Showing 51001 words to 54000 words out of 113443 words

Chapter 18 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7556

aiki shi kaɗai yana faman ɓaɓatu, a gajiye Shatu ta ƙaraso kan ɗaya daga cikin kujerun da suka yiwa katafaren falon nasu ƙawanya ta zauna tana faɗin "Wash Allahna..wallahi duk gaɓoɓina ciwo suke, jikina kamar an min dukan tsiya haka nake ji, Zahra pls jeki dauƙo min ruwa mai sanyi a fridge in ɗan sha, sai mu haura sama gurin Ummi..." Amsawa tayi da "Toh..." Kana ta wuce taje ta ɗauko mata ruwamai sanyi haɗe da kofi ta kawo mata, kaɗan ta tsiyaya ta sha ta ajiye sauran kana ta miƙe ta zari jakarta tayi gaba Zahra ta biyota suka haura sama har zuwa falon Umminsu dake can.


Wani tafkeken haɗaɗɗen falo ne nan ma wanda har yaso yafi na farkon da suka baro kyau da tsaruwa, suna shiga wata hamshaƙiyar mace kyakkyawa ajin ƙarshe a cikin manyan mata ta fito daga wani ɗaki da faskekiyar waya riƙe a hannunta tana latsawa, jikinta sanye cikin wani tsadadden leshinta wanda aka yiwa ɗinkin Abuja bubu taci ɗaurin ɗankwalinta wanda ya ƙara fito da tsantsar hutu da haibarta ga wasu uban gwala gwalai datayi ado dasu a jikinta sai walwali take da ɗaukar ido tana sheƙi, sai dai a kallo ɗaya idan kayi mata zaka hango tsantsar kamaninta da Shatu kamar an tsaga kara babu inda ta barta, dan hatta da yanayin tsarin dirin jikin Shatun da yanayin tafiyarta sak irin na mahifiyar tata ne sai ɗan banbancin abinda ba'a rasa ba, tsaye kawai sukai a tsakiyar falon gaba ɗayansu suka zubo mata idanu, a hankali ta fara saukowa cikin falon lokaci ɗaya tana washe baki cike da fara'a take faɗin "Oyooyo My lovely daughters Oyooyo barkanku da zuwa you are welcome...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙarasa saukowa daga saman benen cikin natsuwa ta ƙaraso gabansu lokaci ɗaya ta jawosu jikinta ta rungume tana shafa bayansu cike da murnar ganinsu tana faɗin "Alhamdulillahi tafiya tayi riba ƴan mata Ummi sun dawo gida cikin ƙoshin lafiya barkanku da dawowa...."
Murmushi Zahra ta saki kafin tace "Thanks my Ummina...." Ta faɗa itama tana ƙara rungumeta, kafin ta ɗan janye jikinta a nata lokaci ɗaya tana duban Shatu data wani kwaɓe fuska cike da shagwaɓa ta matsa daga kusa dasu tayi can gefe tana turo baki tace "Ummi kishin mutuniyar taki fa ya motsa...ji yadda aka wani ja gefe ana turo mana baki kamar zai taɓo bango, da alamar dai nan fushi akayi mana bamu sani ba..." Ta ƙarashe maganar cike da tsokana lokaci ɗaya tana nuna Shatun da bakinta tana ƴar dariya.


A hankali Shatun ta ɗago kai ta watsa mata harara kana ta ƙarasa gaban mahaifiyar tasu ta rusuna a gabanta ta kamo hannayenta tana ɗan murzawa a hankali a hankali kana cikin murya ƙasa ƙasa tace "Ummi kina can kina ta autarki ni kam kinyi banza dani a gefe kuma nayi missing ɗinku keda Abbie na..amma na dawo kuma baki kulani ba sai ta autarki kawai kike..." Ta faɗa a shagwaɓe tana hararar Zahra da tunda ta fara maganar ta riƙe baki kawai tana kallonta a ranta kuwa faɗi take "Kai Allah ya yayewa Aunty Shatu wannan mugun kishin nata...ita kenan komai sai tayi complain ɗinsa abinda bai kai ya kawo ba sai ta nuna tana kishi akansa, anya kuwa zata iya auren mai mata ta zauna dashi...?" Ta faɗa a ƙasan ranta kafin kuma ta fashe da dariya a fili tana cewa "Tabɗi aiko akwai aiki ja agabanki...Ummi kiji mai hali..lallai gaskiyar hausawa ne da suke cewa mai hali baya taɓa fasa halinsa kiga daga dawowa dai har ta fara kawo ƙorafi, wallahi har kinsa na fara tausayawa mijin da zai aureki indai yana da mata dan babu halin ya raɓi matarsa kenan sai kin nuna halinki, wannan ai bazaki bar gidansa ya zauna lafiya ba dan ba zai taɓa yin adalci a tsakaninku ba..."


