abba...insha Allahu bazata sake ba...."




Cike da ɓacin rai yake dubanta kafin yace "Daga yau idan ta sake fita ko nan da ƙofar gida ne bada izininka ba ka kirani, kuma duk wasu abubuwa da take maka marasa kyau idan har bata daina ba ta cigaba ka gaya min, ni kuma zanyi maganinta tunda ita tace faɗa baya taɓa yi mata to ni nasan ta yadda zan bi da ita...." Yana ƙarashe maganar ya juya ba tare da ya sake ko bi ta kanta ba ya tsallaketa ya fice daga gidan yayinda Ya Azeez ya rufa masa baya da sauri don yi masa rakiya.




Sai data jiyo ƙarar tashin mashin ɗinsa kafin ta iya lallaɓawa ta miƙe a hankali tana sake dafe fuskarta da har lokacin take mata mugun raɗaɗin azaba ta ɗauki jakar handbag ɗinta dake yashe a ƙasa ta zuge da sauri ta fito da sabuwar wayarta da take cike da fargabar ko ta fashe sakamakon cillar da jakar da tayi lokacin da taji shigar marin da Abbanta ya ɗauketa dashi. Sai data duba taga babu abinda ya samu wayar sannan ta kaɗa kai ta maida ita cikin jakar ta koma ta jingina da ƙofar ɗakin nata tana sauke numfashi haɗe da ajiyar zuciya.


Tana nan a zaune ya shigo bayan ya kulle ƙofar gidan ya saka sakata ya ƙaraso gabanta ya tsaya tare da zuba hannuwansa duka cikin aljihun wandon jeans ɗin da yake jikinsa ya zuba mata ido yana ƙare mata kallo, a hankali ta ɗago kai tana dubansa kafin ta sakar masa harara cike da jin haushinsa kana ta fara ƙoƙarin miƙewa, saurin ɗagota yayi cike da mugunta ya haɗeta da faffaɗan ƙirjinsa ya fara kissing ɗin wuyanta zuwan cikin kunnenta.


Fizge jikinta tayi da sauri ta matsa gefe tana zafga masa harara, ɗan ɗaga kafaɗarsa yayi alamar ko a jikinsa, kana ya tsura mata idanu yana kallonta ta cikin ɗan hasken wutar solar daya hasko cikin gidan nasu kafin ya miƙa hannunsa cikin tamke fuska ya fincikota ta ƙara faɗowa jikinsa ya haɗeta da ƙirjinsa lokaci ɗaya ya ɗago fuskarta yana kallon cikin ƙwayar idanunta dake cike da ruwan hawaye ya sakar mata wani kyakkyawan murmushi wanda bashi da maraba dana mugunta.


Cike da jin haushinsa ta galla masa harara, amma ko a jikinsa sai ma ya kashe mata idonsa ɗaya yana ci gaba da yi mata murmushin.


A ranta tace "Mugu kawai dole kayi min dariya mana tunda ka haɗa min munafunci kasa an mareni..."


Kamar yaji abinda tace kuwa ya ɗago yana tureta daga jikinsa ya yatsine fuskarsa lokaci ɗaya yana faɗin "Ya mukayi dake ɗazu da safe kafin in fita...me nace dake....?"
Ya faɗa lokaci ɗaya yana tsareta da idanuwansa.


Wani banzan kallo ta watsa mai kafin ta ɗauke kai tana faɗin "Na manta...." Ta faɗa kai tsaye ba tare da fargabar komai ba.


Murmushi yayi kafin yace "To naji wuce kije kiyi sallah dan nasan da wuya idan kinyi daga can inda kike, tunda ko a gidan ne ma dole sai an matsa miki sannan kike yi..acan kuwa ai babu mai matsa miki tunda duk shegiyar ɗarin ce..." Ya ƙarashe maganar yana wucewa ya shige cikin ɗaki ya barta nan tsaye a gurin tana binsa da wata ƙatuwar harara kamar idanunta zasu faɗo ƙasa.




Ta daɗe a tsaye tana saƙa maganganun Abbanta a zuciyarta kafin ta saki ƙaramin tsaki ta shige ɗakin tana ƙunƙunai, zaune a falo ta iskesa yana danne danne a ƴar wayarsa, ba tare data kallesa ba ta wuce ta shige uwar ɗaka sai data fara cire kayan jikinta ta ɗaura zani a ƙirjinta sannan ta ɗebi ruwa a bokiti ta ɗauki kwandon soso ta fita. Har ta cire zaninta ta sagale a jikin katanga ta tsugunna zata fara wankan, ta tuna da jakarta data bro akan gado, aiko da sauri ta rarumi zaninta ta sake ɗaurawa ta fito da gudu.


