Showing 57001 words to 60000 words out of 113443 words

Chapter 20 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7549

abincinsu, Zahra kuwa murmushi kawai tayi ta ci gaba da danna abincinta dan ita dama bata taɓa wasa da cikinta ko a ina ne zagewa take ta ci abincinta hankali kwance babu abinda ya dameta. Ganin yadda ta zage take cin abincin ne yasa Shatu da Ummi haɗa idanu suka yi murmushi, yayinda ita kuwa Zahra ko ajikinta bata san suna yi ba, aikawa cikinta abinci kawai take tare da korawa da sassanyan juice.


Shatu kuwa ko data kammala cin abincin wanda ko rabi bata ci ba, ture filet ɗin tayi ta matsar gefe kana ta miƙe tsaye ta ɗauki wayarta dake aje kan dinning ɗin, kafin ta yagi tissue ta goge bakinta, kana ta juya ta kalli Zahra dake riƙe da wani kofin gilas a hannunta tana shan juice tace "To nidai na kammala saura ke kiyi ki ƙarasa mu tafi..."


Ta ƙarashe maganar tare da ficewa daga dinning area ɗin ta nufi falo, kai kawai Zahra ta kaɗa kana ta dire kofin dake hannunta da sauri ta miƙe tsaye ta yagi tissue ta goge bakinta da hannunwanta, kafin ta suri jakar handbag ɗinta ta wuce tana faɗin "Ummina mun tafi sai mun dawo, me kikeso in taho miki dashi tsaraba...?" Ta faɗa tana ƙarasa saukowa daga dinning area ɗin ta nufi cikin falo inda Shatu ke tsaye tana jiranta, Ummi kuwa dake tsaye a dinning ɗin tana ƙoƙarin tattare kayan da suka kammala cin abinci dasu ne ta ɗago ta kallesu tana sakin murmushi take faɗin "A'a bana buƙatar komai ƴan matana kuje dai Allah ya dawo min daku lafiya, ni kam zanyi online shopping abuna..."


Da sauri Shatu tace "No Ummi kar kiyi dan Allah ki gaya mana abinda kikeso kawai mu siyo miki..."
Ta faɗa a shagwaɓe tana kallonta, ɗan taɓe baki Ummi tayi kana tace "Alright shikenan...perfumes kawai nakeso da turaren ɗaki..."


Ɗan murmushi Shatu tayi tana cewa "Ashe ma duk buƙatar tamu ɗaya ce Ummina, nima turarukan fa nakeso in siya, sai kayan bacci da nakeson canza sababbi saboda nawa duk sun tsufa ina buƙatar wasu..." Ta faɗa tare da juyawa ta kama hannun Zahra tana faɗin "Muje auta, Ummi mun tafi sai mun dawo..."


Kallonsu Ummi tayi cikin kulawa kafin tace "To a dawo lafiya Allah ya tsare..."


Da "Ameen..." Suka amsa kana cikin jin daɗi suka sakai suka fice daga falon.






★★★






Acan Kaduna kuwa Ya Azeez ne tsaye a ƙofar su, inda yake ƙoƙarin kulle ƙofar ɗakin da kwaɗo, a hankali ya juyo lokaci ɗaya yana saka ɗan makullin a cikin aljihun wandon shaddar dake sanye a jikinsa, ɗan kallon tsakar gidan nasu yayi ya kaɗa kai kafin yasa kai zai fice daga gidan, har ya kai bakin ƙofa wayarsa ta ɗauki kara ya dakata ya zura hannu cikin aljihun dake gaban rigarsa ya fito da ita, ganin Ummansa ce yasa da sauri ya zauna saman wani ɗan dutse dake jikin ƙofar gidan nasu ya jingina bayansa da bango kana ya masa kiran cikin girammawa haɗe da tsantsar biyayya yace "Assalamu alaikum..Ummana Barka da rana..."




Daga can ɓangaren kuwa Umma dake zaune a tsakar gidanta tana gyaran shinkafa, sai Iman dake gefenta a zaune tana gyara kayan miya, ta saki murmushi cikin nuna jin daɗi tace "Waalaikums salamu ɗan gidan Ummansa, ya aikin har an fitan ne...?"


A hankali ya saki murmushin shima kana yace "A'a ban fita ba Umma sai yanzu ne dai na fito nake shirin zan fitan..lafiya dai ko...?" Ya ƙarashe maganar tare da ɗan saurarawa.


