Showing 18001 words to 21000 words out of 113443 words
kumfar baki, yayinda ranta yake cike da jin haushinsa na kiranta da yayi da sunan ƴar maula, wai ita Fadwa yau maigadi yake kira da ƴar maula.
Jinjina kai kawai yayi kafin yace "Ai na sani ba abinda kika haɗa da ita face ƙawance, in kuma bayan haka akwai wani abu sai ki gaya min idan yar uwarki ce kullum da zaki wani dinga zaryar zuwa mata gida kullum kina takurawa mutane da shegen yawace yawacen maularki kina wani iyayi da salo sai kace gidan mijinki, ke ko kunyar abun ma ba kyaji...."
Ya faɗa yana jan tsaki cike da takaicinta, dan shi da yasan itace ma da babu abinda zai sashi ya buɗe mata ƙofa, shi haka nan matar sam bata taɓa masa ba bala'in haushinta ma yake ji saboda yadda take nuna musu iyayi da salo idan tazo shiyasa ya tsani tazo gidan, ita kuwa gashi ko a jikinta kusan kullum sai tazo sai kace gidan ubanta.
Horn din da aka saki daga cikin gidan ne yasa ya juya da sauri yana faɗin "Sai ki kauce kiba masu gidan guri zasu wuce..."
Ya faɗa yana komawa ciki da sauri ya fara ƙoƙarin buɗe tangamemen gate ɗin yana sakar mata harara.
Itama Fadwan hararar ta sakar masa tana taɓe baki kafin ta ɗan matsa gefe ta tsaya tana jiran motar ta fito kafin ta samu ta shige ciki, dan ta rantse tunda wannan ɗan iskan ya mata wannan cin mutuncin sai ta shiga ta gayawa Lubna duk abinda yayi mata, dan ta yiwa kanta alƙawarin cewa sai ta haɗa masa sharrin da sai an koresa daga gidan sannan hankalinta zai kwanta tunda shi ɗan iska ne bai da kunya, wanda a ƙalla tana zaton ta girmesa nesa ba kusa ba, dan tayi ƙani dashi. Amma har ya iya kallon tsabar idanunta ya gaggaya mata maganganu iya son ransa har yana kiranta da ƴar maula saboda shi ga tantirin ɗan iska mara kunya, aiko zata nuna masa itama ta fishi rashin mutunci.
Tana nan tsaye tana saƙawa da kwancewa wata hadaddiyar baƙar mota ƙirar Bugatti ta silalo ta fito daga cikin gidan, a hankali ta ɗago kai tana kallon motar wacce gaba ɗaya ta gama tafiya da imaninta, har wata ajiyar zuciya ta sauke da taga yadda motar take wani silalowa tana tafiya a hankali a hankali, ita dai Allah ya sani tana matuƙar ƙaunar ta ganta a cikin galleliyar mota irin haka ace dai wannan tata ce kota mijinta ranar bata san irin farin cikin da zata kwana tana yi ba, ƙara gyara tsaiwarta tayi ta kafe motar da ido ƙirr tana kallo.
Kasancewar akwai tintek a jiki yasa bata gano waye a cikin motar ba sai daya iso gab da ita sannan ya sauke gilashin motar a hankali wani magidanci ne kyakkyawa fari tas tas wanda a ƙalla shekarunsa zasu kai arba'in da biyar zuwa da shida yaji hutu sosai, da ganinsa kasan kuɗi da jin daɗi sun gama zauna masa, yana sanye da wata ubansun shadda fara ƙal sai maiƙo take da yarari tana shaining, shigar tayi masa mugun kyau.
Leƙo da kansa yayi fuskarsa ɗauke da murmushi lokaci ɗaya yana dubanta tun daga sama har ƙasa yace "A'a Hajiya Fadwa manyan mata yau kece a gidan namu tun da safe, to meyasa baki shiga ciki ba kike tsaye a nan waje sai kace wata baƙuwa ai ƙawar taki tana ciki babu inda taje..."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana tsaida motar a gabanta.
Cikin sauri Fadwa ta ɗauke kai dan kar ya fahimci yadda take ƙare masa kallo ta juyo a hankali ta ɗan risina tana faɗin "Barka da safiya ranka ya daɗe, har an fito kenan...?" Ta faɗa cikin tsantsar ladabi tana yin ƙasa da murya.
Sai da ya ƙara ƙare mata kallo a fakaice kafin yace "Allah ya nufa Fadwa mun fito za'a tafi ƙwadago..."