Yana nan zaune a inda ta barshi yaga ta afko cikin ɗakin da gudu tana haki kamar wacce aka koro, a tsorace ya ɗago kai yana kallonta dan har ga Allah ta bashi tsoro, itako kota kansa bata bi ba ta wuce cikin uwar ɗakan, sai data ɗauke jakarta ta ɓoye a cikin kayanta sannan ta fito ta sake ficewa, shi dai binta kawai yake da ido lokaci ɗaya yana girgiza kansa har ta fice kafin ya ɗauke kansa ya maida kan wayarsa ya cigaba da abinda yake yi.




Yana cikin waya da Ummansa ta shigo ɗakin da bokiti ta ajiye kana ta ɗauki buta ta sake fita, koda ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin ta iske still dai yana kan waya da Umman tasa suna ta hira, haka tazo ta sake wucewa ta gabansa taje ta ajiye butar. Tana cikin shafa mai ya shigo da wayar a hannunsa ya miƙa mata lokaci ɗaya yana faɗin "Gashi ku gaisa Umma ce..."


Banza tayi dashi ta miƙe ta raɓa ta gefensa ta wuce ta ƙarasa gurin akwatinta ta buɗe ta fara ƙoƙarin ɗauko kaya, matsawa yayi gabanta ya sake miƙa mata wayar yana faɗin "Ƙarɓa mana Fadwa Ummana ce fa..."


A zafafe ta ɗago kai tana watsa masa kallon banza kafin tace "To don Umman cefa...uwata ce ko kuwa dole ne akace sai na gaisa da itan...?" Ta faɗa cikin nuna zallar rashin mutunci da rashin kunya.
Bai damu ba yace "Amma ai Ummana tamkar uwa take a gareki ko..kuma dan nace ku gaisa ai naga ba aibu bane tunda kema mahaifiyarki ce...?"


Hayayyaƙo masa tayi cike da fitsara take faɗin "Allah ya kyauta min wallahi ni ba mahaifiyata bace babu abinda na haɗa da ita, mahaifiyata tana nan a inda take amma ni bana kalar uwar wasu ince mata tawa haka kawai saboda shisshigi...gaisawa ne dai kuma nace bazan gaisa da itan ba dan ba'a dole dan haka sai a kauce a bani guri..."


Jin tijara takeson yi masa ne yasa da sauri ya maza ya kashe wayar dan kar mahaifiyar tasa taji abinda take faɗi, saboda ko kaɗan baya buƙatar tasan irin zamantakewar auren da suke gudanarwa a tsakaninsu.


Fadwa kuwa tsaki ta saki kafin ta ɗauki kayan baccinta ta matsa gefe ta fara ƙoƙarin sakawa, tsayawa kawai yayi galala yana kallonta ta zura rigar wanda ya kasance doguwar rigar bacci ce irin mai kaurin nan kana ta ɗauki hijabi ta saka ta zari darduma ta shimfiɗa shi dai kawai binta da ido yake, sai da yaga ta tada sallah sannan yaja ƴan ƙafafuwansa a sanyaye ya fice ya koma falo ya zauna ya dafe kansa yana tunanin matakin da ya kamata ya ɗauka akan Fadwa.
Dan har ga Allah ba zai taɓa iya haƙuri ya zuba mata ido yana kallo ta raina mahaifiyarsa ba, zai iya jurewa ya ɗauki komai nata indai zai tsaya a iya kansa ne, amma baya jin zai iya daurewa ya ɗauki raininta akan Ummansa, domin gaskiya bashi da wannan haƙurin kuma baya jin zai iya samunsa indai akan mahaifiyarsa ne domin bai da wanda ya kaita duk faɗin duniyar nan saboda haka bai haɗata da kowa ba kuma baya jin zai iya haɗa matsayinta da kowa, balle har ya bari wani ya nemi taka masa ita ko waye shi kuwa kuma komai matsayinsa a duniya.




Motsinta daya jiyo daga cikin ɗakin ne yasa ya miƙe da sauri ya faɗa ɗakin tana tsaye a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login