Showing 45001 words to 48000 words out of 113443 words

Chapter 16 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7555

Gwamna Road zai juya ya ɗauki hanyar unguwarsu ya hangi wata matashiyar budurwa wacce bazata wuce sa'ar Imaan ƙanwarsa ba tsaye a bakin titi daga gefe tana ɗaga mai hannu, da kamar ba zai tsaya ba har ya wuce sai kuma yayi wani tunani ya dawo da baya da baya a hankali ya gangara gefen titi ɗan nesa kaɗan da ita yayi parking ya tsaya ba tare daya fito ba ya dafe kansa dake tsananin sara masa dan har wani irin jiri jiri yake gani daga zaunen kamar zai kifa ya faɗi.


Cikin sauri ta ƙaraso kusa da napep ɗin ta tsaya daga gefe tana ɗan leƙensa tace "Dan Allah Malam taimako muke nema motarmu ce ta lalace gashi bamu san ko'ina ba mu baƙi ne yau ɗin nan muka shigo garin ga dare ya fara yi bamu san inda zamu dosa ba..dan Allah ka taimaka mana..."


Cikin natsuwa ya ɗan juyo da fuskarsa yana kallonta kafin yace "To yanzu ni wane irin taimako kukeso inyi muku nida ba bakanike ba...?"
Ya faɗa lokaci ɗaya yana ɗauke kansa, ɗan taɓe bakinta tayi kafin tace "Taimaka mana kawai zakayi ka kaimu inda kasan zamu samu bakanike ya duba mana pls...." Ta faɗa kai tsaye tana zumɓura baki, dan ta ga alamar mutumin miskili ne na ƙarshe gashi da alama yana da taƙama da jin kai domin ko magana ta ga da ƙyar yake yin ta yana wani basarwa kamar basarake.


Shiru yayi bai ce mata komai ba, ganin haka yasa ta rausayar da kai tana faɗin "Pls ka taimaka mana dan Allah..."


Ɗan jim yayi yana kallonta daga sama har ƙasa kafin yace "Ina motar taku take...?" Cikin murna tace "Gata can gurin..." Ta faɗa tana nuna mai wata dalleliyar farar mota sabuwa dal dake fake a gefe sai ɗaukar ido take tana sheƙi, cikin mamaki ya juyo ya kalli inda motar take kafin ya sake juyowa yana kallonta yace "Ok shiga muje can bakin tsallaken mu duba ko za'a samu bakanike a gurin sai a kirasa yazo ya duba muku..." Ya faɗa yana ƙoƙarin tada keken, da sauri ta dakatar dashi da faɗin "Yi haƙuri bari in kira Auntyna mu tafi tare kar mu barta a nan ita kaɗai tana zaman jiranmu..." Ta faɗa ba tare data tsaya sauraren amsarsa ba ta juya da sauri ta nufi gurin motar da ɗan gudunta.


Tsintar kansa kawai yayi da fitowa daga napep ɗin ba tare da tunanin komai ba yabi bayanta, domin haka nan kawai ya samu kansa da jin wani mummunan faɗuwar gaba a tare da shi, haka ya dinga bin ta a baya har suka ƙarasa gurin motar a tare yaja ya tsaya a gefe ya zubawa gilas ɗin motar idanu ƙirr kamar wanda akace idan ya ƙifta idon wani abun zai iya faruwa.
Suna ƙarasawa ta zagaya ta gefe mai zaman banza dai-dai saitin inda ya tsaya ta ƙwanƙwasa gilas ɗin motar, a nutse ta sauke gilas ɗin lokaci ɗaya tana gyara kishingiɗar da tayi tamkar wata sarauniya ƙamshin haɗaɗɗen turarenta mai matuƙar tsada ya huro ta ɗago a hankali cikin wata zazzaƙar muryarta mai daɗin saurare tace "Ya akayi autar Ummi an samu bakaniken ne...?" Ta faɗa cikin muryarta mai matuƙar sanyi da sanyaya rai.