Cikin yin ƙasa da murya kamar wacce take gaban ubnata Fadwa tace "To Allah ya tsare yasa an fito a sa'a, Allah ya taimaka kuma ya bada sa'a..." Ta faɗa tana sakin ɗan murmushi, shima sake faɗaɗa murmushin nasa yayi, kafin ya buɗe wata yar loka a gaban motar ya zaro yan ɗari biyar biyar bandir guda ya miƙa mata yana faɗin "Gashi in kin tashi tafiya kya hau mota, na gode sosai kuma naji daɗin addu'arki Allah ya saka da alkhairi..."
Ya faɗa tare da miƙa mata kuɗin hannunsa, aiko zaraf ta miƙa hannu ta karɓe tana washe baki cike da murna take faɗin "Na gode Alhaji Allah ya ƙara maka buɗi da arziki mai albarka da amfani, na gode Allah ya raya maka zuri'a kyakkyawar rayuwa mai albarka...na gode ƙwarai Allah ya biyaka ya ƙara dalili..."
Ta faɗa cikin zumuɗi tana ƙara yashe baki, kaɗa kai kawai yayi yana faɗin "Ameen Ameen...Ameen ya Allah Fadwa na gode sosai da sosai ki gaida maigidan naki..."
Cike da farin ciki itama ta sake risinawa kamar zata kifa tana cewa "Nike da godiya Alhaji, Allah ya saka ya bada lada, Allah ya barku da ƙawata Lubna..."
Ya amsa mata da Ameen ya Rabbi kana ya ja motar ya ƙara gaba abinsa.
Jujjuya kudin Fadwa ta dinga yi a hannuta lokaci ɗaya tana bin bayan motar tasa da kallo har sai da ya ɓacewa ganinta, sannan ta ɗauke idanunta ta buɗe jakarta ta jefa kuɗin a ciki tana sakin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya, kana ta juya ta ƙarasa bakin gate ɗin inda Habu ke tsaye yana ta kallonta fuskarsa ɗauke da matsanancin mamaki, bata bi ta kansa ba ta tura ƙaramar ƙofar tayi shigewarta ciki ta barsa nan tsaye sake da baki yana bin bayanta da kallo.
Har ta kusa isa ƙofar da zata sadata da shiga babban falon gidan ta dakata ta juyo tana kallonsa kamar yadda shima ya tsareta da ido har lokacin yana kallonta, wani dogon tsaki taja kafin ta watsa mai wata muguwar harara ta kallesa sama da ƙasa ta watsar kafin tace "Ba yadda mutum ya iya dani dole ana ji ana gani a barni in shiga, idan kuma ba haka ba a koma gidan mai dattin hula a cigaba da cin arne da kwot. Ƙaramin mara kunya kawai ɗan iska..."
Daga haka ta juya ta cigaba da tafiya tana wani irin taku da rausaya ta shige korido ɗin da zai sadata da ƙofar shiga falon gidan.
Bata tsaya wani ƙwanƙwasawa ba dan tasan Hajiya Lubna bata cika kulle ƙofar babban falon gidanta ba, ba kamar Hajiya Labiba ba da sai kai ta faman tsayiwa kana ƙwanƙwasawa kafin da ƙyar wannan mummunar mai aikin nata tazo ta buɗe maka ba, aiko tana turawa ƙofar ta buɗe ta shige ciki bakinta ɗauke da sallama.
Wata kyakkyawar mace ce black beauty ƴar duma duma hakimce akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman lafiyayyun kujerun da suka yiwa haɗaɗɗen ƙayataccen falon nata da yasha kayan alatu ƙawanya, taci uban kwalliya sai kace wacce tayi shiri zata gasar sarauniyar kyau jikinta sanye da wani tsaddaden leshi maroon colour wanda akayiwa ɗinkin bubu gown sannan aka ƙawata gaban rigar da stone work wanda aka jajjerasa tun daga sama har ƙasa gwanin sha'awa, gashi ta zuba gwala-gwalai jikinta sai sheƙi yake da ɗaukar ido.
Jin sallamar Fadwa yasa ta juyo a hankali cikin wani irin salo ta amsa mata da wata irin murya kafin ta miƙe cikin iyayi da yanga tana faɗin "Barka ƙawata..daga ina kuma haka tun da sanyi safiya aka doko mana irin wannan uban sammako...?"
Ta faɗa kai tsaye tana kallonta.
