Showing 6001 words to 9000 words out of 113443 words
ta ƙara jan ledar gabanta tana kallonsa tace "Madaran fa...?" Murmushi kaɗai yayi yasha kaɗan ya miƙa mata da sauri ta ƙarɓa tana faɗin "Yauwa ko kai fa...." Take faɗa tana shan Youghort ɗin tana wani sauke numfashi ganin in ya tsaya kallonta zai ɓata ransa ne a banza yasa ya buɗe ƙofa ya fita yayo alwala ya dawo yazo ya ƙara kulle ɗakin tana nan zaune ta yi rashe rashe tana cin naman tana korawa da madaran kallo ɗaya yayi mata ya girgiza kai ya shimfiɗa darduma ya daidaici gabas ya tada sallar shafa'i da wuturi.
*Aisha Alto..*
[12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
____________________________
*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*
*SADAUKARWAR SO!!!*
*Sun taso tun yara tare...Iyayensa sun fifitasa akansa shima yafi fifita buƙatun ɗan goggonsa fiye da buƙatunsa, a tasowarsu kowa halayyarsa ta bambanta yana jin daɗi da sha'awar ganin rayuwarsa cikin barkwanci saɓanin shi daya kasance magana ma wahala take mai...Rana tsaka dalilin maƙotaka wata yarinya ta ratso rayuwarsu ya fara sonta ba tare daya sani ba, ashe shima ɗan uwansa ya kamu da soyayyarta, bashi da zaɓi illa yin SADAUKARWAN SO...!*
*Ba tare da kowa yasan yana sonta ba...Ya binne abun a ranshi bai taɓa koda wasa wani daga cikinsu ya fahimci abinda ke cikin zuciyarsa ba...Kamar yadda yayi SADAUKARWAN SO haka shima akayi mai SADAUKARWAN SO...!*
Shin wace irin Ƙauna ce haka a tsakaninsu da har zai iya ma ɗan uwansa SADAUKARWAN SO...?
Nasan kuma dole zaku yiwa kanku waɗannan tambayoyin, kuma zaku zaƙu da son jin amsarta..To tambayar taku ɗaya ce amma amsoshinta suna da yawa kuma ba'a ko'ina ne zaku samu amsarta ba sai a cikin wannan shahararren labarin SADAUKARWAR SO wanda shahararriya kuma fiƙrarriya zaƙaƙurar marubuciya ta rubuta wato *JAMILA UMAR JANAFTY* kuma zaku iya samun duk wannan garaɓasar da romon daɗin labarin ne akan farashi mai rahusa kamar yadda ta saba muku:
*Zaku biya kuɗin karatu ₦300 ta wannan asusun bankin 0552179550 JAMILA UMAR GTB sai a turo shaidar biya ta wannan lambar 09069067488*
*KO*
*Katin MTN ₦400 ta wannan lambar 09069067488*
*Ƴan Niger kuwa zaku iya tuntuɓarmu akan wannan lambar +22794775574*
Karku sake ayi babu ku domin wannan tafiyar miƙaƙƙiya ce mai nisan zango mai neman ƙarin bayani sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 09069067488 muna maraba daku masoya sai kunzo🤝
____________________________
3️⃣
Koda ya idar ya jima zaune a gurin yana addu'o'i kafin ya shafa ya miƙe tsaye lokaci ɗaya yana naɗe darduman ya ajiye kana ya zare jallabiyar dake jikinsa ya haye gado yay kwanciyarsa ya juya mata baya.
Watsawa bayansa wata uwar harara tayi lokaci ɗaya tana taɓe baki kafin ta ɗauke kai ta ci gaba da shan Youghort ɗinta, sai data shanye abunta tas kana ta miƙe ta ɗauki buta ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita tsakar gida taje ta wanko hannunta sannan ta dawo ta sake kulle ƙofar ta wuce uwar ɗaka ta ajiye butar, bata ko kalli ɓarayinsa ba ta haye gado abinta tai kwanciyarta itama ta matsa nesa dashi ta juya masa baya lokaci ɗaya tana sakin gyatsa haɗe da tsaki, duk yana jinta amma yay luf bai ko motsa ba ballantana tasan cewa idonsa biyu, haka tai ta juye juye tana sukur sukur a gadon kamar wata tsutsa duk yana jinta yay banza da ita, sai ma sake matsawa da yayi can ƙarshen gadon ya bar mata sauran filin.
