Showing 96001 words to 99000 words out of 113443 words
ba gaskiya bane wasa yake min..." Ta faɗa cikin matsanancin tashin hankali gwanin ban tausayi.
Rufe mata baki Hajiya Labiba tayi tana faɗin "A'a ba mafarki kike yi ba Fadwa a zahiri ne kike ganin duk abinda ke faruwa kuma gaskiya ne, amma fa nima kaina duk jikina yayi sanyi ban san me zance ba..."
Wani irin mugun kallo Mama ta watsawa Hajiya Labiba kafin tace "Babu wani sanyin jiki, domin indai Alhaji Zailani ne da aka ɗaurawa Fadwa aure dashi ba wannan ne gidansa ba, saboda babu yadda za'ayi ace babban mutum kamarsa da irin manyan motocin da yake hawa ace wai nan ne gidansa, mtsww zancen banza kenan..." Ta ƙarashe maganar lokaci ɗaya tana jan dogon tsaki kafin tace "Ku mu ƙarasa cikin gidan dai dan mu ƙara tabbatar da abinda yake nufi, kafin mu zartar da hukunci..."
Ta faɗa kai tsaye tare dasa kai cikin ƙwarin gwiwa ta shige cikin gidan, yayinda kuma Fadwa da Hajiya Labiba suma suka rufa mata baya cikin sanyin jiki suka doshi cikin gidan.
Basu raina kansu ba sai da suka tsinci kansu a ɗan tsukakken ƙazantaccen tsakar gidan, inda gaba ɗaya ko'ina yake rakwacam da kwatami ga wani ɗoyin bandaƙi dake busowa tsakar gidan yana yi maka sallama.
Ja da baya da sauri Mama tayi ta tsaya tana zaro idanu, kafin ta fara bin tsakar gidan da wani ƙazantaccen kallon ƙyama da ƙyanƙyani bayan ta toshe hanci tace "Kutumar uban nan kai, wai me suke nufi damu ne mutanen nan...?" Maman ta faɗa tare da juyawa da sauri ta fita waje, can sai gasu ita da Baba Salahu sun shigo, kamar kuwa dama jira Mama take su shigo nan ta rufesa da masifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, sai faman zuba masa ruwan bala'i take tana cewa ya kira mata Alhaji Zailanin yazo, wannan wane irin tsabar wulaƙanci ne da iskanci da rainin hankali, taya zaisa akawosu wannan ruɓaɓɓen gidan ace anan ƴarta zata zauna, wallahi bai isa ba bazata taɓa saɓuwa ba sai dai idan ya sakar mata ƴa amma wannan gidan kam ko minti talatin ƴarta bazata iya yi a cikinsa ba, maza maza ya kirasa yazo ya sallamesu an fasa auren tunda abun nasu duk rainin wayau ne da rainin hankali wallahi yau sai ya sakar mata ƴarta, bazata yarda tana ji tana gani ƴarta tayi rayuwar ƙasƙanci a irin wannan matsiyacin gidan ba.
Shi dai tunda ta fara faɗan bai tanka mata ba, hasali ma sunkuyar da kansa ƙasa yayi kawai yana saurarenta, sai da tayi faɗan ta gama sannan ya fito da wayarsa ƙirar Nokia mai tocila ya danna wata number kafin ya kara wayar a kunnensa.
Cikin lokaci kaɗan kuwa aka ɗaga kiran, yayi sallama kafin ya ɗora da faɗin "Munzo gidan amma Mamanta tace bazata zauna ba, sai dai in kiraka kazo ka saketa su koma gida..."
Kasaƙe Mama tayi tana saurarensa amma duk basu jin mai ake cewa daga ɗaya ɓangaren, sai dai kawai gani sukayi ya sauke wayar daga kunnensa yana faɗin "Toh shikenan saika ƙaraso ɗin..." Ya faɗa tare da kashe wayar ya mayar cikin aljihu yana kallon Mama da Fadwa da Hajiya Labiba da sukayi mai caa da idanuwa suna kallonsa.
Tsaki Mama ta saki cikin takaici kafin tace "Ni wallahi sam ban yarda nan gidansa bane, domin ba ta yadda za'ayi a danganta Alhaji Zailani da wannan matsiyacin gidan, sai dai in da wata a ƙasa da mu bamu sani ba..."
Hajiya Labiba ta rausayar da kai tana faɗin "Kiyi haƙuri Mama, mu jira har ya ƙaraso ɗin, sai muji dalilinsu na yi mana hakan..."
