Showing 15001 words to 18000 words out of 113443 words
ai ba sanin muhimmancin sallar kikayi ba ballantana dan bakiyi ba kiji wata kunya..Allah ya shiryeki..."
Aiko tana jin abinda yace ta hayayyaƙo masa da masifa ta shiga faɗan mai maganganu.
Dama wani bala'in haushinsa take ji kan rashin imanin daya gwada mata a daren jiya, sakamakon haka yasa ta rufe ido ta dinga ruwan bala'i, shi dai ko ta kanta bai sake bi ba ya buɗe jakar kayansa ya zaro wata farar riga da baƙin wandon jeans ya zura kana ya ɗauki turarensa mai ɗan sauƙin kuɗi ya fesa, sannan ya ɗauki kofi da abun tace ruwan tea ya fita, sai daya kashe gawayin sannan ya sauke tukunyar ya tsiyaya ruwan tean iya yanda zai yi masa, kana ya rufe sauran ya ɗauki na kofin ya koma cikin ɗakin, har lokacin tana cikin ɗaki tana ta zazzaga ruwan masifa tana kumfar baki, dan haka sai yayi zamansa a falon bayan ya ɗauko sauran bredin daya siyo mata tun shekaran jiya wanda ko taɓashi bata yi ba ya soma karyawa abunsa hankali kwance.
Yana cikin karyawan ne ta fito da buta da bokiti cike da ruwa a hannunta ta fice tana sakin tsaki, shi dai ko a jikinsa bai kulata ba, har ya gama karyawarsa ya miƙe yaje ya ɗauraye kofin ya dawo dashi ya kife sannan ya ajiye mata gudar ɗari biyar a bakin gado, ya ɗauki makullin keke napep ɗinsa yasa kai ya fice.
A tsakar gidan ya isketa tsugunne tana brush, bai kalleta ba yace "Nina fita sai na dawo..."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakai zai fice, jin tayi shiru bata tanka masa bane yasa shi ya dawo da baya ya ƙaraso gabanta ya tsaya lokaci ɗaya yana dubanta kai tsaye yace "Ni dai ina roƙonki dan girman Allah Fadwa ba dan halina ba yau ki daure ki zauna a gidanki karki fita ko'ina, dan Allah ki zauna a ɗakin mijinki ki kula da gidanki ki daina hangen gidan wasu da kalar rayuwar da sukeyi a gidajen mazajensu, kema ki fuskanci taki rayuwar dan Allah..."
Ya ƙarashe faɗa yana tsatstsareta da idanu, ko kallonsa ba ta ɗaga kai tayi ba ballantana yasa ran zata amsa masa, sai ma cigaba da wanke bakinta da tayi tana ƙara haɗe rai, ganin haka yasa ya girgiza kai kafin yace "Ni dai kinji maganata kuma a matsayina na mijinki ɗan uwanki wanda ya isa dake nake baki wannan umarnin, dan haka ko ki ji ko kar kiji wannan ya rage naki nidai ban ce ki fita ko nan da ƙofar gida ba domin ban baki izini ba, duk da dama fitar da kike yi ɗin kai tsaye kike yin abarki ba tare da izinina kike yinta ba, dan haka daga yau na soke kuma idan kika kuskura kika fita bada yawuna ba ban yafe miki ba tunda ke naga alamar lallashi da lallaɓawa basa taɓa miki dole sai an bi dake ta tsiya tsiya sannan ake shiryawa dake, saboda haka wallahi ki kiyaye ni karki sake ki ƙureni na gaya miki...."
Daga haka kawai ya juya yasa kai ya fice daga gidan gaba ɗaya ya barta nan.
Da wata ƙatuwar harara Fadwa ta rakasa kafin ta ɗauke kai lokaci ɗaya tana sakin ƙaton tsaki kamar bakinta zai faɗo ƙasa tace "Aiko wallahi sai na fitan, sai dai kayi duk abinda zakayi ɗin, haba! Mutun sai shegen fi'ili da iyayin banza da wofi sai kace wani uban abun yake ajiye min na azo a gani a cikin gidan da zai wani hanani fita inda naga dama saboda samun waje...Lallai kuwa aiko wlh sai na fita kuma a lokacin dana so naga dama, tunda ba zamansa nake yi ba, dan ni wannan ƙaddararran auren nasa ban wani ɗaukesa a bakin komai ba ji nake kamar ma zaman kaina nake yi ba zaman wani ba, har da zai wani zo ya isheni da wasu surutansa marasa tushe ballantana makama, faƙirin banza kawai faƙirin wofi direban napep...."
Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana kuskure bakinta da ruwa, kafin ta soma ɗaura alwala tana kumbura fuska tana ƙunƙunai.
*Allah ya gafartawa iyayenmu da kakanninmu yasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu🤲*
[12/23, 10:15 AM] Janafty: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DXDyWhc0O3LCKZVYVT5N3M
*WADATAR ZUCCI*
*Wattpad: Aishaalto09*
6️⃣
Koda ta idar da sallahn miƙewa tayi jikinta sanye da hijabin sallar bata cire ba, ta buɗe jakarta ta ɗauki dubu ɗaya acikin kuɗin da Hajiya Labiba ta bata ta fice daga gidan.
Can bakin layinsu taje wani babbba shagon provision ta haɗo kayan tea irinsu madara, milo, sigari kana ta siyo kwai da buredi saboda bata jin zata iya cin wannan bushasshen buredin daya siyo ya kawo tun shekaran jiya ya ajiye.
Sai da mai shagon ya gama haɗa mata komai da take buƙata sannan ta biyasa kuɗinsa ya bata canji ta kamo hanyar komawa gida a ranta tana mitar duk wannan siyayyar fa bai kamata ace kamarta sai ta fita yinta ba, kamata yayi ace tana da komai ajiye a gidanta sai dai kawai tasa ƴar aikinta tayi mata duk abinda take so tana daga zaune, amma ina zata samu haka tana a irin wannan faƙirin gidan.
Bayan ta koma gidan gawayi ta sake haɗawa ta kunna bayan ta shiga ɗaki ta ɗauko kaskon suyan kwai a kwando da wani ɗan silba da cokali sannan ta haɗo da wata yar gora da Ya Azeez yake siyo musu man gyaɗa a ciki ta dawo tsakar gidan ta fasa kwan data siyo ta kaɗa sannan ta ɗora kaskon ta zuba man gyaɗa, sai lokacin ta tuna bata ɗauko maggi ba ta miƙe taje ta ɗauko nan taga tsiren data rage jiya ta ɗauko abunta ta zuba a cikin kwan ta yanka albasa sannan ta zuba a kaskon.
Sai data gama soya abunta tsaf ta juye a filet, kana ta sake maida ruwan lifton ɗin da Ya Azeez ya dafa ya ƙara tafarfasa sannan ta sauke ta juye a kofi ta ɗauka ta kai ɗaki ta ajiye, kana ta zuba ruwa a tukunyar ta sake ɗorawa a mangal ɗin sannan ta koma ta zauna inda ta haɗa tean ta mai kauri wanda yaji madara da milo.
Wani irin tsananin farin ciki yau take ji a ƙasan ranta dan haka cikin jin daɗi ta zauna ta fara karyawa abunta hankalinta kwance babu abinda ya dameta.
Tsaf ta gama cinye abunta tas bata rage komai ba, ta ɗauki pure water ta sha ta saki gyatsa, sai data ɗan yi jim kaɗan sannan ta tashi ta tattare kayan ta kwashe ta kai uwar ɗaka ta ajiye, kana ta cire kayan jikinta ta ɗaura fallan zani ta ɗauki bokiti da soson wanka ta fita zuwa tsakar gida.
Ruwan zafin data ɗora ta juye ta ɗauka ta shige banɗaki dan Allah Allah take tayi ta gama shiryawa taje ta kai ɗinkinta, a gurguje tayo wankan ta fito ta shiga ɗaki sai data goge jikinta tsaf kafin ta ɗauko lotion ɗinta ta ɗan shafa sama sama, bayan ta gama ta ɗauko akwatin kayan kwalliyarta ta zauna zaman dirshan ta shiga tsantsara kwalliyarta kamar wacce zata gurin taron biki, ta ɓata lokaci sosai gurin yin kwalliyar gaba ɗaya ta gama canjawa ta fito tai wani irin fes fess da ita, abunka da farar fata sai ta sake zama kamar wata balarabiya.