Ta jima tana mutsu mutsun kafin zuwa can ya fara jin saukar numfashinta a hankali a hankali alamar tayi bacci, sai da ya bari baccin nata ya ɗan yi nisa tukunna ya juyo ya matso kusa da ita a hankali ya ɗora kansa akan filon da kanta yake cikin natsuwa ya kwanta a gefenta ya juyo da fuskarta suna fuskantar juna ya zuba mata idonsa ƙirr yana ƙarewa ɗan madaidaicin ƙaramin bakinta kallo, kamar ana fizgarsa zuwa gareta haka ya dinga matsar da fuskarsa a hankali a hankali kamar mai jin tsoron kar wani ya kamashi, da haka har ya ɗora bakinsa akan nata ya fito da harshensa ya soma lasar saman lips ɗinta cikin wani irin salo da muradi.
Fadwa kuwa cikin baccin daya ɗan soma ɗaukarta ta fara jin ɗumin wani tattausan abu mai ɗan tsantsi tsantsi da laushi akan lips ɗinta, duk a zatonta mafarki take dan haka ta buɗe baki cikin magagi da shauki, aiko bai yi wata wata ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya zura tattausan harshensa ya kamo nata ya shiga tsotsa cikin wani yanayi mai daɗi haɗe da muradi mai girma, tana jin haka itama ta cafki nasa ido rufe ta shiga basa wani lafiyayyen tsotsa mai cike da zallan shauki da nishaɗi.
Sosai ya zage ido rufe ya tsotse bakinta iya son ransa, wanda shi kansa ya sani inda ace idonta biyu babu yadda za'ayi ta barsa ya matso kusa da ita balle har ya samu damar taɓa wani sassa na jikinta irin haka, shiyasa daya samu wannan damar ya zage ya dama abinsa iya yanda ransa yakeso.
Sai daya gama yamutsata iya son ransa dan sai daya gaji don kansa sannan ya ƙyaleta ya koma gefe ya kwanta yana maida numfashi lokaci ɗaya da ajiyar zuciya, ba daɗewa kuwa wani bacci mai masifar daɗi yayi awon gaba dashi, itako Fadwa gaba ɗaya ba tasan abinda yake faruwa ba, dan ita duk a zatonta mafarki kawai take kuma a cikin bacci komai yake faruwa, ga wani shegen daddaɗan bacci mai cike da nishaɗi daya sake kwasheta cikin ƙanƙanin lokaci sai take jin kanta kamar tana yawo a sararin samaniya ne don daɗi, shiyasa gaba ɗaya bata san abinda ya wakana ba a tsakaninsu.
Da asuba tun misalin ƙarfe 5am. Ya tashi ya lalubo wayarsa ya kunna fitila ya haska fuskarta tana ta sharar bacci abunta hankali kwance ta ƙanƙame filo a ƙirjinta, ɗan murmushi yayi kana ya shafa kumatunta lokaci ɗaya yana faɗin "Rigimammiya kawai...ji ɗan bakin rashin kunyar...." Ya faɗa yana zuro ƙafafuwansa ƙasa ya sauko daga kan gadon bayan ya ajiye wayar a gefen gado yaje ya ɗibi ruwa a bokiti sannan ya ɗauki buta ya fita ya shiga banɗaki yayi wanka kana ya ɗauro alwala ya fito ya dawo ɗakin ya zura wata jallabiyarsa ruwan madara ya fesa turare kana ya ɗauki casbaha ya fita ya tafi masallaci.
Koda aka idar da sallan bai fito daga masallacin ba ya zauna ya ɗauki Kur'ani ya soma karatu cikin daddaɗar muryarsa mai sanyi da daɗin saurare, sai da gari yayi haske sosai sannan yayi addu'a ya shafa kana ya rufe Kur'anin ya maida gurin da ake ajiyewa ya ajiye kana ya fito ya nufo gida.
Sosai yayi mamakin ganinta riƙe da buta ta fito daga banɗaki, dan shi duk a tunaninsa zai zo ne ya isketa kwance akan gado tana sharar bacci kamar yadda ta saba bai taɓa zaton zai dawo ya iske ta tashi har ta ɗauki buta tana ƙoƙarin yin alwala ba, ya ɗauka idan ya dawo sai yay ta tashinta ya dinga nacin taje tayi alwala tazo tayi sallah tukunna ya samu da ƙyar da suɗin goshi ta tashin, amma sai yaga saɓanin hakan, wai yau Fadwa ce da kanta ta tashi ta fito tunda sanyi safiya ba tare da ya dawo yasha wahalar tashinta ba, kai gaskiya abun ya faranta ransa sosai yaji daɗi. Ina ma ace zata ɗore a haka..? Aiko da babu wanda zai kaisa farin ciki.