Numfashi ta sauke a hankali kafin tace "Dama na kiraka ne inji kasan yau ake bikin Fahad abokinka ɗan gidan Alhaji Sale Musawa amma shine ko kaɗan baka taɓa gaya min ba...?"


Da sauri ya zaro idanuwansa waje cike da mamaki kafin yace "Wane Fahad ɗin kuma Umma..ba dai Fahad nawa dana sani ɗan gidan Alhaji Sale abokin Abbana ba...?"


Cikin sanyi tace "Shi ɗin dai Fahad na Kano AbdulAzeez shi nake nufi yau ake ɗaura masa aure..."


Cike da tsantsar mamaki yace "Amma shine bai gaya min ba Umma..? Kuma fa ko jiya sai da ya kirani da yamma mukayi waya dashi, yake tamabayata yaushe zan shigo nace masa sai ƙarshen watan nan..."


Umma tace "To ka daina mamaki nima yanzu Hajiya Zabba'u ta kirani take tambayata ya bata ganni a gidan biki ba, shine nake tambayarta bikin wa tace na Fahad, nace ai ban sani bane tace aiko yau ne ɗaurin aurensa amma ɗaurawa kawai za'ayi yau ɗin, taron bikin kuma sai nan da sati ɗaya za'ayi, shine nace bari in kiraka inji koka sani shine baka gaya min ba. Ai da naje wallahi ko dan saboda Hajiya Fiddausi mutuniyar kirki matar akwai ta da mutunci da son mutane gata da fara'a, tun lokacin da abun nan ya samu mahaifinka bata taɓa gajiyawa da yi mana abun arziki ba ita kenan kullum akan hanyar kawo mana abun alkhairi, ita da mijinta suna da karamci sosai wallahi, inda da hali da ka halacci bikin nan idan aka gama komai saika dawo..."


Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "Insha Allahu kuwa Umma zanje, za'a san yadda za'ayi. Amma yau..."


Saurin katsesa tayi da faɗin "Amma da so samu ne Yayan Imaan daka tafi tun yau ɗin kawai sai dai su ganka kwatsam..."


Ɗan jim kaɗan yayi kafin yace "Amma Umma kinsan ɗaurin auren safe Kano sukeyi nasan yanzu an riga da an gama ɗaurin auren, kawai dai dana bari zuwa nan da sati ɗayan sai in tafi ayi bikin dani a gama sannan in dawo..."


Ɗan gyara zama Umma tayi daga can ɓangaren tana cewa "Nidai inda hali ka tafi yau ɗin kawai dan Allah..." Ta faɗa kai tsaye cikin bada umarni.


Idonsa ya lumshe fahimtar da yayi cewa umarni ne kai tsaye mahaifiyar tasa take bashi, dan haka cikin sanyi yace "Insha Allahu duk yadda kikace hakan za'ayi Ummana, ina nan zan biyo idan na shirya, zanzo muyi sallama kafin in wuce..."


Cikin jin daɗi tace "Toh shikenan ina jiranka saika ƙaraso, amma kayi sauri ka shirya kar yamma tayi kasan yanayin hanyar sai a hankali. Ka gaida Fadwa Allah yayi muku albarka yasa a gama lafiya..."
"Ameen Ameen Ummana, Ameen ya Allah..." Ya faɗa cike da jin daɗi, kana daga haka sukayi sallama ta kashe wayar.




Ya jima a tsaye shiru yana tunani kafin ya juya da sauri ya buɗe ƙofar ya koma cikin ɗakin, kasancewar dama bai wani daɗe da yin wanka ba yasa ya tuɓe kayan jikinsa a gurguje, ya buɗe jakarsa ya zaro wata shaddarsa mai kyau kalar sky blue wacce bata wani sha jiki sosai ba ya hau shiryawa cikin sauri sauri, sosai shaddar tayi masa bala'in kyau ta haska fatarsa, yana gamawa ya ɗebi ƙananan kayansa kala biyu da jallabiya guda ɗaya, ya haɗa da abubuwan da yasan zai buƙata ya saka a wata ƙaramar jaka irin ta matafiya ya sagala a gefen kafaɗarsa, kana ya ɗauki wandon kayan daya cire ya kwashe kuɗaɗen dake ciki wanda basu wuce dubu huɗu da ɗari biyar ba ya zuba a cikin aljihunsa sannan ya ɗauki makullin napep ɗinsa ya fice daga ɗakin.
Kulle ƙofar ɗakin ya soma yi kafin yasa kai ya fice daga gidan gaba ɗaya yaja ƙofar ya kulle ta can waje, kana ya nufi kekensa inda yayi parking daga can gefe guda ya shiga yaja, gidan bulon da yake kai ajiya direct ya nufa yaje ya ajiye keken acan haɗe da basu ɗan makullin kana daga nan ya fito ya tari mashin ya hau, bayan ya gaya masa inda zai kaishi yaja suka wuce.






