Sai data kama shafe shafenta tsaf kana ta tashi taje ta sauko da babban akwatinta dake shaƙe da kaya ta buɗe ta zaro wata sabuwar atamfarta Chiganvi wacce ƙawarta Hajiya Lubna ta ɗinka musu dukansu sukayi anko ita da sauran ƙawayensu ranar sunan yayarta Hajiya Kalsoom data haihu suka saka.
Sosai kuwa atamfar tayi mata mugun kyau, kasancewarta fara atamfar kuma ta kasance kalar blue ce da yellow a jiki, anyi mata ɗinkin riga da siket wanda ya zauna a jikinta sosai ya fito da shape ɗinta tayi wani fayau da ita a ciki, sai data gama feshe jikinta da turare ko'ina ya ɗauki ƙamshi sannan ta ɗauko ɗan madaidaicin yellown gyalenta ƙarami ta yafa a kanta dan bata so ta ƙara ɓatawa kanta lokaci gurin tsayawa ɗaurin ɗankwali, a mugun ƙagare take ta ƙosa ta bar gidan jinta take kamar tana kan ƙaya, shiyasa kawai ta bar ɗankwalin akan gado ta ɗauki blue ɗin handbag ɗinta bayan ta zura takalmanta masu tsinin dunduniya suma kalar blue kana ta kwashe kuɗin dake cikin waccan jakar data fita da ita jiya ta zuba cikin wanda zata fita da ita yau kafin ta ɗauki ledar leshinta da zata kai ɗinki, kafin ta ɗauki kwaɗo ta fito ba tare data sake bi takan komai ba tasa kai ta fice abunta, dan ko ɗari biyar ɗin ma daya ajiye mata bata kalla ba saboda bata jin akwai abinda zata yi da ita tunda Allah ya hore mata kuma ya rufa mata asiri ya hore mata tana da kuɗi.
Sai data kulle ƙofar ɗakin kana ta fice daga gidan tana wani irin taku cikin yanga ta kulle ƙofar gidan ta jefa ɗan makullin cikin jakarta sannan ta fara takawa zuwa bakin titi tana yatsine fuska cikin wani taku irin nasu na manyan mata masu ji da kansu tana wani rausaya jiki kamar ba matar aure ba.
A haka tazo ta wuce ta gaban gungun mazan dake zaune akan layin inda suke haɗa ƴar ƙaramar majalisarsu da safe kafin kowa ya kama gabansa ya tafi gurin aikinsa, haka idan suka kuma dawo da dare ma sukan ɗan zauna su taɓa ƴar hira kafin kowa ya shiga gidansa, aiko tana gittawa ta gabansu duka suka bita da ido yadda take wani yauƙi da yarari da yawa a gurin sai data tafi da hankali da natsuwar su, ita kuwa ko ajikinta tayi gaba abunta tana ci gaba da takunta ɗaya bayan ɗaya cike da ginshira ta barsu da shaƙar daddaɗan ƙamshin turarenta mai matuƙar daɗi da sanyaya zuciyar duk wanda ya shaƙesa.
Tana gab da fita daga cikin layin nasu ne ta hau kan titi wani mai keke napep ya taho aguje yazo yaci burki a gabanta, cike da iyayi da yanga ta ɗaga kai tana kallonsa kafin ta juya cikin iyayi tana faɗin "Bawan Allah ban tsaidaka ba ai...kana iya ƙarawa gaba..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana matsawa gaba kaɗan ta tsaya tana yatsina fuskarta kamar taga kashi.
Zuro kansa waje yayi daga cikin keke napep ɗin yana dubanta fuskarsa cike da mamaki yace "Haba Hajiya...naga ai kamar abun hawa kike jira shiyasa na tsaya, kuma dan na tsaya ki shiga ai ba laifi bane...kamar ma na taimaka miki ne tunda baki sani ba kila kita jira kizo baki samu ba, kinga sai ki ɓatawa kanki lokaci tunda daga gani kamar gurin aiki zaki..." Daga haka ya sake gunguro keken nasa ya ƙaraso gabanta ya tsaya lokaci ɗaya yana faɗin "Muje Hajiya...ina za'a kaiki...?
Wani ƙululun baƙin ciki ne da takaici lokaci ɗaya ya turnuƙe Fadwa ta ɗago a zafafe tana watsa mai harara cikin ɓacin rai take cewa "Wai wannan wane irin naci ne..? Nice na tsayar da kai da zaka dameni ko kuwa hawa keken naka dole ne da zaka takura min ko yaya...?"
