Showing 9001 words to 12000 words out of 113443 words
ƙawarta Hajiya Lubna hakan bai hana Fadwa zarya gidanta akai akai ba domin ko kaɗan matar bata da matsala akwaita da son mutane ba kamar ƙanwarta Hajiya Lubna ba mai shegiyar rowar tsiya da iyayi, duk daya kasance Hajiya Kalsoom ɗin tana auren mataimakin gwamnan jihar Kaduna ne kuma gashi shahararren ɗan kwangila wanda ake damawa dashi a yanzu amma hakan bai sakata girman kai da ɗagawa ba.
Sai data gama ƙarewa falon kallon tsaf tukunna ta samu waje kan luntsuma luntsuman kujerun da suka yiwa katafaren falon ƙawanya ta zauna tana ƙurawa faskeken talabijin ɗin daya kusan mamaye rabin bangon falon ido wanda duk ranar da tazo gidan sai ta yi masa irin wannan kallon ƙurullan dan har ta saba ko gajiya bata yi abun ya gama bin jikinta.
Tana nan zaune wata hamshaƙiyar mace kyakkyawa black beuty ta sauko cikin shiga ta alfarma jikinta sanye da tsadadden leshi wanda aka tsantsarawa ɗinkin Abuja bubu ta sha adon gwala-gwalai hannu da wuyanta sai walwali take tana sheƙi, fuskarta ɗauke da fara'a ta ƙarasa saukowa cikin falon tana murmushi take faɗin "Barka da zuwa Hajiya Fadwa, ina ta cigiyarki dama kwana biyu na ɗauka ko bakya ƙasar ne da naga baki zo ba....?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana zama a kusa da ita.
Washe baki Fadwa tayi cike da fara'a tana faɗin "Wace ni Aunty Kalsoom...Ina nan babu inda naje kwana biyu ne abubuwan sai a hankali, ya shirye shiryen bikin....?"
Hajiya Kalsoom tace "Alhamdulillahi gashi nan anata yi, fatan dai kinyi ankon....?"
Fadwa ta sauke numfashi tana faɗin "Eh Hajiya Labiba ta siyan min har ta kai mana gurin ɗinki sauran kuma ta bani gobe insha Allahu zan kaiwa telana...."
Hajiya Kalsoom ta kaɗa kai lokaci ɗaya tana faɗin "Ok ba matsala Allah ya kaimu goben lafiya...."
Ta faɗa tana gyara zamanta kafin ta ƙwallawa mai aikinta Halima kira, ta fito daga kichin da sauri tazo ta durƙusa a gabanta cike da ladabi tace "Gani Hajiya..." Cikin bada umarni Hajiya Kalsoom tace "Kije ki haɗowa Hajiya Fadwa abinci ki kawo mata...." Ta faɗa kai tsaye tana kallon Fadwa da ta wani yatsine baki tana watsawa mai aikin kallon banza tace "Inda akwai abinda kikeso a haɗo miki dashi ki gaya mata..."
Saurin girgiza kai Fadwan tayi tana faɗin "A'a babu Aunty Kalsoom, ta kawo min ko mene ne ya isa....Allah ya saka da alkhairi ya ƙara arziki...."
Cikin jin daɗi Hajiya Kalsoom ta amsa da Ameen tana sakin murmushi, kana tace "Halima tashi ki je ki kawo mata..." Tace "Toh Hajiya..." Ta faɗa tana miƙewa ta wuce kichin, ba jimawa ta dawo falon hannunta ɗauke da babban faranti ta ajiye a gaban Fadwa bayan ta janyo ƙaramin tebur ta ɗora akai, sai data zuba mata komai ta aje mata kana ta bar gurin.
Nan Fadwa ta zage ta buɗe ciki ta kwashi abinci tana ci suna hira da Hajiya Kalsoom sai da taci tai nak abinta, kana ta kora da sassanyan lemun abarba wanda yaji madara da kayan haɗi. Sai da taji cikinta ya cika taf sannan ta ture farantin gefe ta zari tsinken sakace ta saka a baki ta saki gyatsa kana ta sake yin balans a kujera bayan ta zare gyalen dake kanta sanyin Ac na ratsata yana shigarta ta ko'ina ta lumshe idanu tana ƙara godewa Allah daya sa tasan su Hajiya Lubna da Hajiya Labiba a rayuwarta, dan silarsu gashi tasan mutane da dama waɗanda ko ba dasu ba idan taje gidajensu babu mai wulaƙanta ta.