*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:18 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*






2️⃣3️⃣




Koda mai mashin ɗin ya saukesa a kofar gidan Umman bai wani daɗe sosai ba, dan ko zama baiyi ba daya shiga, suna ƙara gaisawa kawai yayi mata sallama ya fito ya sake tarar mashin ya hau kai tsaye ya nufi tasha.
Yana isa can ma bai wani jima sosai ba ya hau motar Kano suka kama hanya.



★★★★




*4pm.*


Ummi ce zaune saman ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun da suka zagaye katafaren falonta sukayi masa ƙawanya, riƙe take da remote control a hannunta tana canja tashoshi, tashar Sunnah TV ta kamo inda taga an sako wa'azin mutuminta Malam Aminu Daurawa wanda yake bada fatawa akan haƙuri da juriya a zamantakewar aure, kasancewar tana tsananin son wa'azinsa yasa gaba ɗaya ta natsu ta maida hankalinta kacokan kan talabijin ɗin, ta ƙara gyara zama lokaci ɗaya ta ƙaro volume tana saurare.


Buɗe ƙofar falon da akayi ne yasa ta ɗan juyowa a hankali, taga Zahra ce ta gyara zama da sauri ta kalleta, ƙaramin murmushi ta saki kafin tace "Welcome my princess an dawo..."
Ta faɗa tare da ajiye remote ɗin hannunta ta buɗe mata hannuwanta alamar tazo gareta.




Ɗan kwaɓe fuskarta Zahran tayi kana ta fara takowa a hankali ta ƙaraso gabanta tazo ta dire shopping bags ɗin dake hannunta kafin ta faɗa saman kujera lokaci ɗaya tana faɗin "Wash Allahna Ummi na gaji sosai wallahi..."


Cikin sauri Shatu dake shigowa cikin falon itama hannunta riƙe da wasu shopping bags ɗin tace "Aikin uban me kikayi da har kika gajin..? Ummi kiji min wannan ragguwar autar taki da wani iyayi fa...?"


Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana dire jakunkunan a gaban Ummin, kafin ta ɗago tana cewa "Sannu da gida Ummina..." Ta faɗa tare da zama a kusa da Zahra data wani dafe kai tana yamutse fuska.
Watsa mata harara Shatu tayi kafin ta saki tsaki ta miƙe tana hararar Zahran take faɗin "Mutum sai shegen rakin tsiya abu ba abu ba duk kibi ki damu mutane da ƴan ƴan ƴan..wai ke a dole kin gaji sai kace wacce ta ɗauko Sahad Store gabaki ɗaya a kanta..."


Ummi dake kallonsu tana dariya tace "A'a fa ƴan mata, ya kamata ki tausaya mata tsakani da Allah, tun fa ɗazu kuka fita kusan awa uku kenan ga zafin gari ga rana, taya za'a ce mutum ba zai jigata ba dan Allah...?" Ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi tana hararar Shatu.


Ɗan taɓe baki Shatu tayi ta harari Zahran kana ta ɗauki handbag ɗinta data ajiye tana faɗin "Ummi nidai bari inje inyi sallahr la'asar, lokaci har ya wuce muna gurin siyayyar kaya..." Ta faɗa tana wucewa da sauri ta haura sama zuwa ɗakinsu.


Miƙewa itama Zahran tayi lokaci ɗaya tana faɗin "Nima bari inje inyi Sallah Ummi, idan na idar na ɗan watsa ruwa zan sauko..." Ta faɗa tana ɗan yatsine fuskarta alamar gajiya.
Kaɗa mata kai Ummin tayi tana faɗin "Ok a sauko lafiya, amma ki gayawa Shatu nace idan tayi sallah maza ta sauko falo karta sake ta kwanta, dan nasan halinta ba takamaiman lokacin bacci gareta ba ko wane lokaci tayi ra'ayi kwanciyarta kawai take yi..." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar remote ɗinta tana ƙaro volume, gyaɗa mata kai Zahra tayi kana ta ɗauki wayarta itama tayi gaba, cikin natsuwa ta fara hawa matattakalar benen tana takawa a hankali a hankali har ta haura saman ta nufi ɗakinsu.