Sanin halinta da Fadwa tayi ne yasa hakan bai wani dameta ba, sai ma washe mata baki da tayi tana faɗin "Wallahi daga gurin Sadeeq tela nake na kai masa ɗinki, shine nace bari in ƙaraso mu gaisa dan mun kwana biyu bamu haɗu ba..."
Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana zama kan kujerar da take facing din wacce Hajiya Lubnan ta tashi akai.
Ɗan taɓe bakinta Hajiya Lubna tayi kafin ta koma ta zauna itama tana faɗin "Ok yayi kyau, to ya gidan..ya kuma mai keke napep ɗinki an fita hayis ɗin kenan....?" Ta faɗa cike da rainin wayau lokaci ɗaya tana kallonta.
Taɓe baki Fadwa tayi itama kafin ta zare gyalen dake jikinta ta ajiye tana faɗin "Aiko kamar kin sani ƙawata ɗan wahalar ya fita tun sassafe, ana can kuma ana yawon gararanba a kwalta...."
A wulaƙance Hajiya Lubna take dubanta tana wani yatsine fuska tace "Ai dama abinda ya kamaceku kenan tunda dama tun asali ba wani abun arziki ke gareku ba kema dan kinƙi natsuwa ne a guri guda ki maida hankalinki kan mijinki ki zauna lafiya shiyasa kika kasa gane abinda ya kamaceki. Kwaɗayinki da son abun duniya ne ya gama rufe miki ido shiyasa kullum kike gantali a titi kin kasa zama guri guda balle ki natsu ki kama kanki ke kenan yawon bin gidajen ƙawaye kina naniƙe musu, kamar kema ba miji nan gareki ba duk kin bi kin hana kanki sukuni kina wahalar da rayuwarki a banza kin gama ƙasƙantar da kanki a wofi...." Ta ƙarashe faɗa lokaci ɗaya tana jan tsakin takaici kafin ta ci gaba da faɗin "Amma fa kiyi haƙuri idan maganata tayi miki zafi kinji ƙawata....?"
Ta ƙarashe maganar tana watsa mata wani kallon gefen ido, kana ta shiga kwallawa mai aikinta Adama kira ta fito daga cikin kichin da sauri tazo gabanta ta duƙa tace "Gani Hajiya..."
Ba tare data ɗago kai ta kalleta ba tace "Jeki haɗowa ƙawata abun kari dan nasa da wuya idan ma ta karya daga gidanta ta fito, yi sauri kije ki haɗo mata...."
Ta faɗa cikin halin ko in kula kafin ta juyo ta fuskanci Fadwa data jingina kanta da jikin kujera ta lumshe idonta ko a jikinta, tace "Bari a kawo miki breakfast dan nasa ƙila haka nan kika fito ba tare da kin tsaya kinyi karin kumallo a gidanki ba....?"
A mai makon Fadwa ta nuna taji haushin maganar da Hajiya Lubnan ta gaya mata, amma sai bata nuna komai ba, kawai ta share ta saki murmushi lokaci ɗaya tana faɗin "Wallahi kamar kuwa kin sani ƙawata..ruwan lifton kaɗai na sha na fito, dan wani matsiyacin buredi ne ya siyo ya kawo ya ajiye min tun shekaran jiya waccan yau kusan kwanansa uku kenan a haukansa wai ni zanci, ni kuwa ina zan iya wannan rayuwa ta wulaƙanta kai. Dan ma Allah yasa ina daku a garin nan da na shiga uku da uƙubar rayuwa..."
Ita dai Hajiya Lubna bata tanka mata ba ta ɗauki remote tana canza tashoshi daga Tauraruwa Tv zuwa MBC Bollywood.
*Ya Allah ka gafartawa iyayenmu da kakanninmu, kasa aljanna fiddausi ta zamo makoma agaresu damu baki ɗaya🤲*
[12/23, 10:16 AM] Janafty: *WADATAR ZUCCI*
*Wattpad Aishaalto09*
8️⃣
Amma abun mamaki duk wannan ɗaure ɗauren fuskar da shan ƙamshin da Hajiya Lubna take bai wani ɗaɗa Fadwa da ƙasa ba ballantana ya dameta, abinda zaiyi matuƙar baka mamaki da takaici ma bai wuce nunawa da tayi ko a jikinta babu abinda ya dameta ba.