Wani bacci mai daɗi Fadwa taji ya fara ɗaukarta dan haka ta zame nan kan doguwar kujerar tai kwanciyarta abinta, ganin haka yasa Hajiya Kalsoom ta tashi ta koma sama ta shiga ɗakinta ta barta nan.
*********
A ɓangaren Ya Azeez kuwa tun misalin ƙarfe 12pm. Na rana ya koma gida domim ya kaiwa Fadwa kuɗin abinci kamar yadda yayi mata alƙawari, amma sai me...? Yana zuwa ya iske ƙofar gidan nasu a kulle da ƙaton kwaɗo alamar matar gidan bata nan, ya daɗe tsaye a ƙofar gidan yana kallon hanya amma babu ita babu alamarta, yafi awa ɗaya tsaye a ƙofar gidan kafin ya haƙura ya shiga keke napep ɗinsa yaja ya wuce ya koma bakin sana'arsa, zuciyarsa cike taf da baƙin cikin irin halin da Fadwa ta jefa kanta a ciki.
**********
Fadwa kuwa tana can gidan Hajiya Kalsoom inda taci baccinta ta ƙoshi hankali kwance babu abinda ya dameta, sai bayan la'asar sannan ta tashi ta shiga ɗakin baƙi dake nan cikin falon ta ɗauro alwala tayi sallar azahar da la'asar kafin ta fito falo ta zauna ta kunna kallo.
Haka tai ta zama a gidan har bayan sallar magriba sannan bayan ta ci abinci Hajiya Kalsoom ta haura sama ta ɗauko kuɗi ta bata tace ta biya kuɗin ɗinki kana ta kira direbanta tasa ya maida ita gida, Fadwa bakinta ya kasa rufuwa sai fara'a take tana faman washe baki ta tura kuɗin ta a jaka tana ta yiwa Hajiya Kalsoom godiya kamar zata ari baki.
Haka ta rakota har gurin mota direban ya buɗe mata gidan baya ta shiga ta zauna tana ƙara jin kanta wani iri ta hakimce tana wani saki ƙayataccen murmushi, lallai arziki yayi a rayuwa yau itace a cikin wannan danƙareriyar motar za'a kaita gida. Lallai dole talaka ya ƙara tashi tsaye gurin roƙon Allah kan yayi masa tsari da talauci, dan babban ƙalubale ne mai tarwatsa rayuwa.
Suna karyo kwanan layinsu tun daga nesa ta hangosa zaune a kan wani ɗan dakali da ƴar wayarsa a hannu yana daddannawa, dan haka tace direban ya tsayar da motar ɗan nesa kaɗan da gidansu daga can gefe, ta ɗauki jakarta ta buɗe motar ta fito tana yi masa godiya ta wuce tana wani ƙara tamke fuska alamar bata san raini.
*Aisha Alto...*
[12/23, 10:15 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
_Ina mai bawa makaranta littafin nan haƙuri a bisa jina shiru da ku kayi kwana biyu, hakan ya faru ne ta dalilin rashin mahaifina da nayi, to Alhamdulillahi mun gode Allah yanzu na dawo zanyi ƙoƙari in ƙarasa muku kamar yadda na fara. Nagode matuƙa Allah yabar zumunci da Ƙauna. Son So FISABILILLAHI🤝_
4️⃣
Kamar ance ya ɗago kai ya hangeta tana tahowa cikin wani irin taku tana rangaji, tsam ya mike tsaye lokaci ɗaya yana maida wayarsa cikin aljihu ya matsa jikin ƙofar gidan ya tsaya yana jiran ta ƙaraso, Fadwa kuwa ganin haka yasa ta ƙara wani shan mur ta nufosa tana zuwa ko kallonsa ba tayi ba ta zura hannu a cikin jakarta ta lalubo makulli ta buɗe ƙofar ta tura lokaci ɗaya ta buɗe ta shige ciki abinta ba tare data waigo ta kalli inda yake ba.