Shatu da tunda ta fara maganar take kallonta a fusace ta miƙe tayo kanta gadan gadan tana faɗin "Ummi kiji mugun bakin da yarinyar nan take min agabanki wai zan auri mai mata...wai nice zan zauna da kishiya...Ummi dan Allah kiji min wani mugun fata fa da take min..." Ta ƙarashe maganar a shagwaɓe tana zumɓuro ɗan ƙaramin bakinta lokaci ɗaya tana ƙoƙarin fizgo Zahra data maƙalƙale a bayan Ummin ta ruƙunƙumeta suna mata dariya.


Cikin ƙulewa Shatu tace "Ummi kema harda tayata kuna min dariya ko..kenan kema fatan in auri mai matan kike min....?" Ta faɗa cikin rawar murya kamar zatayi kuka, sake kwashewa sukayi da dariya ta ƙara ƙulewa a fusace ta juya zata wuce da sauri Ummi ta riƙo hannunta tana ƙoƙarin danne dariyarta take faɗin "Haba mana ƴan matan Ummin ta meye na fushin kuma...ni yaushe kikaji nace zaki auri mai mata har ki zauna da kishiya...?" Ta faɗa tare da jawota jikinta ta rungumeta tana shafa bayanta alamar lallashi tana cewa "Ƙyale autar Ummi kinji, ki kwantar da hankalinki insha Allahu da ke kaɗai mijinki zai zauna ba zai taɓa haɗaki da kowacce mace ba, amma banaso kikesa hakan aranki har abun yazo yayi tasiri a zuciyarki...nafi son ki barwa Allah yinsa kawai komai yayi akanki shine dai-dai kinji ƴan matana..ki daina nuna zaɓinki akoda yaushe kice ke dole dole sai lallai abinda kikeso kuma kike buri shi Allah zai baki, ki sani shi fa Allah ba'ayi masa dole, ki bar masa komai shi kaɗai yasan irin tanadin alkhairin da yayi ma rayuwarki kinji...?" Ta ƙarashe maganar cikin lallashi da lalama lokaci ɗaya tana share mata hawayen da suka fara zubowa kan fuskarta, a hankali ta gyaɗa mata kai cikin sanyi jiki kana tace "Insha Allahu Ummi na daina bazan sake ba...."
Da sauri Zahra ta kaɗa kai tace "Yauwa gara dai ki daina ɗin ko Ummi tunda babu kyau kuma bakisan wanene mijinki ba....? Ƙila ma mai mata uku ne kece zakije a ta huɗu...."


Wata dariya ce ta kubcewa Ummi lokaci ɗaya tana riƙe hannun Shatu data kawowa Zahra duka a gefen kafaɗarta ta janyeta da sauri tare da turata baya tana cewa "Ki gudu nidai babu ruwana idan ta kamaki tunda ban ce ki tsokaneta ba...." Ta faɗa tare da kamo hannun Zahran ta nuna mata saman bene alamar ta gudu kar Shatu ta kamata, aiko da sauri Zahra ta tattare siket ɗin jikinta taja shi sama kana ta juya a guje ta fara haurawa matattakalar benen da gudu ta haye tare da yiwa Shatu dake bin ta da kallo gwalo tana faɗin "Kina taɓani wallahi saina gayawa Abbie ince kin samu miji a Kaduna kuma...." Maganarta ce ta katse lokacin da taga Shatun tayo kanta cikin fushi tana faɗin "Bari in taɓakin sai kiji daɗin faɗa masa ɗin dan ubanki...." Ta faɗa lokaci ɗaya tana haurawa saman da sauri itama, ko kafin ta ƙarasa gareta tuni Zahra ta buɗe wani ɗakin dake kusa da ita ta faɗa ciki da sauri ta mayar da ƙofar ta rufe tana sauke numfashi.


Ƙwaffa Shatu tayi, kafin cikin ƙufula ta sauko daga saman benen tana kumbura fuska ita a dole an ɓata mata rai.