Saboda a ganinta ta daɗe da sabawa da halinta na wulaƙanci da nuna kai ba komai bane a gurinta, dan ma wai ita ɗin Fadwan ƙawarta ce kuma tana sonta shiyasa bata cika nuna mata halinta na rashin son wani ya raɓeta ba take ɗan dannewa wani lokacin ta nuna ana tare.
Amman duk da haka wata rana a fakaice take gaggaya mata maganganu akan kwadayinta da son abun duniyarta, itako Fadwa sai ta nuna ko a jikinta abun baya damunta saboda in da sabo yaci ace zuwa yanzu ta daɗe da sabawa da halin ƙawar tata.
Tana nan zaune mai aikin ta shiryo mata abun kari a ɗan madaidaicin faranti ta kawo mata har gabanta, sai data jawo ƙaramin tebur ta ɗora mata akai kana ta ɗauki filet ta fara zuba mata soyayyen dankali da kwai sannan ta zuba mata souce ɗin hanta a gefe ta ɗora mata da cinyar kaza ta ajiye a gabanta, ta ɗauki kofi tana ƙoƙarin haɗa mata tea ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu tana cewa "A'a jeki barshi wannan ma ya isa...."
Ta faɗa tare da ɗaukar fork ta fara cin soyayyen dankalin hankalinta kwance ba tare data ko ɗaga kai ta kalli inda Hajiya Lubna take zaune ba, saboda taga take takenta so take ta dinga mata abinda zaisa tayi zuciya tace ta daina zuwa gidanta, ita kuma bata ga wannan ranar ba. Dan ko dukanta tayi ta mata korar kare sannan ta haɗa mata da har da zagi ta uwa ta uba ba zai hanata zuwa gidanta ba sai tazo ko dan daɗin da take ci, ga kuma haɗaɗɗun suturu da ɗinkunan kece raini da suke mata ita da Hajiya Labiba.
Aiko dan wannan ta ƙara daurewa ta cigaba da jure wulaƙancinta tayi ta bibiyarsu kafin itama lokacinta yayi burinta ya cika taga ta samu abinda take so.
(Lallai wannan shi ake kira da inda kwaɗayi dole ka jure wulaƙanci😂)
A ɓangaren Hajiya Lubna kuwa ta wutsiyar ido ta dinga ƙarewa Fadwa kallo wacce ta zage tana ta tura dankali da kwai sai kace wata mayunwaciya ko wacce ta kwan ta wuni bata ci komai ba, sakin tsaki tayi cike da takaicinta kafin ta ɗauke kai tana faɗin "Kinje gidan Hajiya Labiba kuwa..ko can ɗin ma kin kwana biyu baki leƙa ba...?"
Fadwa data cika bakinta da naman kaza ta ɗago tana girgiza mata kai kafin tace "Jiya ma ai can na wuni abuna muka sha hirarmu da ita...kinsan ita akwai son mutane shiyasa da wuya kiga nayi kwana biyu ban leƙata ba, kullum ina kan hanyar zuwa gidanta saboda ita mai jama'a ce...."
Ta faɗa cike da tura haushi tana kallonta, itama Hajiya Lubnan fahimtar da tayi magana ce kawai Fadwan ta gaya mata a fakaice yasa ta jinjina kai lokaci ɗaya tana murmusawa kafin tace "Aiko kin kyauta, Allah ya bar zumunci da ƙauna..."
Cikin taɓe baki Fadwa ta amsa mata da "Ameen Ameen dai...."
Daga haka gaba ɗaya sukayi shiru babu wanda ya sake magana a cikinsu, har Fadwa ta kammala cinye dankalinta tas kana ta sha ruwa mai sanyi, ta saki gyatsa kafin ta soma ƙwallawa Adama mai aikin Hajiya Lubnan kira ba ɓata lokaci tazo ta risina a gabanta tace "Gani Hajiya..."
A yatsine Fadwa ta nuna mata farantin dake gabanta ba tare da tace komai ba tayi mata alama da ta kwashe kayan, da sauri ta tashi ta tattara kayan ta kwashe ta wuce ta kai kichin kana ta cigaba da aikinta.
Ita kuwa Fadwa komawa tayi ta jingina da jikin kujerar tana wani lumshe ido alamar cikinta ya cika taci tayi hani'an.
Ita dai Hajiya Lubna kallon ikon Allah kawai take tana ƙara mamakin Fadwa da ƙarfin halinta, baki ta taɓe kafin ta miƙe tsam tana girgiza kai ta wuce ta haura sama inda ɗakinta yake.