Sosai lamarin nata ya ƙara ɗaure mai kai ya bashi mamaki amma sai bai ce komai ba ya kaɗa kai yabi bayanta zuwa cikin gidan, koda ya shiga ya iske har ta buɗe ƙofar ɗakin ta shige abinta, dan haka ya ɗaga labulen shima ya shiga cikin ɗakin. A falo ya isketa zaune tayi rashe rashe ta miƙe ƙafafuwanta ta cire gyalen doguwar rigar dake jikinta ta wurgar gefe, tana ganinsa ta miƙe da sauri zata shige uwar ɗaka. Cikin zafin nama ya fizgota da ƙarfi ta dawo da baya ya hankaɗata ta tafi taga taga kamar zata kifa Allah ya taimaketa tayi saurin dafe bango, ta ɗago a tsorace lokaci ɗaya tana watsa masa wani mugun kallo cike da masifa tace "Malam lafiya zaka wani fizgoni haka kamar wata tsumma..ko kana bina bashi ne ko kuma so kake ka ji min ciwo ne....?"
Bai tanka mata ba illa shan gabanta da yayi ya tsareta da ido yana faɗin "Bana binki bashin komai Fadwa amma daga ina kike shine kawai abinda nakeso inji, domin wannan shegen yawon naki mara dalili ya isheni na gaji bansan ya kikeso in yi da raina ba....?" Ya ƙarashe maganar cikin sanyin muryarsa lokaci ɗaya yana kallonta.
Sakin tsaki kawai Fadwa tayi ta raɓa ta gefensa ba tare da tace komai ba ta shige cikin ɗaki ta barsa nan tsaye sake da baki yana aikin binta da kallo cikin tsantsar takaicinta, dan Allah ya gani lamarin Fadwa ya gama isarsa ya fara gajiya da abubuwan da take masa, amma yasan yadda zaiyi da ita matakin gyara mata zama kawai zai ɗauka sai yaga yadda zatayi, gajiya yayi da tsaiwar ya kaɗa kai ya juya shima ya fice daga gidan ya nufi bustop ɗin unguwarsu.
Gurin mai soya doya da kwai ya fara zuwa ya siya na ɗari biyu ya biya kuɗin sannan ya juya ya nufi gurin mai tsire shima ya siya na ɗari uku kana ya siyan mata madarar holandia yoghut mai sanyi shi kuma ya siyan ma kansa pure water guda biyu ya nufo gida.
Sai daya tsaya a wani shago nan kusa dasu ya siya maganin sauro da ƙyandir kasancewar unguwar tasu suna da matsalar rashin wuta, dan sai suyi kusan kwana uku huɗu har biyar ma ba'a kawo musu ba, kuma yasan Fadwa bata son zama a duhu, shiyasa kullum sai ya siya idan zai shiga gida.
Dan yasan halinta sai tai ta complain tana masifa tace ya barta a cikin duhu.
Sai daya rufe ƙofar gidan yasa sakata, sannan ya wuce ya shiga ɗakin ya iske falon tsit alamar har lokacin bata fito ba tana can cikin uwar ɗaka, sai da yayi sallama kana ya ɗaga labulen uwar ɗakan ya shiga.
Ko ɗago kai ba tayi ta kallesa ba, ballantana yasa ran zata amsa mai sallamar da yayi, tana zaune tayi rashe rashe a tsakiyar ɗan madaidaicin gadon six by six ɗinsu na katako, da kuɗi zube a gabanta tana ƙirgawa cike da jin daɗi sai faman washe baki take tana ƙara lissafa kuɗin cike da farin ciki.
Sosai lamarin nata ya bashi matuƙar mamaki, gefe guda na zuciyarsa kuwa, sai ya shiga tambayar kansa da cewa ina ta samu waɗannan kuɗi masu yawa haka, waye ya bata, me tayi da aka bata su...ko dai...ko dai...?
Da sauri ya kori sheɗan da banzan tunanin da yake son bijiro masa dashi akanta.
Kafin ya fara takawa a hankali a hankali har ya ƙarasa kusa da ita bayan ya ajiye ledar dake hannunsa cikin nutsuwa ya zauna a bakin gadon kusa da ita ya zuba mata ido ƙyam yana kallonta, ganin irin kallon tuhumar da yake aika musu dashi ne lokaci ɗaya ita da kuɗin dake zube a gabanta yasa ta ɗago kai tana harararsa kafin cikin tsiwa tace "Lafiya dai ko aka zo aka wani tasani gaba ana ƙare min kallo...?"
Bai tanka mata ba, sai ma ƙara tsareta da yayi da ido ƙirr yana kallonta, kafin kawai taga ya miƙa hannu kan kuɗin zai kwashe, aiko da sauri ta buge hannunsa, ta tattare kuɗinta ta ɗaga cinyarta ta tusa a ƙarƙashinta ta danne, kana ta ɗago tana aika mai da wani mugun kallo tana faɗin "Ina ruwanka da kuɗina da zaka taɓa min..? Ko kuma ka ajiye kuɗin da suka kai yawan wannan ne anan ɗakin baka gansu ba da kake tunanin naka ne na kwashe...?"