Lokaci guda Ya Azeez yaji gwiwarsa tayi masa wani irin sanyi ya ɗago kai da sauri, a cikin kyawawan idanuwanta masu matuƙar girma da haske nasa suka sauka domin hasken motocin da suke ta wucewa sun hasko gurin da kyau ga kuma hasken solar dake nan burjik akan titi, hakan sai ya bashi damar ƙarewa kyawawan brown ɗin ƙwayar idanunta kallo, wani irin dam yaji gabansa ya buga yayinda zuciyarsa ta hau bugawa da sauri da sauri da wani irin mugun gudu dan lokaci guda yaji yana neman rasa natsuwarsa, ganin yadda ya wani ɗauke kai da sauri ne ya juya zai wuce yasa ta rausayar da kai tana duban ƙanwar tata dake tsaye tana kallonta tace "Wannan shine bakaniken...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙarewa bayansa kallo a fakaice, da sauri ta girgiza kai tana faɗin "A'a fa Aunty bashi bane...wannan mai keke napep ne na roƙesa zai taimaka mana ya kaimu inda zamu samo bakaniken shine nace bari in kiraki sai muje tare..." Cikin natsuwa tace "Ok aiko mun gode sosai Malam Allah ya biyaka...?" Ta faɗa kai tsaye tana ƙoƙarin buɗe motar ta fito.


Ƙarar tsadaddiyar wayarta ƙirar iPhone 12pro max dake riƙe a hannunta ne ya dakatar da ita daga ƙoƙarin fitowa da take daga cikin motar, ta ɗago a tsorace tana zaro manyan idanuwanta waje tace "Oh my God...Zahra Abbie ne yake kirana...mun shiga uku yau..." Ta faɗa fuskarta cike da tsoro ƙarara tana kallon ƙanwar tata, a tsoracen itama ta kalleta kafin tace "To ki ɗauka mana Aunty kiji abinda zaice miki...." Saurin girgiza kai tayi kafin tace "In ɗauka fa kikace Zahra...to mezan gaya masa idan na ɗauka ɗin...?"
Ta faɗa tana tsareta da ido, ɗan ɗaga kafaɗarta tayi kafin tace "Sai kice masa kawai muna hanya mun kusa isa Abujan...nasan ai bazai yi mana faɗa ba sai dai kawai zaiyi faɗan meyasa muka tsiri yin doguwar tafiya mu kaɗai ba tare da direba ba alhalin munsan baya son fitarmu ko cikin gari ne mu kaɗai irin haka ba tare da wani babba a tare damu ba...ki ɗaga kawai insha Allahu bazai yi miki faɗa ba dan nasan abinda kike tsoro kenan..."


Murmushi ta saki saboda tasan wayon Zahra so kawai take ta ɗauka taji abinda Abbie ɗin zaice musu dan haka ta ɗauka kai tsaye tana cewa "Barka da dare Abbie ya Um...."


Tsit tayi tana zaro dara daran manyan idanuwanta waje cike da tsoro, kafin ta cire wayar a kunnenta ta miƙawa Zahra tana gyaɗa mata kai, a sanyaye ta ƙarɓa ta manna a kunnenta itama ta ɗan saurara, can sai ta kaɗa kai tana turo baki a shagwaɓe tace "Ayya Abbie wallahi har fa mun kawo Kaduna motar mu ta lalace shine muka tsaya za'a duba mana, amma da tuni mun isa, kuma babu abinda ya faru damu..." Ɗan jim ta sake yi tana sauraren maganar da ake mata ta cikin wayar kafin ta sake shagwaɓe fuska kamar zata fashe da kuka tana faɗin "Ai Aunty Shatu ce tace mu tafi kawai kuma har mun gayawa Aunty Salma ma muna hanya..."




Sai a lokacin Ya Azeez ya ɗago da sauri ya kalleta, dan tun lokacin da ta fara wayar ya matsa gefe ya zaro wayarsa daga cikin aljihu yana dannawa, a hankali yaga Zahran ta ciro wayar daga kunnenta ta miƙa mata amma sai taƙi ƙarɓa ta watsa mata harara tana ɗauke kanta gefe, sake maida wayar tayi kunnenta tana faɗin "Abbie taƙi ƙarba sai hararata take..."


Da sauri ta fito daga motar ta fizge wayar a hannunta tana watsa mata harara kafin ta manna a kunnenta cikin zazzaƙar muryarta tana cewa "Sharri fa take yi min Abbie...ni bance mata bazan karɓa ba..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana ƙara galla mata harara, sun ɗan jima suna magana kafin suka yanke wayar ta mayar da ita cikin jakar dake hannunta ta ɗago tana kallonta tace "Ai shikenan kuma hankalinki ya kwanta, sai ki wuce mu tafi an fasa zuwa Abujan Abbie yace mu bar motar anan zai yi magana da abokinsa Alhaji Mudi ya turo direbansa ya ɗauki motar, mu kuma muje mu kama hotel mu kwana gobe da sassafe mu koma gida..." Ta faɗa tana dungure mata kai, saurin matsawa tayi gefe tana turo baki kafin tace "Ai kece kika ja tunda wayarki ya kira kuma kina sane kika ɗauka..." Ta faɗa tana kwaɓe fuskarta kamar zata fashe da kuka, cikin mamaki take kallonta kafin tace "Oh haka ma zakice..amma ina ce ke kikace in ɗauka inji me zai ce...?"