Fadwa kuwa ganin irin kallon ƙurullar da yake mata ne yana sakin wani makirin murmushi cike da jin daɗi yasa ta kallesa a yatsine tana watsa masa harara tace "Wannan kallon fa Malam lafiya....?"
Ya Azeez ya sauke numfashi yana faɗin "Lafiya ƙalau wallahi, kawai dai naji daɗin ganinki ne yau kin tashi da wuri zakiyi sallah shiyasa murnata ta kasa ɓoyuwa...."
Saboda takaici Fadwa bata samu daman magana ba ta raɓa ta gefensa ta wuce can nesa dashi ta nemi waje ta tsugunna ta fara alwala, da sauri ya ƙarasa kusa da ita ya tsaya yana ƙare mata kallo cikin mamaki kafin ya miƙa hannu ya karɓe butar dake hannunta lokaci ɗaya yana faɗin "Wai kin ma yi wanka kuwa da kike niyyar yin alwala....ko kuwa ke a naki haukan zakice bakiji wani sauyin yanayi a tattare da jikinki ba wanda ya cancanci ace dole sai kin...."
A zafafe ta fizge butar a hannunsa tana faɗin "Don Allah Malam ni bani inyi alwala ta bazanyi wankan ba ko dole ne...." Ta faɗa kai tsaye tana watsa masa kallon banza.
Murmushi yayi kawai kana yace "Aiko dole ne sai kinyi wanka Malama tunda ya kamaki, dan haka ki tashi kawai kije kiyi wanka sannan sai kizo kiyi alwala kiyi sallah. Dan wallahi bazan taɓa bari kiyi sallah a haka da najasa a jikinki ba tare da kinyi wanka ba...."
Tsabar takaici da baƙin ciki da suka turnuƙe Fadwa kasa cewa komai tayi kawai ta juya da nufin ci gaba da ɗaura alwalarta, taji ya sake fizge butar a hannunta yana faɗin "Ai wallahi duk abinki bazan taɓa bari kiyi sallah a haka ba sai kinyi wanka, dan ni ba jahili ba ne...."
Yana gama faɗin haka ya juya da butar a hannunsa ya shige ɗaki, ba jimawa ya sake fitowa da butar a hannunsa wacce yaje ya cikota da ruwa yazo ya dire a gabanta yana faɗin "Gashi nan ki tashi kije kiyi wanka sai kiyi alwalar kiyi sallah...." Ya faɗa lokaci ɗaya yana juyawa ya wuce ya barta nan.
Fadwa data daskare a tsugunne tana kallonsa cikin mamaki da al'ajabin dagewar da yayi kan dole sai tayi wanka kafin tayi sallah, tai ɗan jim cikin nazari kana ta sauke numfashi a hankali tana faɗin "Kutt kar dai ace dama ba mafarki nayi ba a zahiri ne abun nan ya wakana..to idan a zahiri ne ta ya hakan ta faru..? To idan kuma mafarkin ne ma ta ya akayi zai sani har ya matsa yace dole sai nayi wanka, ai kuma koda mafarkin ne ma ya zama dole ne sai nayi wankan...kanbuu kar dai kuma ace sakar mai jiki naje nayi yay yadda yake so dani tunda nasan halinsa kamar maye yake....?" Ta faɗa a fili tana miƙewa tsaye cike da baƙin ciki kafin tace "Tabɗi aiko daya gama dani, ni kuma da na cika banza shashasha sauna wallahi...." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana duban jikinta.
Haka tai ta juyi tana ƙara nazarin jikinta, amma duk bata gano komai ba ta ja wuyar rigar baccin dake jikinta data kasance mai faɗi ta leƙa ƙirjinta nan ma bata ga alamar komai ba. Rasa abun yi tayi kawai sai ta ɗauki butar ta wuce banɗaki taje tayo wankan kana ta ɗauro alwala ta fito tana zagin Ya Azeez a zuciyarta ta shiga ɗaki, a falo ta iskesa zaune yana ta danne danne a ƴar wayarsa bata ko kalli inda yake ba ta dangwarar da butar ta wucesa fuuuu ta shige cikin uwar ɗaka, ko ɗago kai baiyi ya kalleta ba shima ya ci gaba da abinda yake yi.