Ta faɗa kai tsaye tana wani tsatstsaresa da idanu cike da fitsara.
Ba tare daya kulata ba ya sake kai hannu a karo na biyu zai janyeta gefe domin ya kwashe kuɗin, ta riƙe hannun nasa ta matsa gefe da sauri tana faɗin "Oh ni Fadwa! Yau ina ganin wata lukutar masifa, wai dan Allah meye nufinka dani ne, ina ruwanka da kuɗina...?"
Ta faɗa lokaci ɗaya tana watsa mai wata muguwar harara kamar ƙwayar idanuwanta zasu faɗo ƙasa.
Ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke kana ya dubeta cikin natsuwa yana faɗin "Akwai ruwana har da tsakina Fadwa, tunda dai a ƙarƙashin ikona kike..kinga kuwa duk wani abu da yake naki shima ya zama a ƙarƙashin ikona, kuma dole ne idan na ganki da abu ko menene in tambayeki a ina kika samu, balle abinda na san baki dashi kuma nima da ya kamata in baki bani dashi, kinga kuwa dole zan tuhumeki inji a inda kika samesu..."
Daga haka ya sake miƙa mata hannunsa lokaci ɗaya yana kallonta cikin ido yace "Ciro kuɗin ki bani su nan, kuma sannan ki gaya min gidan uban da kikaje da kuma aikin da kikayi musu, wanda ya kai su ɗauki wannan uban kuɗin haka su baki....?"
Wani mugun kallon haushi Fadwa ta watsa masa tana ƙara haɗe fuska take faɗin "Gidan Hajiya Kalsoom naje yayar ƙawata Hajiya Lubna kuma ai kana ganin irin motar da aka saukeni a ciki zaka san ba daga gidan matsiyata nake ba, kuma kuɗi ma daka gani itace ta bani su dubu hamsin gasu cas tace in kai ɗinkin less ɗin da Hajiya Labiba ta siyan min na ankon ƙanwarsu Lubna ƙawarmu, sannan zan siya takalmi da jaka da gyale mahaɗin leshin da sauran abubuwa, dan haka akan me zaka wani tsareni kace sai na baka..? Ni wallahi Allah ya gani bazan iya ɗaukar kuɗina ina baka ba, ina dalili...!
Ta faɗa lokaci ɗaya tana watsa mai wani kallon banza cikin nuna tsantsar jin haushinsa.
Ɗauke kansa yayi da sauri ya haɗe fuska bai ce komai ba.
Ganin bai sake tanka mata bane yasa ta miƙe da sauri ta tattare kuɗinta ta kwashe ta buɗe jakarta dake rataye a ɗakin ta zuba aciki, kana ta dawo ta zauna tana rarraba ido.
Kafeta da ido yayi kawai yana kallonta kafin ya tashi, tana ganin ya miƙe itama ta miƙe zumbur ta matsa gurin jakarta ta riƙe ƙugu ta tsaya, dan ita a tunaninta jakar zai ɗauke. Shiko ko kallonta bai sake yi ba.
Ya juya yaje ya ɗauko filet guda biyu a kwando ya dawo ya buɗe ledar daya shigo da ita ya ciro ƙunshin tsiren ya juye kana ya fito da ɗayar ledar itama ya juye doya da kwan dake ciki a ɗayan filet ɗin sannan ya fito da holandia ya ajiye, kana ya miƙe ya ɗauki buta ya fita waje yaje ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna, duk hakimar na nan tsaye ta zuba mai ido tana kallonsa, ɗaukar filet ɗin tsiren yayi ya tura gabanta yana faɗin "Gashi nan ki zauna kici karya huce, dan idan ya huce ba zai yi miki daɗin ci ba..."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana matso da ɗayan filet ɗin doya da kwan gabansa ya saka hannu ya fara ci.
Ba kunya kuwa Fadwa ta dawo kusa dashi ta zauna ta jawo filet ɗin gabanta ta saka hannu ta fara ci hankali kwance, tana korawa da madarar holandia yoghut ɗin.
Shi dai sai kallonta kawai yake bai ce komai ba.