Ummi dake tsaye har lokacin tana kallon diramar tasu ta kamo hannunta tana dariya take faɗin "Haba mana ƴan matan Umminta inda sabo ai yaci ace zuwa yanzu kin gama sabawa da halin tsokanar Zahra, amma ke kullum sai ki dinga biye mata ku dinga abu sai kace wasu ƴan ƙanana yara...? Idan fa kikaci gaba da biyewa halin Zahra wata rana koda kinyi aure idan ta kai miki ziyara gidanki haka zata dinga miki, dan sai tasan yadda tayi ta tsokaneki kika biye mata kuka raba hali har a gaban mijinki ita babu ruwanta, dan haka ki daina kinji ƴan matana....?"


Shatu ta kaɗa kai ba tare da tace mata komai ba, hakan yasa Ummi ta ƙara kamota tana faɗin "Haba to ki ɗan saki fuskar taki mana tunda ya wuce ai bazata ƙara ba, yanzu kije ki watsa ruwa a jikinki kiyi sallah sannan saiki sauko kizo kuci abinci, dan nasan ma da wuya idan kun karya kuka kamo hanya..."
Da To Shatu ta amsa mata still tana kumbura baki, kana ta wuce ta haura sama zuwa ɗakinsu, yayinda ita kuma Ummin ta juya ta shige kichin ɗinsu dake cikin falon domin ta haɗo musu abincin kafin su gama shiryawa su sauko.






*******




Misalin ƙarfe 4pm. Ya Azeez ne zaune a cikin keke napep ɗinsa dake fake a gaban wani masallaci, wanda fitowarsa daga cikin masallacin kenan inda ya gabatar da sallar la'asar ya daɗe a zaune shiru gabaki ɗaya ya rasa meke yi masa daɗi kasancewar tun ɗazu da ya baro tasha inda ya kai su Shatu suka shiga motar Kano, ya dawo gabaki ɗaya ya kasa natsuwa zuciyarsa kwata kwata ta hanasa sukuni sai faman hasaso masa wasu manyan abubuwa masu matuƙar jan hankali take a game da ita, a hankali ya sauke ajiyar zuciya cikin son kawar da tunaninta a zuciyarsa ya zaro makulli a cikin aljihunsa ya tada napep ɗin yana ƙoƙarin ja kenan wayarsa dake cikin aljihun gaban rigarsa ta ɗauki ƙara, zaro ta yayi daga cikin aljihun yana duba mai kiran numbern Fadwa ce ya gani wacce yayi saving ɗinta da MY FADWA.
Shiru yayi yana bin wayar da kallo dan haka kawai da yaga kiran nata ya tsinci kansa da samun mummunar faɗuwar gaba, da kamar ba zai ɗauka ba amma sai yayi wani tunani ya saki murmushin takaici kana ya ɗaga kiran ya kara wayar a kunnensa yayi shiru ba tare da yayi magana ba.




Daga can ɓangaren Fadwa kuwa tana gefe cikin babban filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe International Airport dake Abuja, wanda saukarsu kenan ita da gogaggun ƙawayenta da wasu manyan mata masu faɗa aji tana tsaye a jikin wata doguwar mota baƙa wuluk ƙirar Lemoxin sabuwa dal mai kyau sai ɗaukar ido take irinna sabunta, sanye take da doguwar riga na wani arnen leshi mai kyau da tsada kalar baƙi sai head ɗin kanta kuma golding color fuskar nan taci uban make-up sai kace wata amarya.
Jin ya ɗaga wayar amma yayi shiru yaƙi magana, yasa ta ƙufula cikin ƙosawa tace "Ka ɗaga wayar amma shine kayi shiru saboda ga mai kuɗin banza ta kiraka ko...?"


Ta faɗa tana hararar wayar kamar tana kallonsa, shiru yayi yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa kafin yace "Ai kece kika kirani bani na kiraki ba, saboda haka kece ya kamata ki fara faɗin abinda ke ranki tunda bansan dalilin kiran naki ba...."


Haɗe rai tayi tai kicin kicin da fuska tace "Nidai bana kiraka dan inji ƙorafinka bane dama na kiraka ne kawai dan in sanar da kai cewa mun tafi Abuja kai amarya dan haka koda ka koma gida karkace zaka tsaya jiran dawowata inzo in buɗe maka ƙofa na bar maka ita a buɗe kawai kana zuwa ka shige abinka ka kulle karka tsaya jirana, dan ban san ranar dawowata ba domin anan ɗin ma wani sabon bikin yau za'a fara kuma sai nan da kwana uku za'a gama sannan idan muka kai amarya gidanta Asokoro washegari sai mu kamo hanya mu dawo gida, saboda haka sai nan da kwana huɗu ko biyar zan dawo..."