*******




Ƙarfe 4:40pm. Dai-dai na yamma direban daya ɗauko su Ya Azeez tun daga Kaduna ya shigo garin Kanon dabo, wanda kuma bai diresu a ko'ina ba sai a Na'ibawa Ƴan Lemu.
A hankali ya buɗe murfin motar ya fito riƙe da jakarsa a hannu, kafin cikin natsuwa ya lumshe kyawawan idanuwansa masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali.
Kana a hankali ya sauke numfashi yana sake shaƙar iskar garinsa mai cike da ɗimbin tarihi a rayuwarsa.


A hankali yake jin wani irin mugun farin ciki yana ratsa ruhi da gangar jikinsa, wanda yasa yake jin kansa cikin wani irin yanayi mai masifar daɗi, yayinda a nutse zuciyarsa ta dinga tariyo masa wasu abubuwa da dama waɗanda suka shuɗe a lokacin da mahaifinsa yake a raye.
Cikin sanyin jiki yasa hannu ya share ƴar ƙwallar dake shirin zubo masa ya girgiza kansa a hankali kafin a fili ya furta "Allah ya gafarta maka Abbana, Allah yasa kana kyakkyawan matsayi a cikin aljanna fiddausi maɗaukakiya..."
Ya faɗa yana rataya jakarsa a gefen kafaɗarsa ya juya cikin takunsa mai cike da zallar natsuwa ya fara kutsawa cikin mutanen dake ta kai kawo a gurin suna ta hada hada, har ya isa inda masu daidaita sahu suka faka a gefen titi, ya tsallaka ya tare wani ya shiga bayan ya faɗa masa unguwar da zai kaisa yaja suka kama hanya.


Koda suka ƙarasa cikin unguwar ta Medile, gaban wani katafaren ƙerarren gida mai ɗauke da tangamemen gate kalar ruwan madara ya nunawa mai adaidaita sahun yace ya tsaya.
Fitowa yayi daga cikin adaidaitan ya biyasa kuɗinsa, kafin ya juya a hankali cikin natsuwa ya tunkari gate ɗin gidan lokaci ɗaya yana gyara zaman jakarsa dake rataye a gefen kafaɗarsa, ƙarasawa yayi bakin gate ɗin ya tsaya daga ɗan gefe kaɗan dai-dai inda ƙaramar ƙofar take, kai tsaye ya saka hannu ba tare da tunanin komai ba ya fara ƙwanƙwasa ƙofar a hankali yana ɗan waigawa bayansa lokaci bayan lokaci yana kallon cikin unguwar dake nan tsit babu motsin mutane ko kaɗan, sai ƴan ɗaiɗaikun motocin dake ɗan giftawa jefi jefi suna wucewa zuwa gidajensu.




Dai-dai lokacin kuma aka wangale tangamemen gate ɗin wata mota ƙirar Benz baƙa wuluk ta silalo a hankali ta fito daga farfajiyar gidan, wani irin wawan burki mai motar ya taka a gabansa, ɗago kansa yayi a hankali yana kallon motar da sauri wanda ke cikin motar ya buɗe ya fito, wani kyakkyawan saurayi ne irin black beauty ɗin nan, wanda a ƙalla shekarunsa zasu iya zuwa ɗaya dana Ya Azeez ɗin. Sanye yake da wata tsadaddiyar shaddar gezner fara sol mai masifar kyau da yarari sai ɗaukar ido take tare da zuba wani irin sheƙi na musamman, kai da ganin yanayin shigar da yayi tun daga sama har ƙasa da yadda fuskarsa ke ɗauke da murmushi take kuma fitar da wani annurin farin ciki na musamman zaka fahimci cewa shi ango ne.
Cikin sassarfa ya iso gaban Ya Azeez ɗin wanda tunda yayi masa kallo ɗaya ya wani ɗauke kai gefe yasha mur kamar bai gansa ba.