Sai da ta kusan cinyewa dan ɗan sauran daya rage bai wuce yanka uku ko huɗu ba sai ƴar diddigar ƙuli ƙuli dasu albasa, sannan ta cire hannunta ta tura mai filet ɗin gabansa lokaci ɗaya tana suɗe hannunta take faɗin "Alhamdulillahi ya Allah ka ƙara wadatamu da wadatarka ka yaye mana talauci, gaskiya arziki yayi a rayuwa Ya Azeez talauci mugun ciwo ne, yanzu da kullum ina samu kana kawo min irin wannan kayan daɗin ai da babu abinda zai dameni...amma nasan na jiya da yau ne kawai ƙila kuma sai nan da tsakiyar wata kafin in sake samun wani irin haka, gashi ni kuma bakina ya riga ya saba da cin daɗi, shiyasa kwata kwata bana iya haƙuri nake tafiyata gidan ƙawayena inci abun da raina yakeso in ƙoshi, saboda nasan ba samu nake a gidana ba su kuwa komai na jin daɗin rayuwa akwai a gidajensu suna dashi, kuma komai nakeso idan naje shi ake yi min, shiyasa a kullum nake ƙara godewa Allah daya dubeni ya bani ƙawaye na gari ƴaƴan masu arziki kuma matan masu kuɗi, kaga nima da haka na samu ai da nafi kowa sa'a a duniya da jin daɗi...."
Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana ƙoƙarin miƙewa bayan ta ɗauke kwalin holandia yoghut ɗinta ta ƙarasa shanyewa kana ta ajiye masa fankon kwalin agabansa, ta fice zuwa falo ta ɗauki buta ta fita tsakar gida taje ta wanke hannunta kana ta dawo ta zauna a falo, ɗan jim tayi kafin ta tashi tana jan siririn tsaki a fili tace "Kai! Wallahi talauci bai yi ba, haba ina tsiya taga rana wannan wace irin masifa ce...ace yanzu ko ɗan irin talabijin ɗin nan na zamani da mutum zaiyi kallo ma babu, ballantana akai ga maganar wata shegiya fanka da generator, wanda idan zafi ya ishi bawa yadda bamu da wutan nan zan ɗan dinga kunnawa ina ɗan shan iska ko na rage wani raɗaɗin...?
Ta faɗa cike da baƙin ciki kana ta bankaɗa labule ta shige cikin ɗakin ta wucesa ta haye gado ta kwanta abinta tana jan tsaki.
Shiko dama tunda ta ajiye masa filet ɗin tsiren a gabansa bai ɗaga kai ya kalla ba ballantana yayi tunanin ɗauka ya kai bakinsa, ya cigaba da cin doya da kwansa hankalinsa kwance, sai daya cinye abunsa tsaf yasha pure water ɗaya yayi hamdala, kana ya tattare kayan ya ɗauke ya matsar dasu gefe ya ajiye, sannan ya miƙe yaje ya ɗaurayo hannunsa a waje, ya dawo ɗakin ya tsaya a kanta lokaci ɗaya yana ɓalle maɓallan gaban rigar dake sanye a jikinsa yake faɗin "Kinyi magriba da isha'i ne da kika kwanta zakiyi bacci, ko kuwa kin manta da anayi ne tunda ba damunki dama sallar tayi ba..?"
Ya faɗa yana ƙoƙarin cire rigarsa bayan ya gama ɓalle maɓallan.
Banza tayi dashi bata kulasa ba, sai ma lumshe idanuwanta da tayi kamar mai bacci, kaɗa kansa kawai yayi kafin yace "Malama ki tashi kiyi sallah kafin ki kwanta, dan kinsan ba barinki zanyi kiyi bacci ba alhalin nasan bakiyi sallah ba...dan haka gara kawai ki tashi tun kan ranki ya ɓaci kiyi sallah kafin ki kwanta.."
Ya faɗa yana ƙarasa cire rigarsa ya ajiye kafin ya cire dogon wandon dake jikinsa, yayi saura daga shi sai ɗan gajeren wando ya ɗauko bokiti ya cikasa da ruwa sannan ya ɗauki brush ya matsa makilin akai kana ya ɗauki kwandon soson wanka ya juya zai fice daga ɗakin bayan ya sake jaddada mata kan cewa ta tabbatar ta tashi tayi sallolin da ake binta kafin ya fito wanka ya dawo ɗakin.
Tana jinsa tayi banza dashi ta sake gyara kwanciyarta abinta.
Tsawon mintuna