Cikin sangarta da shagwaɓa tace "Amma ai ni ban matsa miki nace dole sai kin ɗauka ba kika ɗauka..ko Malam...?" Ta ƙarashe maganar da sigar tambaya tana kallon Ya Azeez dake tsaye ya harɗe duka hannuwansa a ƙirji yana kallon diramar tasu cike da nishaɗi, itama juyowar tayi ta kallesa da idanuwanta masu kashe jiki da saukar da kasala tace "Amma ai kana ji lokacin da tace in ɗauka ko tsakani da Allah...?"


Rasa abin cewa yayi kawai ya juya ya fara tafiya yana faɗin "Muje nidai in kaiku inda za'a samu bakaniken dare yana ƙara yi inaso inje gida in huta..."


Ya faɗa yana yin gaba da sauri, bin bayansa itama Zahra tayi da sauri tana faɗin "Aunty Shatu muje dan Allah wallahi dama na gaji na ƙosa in samu inda zan ɗan kwanta in huta..."


Banza da ita tayi ta danna wani ɗan madanni dake jikin makullin motar boot ɗin ya buɗe ta zura hannu ta ɗauko wani ɗan madaidaicin ƙaramin akwatin matafiya ja mai kyau ta dire a ƙasa kana ta sake dannna madannin boot ɗin ya rufe ta kulle motar ta ɗauki akwatin tabi bayansu, har sun shiga cikin napep ɗin yana ƙoƙarin kunnawa ta ƙaraso ta shiga itama ta zauna a kusa da Zahra tana harararta, ɗauke kanta tayi da sauri tana faɗin "Nidai Allah ya baki haƙuri Aunty Shatu..."


Banza tayi da ita bata tanka mata ba sai ma ɗauke kai da tayi cike da jin haushinta, duk yana kallonsu ta madubin dake jikin napep ɗin. Ganin ya kunna keken amma ya tsaya bai tafi ba yasa ta ɗago karaf kuwa idanunsu ya sarƙe cikin na juna da sauri ta duƙar da kanta dan haka nan kawai taji jikinta ya ɗauki rawa ta kasa jurar kallon ƙwayar idanunsa, wani yawu yaji ya sarƙe masa maƙoshi a hankali yayi gyaran murya cikin wani yanayi kafin yace "Ina mukayi yanzu neman bakaniken zamu ko...?" Tsagal Zahra tace "A'a Hotel mai kyau zaka kaimu mu kama ɗaki ko Aunty Shatu na...?" Ta faɗa kai tsaye tana kallonta, banza da ita tayi bata tanka mata ba. Shima kallonta yayi kafin yaja keken a hankali ya juya suka koma ta kan titin Gwamna Road.




Wani haɗaɗɗen Hotel dake cikin gari ya kai su suka kama ɗaki, bayan ta biya suka fito ta tsaya daga gefe tana kallonsa yana cikin keke napep ɗin a zaune yana ta faman danna ƙaramar wayarsa, kallon Zahra tayi dake gefenta tace "Kije ki ɗauko mana akwatinmu kar mu tsaidashi sannan kiyi masa godiya ki kuma tambayesa nawa ne kuɗinsa mu biyasa ya tafi kar mu sake ɓata masa lokaci..."


Haɗe fuska Zahra tayi tana kallonta kafin tace "Haba Aunty! Muje dai tare kiyi masa godiya daga nan saiki biyasa hakkinsa tunda kinga yayi mana ƙoƙari sosai ya taimaka mana, ya kamata mu nuna masa jin daɗin mu..."


Shiru tayi tana kallonta kafin ta kaɗa kai tace "Ok muje..."


Daga haka suka nufi gurin keke napep ɗin Zahra ce a gaba kafin ita, a hankali take tafiya har suka ƙarasa, Zahra ta zagaya ta gefen da yake ta ɗauko akwatinsu dake bayan napep ɗin ta dire a ƙasa kana ta juya tana kallon Auntyn tata dake tsaye tana faɗin "Aunty Shatu kizo kiyi masa godiyan mana ya wuce abinsa kar mu sake ɓata masa lokaci..."