Sai data ɗaura zani akan rigar baccin dake jikinta kana ta zura hijabi ta shimfiɗa darduma ta tayar da sallah, bayan ta idar ta daɗe a zaune kafin ta tashi ta linke darduman ta sagaleta a jikin ƙofa ta fita falo, har lokacin yana nan zaune a inda ta barsa, sai dai yanzu ba danna wayar yake ba tana ajiye ne a gefensa ya jingina da bango ya lumshe idanunsa kamar mai bacci, ba tare da tunanin komai ba ta ƙarasa ta tsaya a kansa ƙerere tana faɗin "Nifa yunwa nake ji Malam kaji dani..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana watsa mai wani kallon sama da ƙasa.
Shiru yayi bai tanka mata ba, ya buɗe idanunsa a hankali ya ɗauki wayarsa yana duba lokaci ƙarfe 7:49am. Ya gani sai da ya maida wayar ya ajiye kana ya ɗago kai ya kalleta cikin natsuwa yace "Yi haƙuri ina zuwa bari inje in haɗo miki kayan tea..." Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa, da sauri ta matsa gefe tana wani kumbura baki cike da shagwaɓa tace "Nidai dan Allah ya Azeez yau ɗaya ka ɗan haɗo min har da soyayyen kwai dan Allah kaji....?" Ta ƙarashe maganar a shagwaɓe tana harararsa a fakaice.
Bai ce komai ba ya ratsa ta gefenta ya shige uwar ɗaka bai wani jima ba ya fito ya fice daga ɗakin ba tare da ya kalleta ba ya zura silifas ɗinsa ya fice daga gidan.
Ɗan taɓe baki tayi kana ta samu guri ta zauna lokaci ɗaya tana ƙarewa falon kallo a ranta tana ji kamar ta ɗora hannu akai ta rushe da kuka saboda tsabar baƙin ciki da takaici, wai kamar ita ace wannan fankan fayau ɗin shine falonta, ba kujeru ba komai sai kace wani zauren almajirai.
Tana nan a zaune ya dawo da baƙar leda riƙe a hannunsa ya shigo ɗakin bakinsa ɗauke da sallama ba tare daya jira amsawarta ba ya nufeta direct ya dire mata ledar a gabanta yana faɗin "Gashi nan na haɗo miki har da ruwan lifton, sai ki haɗa tean kawai...." Ya faɗa yana juyawa ya shige cikin uwar ɗaka.
Da kallo kawai ta bishi ba tare da tace komai ba ta miƙe ta bi bayansa taje ta ɗauko kofi da cokali ta dawo ta zauna ta buɗe ledar ta fito da abubuwan dake ciki, washe baki tayi cike da murna ta yagi wainar kwan ta tusa a bakinta ta fara taunawa tana wani lumshe idanu cike da jin daɗi kafin ta ɗaga murya ta yadda zai iya jiyota daga can cikin uwar ɗakan tace "Allah sarki Ya Azeez gwarzon Fadwa, na gode Allah ya ƙara dalili, lallai yau litinin ɗin tawa ce Allah ya kawo arziki lodi lodi kai ta siyo min kayan daɗi ina ci...." Ta faɗa tana ƙara yago kwan ta haɗa da biredi ta danna a bakinta.
Yana jinta bai tanka mata ba ya girgiza kai kawai, ya ɗauki bokiti ya cikasa da ruwa ya fito ya ɗauki soson wanka ya fice, da wata ƙatuwar harara ta rakasa tana sakin tsaki ƙasa ƙasa tace "Ji ina masa magana yayi banza dani sai kace kurma, mutum sai shegen faɗin rai da girman kan tsiya kamar wani mai faɗa aji...."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana jawo kofi ta juye ruwan lifton ɗin a ciki kana ta zuba madara da milo ta haɗa tean ta mai kauri ta jujjuya ta soma kurɓa tana wani lumshe ido.
