Showing 111001 words to 113443 words out of 113443 words
baku taɓa zato da tsammanin ba shine ya farun.
Kunga wannan shine hukunci Ubangiji Buwayi gagara misali wanda ba'ayi masa dole..."
Ya ƙarashe maganar lokaci ɗaya yana share hawayen dake ƙara taruwa a cikin idanunsa.
Cikin kukan nadama da tsantsar danasani Mama tace "Na roƙeƙa ka yafe min AbdulAzeez nayi nadamar abinda na aikata maka, ban kyautawa kaina ba..tabbas idan na mutu da irin halin nan sai Allah ya hukuntani, domin na kasance cikin mutane masu saurin manta alkhairi a rayuwarsu, ban kyautawa kaina ba, nayi nadamar butulcin da nayi a rayuwata..."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara fashewa da wani kuka mai ƙarfi da nadamar abinda ta aikata, dan dama tunda akai auren Fadwa taga yadda abubuwa duk suka runcaɓe musu cikin lokaci ƙanƙani, tun daga nan ta tsorata da lamarin duniya, shiyasa duk ta watsar da komai take kuma ƙoƙarin daidaita al'amuranta da zamantakewarta da kowa a yanzu.
A hankali kuma cikin rauni da sanyin murya itama Fadwa tace "Wallahi ban taɓa jin nadama da danasani a rayuwata ba irin na yau Abba, nayi baƙin cikin kasancewata a raye har na tsawon wannan lokacin da zanga tashin hankalin abubuwa iri iri waɗanda ban taɓa tsammatan zan fuskancesu ba a rayuwata, na tafka babban kuskure a rayuwata nayi kuskure Ya Azeez na roƙeƙa ka yafe min ba dan halina ba dan Allah..." Ta faɗa tare da rushewa da wani irin kuka gwanin ban tausayi, domin a lokaci guda ta ji gaba ɗaya komai ya tsaya mata cak, saboda ko a lokacin da aka kaita gidan Ya'u mai kifi bata ji zafi da raɗaɗin baƙin cikin da take ji yanzu a zuciyarta ba, gabaki ɗaya duniyar tayi mata duhu dinɗim lokaci ɗaya sai abun ya zame mata biyu kukan zuci dana fili, domin tasan yanzu Ya Azeez yayi mata nisa ta rasashi kenan har abada, ga kuma zama da mugun mutumin da Allah ya haɗata dashi a yanzu.
Ya Azeez kuwa jin abinda Fadwan ta faɗa ne yasa shi juyawa a hankali ya sauke idanunsa akanta, wanda kuma tunda ya zauna ɗin sai yanzu ne ya kalli inda take.
Sosai yay mamakin ganin yadda ta koma, duk ta rame ta wani ƙarmashe, sai ɗan wuya bakinta kuwa duk ya bushe, ga wasu koɗaɗɗun kaya da take sanye dasu a jikinta duk sun soshe, gaba ɗaya ta zama abar tausayi.
A hankali kuma ya janye kallonsa daga kanta, tare da runtse idanunsa kana cikin nuna tsantsar tausayi da kulawa yace "Ki bar faɗin haka Fadwa, komai daya faru dama tuni Allah ya ƙaddara hakan sai ta faru, dan haka ni ban riƙeku a zuciyata ba. Na daɗe da manta komai daya faru ya wuce..."
Ya faɗa yana ƙara riƙe hannun Shatu dake cikin nasa yana ɗan murzawa a hankali.
Cikin tsananin jin daɗin maganarsa Abba yace "Allah yayi maka albarka, Allah yasa ka rabu da mahaifiyarka lafiya, Allah ya albarkaci rayuwar aurenka ya baku zuri'a ɗayyiba..."
Da sauri Mama ta amsa da Ameen ya Rabbi, kana kuma ta ɗora da faɗin "Kaga dai yadda duniya ta mayar damu AbdulAzeez..ni na dinga uzzurawa Fadwa na dinga goyon bayan ƙinka da take, ina ƙara ƙarfafa mata ƙiyayarka a zuciyarta na dinga bata shawarwarin banza da wofi, sai gashi duk fatan sharrin da nake binka dashi ya ƙare akaina da ƴata, kai kuma kana cikin alkhairi, gashi kuma duk da haka ban isa hana abinda Allah yaso ba, yanzu ga ijabar Ubangiji nan ina gani akan Fadwa.
Dama kuma duk wanda za'a yiwa hassada ko a cutar dashi to zaiyi ta samun cigaba ne a rayuwarsa, kuma zai ga ribar haƙuri tun a duniya kafin kuma ya iske ladan lahira..."