Ba jimawa sai gata ta fito hannunta riƙe da wani ɗan madaidaicin gyale da jaka a hannunta wanda suka shiga da kayan jikinta, saukowa tayi zuwa cikin falon ta ƙaraso inda Fadwa take kishingiɗe akan doguwar kujera ta zuba mata ido tana kallonta.
Ganinta cikin shirin fita ne yasa Fadwan ta tashi zaune da sauri daga kishingiɗar da tayi tana faɗin "Zaki fita unguwa ne ƙawata...?"
Gyaɗa mata kai Hajiya Lubna tayi lokaci ɗaya tana saƙala jakar handbag ɗinta a tsintsiyar hannunta take faɗin "Eh inaso zan shiga kasuwa ne akwai abubuwan da nake so in siya zanyi amfani dasu anjima kafin Alhajina ya dawo...ko zakije ne...?"
Ta faɗa tana duba agogon tsadaddiyar wayarta ƙirar iPhone 11 pro max dake hannunta.
Tashi zaune Fadwa tayi da sauri tana faɗin "Aiko nima shawarar shiga kasuwar dama nake ina so zan siya waya bari in tashi mu tafi tare daga can kawai sai in wuce gidan Ƙawata..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa ta yafa gyalenta kana ta ɗauki jakarta ta sagala tace "Muje ko...?"
Ta faɗa tana yin gaba, Hajiya Lubna kuwa kichin ta wuce inda ta iske Adama na wanke wanke ta sanar mata da cewa zata fita ta kula da gidan, sannan ta fito ta bi bayan Fadwa wacce tuni ta daɗe da fita daga falon.
A sabuwar Prado ɗin Hajiya Lubnan wacce mijinta ya siyan mata ko sati ba ayi ba suka fita, wanda tunda suka fita tafiya kawai suke kamar kurame ba wanda ya tanka ma wani a cikinsu har suka shiga kasuwa.
Royal Plaza suka fara zuwa inda Fadwa ta siya wayarta ƙirar Infinix smart 5 sabuwa dal a kwalinta ta lale kudinsu ƙyal dubu hamsin ta basu, ita dai Hajiya Lubna sai kallonta kawai take cike da al'ajabi tana mamakin inda ta samu kuɗi haka, amma da tayi wani tunani sai ta kaɗa kai kawai ba tare da tace komai ba, amma tabbas tasan babu wanda zai iya bata waɗannan kuɗaɗen sai Hajiya Labiba ko Aunty Kalsoom domin sune suke ɗaure mata gindi akan komai take yadda take so.
Daga nan cikin kasuwa sukayi inda ta raka Hajiya Lubna gurin ƴar Sudan mai tutaren manyan mata, tai mata haɗin turarukan data saba haɗa mata masu tsada kana daga nan kuma suka wuce wani haɗaɗɗen babban shagon saida jakunkuna da takalma masu tsada ta zaɓi duk kalolin da takeso, sannan tace itama Fadwa ta zaɓi jaka da takalmi kala ɗaya irin wanda takeso, aiko Fadwa kamar bakinta zai yage saboda tsabar murna tai ta washe baki.
Sosai suka daɗe a kasuwar dan sai gurin gab da la'asar sannan suka bar kasuwar suka nufi gida, dan sai da Hajiya Lubna ta gama duk wata siyayyar da zatayi wacce duk abinda ta siya sai tace Fadwan itama ta ɗauka, saboda tasan halinta ba ƙaramin aikinta bane tai ta terere da ita tana gayawa ƙawayensu tace ta rakota kasuwa amma taƙi sai mata komai shiyasa hatta da sababbin kayan baccin data siya sai data siyan mata itama kana suka bar kasuwar.
Tun a hanya kafin su ƙarasa gida Fadwa tasa Hajiya Lubna ta sauketa a Laventis Round About ta hau napep ta nufi Gwamna Road gidan Hajiya Labiba, ita kuma Hajiya Lubna ta wuce gidanta.
Ana kiran sallar la'asar ta isa gidan sai da ta fara saka chajin sabuwar wayarta sannan tasa Rabi ta zubo mata lafiyayen abincin data gama girkawa taci ta ƙoshi tayi hani'an sannan ta tashi ta haura sama ɗakin Hajiya Labiba taje tayi sallah inda ta haɗa azahar da la'asar kafin tana idarwa suka sake saukowa falon ƙasa tare.
Nan suka zauna sukai ta hira har wayar Fadwan ta