Bai wani jima sosai ba ya fito tana cikin karyawa ya shigo ɗakin ya wuceta ya shiga ciki sai daya shafa mai sama sama kana ya ɗauki wata rigar T-shirt ɗinsa blue mai gajeren hannu da baƙin wandon jeans ya saka kana ya ɗan fesa turare ya ɗauki makullin keke napep ɗinsa ya fice, har yasa kai zai fice ya dawo da baya da sauri ya ƙarasa kusa da ita yana faɗin "Ni zan fita aiki, zuwa anjima da rana idan Allah ya kaimu zan dawo in kawo miki kuɗin abinci kiyi haƙuri yanzu ba ko sisi a hannuna dama wanda zan bar miki ɗin ne dashi na siyo miki kwai, kinga ni ko karyawar ma ban samu na yi ba sai na fita tukunna..dan haka kiyi haƙuri zan dawo in kawo miki...."
Ko gama rufe baki bai yi ba ta ɗago kai tana faɗin "Ba damuwa saika dawo ɗin...."
Ya amsa yana ƙarasa ficewa daga ɗakin, kamar kuwa daman jira take ya fice ta ɗaga kofin tean da sauri ta ƙarasa shanyewa a gurguje ta cinye kwan kana ta ƙulle sauran buredin ta miƙe ta tsallake kofin da ledojin ta barsu nan ta wuce taje ta ɗauki bokitin daya fito wanka ta diɓi ruwa ta ɗauki kwandon soso ta wuce banɗaki.
A gurguje tayo wankan ta fito tazo ta shafa mai ta zauna ta tsantsara kwalliyarta mai kyau da burgewa kana ta buɗe akwatinta ta ɗauko wata baƙar doguwar rigarta wacce tasha kwalliyar duwatsu masu walwali tun daga sama har ƙasa ta zura kana ta yana gyalen a kanta ta ɗauki ƙaramar hand bag ɗinta ta sagala a kafaɗarta ta ɗauki kwaɗo ta fice tana taku ɗai ɗai.
Sai data fara kulle ƙofar ɗakin sannan ta juya ta nufi ƙofar gidan cikin wani irin taku ta fice ta jawo ƙofar gidan itama ta kulle, kana ta jefa ɗan makullin a cikin jaka ta wuce ta nufi bakin titi, mai napep ta tare ta hau bayan ta gaya mai inda zai kaita yaja suka wuce.
Gaban wani tangamemen haɗaɗɗen gida mai ɗauke da wani ƙaton gate ruwan madara a cikin unguwar Rimi Gra Fadwa ta nuna ma mai napep ɗin yayi fakin ta fito ta buɗe jakarta ta ɗauki ɗari biyar cikin irin kuɗin da Hajiya Labiba ta bata jiya ta miƙa masa kana ta juya cikin iyayi da yanga ta tura ƙaramar ƙofar ta shige, security's ne kota ina suna ta zagaye a fankacecen harabar gidan. Haka ta dinga wucesu tana ratsesu ba tare da tsoron komai ba suma kuma babu wanda yabi ta kanta dan sun santa ƙawar matar gidan ce tana yawan zuwa akai akai shiyasa duk suka ganeta.
Direct ƙofar da zata sadata da shiga babban falon gidan ta nufa kai tsaye ta danna wani abu a gefe yayi ƙara zuwa can sai ga wata ƴar matashiyar budurwa wacce da ganin mai aiki ce tazo ta buɗe mata, tana ganin itace ta saki ƙaramin tsaki ƙasa ƙasa yadda bazata jita ba a daƙile tace "Sannu da zuwa Hajiya shigo...." Ta faɗa tana matsawa daga hanya, wani kallon sama da ƙasa Fadwa ta watsa mata a wulaƙance tana faɗin "Dama fa tsiyar talaka kenan bai iya samun guri ba, ni dalla matsa min a hanya in wuce bake nazo gani ba da wasu shegun koɗaɗɗun kayanki kamar na masu sharar titi...." Ta faɗa tana tureta gefe ta shige ciki.
Da kallo kawai budurwar ta bita kafin ta girgiza kai ta maida ƙofar ta rufe ta juya ta wuce kichin abinta tana ƙunƙunai da zagin Fadwan a zuciyarta.
Fadwa kuwa duk bata san tana yi ba tana can gurin ƙarewa haɗaɗɗen falon mai kama da aljannar duniya kallo wanda ya gaji da haɗuwa ya tsaru iya tsaruwa kamar fadar wani hamshaƙin sarki ko shugaban ƙasa, dan kaf cikin ƙawayensu ta sani babu wacce gidanta ya kai kwata kwatan haɗuwan na Hajiya Kalsoom duk da ta kasance yaya ce a gurin