Wani wawan tsaki Maman ta saki kafin tace "Muna nan muna jiran isowarsa ɗin ai yazo ayi duk wacce za'ayi..."
Hajiya Labiba tace "Adai yi haƙuri Mama abi komai a hankali..."
Dan takaici Mama bata ƙara magana ba ta koma gefe ta jingina da jikin bango tana sauke numfashi, itako Fadwa dama duk maganganun da suke tana jinsu amma bata da lokacinsu ne ballantana ta tanka musu, saboda a ganinta ita damuwarta tafi gaban tsayawa ta biyewa wannan shirmen surutan nasu na banza ballantana har ta tayasu.
Suna nan tsaye cirko cirko a tsakar gidan kowa na saƙawa da kwancewa, Fadwa dai na tsaye da tunani barkatai a ranta daya cunkushe mata zuciya, domin a yanzu ta fara ɗiga ayar tambaya akan Alhaji Zailani da dalilinsa na sawa a kawosu nan gidan, sai dai kuma bata fatan abinda zuciyarta ke zargin ya tabbata har ya zamo gaske.
Suna nan tsaye kuwa sai ga Alhaji Zailanin ya shigo gidan faram faram yana tattare babbar rigar shaddarsa ta ɗaurin aure.
Ganinsa ne yasa Mama matsowa da hanzari tana washe masa baki tana faɗin "Yauwa gwara da Allah ya kawoka Alhaji, kaga wannan matsiyacin gidan direbanka ya kawo mu ya zube wai nan kace Fadwa zata zauna, kuma ance ba wancan gidan da ƴan uwanta sukaje suka gani bane shine abun yake bamu mamaki nace a kiraka kazo saboda inaga shi bai san wancan sabon gidan da ka ginawa Fadwan bane shiyasa ya kawo mu nan..."
Wani irin kallo Alhaji Zailanin ya watsa mata kafin yace "Ita Fadwan tafi ƙarfin zama a wannan gidan kenan kike nufi ko me...?" Ya faɗa kai tsaye yana watsa mata wani ƙasƙantaccen kallon da yasa Maman saurin matsawa gefe tana kallonsa.
Zaro idanuwa Mama tayi cike da tsoro kafin tace "Amma baka ga yanayin gidan bane..? Ai kaima kanka kasan babu ta yadda za'ayi Fadwa data saba da rayuwar jin daɗi ta zauna a irin wannan matsiyacin gidan balle har ta iya yin wata rayuwa a cikinsa ba..."
Cikin matsanancin ɓacin rai Alhaji Zailanin ya kalli Mama kafin yace "Dame gidan uban ita Fadwa ɗin yafi wannan amma har ta iya rayuwa a cikinsa na tsawon shekaru, sai wannan ɗin ne saboda tsabar rainin wayau da rainin hankali zakice bazata iya rayuwa a cikinsa ba, dame gidan nata uban yafi nawa da har kike faɗin haka...?" Ya faɗa cikin tsawa yana tsatstsareta da idanu cike da rashin kunya.
Wani irin rawa da kakkarwa jikin Fadwa da Mama ya ɗauka lokaci ɗaya yayinda suke kallonsa fuskokinsu ɗauke da tsananin mamaki da al'ajabin yanayinsa, ganin irin kallon da suke masa ne kuma yasa shi ƙara tamke fuska, kafin kuma cikin tsantsar rashin mutunci da rashin kunya yace "Ki buɗe kunnuwanki da kyau ki jini wannan gida da kike gani shine asalin gidan da Fadwa ƴarki zata zauna a cikinsa kuma zama na har abada, domin aurena da ita babu saki babu yaji kuma ban da wannan gidan bani da wani gida da ya kai min shi ballantana har ya fishi, saboda haka ku kama hanya ku fita ku bar min gidana tun kafin in fito miki a ainihin Ya'u na, sannan in nuna miki asalin kalata, domin ni ɗin nan da kike gani kallon kitse kike yiwa rogo ko ince kuna yi min kallon biri ne ni kuma ina yi muku na ayaba, dan ni ɗin nan da kike gani cikakken ɗan jagaliya ne na bugawa a jarida kije kuma ki tambayi duk wanda zaki tambaya tun daga kan farkon unguwar nan har zuwa ƙarshenta, kice musu waye Ya'u mai kifi daga yaro har babba babu wanda bai sanni yasan tarihina ba kuma babu wanda ba zai gaya miki asalin waye ni ba, saboda haka sahunki a likafa ki fita ki bar min gida, amarya dai tawa ce tunda na biya sadaki an ɗaura mana aure shaidu sun shaida kuma kun kawota gidan mijinta, saboda haka ga hanya fita ku kama gabanku kuma daga yau kar in sake ganin ƙafar ko waye daga cikinku a gidana, domin ni jajirtaccen namiji ne dan haka bazan ɗauki irin iskanci da wulaƙancin da kuka dinga yiwa wancan mijin nata na farko da kuka raina ba, ni ɗin nan na isheku riga da wando har da ƴar ciki.