Ɗago kyakkyawar fuskarsa yayi ya kalleta da idanuwansa masu cike da gajiya wanda itama dai-dai ta ɗago kai ta kallesa suka haɗa ido tayi saurin ɗauke kanta tana jin faɗuwar gaba kafin cikin zazzaƙar muryarta tace "Mun gode da taimakon da kayi mana...Allah ya saka maka da mafificin alkhairinsa ya biyaka da gidan aljanna fiddausi...mun gode sosai..." Ta faɗa tana ɗan matsawa gefe tayi shiru.


Jin bata sake cewa komai ba ne yasa Zahra ta ɗago ta kalleta kana cikin yin ƙasa da murya tace "To baki tambayesa nawa zamu bashi ba Aunty Shatu...kuma kinyi shiru...?"


Har lokacin kallonta yake yi ƙirr ya kasa ɗauke idanuwansa daga kanta, ɗagowa tayi ta saci kallonsa itama karaf suka sake haɗa ido da sauri ta sauke kanta ƙasa tana faɗin "Nawa zamu baka...?" Jin yayi shiru bai yi magana ba yasa ta sake cewa "Ina nufin kuɗin kawo mu nan da kayi...nawa ne...?"
Ta faɗa tana kallon Zahra data zuba mata ido ƙirr tana kallonta, watsa mata harara tayi kafin ta ɗauke kanta a ranta tana faɗin "Kyaji dashi dai munafuka..."


Jin ya tada napep ɗin ne yasa ta juyo da sauri tana kallonsa amma sai ta ga ya kauda kai shima da sauri ya juya gurin Zahra yana faɗin "Ku barshi bazan karɓa ba na yafe muku..sai da safe...." Ya faɗa yana ƙoƙarin jan napep ɗin zai wuce.


Cikin sauri Zahra ta karɓi jakar hannun Auntyn tata ta buɗe ta zaro wayarta dake ciki ta cire code ɗin ta miƙa masa tana faɗin "Gashi ka saka mana numbern wayarka saboda gobe da safe idan muka tashi tafiya in kiraka ka kaimu tasha...ko Aunty Shatu tunda kinga dole goben a motar kasuwa zamu koma gida...?" Ta faɗa kai tsaye fuskarta ɗauke da murmushi tana kallonta, gyaɗa mata kai kawai tayi ba tare da tayi magana ba ta ɗauki akwatin ta wuce ta barta nan tsaye tana mamakin shegen rawar kan tsiya irin na ƙanwar tata daga haɗuwa da mutum duk tabi ta damu dashi sai wani shisshige masa take tana neman zubar mata da mutunci.


Ita kuwa Zahran ko a jikinta sai daya gama karanto mata numbern ta kwashe ta loda acikin wayar tayi saving ɗinta kana tayi masa godiya ta juya da gudu tabi bayan Auntyn tata wacce ta daɗe da shigewa ciki.
Shima sai daya ga shigewarta cikin hotel ɗin kana yaja napep ɗinsa ya wuce yana mamakin kansa da ɓata lokacinsa da yayi akansu haka kawai ba tare da ya sansu ko ya taɓa ganinsu ba.




















*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:17 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*






*Wattpad: Aishaalto09*








1️⃣9️⃣






Fadwa kuwa lokacin data shiga gidan ta iske komai yana nan a yadda ta barsa babu abinda ya sauya alamar dai tunda ta fita ga dukkan alamu Ya Azeez bai dawo gidan ba kwata kwata, kasancewar tana da tabbacin in har da ya dawo gidan tun daga ƙofar gida zata fara gano hakan dan tana shigowa cikin unguwar zata hangi keke napep ɗinsa fake a ƙofar gidan nasu yana zaune a gefe yana dakon zaman jiran dawowarta tazo ta buɗe masa ƙofa, amma sai gashi yau da ta bar masa gidan a buɗe ta fita taje inda zata har ta gama duk abinda zata yi ta dawo amma shi bai dawo ba.