Cikin baƙin ciki da ɓacin rai yace "Kin kuwa san abinda kike faɗi Fadwa...Abuja fa kike gaya min kin tafi kai amarya ba tare da sanina ba...?"


Ƙaramar dariya ta saki kafin tace "Oh daman kai duk a naka haukan ɗauka kake dole sai da saninka sannan zan fita inje duk inda zanje...tabɗi ashe bani da ƴancin fita inda naso naga dama kenan sai da yardarka...?"
Bata bashi damar magana ba ta cigaba da faɗin "To idan ɗaukar hakan kake kayi maza ka sauke dan ni ba irin matan nan bane marasa sanin ciwon kansu waɗanda suke zaman rashin ƴanci a gidajensu ba..nidai Allah ya sani na fita hakkinka tunda na gaya maka nayi tafiya kuma na gaya maka inda naje dan haka sai na dawo...." Daga haka ta yanke kiran tana sakin wani ƙaton tsaki tace "Matsiyaci kawai faƙirin banza...." Ta faɗa tana jefa wayarta cikin jaka bayan ta kasheta gaba ɗaya dan ma kar yayi tunanin sake kiranta ya dameta.




























*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*








2️⃣1️⃣






Wani ƙatoton abu ne mai tsananin baƙin ciki da ɓacin rai Ya Azeez yaji yana taso masa tun daga ƙasan zuciyarsa ya tsaya masa cak a maƙogoro ya kasa wucewa, wayar yabi da kallo cikin sanyin jiki da mamaki kafin ya soma jujjuyata a hannunsa yana sakin ajiyar zuciya.


Tabbas sai yau ne ya sake tabbatar da cewa Fadwa ta gama rainasa, ta maidashi banza wofi mara amfani wanda bai san ciwon kansa da abinda yake damunsa ba.
Amma tabbas kam a wannan karon an kawo dai-dai inda ba zai iya haƙuri ba dole sai ya ɗauki mataki akanta, saboda ya gaji da waɗannan mugayen halayen nata domin Allah ma ya sani kuma ya gani yayi iya bakin ƙoƙarinsa a kanta dan ta gyaru amma bata gyarun ba, dan haka anzo dai-dai gaɓar da dole zai san abun yi domin ba zai taɓa yarda haka kawai ya zuba mata ido ta maidashi wani lusarin namiji mara iko da isa da gidansa ba.
Kunna napep ɗin yayi ya tada kana yaja ya soma tafiya a hankali a hankali cikin sanyin jiki yana ƙara nanata maganganun da Fadwan ta gaya masa a zuciyarsa yana ƙoƙarin bawa kansa haƙuri.
A haka da wannan tunanin ya ƙarasa gidan Ummansa, koda yaje sai bai nuna mata komai ba ya saki jikinsa ya zauna sukai ta hira da ita kamar babu abinda ke damunsa.
Nan ko zuciyarsa danƙare take taf da baƙin cikin abinda Fadwa tayi masa, nan yai ta zaune har bayan sallar Isha'i suna tare da Ummansa da ƙanwarsa Imaan suna ta hira abun su gwanin sha'awa, Umma ta gama girkin dare ta zubo masa yaci ya ƙoshi kana ya tashi yayi musu sallama ya fita ya ɗauki keke napep ɗinsa ya wuce ya nufi gida.








*******




*KANO*




Lafiyayyen ɗaki ne mai bala'in kyau wanda za'a iya kiransa da aljannar duniya, an ƙayatashi da duk wasu abubuwa na ƙayata ɗaki dan more rayuwar duniya da jin daɗin ya'yan gata, ga wata luntsumemiyar doguwar kujerar sofa mai shegen laushi da taushi dake tsakiyar ɗakin, sai ga kuma wani ƙaton Royal bed dake ɗauke da shimfiɗa na wani lallausan zanin gado na alfarma mai kamar bargo ɗaya ƙarawa ɗakin haske da kyau, ga kuma wani sanyin Ac mai haɗe da ƙamshin daddaɗan turaren wuta dake tashi kaɗan kaɗan a cikin ɗakin.