Saboda haka ga hanya nan maza ku fice min daga cikin gida kowacce ta kama gabanta..." Ya ƙarashe maganar cikin tsawa da hargowa kamar zai kaiwa Maman duka.
Daga Mama har Fadwa da Hajiya Labiba kuwa gaba ɗaya jikinsu rawa ya ɗauka, kafin Mama ta iya ƙarfin halin buɗe baki cikin tsananin kaɗuwa da tsoro tace "Wane irin magana ne..wa.. wannan Alhaji..? A maimakon muga ɗorewar daɗi da farin ciki kamar yadda ka faro mana sai kuma kwatsam rana ɗaya yau ka canza mana gabaki ɗaya kamar baka sanmu ba...?"
Watsa mata harara yayi kafin yace "Dawa kuke tunanin ɗorewar daɗi da farin ciki a tare dashi..? Kin ko san ma dawa kike magana kuwa..? Kai ga dukkan alamu dai har yanzu baki fahimci inda maganata ta dosa ba, amma bari in yi miki gwari gwari saboda kar in barki a duhu..."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakin wani munafukin murmushi kafin ya ɗora da faɗin "Ni ɗin nan da kike gani ban je neman auren ƴarki dan ina sonta ko domin tana burgeni ba, hasalima naje nemanta ne domin in bata shawara sannan in nusar da ita illar abubuwan da take yi wanda har ya jawo mata rashin samun kwanciyar hankali a gidan mijinta sannan kuma cikin hikima in ganar da ita babban kuskuren data tabka a rayuwarta na rabuwa da mijinta da tayi, amma sai me..?
Tun a zuwan farko da nayi gidanku na fahimci maganar da mutanen unguwar ke faɗa a kanku ke da ita na tsantsar kwaɗayi da son abun duniya da rashin wadatar zuciya gaskiya ne, wanda hakan yasa na sake komawa na yo sabon shiri kafin na sake dawowa da ƙarfina da nufin siye zuciyarta da taki gabaki ɗaya, kuma sai gashi ban sha wata wahala ba domin dukkanku kun kasance masu kwaɗayi da son abun duniya, shiyasa tun a ranar farko na ƙara fahimtarku na gano inda kuka dosa da yanayinku gabaki ɗaya, wanda ni kuma hakan yasa na ƙara zage damtse na shiga na fita na aro duk wani abu da nasan zai ƙara dulmiyaku har ku shagala da son gano ko ni ɗin wane ne na gama siye zuciyarku da bakunanku da abu mafi soyuwa a gareku wato kuɗi.
Saboda nasan idan naje gidanku a yadda nake bani da komai da wuya ki saurareni saboda dogon burin da kuka ɗauka ke da mahaifiyarki kuka ɗorawa kanku.
Hakan yasa naje nayo aron haɗaɗɗiyar mota da kuɗaɗe masu yawa nazo har ƙofar gidanku na aika akayo min sallama dake, sannan nace kiyi min iso inaso zan shiga in gaida mahaifiyarki..." Ya faɗa yana sakin wani makirin murmushi kafin ya cigaba da faɗin "Nayi mamaki sosai na irin tarbar dana samu a gun mahaifiyarki, domin ko kaɗan bata tambayeni waye ni da sana'ata ba, kawai ina zube mata kuɗi ta hau rawar jiki tana yaƙe baki, tun daga nan na ƙara tabbatar da ku ɗin ko su waye.
Daga nan na dinga ƙoƙarin son inga na burgeki, wanda hakan yasa kina gaya min kina son waya naje kai tsaye na aro waya mai tsada a gurin wani na kawo miki.