Ɗaga kafaɗarta tayi alamar ko a jikinta hakan bai dameta, ta tura ƙofar ɗakin ta shige abin ta tayi wurgi da ƴar jakar dake hannunta kana ta cire kayan jikinta ta jawo zani ta ɗaura ta ɗebi ruwa a bokiti ta ɗauki sabulun wankanta da soso ta fice zuwa banɗaki, wanka tayi haɗe da alwala tazo tayi sallah, sai data rama duk sallolin da ake bin ta tsaf tukunna, kasancewar dama ko azahar bata samu tayi ba sakamakon aiki daya kacame musu suna ta hidima, sai a lokacin ta haɗa duka har da la'asar da magriba da isha'i tayi kana ta tashi taje ta buɗe ƙaramin akwatinta ta ɗauko ƙananun kayan shan iska kasancewar garin akwai ɗan zafi zafi ta saka kana ta ɗan fesa turare sama sama ta sha ruwa ta haye gado ta kwanta dan ta gaji sosai kuma bata jin yunwa saboda sai data ƙara cin abinci a gidan Hajiya Kalsoom tayi nak abin ta sannan tayo guzurin wani ta taho dashi gida.








A ɓangaren Ya Azeez kuwa koda ya isa unguwarsu lokacin ƙarfe 12:30am dai-dai na dare, cikin layinsu babu kowa duk ƙafafuwa sun ɗauke ko'ina yayi tsit sai hasken solar kawai daya haske ko'ina yayi fayau, ganin hakan yasa bai nufi gida ba direct ya wuce kai tsaye gidan bulon da yake kai ajiyar napep ɗinsa ya kai ya ajiye kana ya kwashi kwalayen indomie da taliya da sauran kayan cefanen da ya siyowa Fadwa ya nufo gida.




Lokacin daya isa gidan ya iske Fadwa ta daɗe da yin bacci, dan haka yana shiga shima ya ajiye kayan dake hannunsa ya fita yaje ya kullo ƙofar gidan yasa sakata sannan ya dawo ya tuɓe kayan jikinsa ya ɗebi ruwa a bokiti yaje yayo wanka ya ɗauro alwala kana ya dawo ɗakin ya zura jallabiya ya shimfiɗa darduma ya hau ya daidaita tsaiwarsa ya tada sallah, sai da yayi shafa'i da wuturi kana yayi adduoinsa ya shafa ya miƙe ya linke darduman ya ajiye sannan yayi shimfiɗarsa yau ma a nan falon yayi kwanciyarsa ba tare daya sake bi takan Fadwa dake uwar ɗaka tai ɗai ɗai abin ta, tana sharar baccinta hankali kwance ba tare da tasan ya ma dawo gidan ba.






*******




Washegari da misalin ƙarfe 10am na safe Zahra ce zaune akan makeken gadon dake ɗakin da suka kama a cikin Hotel ɗin, shirye take tsaf ta yana ɗan madaidaicin ƙaramin gyale a kanta, tana riƙe da faskekiyar wayar Shatu a hannunta tana ta faman latsawa, yayinda ita kuma Shatun ke tsaye a gaban ƙaton madubin dake ɗakin ta gama shiryawa cikin wata tsadaddiyar doguwar riga ƴar Oman mai mugun kyau wacce taji stones tana ta sheƙi da walwali, tayi rolling ɗin gyalen rigar a kanta tayi kyau sosai ta fito kamar wata balarabiyar ƙasar Saudiya, dan rigar sosai ta karɓi jikinta ta fito da faffaɗan hips ɗinta masu kyau da ɗaukar hankali saboda rigar irin mai shape ɗin nan ce gashi ta ɗan kamata kaɗan sai tayi mata kyau ta ƙara fito da zallar kyaunta da yarintarta, sai data fesa turare a jikinta kana ta ɗauki ƴar jakar handbag ɗinta ta riƙe a hannunta ta jawo akwatinsu ta ƙaraso gaban Zahra dake nan zaune ta haɗe fuska tana ta faman latsa waya tana sakin tsaki, tsayawa tayi tana dubanta kafin ta zauna kusa da ita tana faɗin "Wai lafiya kike ta faman ɗaci kina wani ɓaɓɓata rai sai kace wacce akayiwa wani laifi..ko dai baki son komawa gidan ne yau sai in kira Abbie in gaya masa kinga ni sai in tafi kawai in barki a nan ɗin, tunda haka kika fi buƙata...?"


Banza tayi da ita bata tanka mata ba, ta sake danna wata lamba ta kai wayar kan kunnenta, jim kaɗan ta sake sauke wayar daga kunnenta tana sakin tsaki kafin cikin ƙosawa tace "Ikon Allah to ko dai ba asalin numbernsa bace dama ya bani...? Ƙila

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login