Abba yace "Allah yasa mudace..."
Dukkansu suka amsa da Ameen, kana daga haka kuma suka cigaba da hira har zuwa wani lokaci, kamar wani abu bai taɓa haɗasu ba, suna gidan kuma har lokacin dawowar su Ilham da Amatullah daga makarantar islamiyya yayi suka dawo.
Koda suka ga Ya Azeez kuwa suma sunyi matuƙar mamaki sosai, dan Ilham har da kukan farin ciki sai da tayi.
Suna gidan kuwa har bayan sallah isha'i, bayan Abba da Ya Azeez sun dawo daga masallaci ne kuma Ya Azeez ɗin yace Shatu da Imaan su tashi su tafi, amma Abba ya hana yace sai an gama abinci sunci kafin su tafi, dan haka babu yadda Ya Azeez ya iya ya koma ya zauna suka ci gaba da hirar yadda abubuwa suka kasance musu, inda anan ne kuma Abban ke labarta musu yadda auren Fadwa da Ya'u mai kifi ya kasance.
Wanda kuma zuwa lokacin tuni Abban ya kora Fadwa yace ta tafi gida kar mijinta ya koma gidan ya iske bata dawo ba, haka nan kuma ba dan taso ba ta tashi ta tafi, dan ɗan zaman da sukayi da Shatu kuwa har taji Fadwan ta shiga ranta, dan haka koda ta tashi tafiya Shatu da Imaan dasu Ilham ne suka rakata har soron gidan, sai bayan da Fadwan ta wuce ne kuma Shatun taba Ilham kuɗi da zasu haura dubu hamsin tace ta kaiwa Fadwan gida ta fara sana'a.
Sosai Abba da Mama sukai tai mata godiya, dan Mama kam har da kwallar murna sai da tayi.
Koda suka tashi tafiya kuwa Ya Azeez kayan daya kawowa Abba ya bashi, ita kuma Mama ya bata kuɗi masu yawa kana kuma ya ba su Ilham suma yace su siya kayan kwalliya su kuma sake uniform ɗin islamiyyarsu.
Suna gidan har kusan ƙarfe 9:30pm. Sannan bayan Mama ta gama girki sunci sun ƙoshi sukayi musu sallama Abba yana ta saka masa albarka yana masa addu'a har da kwallarsa, dan har lokacin idan ya tuna ya kan ji baƙin cikin rabuwar Ya Azeez da Fadwa, dan dai babu yadda zaiyi ne kawai dole sai haƙuri.
Koda suka koma gidan Umma kuwa, Ya Azeez sashensa dake gidan ya buɗe shida Shatunsa suka shige, dan dama sai fargaba yake kar Shatun tace zata kwana a ɓangaren Umma, sai gashi kuwa ba tayi musu ba ta biyosa sukayi kwanciyarsu abinsu.
Washegari kuwa Ya Azeez tunda wuri ya fita shida direban Umma, suka shiga cikin gari suka haɗo kayan abinci masu yawa ya aika direban da kayan da kuɗi aka kai can unguwar Mu'azu gidan Abba, sannan kuma ya kira Abban a waya ya gaya masa a ɗebi kayan abincin da kuɗin daya aiko direban dashi a haɗa duka a kaiwa Fadwa.
Kwanansu biyu a garin kuma Shatu ta matsawa Ya Azeez yasa direba ya kaita gidan Fadwan, karku so kuga yadda Fadwa tai murna da ganin Shatun.
Can ta wuni ranar sai dare sannan Ya Azeez ɗin sukaje da direba suka ɗaukota suka dawo gida.
Da daddaren ranar kuwa Shatu da zazzaɓi mai tsanani ta kwana, sai faman kuka take tana ta nuƙurƙusarsa, ko kanta bata iya ɗagawa saboda tsabar zafin da jikinta yay mata, sai da yaje ɗakin Umma ya karɓo mata magani tasha sannan ta ɗan samu zazzaɓin ya lafa mata, bayan sallar asuba har ta ɗan samu bacci.
Satinta guda tana jinya sannan ta samu sauƙi sosai ta warware, sai rashin ƙwarin jiki kawai da take ɗan fama dashi.
Washegarin ranar kuma suka bar Kaduna zuwa Kano.
Bayan sati biyu da tafiyarsu Shatu da Ya Azeez ne kuma Fadwa da mijinta Ya'u mai kifi sukaje har gida suka yiwa Abba da Mama sallama kan zasu koma Birnin Kebbi garin mijin da zama, wanda kuma zuwa lokacin tuni Ya'un yayi sauƙi ya rage wasu abubuwan da yake mata sosai, shiyasa yanzu itama ta saki jikinta suna zaune lafiya basu da wata matsala, Umma kuwa koda Fadwan taje mata sallama tayi mata nasiha sosai sannan ta bata kuɗi masu yawa tace idan sukaje can garin ta kama sana'a.