Wanda kuma a ranar na haɗu da mahaifinki mutumin kirki ya tambayeni waye ni sannan meye sana'ata duk na faɗa masa gaskiya, cewa ni mai cin kasuwar ƙauye ne inda nake siyo dabbobi da kayan miya ina siyarwa, sannan ina soya kifi a bakin titin layinmu ban ɓoye mai komai ba, duk a tunanina mahafinki bazai yarda in aureki ba sai gashi kai tsaye yace ya bani ke in turo magabatana a tsaida magana.
Ban taɓa zaton zan sameki cikin sauƙi haka ba, shiyasa tunda aka ɗaura aurena dake yau nake cikin tsantsar farin ciki duk da yake babu mutum ko ɗaya a cikin dangina da iyalina da yasan cewa na ƙara wani auren a birni, domin ban sanar dasu komai ba, amma duk da haka ina cikin matuƙar farin ciki da jin daɗi sosai..." Ya ƙarashe faɗa yana murmushi mai cike da tarin ma'anoni.
Fadwa kuwa tunda ya fara maganar jikinta ya ɗauki wata matsananciyar kakkarwar tashin hankali da ɗimuwa, lokaci guda gaba ɗaya kunnuwanta suka daina jiye mata sautin muryarsa sai shuuuuuu kawai da suka ɗauka ji take kamar ba gaske ba, dama ranar yau ɗin ta zame mata tamkar a mafarki ba gaske ba.
Jan kumatunta tayi da ƙarfi ta shafa fuskarta yanzu kam ta tabbatar da ba mafarki take ba, da gaske ne komai dake faruwa a gabanta, sai dai bata san me zatayi ba kukan baƙin ciki ko nadama..?
Idan na baƙin ciki ne anya ya dace ta tsaya tunanin abinda ya kamata da wanda bai kamata ba..? Idan kuwa na nadama ne ya dace ta tsaya saurarar zantukansa wanda furtasu yake dai-dai da yankewar numfashi daga gangar jikinta ta yanke jiki ta faɗi ƙasa..?
Wani irin mummunan bugawa zuciyarta tayi da mugun ƙarfi ta zame ta zauna daɓas a ƙasa tana dafe kai cike da matsanancin tashin hankali kafin tace "Wane irin laifi nayi maka dana cancanci irin wannan sakayyar daga gareka, mena yi maka daka zaɓi ka muzgunawa rayuwata ka wulaƙantani a idon duniya irin haka..mena tsare maka dan Allah wane irin zunubi na aikata maka da zakayi min sakayya irin wannan..me nayi maka da zafi haka...?" Ta faɗa lokaci ɗaya tana jin saukar wasu zafafan hawaye daga cikin idanunta.
Cikin damuwa Hajiya Labiba tace "Nima dai tambayar da nake son yi masa kenan kika rigani..."
Mama kuwa baya taja tana dafe ƙirji gaba ɗaya ta gama cika da mamakinsa hakan yasa bakinta yayi mata nauyi ta gaza iya furta komai sai faman kallonsa kawai da take tana jinjina kai cikin matsanancin mamaki da al'ajabi, a hankali take ƙoƙarin tattare maganganunsa tana aunawa a mizanin da zata iya fassarawa da yaren da zata iya ganewa domin maganganun nasa sunyi mata kama da saukar aradu nauyinsu yayi mata yawa.
Shiko Ya'u ko kaɗan bai ji tausayin Fadwa ba, sai ma sake matsawa da yayi gabanta yana murmushi ya kai hannu yana ƙoƙarin riƙota tai saurin ja da baya ta miƙe tsaye tana girgiza masa kai hawaye na ƙara zubo mata.
Sake matsawa yayi kusa da ita zai kamota, sai ta fashe da wani matsanancin kuka tana girgiza kai kafin tace "Na roƙeƙa da girman Allah ka barni ka rabu dani, na haɗaka da girman Allah..." Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka mai ƙarfi.
Ya'u ya bita da kallo kafin kuma ya maida kallonsa kan Baba Salahu dake tsaye yana ta kallonsu cikin al'ajabi, taɓosa Ya'un yayi yana faɗin "Kwashesu ka mayar dasu gida dare na ƙara yi..."
Kallonsa Mama tayi kafin tace "Ban gane a kwashemu a mayar damu gida ba, ita Fadwan kuma fa, kana nufin anan zamu barta kenan ko me kake nufi...?"