Cike da mamaki mai keken ya zuba mata ido kafin yace "To laifi ne dan naso taimaka miki...?"
Cikin zafin rai tace "Ba laifi bane amma ka dubeni da kyau ka gani nafi ƙarfin kace zaka taimaka min, sai dai ni ka nemi taimako a gurina in taimaka maka, domin kaine kake a wahale kake neman taimako...."
Cike da mamaki ya riƙe baki yana kallonta kafin yace "Ikon Allah..ashe kuma taimako yana juyewa ya zama masifa da bala'i ban sani ba...?"
Fadwa da kalmar taimakon da yake ta maimaitawa ta fara ɓata mata rai tace "Wai kai kaga nayi maka kama da wacce zata nemi taimako a gurinka ne..ko kuwa nice na tsayar da kai nace dole saika ɗauke ni da zaka buwayeni...?"
Kaɗa kai mai keke napep ɗin yay kafin yace "A'a baki ce ba Hajiya, amma Allah ya baki haƙuri...."
Da sauri Fadwa tace "Ameen Ameen, sai kuma ka ƙara gaba. Haba ina dalili haka kawai daga ganina zaka wani ci burki a gabana ka dameni da sai na hau wani shegen ruɓaɓɓen kekenka...Sai kace saboda ni kaɗai yau ka fito..?
Haka kawai ka shafa min masifa..ƙilan ma ƙararren kwana gareka inzo in hau keken naka kaje kayi hatsari ka mutu ni injijji ciwo ka barni da bala'in neman kuɗin magani ina zauniyata lami lafiya, ko kaje can ka watsar dani a gefen titi ka ɓata min lafiyayye jikina da tabbai. Dan ni tunda naga wannan shegen nacin naka nasan ba haka nan bane, shiyasa ma ni bana taɓa hawa keken da nasan bani na tsayar dashi ba, dan yawancinku masu rawar jikin ku ɗauki mutum ɗin nan duk masu tafe da tsautsayi ne wasu da ƙarar kwana, haka kawai suje su mutu su barka da wahalar rayuwa..."
Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tare da jan tsaki, kafin ta wuce ta ƙara gaba ta barshi nan sake da baki yana bin bayanta da kallon al'ajabi da mamaki, sai da ta ɗan yi nisa kafin ya kunna mashin ɗinsa ya wuce. Itako Fadwa sai data ƙarasa bustop inda take hawa napep wani lokacin sannan ta hau bayan ta gaya masa Unguwar Rimi zai kaita inda shagon telanta yake kafin yaja suka wuce.
Koda suka ƙarasa ta iske shagon telan nata a kulle bai riga ya fito ba, gashi ba waya a hannunta balle ta kirasa, dan tunda wayarta ta samu matsala ta jefar da ita bata sake bi ta kanta ba, dan bata jin zata iya gyara waya kuma sannan taci gaba da amfani da ita a ganinta tafi ƙarfin hakan. Dan haka kawai sai ta samu benci ta zauna a bakin shagon da nufin zata jirasa har zuwa lokacin da zai fito.
Gurin ƙarfe 9am dai-dai kuwa sai ga wani matashin saurayi irin ƴan gayun nan ya iso akan farar mashin ɗinsa wayyo kuɗina, yana ganinta ya sauka daga kan mashin ɗin bayan yayi parking ɗinsa a gefe guda ya ƙaraso gabanta da fara'arsa yana faɗin "A'a Hajjaju yau kece tunda sassafe...meyasa baki kirani a waya nazo gida na ƙarba ba...?"
Sauke numfashi Fadwa tayi tana yatsine fuska kafin tace "Wayan ne ya lalace kuma har yanzu ban siya wani ba, amma insha Allahu kwanan nan nake so in siya sabuwa..." Ta faɗa tana ɗaukar ledan da tazo da ita ta miƙa masa kafin taci gaba da faɗin "Gashi ai kana da measurement ɗina kayi amfani dashi ba sai ka sake gwadani ba, amma inaso ka ƙure basirarka kayi min ɗinki na garari da ɗaukar magana, dan so nake in cinye gurin da kwalliyata saboda manyan mata isassu za'a haɗa agurin bikin inaso idan na isa gaba ɗaya kallo ya dawo kaina gaba ɗaya in ɗauke hankalin mutane gurin..ka dai gane ai..."
Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana buɗe jakar hannunta ta ƙirgo kuɗi dubu goma sha biyar cif ta miƙa masa, cikin murna ya karɓe yana faɗin "Insha Allahu karki damu Hajiyata zan finfaki sai kin fi kowa a gurin nan nayi miki wannan alƙawarin..."
Cikin jin daɗi Fadwa tace "Yauwa Sadeeq shiyasa bana jinka, ina alfahari da kai ta wannan fannin..." Ta faɗa tana maida jakarta ta rufe kana ta miƙe tsaye tana faɗin "Ƙarfe nawa ne yanzu duba min..kasan ba waya a hannuna kuma gashi inata sauri ban tsaya na saka agogo ba na fito..."
Agogon fatan dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya duba kafin ya ɗago kai yana faɗin "Ƙarfe tara da kwata yanzu Hajjaju..."
Jinjina mai kai Fadwa tayi tana gyara zaman gyalen dake kanta lokaci ɗaya tana faɗin "Yauwa bari kawai in ƙarasa ƴan majalisu gidan Hajiya Lubna, dan nasan zuwa yanzu ita mijinta ya daɗe da fita..." Ta faɗa kai tsaye tana yin gaba, da sauri ya biyo bayanta shima domin yayi mata rakiya, a bakin titi suka tsaya, sai data tari keke napep ta gaya masa inda zai kaita sannan ta shiga sukayi sallama da telan akan nan da kwana uku ko huɗu ta zo ta karɓi ɗinkin ko kuma ya kawo mata gidan Hajiya Labiba, tunda yasan gidan wani lokacin ma tare yake musu ɗinki ya kai musu har gida.
*Allah ya gafartawa iyayenmu da kakanninmu yasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad Aishaalto09*
7️⃣
Ƙofar wani haɗaɗɗen gida mai ɗauke da tangamemen farin gate ta nunawa mai Napep ɗin ya tsaya ta sauka, ta buɗe jakarta ta zaro ɗari biyar ta miƙa mai, ba tare data tsaya karɓan canjinta ba ta juya ta fara takawa a hankali ta ƙarasa bakin gate ɗin ta fara ƙwanƙwasa ƙaramar ƙofar a hankali.
Ta jima sosai a tsaye tana ƙwanƙwasawa amma babu motsin wanda taji ballantana tayi tunanin za'a zo a buɗe mata, tun tana bugawa a hankali har ta fara gajiya ta koma bugawa da ƙarfi tana jan tsaki, gajiyar da tayi da tsaiwar ne yasa ta yanke shawarar ta juya kawai ta tari Napep ta wuce gidan Hajiya Labiba tunda nan basu da niyyar buɗe mata balle tasa ran zata shiga ciki, to ko dai itama Hajiya Lubnan yau basu tashi da wuri bane..?
Tunanin hakan da tayi ne yasa kawai ta juya ranta a ɓace ta fara tafiya da niyyar ƙarasawa bakin titi don ta tari Napep, har ta kusa bakin titin taji an buɗe gidan da sauri ta juyo ta koma tana jin wani baƙin ciki a ranta, tana zuwa taga maigadin a tsaye ya babbake hanya yana watsa mata wata muguwar harara, a ɗage itama take kallonsa kafin ta saki tsaki lokaci ɗaya tana faɗin "Dalla Malam ni matsa ka bani hanya, ka wani babbake ka tsare hanya sai kace gidan ubanka..ni matsa ka bani guri da shegun idanuwanka sai kace na jemage..." Ta ƙarashe maganar a zafafe tana watsa masa wani banzan kallo.
Shima kallon banzan ya watsa mata kafin yace "Bazan matsa ba ai kema nan ɗin ba gidan naki uban bane da zaki nemi ki gaya min maganar banza kwaɗayayya kawai ƴar maula..."
Wani zabura Fadwa tayi tana kallonsa kafin ta matsa kusa dashi a fusace tana faɗin "Yau ni kake kira da ƴar maula...? Kasan matsayina a gurin matar gidan da zaka kirani da ƴar maula...? Lallai Habu yau ƙarshen gadinka anan gidan ne yazo, tunda kai baka gaji arziki ba zan nuna maka na fika rashin mutunci ɗan iska kawai maigadi..."
Ta faɗa tana