BAYAN WATA BIYU
A haka dai rayuwa tai ta gangarawa da daɗi ba daɗi, haka abubuwa sukayi ta canzawa yau daɗi gobe kuma akasinsa, zuwa yanzu kam komai ya gama daidaita a zaman Fadwa da Ya'u mai kifi.
Domin kuwa yanzu sana'ar kayan koli take sosai da zannuwa, cikin unguwar da suke a can Birnin Kebbin kuwa da maƙotanta babu wanda bai santa ba, shiko Ya'u tuni ya daina sana'ar siyar da kifi shima yanzu sana'ar siyar da dabbobi yake yi, kuma dukkansu sana'ar ta karɓarsu suna ganin buɗi sosai.
Dan Fadwa kam zuwa yanzu har ƙiba tayi ta murmure abinta, alamar dai bata tare da wata matsala hankalinta kuma a kwance take gudanar da sana'arta bata jin damuwar komai a ranta tana zaune da mijinta lafiya da abokiyar zamanta.
***********
A ɓangaren Ya Azeez da Shatunsa kuwa suma hakan ne ya kasance, dan duk wani jin daɗin rayuwa babu wanda basu jiyar da junansu.
Hakan yasa har wata shaƙuwa ta musamman suka ƙara ga wani ji da juna da sukeyi tamkar zasu haɗiye kansu saboda tsabar ƙauna, kuma ko a gaban waye basu iya ɓoye tsantsar soyayyar da suke yiwa junansu shiyasa mutane da dama suke sha'awar yanayin zamansu, wasu kuma suke koyi da kalar soyayyar su mai matuƙar burgewa.
Yau ɗin ta kama Lahadi Ya Azeez yana gida bai fita ko'ina ba, duk da Fahad nata damunsa da kira kan ya fito ya rakasa gidansu Basma zaije ganinsu ita da yaronsa, wanda watansa biyu kenan da haihuwa, amma yaƙi da yaga ma zai damesa da kira ya takura masa kawai sai ya kashe wayar gaba ɗaya ya ajiye, domin yau hutawa yake so yayi a gida tare da iyalinsa, dan haka baya jin zai fita ko nan ne da ƙofar gida, ranar yau ɗin gaba ɗayanta ta Eishatunsa ce, shiyasa baya buƙatar takura.
Shiko Fahad a nashi ɓangaren jin abokin nasa ya kashe wayarsa ne yasa ya kaɗa kawai ya shiga motarsa ya nufi gidansu Basman, yana tuƙi yana mitar ya gaji da zamanta a gidansu daga zuwa wankan gida taje ta wani rashe ƙafafu tai zamanta, ko damuwa da lamuransa ma ba tayi balle tayi tunanin dawowa gida, sai dai kullum yay ta zarya akan hanya ba dare ba rana.
A shirye ta fito cikin wasu haɗaɗɗun tausasan riga da wandon English wears masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, sosai kayan suka karɓeta sukayi mata masifar kyau, ta kama dogon gashinta da ribbon sai ta fito kamar wata ɗiyar indiyawa, ga cikinta ɗan wata uku daya fara fitowa yay ɗas a jikinta gwanin ban sha'awa.
A hankali ta ƙaraso kusa dashi ta zauna lokaci ɗaya tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.
"Babyna zaki zautani fa da wannan kyaun naki..."
Ya faɗa tare da sumbatar kumatunta duka biyu, yana faɗin "Kinyi kyau sosai, gaskiya dole zan biya kuɗin kwalliyar nan da akayi min ta musamman..."
Murmushi tayi tana kallonsa kafin ta sumbaci kumatunsa shima tana faɗin "Na gode Habiby na..."
Ta faɗa tare da ɗan shafa gefen wuyansa tana kallonsa, kana kuma cikin shagwaɓa tace "Habiby zan sha fura da gyaɗa, da gwaiba da yalo..."
Saurin ɗauke kai yayi daga kallonta ya kalli gefe yana dariya.
"Fura da gyaɗa da gwaiba kuma har da yalo Baby...?"
Ya faɗa lokaci ɗaya yana tsura mata idanu.
Rausaya kai tayi tana turo bakinta gaba kafin tace "Eh su nake sha'awar ci yau..."