Wani irin banzan kallo ya juyo ya watsa mata kafin yace "Abinda nake nufi kenan, ku fita ku bar mana gida inaso zan huta da amaryata, idan kuma kika zaɓi akasin haka to ki tabbatar da a yau ba sai gobe ba zaku biyani duk abinda na kashe muku tun daga ranar dana fara zuwa gidanku har kawowa yau da aka ɗaura mana aure, komai da komai yana nan a rubuce tsaf a takarda na gama lissafawa, idan kuka biyani yanzun nan zan saki ƴarki ku ƙara gaba, zaɓi ya rage naki..." Ya faɗa kai tsaye yana kallon cikin ƙwayar idanunta.
Baki Mama ta rufe cikin kaɗuwa tana faɗin "Yanzu ashe dama baka da mutunci ban sani ba, ashe abinda ka tanada zakayi mana kenan ko..? To wallahi bazan taɓa ƙyaleka ba, kuma wallahi sai kasan mu ka wulaƙanta..."
Wani kallo Ya'u ya sake watsa mata kafin ya nuna mata hanyar fita yana faɗin "Fitar min daga cikin gida tun kafin in sauya tunanina a kanki, idan kuma kina ganin wasa ne ki jira ina zuwa..." Yana gama faɗin hakan ya fizgi hannun Fadwa dake duƙe tana rusa uban kuka ya jata tana tutturjewa tana ihun kuka ya shige da ita wani ɗaki kafin ya mayar da ƙofa garam ya rufe yana faɗin "Karku yarda in sake fitowa in iskeku a cikin gidana, idan ba haka ba kuwa duk abinda nayi muku kune kuka jawa kanku..."
Tsayawa akai kallon kallo tsakanin Hajiya Labiba da Mama, kafin Hajiya Labiba tayi ƙarfin halin riƙo hannun Mama dake tsaye kamar an dasata tace "Mama muje dan Allah kar ya sake fitowa ya iskemu yayi mana rashin mutunci, dan naga alamun bai da kunya zai iya aikata abinda ya faɗa..." Ta faɗa tana janta da hanzari suka fice daga gidan, yayinda Baba Salahu shima ya rufa musu baya da sauri suka fice tare.
Koda suka fito waje kuwa da ƙyar Hajiya Labiba ta iya lallaɓa Mama data toge a bakin motar ta kafe tace babu inda zataje har sai Ya'u ya sakar mata ƴarta.
Sai da ƙyar da ya Allahu sannan Hajiya Labiba da Baba Salahu sukayi da gasken gaske kafin ta haƙura ta shiga bayan motar ta zauna tana ta sauke numfarfashin wahala da tashin hankali, kafin itama Hajiya Labiba ta zagaya ta shiga ta zauna a kusa da ita kana Baba Salahu shima ya shiga yaja motar suka bar unguwar.
A ɓangaren Fadwa kuwa sosai hankalinta yay mugun tashi, sai tutturjewa take tana ihun kuka amma ko kaɗan Ya'u bai ji ɗigon tausayinta a ransa ba, haka ya wancakalar da ita a saman wata ƴar yaloluwar katifa mai kamar tabarma dake tsakar ɗakin.
Fashewa tayi da wani sabon kuka tana faɗin "Dan girman Allah na haɗaka da Allah da Manzonsa kayi haƙuri ka rabu dani na tuba ka taimaka min..." Take faɗa tana jan ajiyar zuciya tamkar numfashinta zai ɗauke yabar gangar jikinta, saboda tsabar tashin hankali da tsantsar damuwar da take ciki.
Miƙewa tsaye yayi yana murmushi ya cire babbar rigar shaddar dake jikinsa ya aje gefe, kana ya kai hannu ya kamo hannunta yana shafawa cikin wani irin salo yana faɗin "Haba mana amaryar Alhaji Muhammad Al'ameen Zailani, kiyi haƙuri ki rungumi angonki mana..."
Fizge hannunta tayi ta miƙe tsaye da sauri tana zaro ido lokaci ɗaya tana girgiza masa kai.
Murmushi ya sakar mata yana ƙoƙarin sake kai hannu ya riƙota ta ƙara matsawa can gefe ta manne a jikin bango tana kakkarwa da tsiyayar hawaye.
"Dan darajar iyayenka ka ƙyaleni, na roƙeƙa dan Allah..."
Ta faɗa tana ƙara matsawa baya tare da haɗa hannayenta guri ɗaya alamar roƙo.
Matsawa yayi da sauri ya riƙota lokaci ɗaya ya haɗeta da ƙirjinsa ya ruƙunƙumeta yana sauke numfarfashi haɗe da ajiyar zuciya.
Mutsu mutsu ta hau yi tana ƙoƙarin