Fuskarsa ɗauke da matsanancin mamaki ya zaro idanu waje yana faɗin "Laaaa AbdulAzeez Naseer Arabi..." Ya faɗa cike da tsananin farin ciki, da kuma mamakin ganinsa a dai-dai wannan lokacin yana kallonsa.
"Wai dan Allah da gaske kai ne Arabi...?" Ya faɗa cike da al'ajabi yana ƙoƙarin kamo hannunsa, saurin janye hannunsa Ya Azeez yayi tare da watsa masa wani mugun kallo cikin ɓacin rai ya ɗauke kai yana cewa "A'a bani bane mai kama dani ne..." Bai bashi damar magana ba ya ci gaba da faɗin "Wallahi ka bani matuƙar mamaki Fahad, wai ace duk yadda muke da kai yau aurenka amma koda wasa baka taɓa faɗa min ba..kuma kusan kullum sai munyi waya da kai amma saboda bani da komai yanzu bani da abinda zan iya baka amatsayin gudunmawata, kuma ni ba kowa bane, ban kuma mallaki komai ba shiyasa kaƙi sanar dani aurenka saboda ban cancanci zuwa bikinka ba..? Ko kuma kar inzo in zubar maka da kima da mutuncinka a idanun abokanka saboda ni ba ɗan kowa bane sannan ban tara komai ba ko...?" Ya ƙarashe maganar cikin ƙunar rai da tsakanin jin zafin abinda Fahad ɗin yayi masa na ƙin gaya masa aurensa da bai ba, wanda shi lokacin da nashi auren da Fadwa ya tashi sai da ya kirasa ya faɗa masa kuma yaje har garin Kaduna akayi komai dashi kuma ya bashi abun arziki sannan ya dawo, amma saboda shi ba komai bane yanzu basu da wani mai tallafa musu sai mahaifinsa shiyasa zai yi masa haka..?




Shi kuwa Fahad gaba ɗaya ji yayi gwiwarsa tayi bala'in sanyi, ko ba komai bai kamata ya yiwa AbdulAzeez haka ba, duba da irin zaman amana da mutuncin da iyayensu sukayi, da irin shaƙuwar dake tsakaninsa dashi kansa AbdulAzeez ɗin, wanda a duk faɗin garin Kano da cikar ta bashi da wani amini ko shaƙiƙi da ya kai masa AbdulAzeez ɗin, haka kuma shima AbdulAzeez ɗin a nasa ɓangaren bai da wani amini da ya kai masa Fahad ɗin duk faɗin garin Kano da kewayenta.


Har ga Allah shi da kansa ya sani bai kyauta masa ba, kuma ba yayi hakan da wata manufa bane a ransa kawai yayi ne domin kar ya takura masa, saboda yasan halinsa shi mutum ne mai bala'in kawaici da takura kai dan kawai yaga ya farantawa wanda yake tare dashi, shiyasa ya barshi bai gaya masa ba, amma ko kaɗan bai san abun zai ɓata masa rai har haka ba..


"Kai ni gurin Mami nidai inyi mata Allah sanya alkhairi, in kama hanya kafin dare yayi min..."
Maganar Ya Azeez ta katsewa Fahad ɗin tunanin da yake yi da sauri ya ɗago kai ya kallesa, kafin cikin sanyin jiki yace "Dan girman Allah aboki ka fahimceni..wallahi banyi hakan da wata niyya ba, amma idan kana ganin kam..."


Ɗaga masa hannu Ya Azeez yayi da sauri yana faɗin "Nidai ba saboda kai dama nazo ba, idan kuma gidan ma bazaka iya bari na in shiga bane to sai in koma inda na fito..."
Ya faɗa kai tsaye yana dubansa.
Saurin kallonsa Fahad ɗin yayi kafin ya juya lokaci ɗaya yana faɗin "Ai ban isa ba aboki kaima gidanku ne, amma please nidai ina ƙara roƙonka ka yafe min dan girman Allah ba dan ni ba..." Ya faɗa yana riƙe hannunsa lokaci ɗaya suka fara tafiya, banza dashi Ya Azeez ɗin yayi ya ɗauke kai gefe, ganin haka yasa Fahad ɗin sake dubansa fuskarsa cike da damuwa yace "Please mana abokina..." Wani banzan kallo Ya Azeez ɗin ya sake ɗago kai ya watsa masa kana ya juya cikin sauri ya isa bakin gate ɗin gidan ya tura ƙaramar ƙofar kai tsaye ya shige ciki, da hanzari shima Fahad ɗin yabi bayansa ba tare daya sake ko bi ta kan motarsa daya bari fake a gurin ba ballantana har ya kula da cewa abokansa da suka fito tare suna ciki ba, ya bishi suka shige gidan a tare yana ƙara yi masa magiyar ya tsaya ya sauraresa, amma ko waigowa Ya Azeez bai yi ba sai ma sauri daya ƙara ya nufi ƙofar da zata sadashi da shiga babban falon gidan.


Da sauri wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login