Murmushi yayi tare da kai hannu ya lakace mata hanci yana dariya, haka take masa kullum musamman idan taga yana zaune baya komai ta dinga ƙaƙale ƙaƙale kenan duk dan ta sakasa aiki, wata rana kuwa har wanka sai shi zatace yay mata.
Babu ranar kuma da bazata sashi zuwa nemo mata abubuwan ciye ciye da kwaɗayi irin na masu ciki ba, haka zata tashesa cikin dare tace zata ci abu, idan bai nemo mata ba kuma ta tasashi a gaba tai ta kuka kamar wata ƙaramar yarinya, wani lokacin idan yaga dare yayi kuma sai ya lalaɓata yace ta kwanta zai nemo mata, da haka zai samu da ƙyar tai shiru har bacci ya ɗauketa, wani lokacin kuma haka zai fito ya gama bulayinsa ya dawo bai samo abinda take son ba.
Bama kamar yanzu da cikin yake ƙara girma, gashi kuma kullum kamar ƙara mata son yawo ake, idan kuma yace zai hanata nan ma wata rigimar ce zai tsokalowa kansa, yau ma da ƙyar ya hanata zuwa gidan Husna ƙawarta, wacce akayi bikinta sati uku da suka wuce.
Dan har ta shirya yace ba inda zataje, tunda shima yau a gidan zai wuni ba inda zaije.
Abun mamaki kuma sai yaga ba tayi gardama ba ta haƙura ta zauna a gida, shine yanzu kuma aka fito za'a bashi aikin nemo fura dasu gwaiba da yalo.
Tsadadden agogon fatar dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ɗaga ya kalla, ƙarfe 5pm. Dai-dai ya gani.
Sanin kuma yanzun nan zata iya dasa mai rigima ne yasa ya riƙota jikinsa ya rungumeta sosai, kana a sanyaye yace "Kinga dai yau gaba ɗaya bana jin daɗi duk jikina ciwo yake, ko zamuje kidan daddanna min jikina ko zanji daɗi, idan yaso daga baya sai inje in siyo miki, ko bazaki iya ba...?"
Da sauri kuwa ta girgiza mai kai tana ƙara cusa kanta a tsakiyar faffaɗan ƙirjinsa, kana kuma cikin yin ƙasa da murya tace "Zan iya mana, Habiby ina matuƙar sonka fa..."
Manyan idanuwansa ya lumshe sakamakon jin daɗin kalamanta, domin yana matuƙar son yaji kalmar a bakinta tana matuƙar yi mai daɗi ta kuma sanyaya masa rai.
A hankali ya raɗa mata a kunne "Nima ina matuƙar ƙaunarki sosai Habeebtyna..."
Murmushi tayi kana a hankali tace "Shikenan muje inyi maka tausan..."
A hankali ya miƙe tsaye da ita a jikinsa suna tafiya cikin natsuwa suka nufi bedroom ɗinsu.
Cak ya ɗagata ya ɗorata saman gadonsu, ya kwantar da ita lokaci ɗaya yana zura hannunsa cikin rigarta kana kuma cikin raɗa yana furta mata "Zaki iya kuwa Babyna...?"
Ɗaga masa kai tayi a hankali tana wani lumshe idanunta, sake matsa hannunsa yay akan abinda yafi so, kana ya girgiza mata kai yana wani lumshe manyan idanunsa murya ƙasa ƙasa yana faɗin "Kin tabbatar dai bazan takura Babyna ba ko...?"
Sake ɗaga mai kai tayi cikin fitar hayyaci da muradi mai girma, kana ta ɗago kanta cikin sauri ta haɗe bakinsu waje ɗaya, sannan ta jawosa gaba ɗaya ya faɗo kanta ya zamana tana ƙasa shi yana samanta, sannan ta ja musu lallausan bargo ta lulluɓesu.
*ALHAMDULILLAHI*
*ALHAMDULILLAHI*
*ALHAMDULILLAHI*
Daga nan na kawo ƙarshen wannan labari mai suna *WADATAR ZUCCI*
Ina roƙon Allah ya yafe min kurakuran da nayi a cikinsa, ya kuma bani ladan abinda na rubuta dai-dai a cikinsa.
Masoyana aduk inda kuke ina matuƙar godiya Allah ya barni daku, ina muku fatan alkhairi, sai mun sake haɗuwa idan mai kowa mai komai ya amince.
Sannan ina roƙon duk wanda ya karanta wannan littafin ya yiwa mahaifina marigayi Alhaji Muhammad Alto addu'a, Allah ya sanyaya makwancinsa yasa aljanna fiddausi maɗaukakiya ta zamo makoma agaresa da dukkanin sauran musulmi baki ɗaya Nagode.
*22-12-2021*