Shatu ce tsaye a gaban tangamemen madubin dake ɗakin, wanda da alama fitowarta daga wanka kenan tana ɗaure da wani ɗan madaidaicin ƙaramin tawul kalar pink a jikinta wanda yake ɗan ɓingil dashi dan ko gama rufe cinyoyinta bai yi ba, sai wani ƙarami dake riƙe a hannunta tana goge ruwan fuskarta dashi, a hankali take ƙarewa kanta kallo ta cikin tangamemen madubin dake jingine da bangon ɗakin wanda ke shaƙe da tsadaddun kayan kwalliyarta da kalolin turarukanta masu tsananin tsada sai wasu manya manyan kwalaben turarukan humra dake jere a gefe cikin wani ɗan madaidaicin show gilas, a hankali ta janyo kujerar gaban madubin ta zauna lokaci ɗaya tana ɗan zame tawul ɗin dake jikinta ta ɗan jashi sama kaɗan wanda hakan ya bawa santala santalan fararen cinyoyinta dake sheƙi da ɗaukar ido damar bayyana.
A hankali ta miƙa hannu gaban madubin ta ɗauko robar tsadadden lotion ɗinta Makari ta buɗe ta tsiyaya a tafin hannunta ta murza kafin a nutse ta soma shafawa lallausar fatar jikinta cikin wani irin salɓi da yanga, ta ɗauki kusan mituna ashirin tana shafa man a jikinta kafin ta gama ta mayar ta ajiye kana ta ɗauko turaren body spray ɗinta na Smart Black ta fashe ilahirin jikinta dashi, kana ta ɗauki turarukan arabian oud ɗinta kala daban daban ta goga a kowanne lungu da saƙo na jikinta.
Cikin lokaci ƙalilan kuwa ɗakin ya ƙara ɗaukar wani sassanyan ƙamshi mai tsananin daɗi da sanyaya rai.


Bayan ta gama fesa turaren ne, ta ɗauki lipgloss ta ɗan goga a lallausan pink lips ɗinta wanda suke nan sirara dasu masu ɗan faɗi kaɗan, sai suka ƙara fitar da tsantsar kyaun fuskarta sosai.
Miƙewa tayi daga kan kujerar ta wuce ta ƙarasa gaban wani kafcecen wardrobe ɗinta daya kusan mamaye rabin bangon ɗakin ta buɗe, kaya ne kala kala jere reras a ciki, kama daga kan less, atamfa, materials, shadda, english wears da dogayen riguna haɗaɗɗu irin na larabawa da na turawa suma kaloli daban daban kowanne da ɓangarensa, a hankali ta shiga duba ɓangaren inda dogayen rigunanta suke, tsayawa tayi shiru tana ƙarewa jerin kayan dake cikin wardrobe ɗin kallo kafin ta miƙa hannu ta zaro wata tsaleliyar doguwar rigarta mai kyau ƙirar Armani kalar ja ta saka, kana ta naɗe kanta da ɗan ƙaramin mayafin rigar, ta sake feshe jikinta da turare kana ta ɗauki wayarta dake aje kan bedside drower ta zura bedroom silifas ɗinta ta fice daga ɗakin lokaci ɗaya tana duba agogon dake jikin wayarta, ƙarfe 7pm dai-dai ta gani da sauri ta ƙarasa sauka daga matattakalar benen ta nufi cikin falon inda take jiyo muryar Zahra, wacce gaba ɗaya surutanta ya cika falon sai karaɗi take tana zuba labari kamar an kunna tsohuwar radio.


Ƙarasawa tayi cikin falon bakinta ɗauke da sallama, wani farin dattijo ne kyakkyawa wanda a ƙalla shekarunsa zasu iya kaiwa 62 zaune saman ɗaya daga cikin manyan luntsuma luntsuman kujerun da suka yiwa katafaren falon nasu ƙawanya, jikinsa sanye cikin shigar tsadaddiyar shaddar gizner fara ƙal wacce aka zubawa uban aiki irin na manyan ƴan kasuwar dake garin Kano, wanda ya ƙara fito da haiba da kwarjininsa na musamman daya cika falon.
Alhaji Bello Ɗan Ƙwarai kenan kamilin mutum mai cikar zati da kamala mai fara'a da son mutane, ga dattako da son taimakon na ƙasa dashi.


Sallamarta ce tasa Zahra yin tsit kamar anyi ruwa an ɗauke ta fara zare ido, ita ko Shatu ko kallon ɓarayin da take ma ba tayi ba ta tsallaketa ta isa gabansa cikin murna da ɗokin ganinsa ta duƙa kusa dashi tana faɗin "Abbie ashe ka dawo tun ɗazu shine ba'a gaya min ba...?" Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login