Showing 99001 words to 102000 words out of 113443 words

Chapter 34 - WADATAR ZUCI Complete Book by Aisha Alto.txt

22 Feb 2025

7560

ƙwatar kanta amma ina ya riƙeta gam gam babu ta yadda za'ayi ta iya ƙwatar kanta.
Haka ta gaji da mutsu mutsun dan kanta ta haƙura ta lafe a jikinsa yayinda take ƙara fashewa da wani kuka mai ƙarfi da matuƙar ban tausayi, da sanyaya jikin duk wanda ya saurara.






Itako Mama koda ta koma gida banda sannu da zuwan da ƴan uwanta sukayi mata babu abinda ya sake shiga tsakaninta da kowa, haka ta shige ɗakinta ta haye gado ta kwanta tana ta juye juye ranta fal da tunanin makomar rayuwar Fadwa a gidan Ya'u mai kifi.


Tambayan duniyan nan kuwa Abba yayi mata amma tace mai lafiya ƙalau babu komai, kawai gajiyar biki ce take nuƙurƙusarta, daga ƙarshe dai haka Abba ya zura mata ido kawai ya ƙyaleta ba tare daya sake tanka mata ba.


Ita kuwa Hajiya Labiba tun a daren ta dinga kiran wayar ƙawayensu tana gaya musu abinda ya faru.
Inda Hajiya Lubna sosai abun ya taɓa ta ta, wanda da yawa kuma daga cikin ƙawayensu dariya suka dinga yi suna jin daɗin abinda ya faru da Fadwa, dan dama tuni take basu haushi da wannan iyayin nata na banza da wofi.






Washegari


Fadwa ce durƙushe gaban murhu ta haɗa itace tana ta hura wuta da bakinta, yayinda kuma idanuwanta suka kaɗa sukayi jajir hawaye sai tsiyaya suke daga cikin idanunta suna mata wani mugun raɗaɗin azaba, kwana ɗaya tak tayi amma duk tai wani wujiga wujiga da ita gwanin tausayi.
Gefe kuma Ya'u mai kifi ne tsaye daga shi sai gajeren wando a jikinsa yana riƙe da mafici yana fifita sai wani banzan kallo yake jefa mata.
A hankali ta miƙe taje ta ɗauko tukunya tazo ta zuba ruwa tana ƙoƙarin ɗaurawa akan murhun ya karɓe tukunyar yana faɗin "Dalla ki hura wutar ta kama tukunna kafin ki ɗora tukunya, ko a gidanku haka wannan tsohuwar uwar taki ta koya miki ɗora tukunya ba tare da ice ya kama ba...?" Bai bata zarafin magana ba ya cigaba da faɗin "Ko da yake ba abun mamaki bane tunda babu abinda ke gabanta sai son abun duniya, bai zama lallai ma ta tsaya koya miki girkin ba tunda in banda son kuɗi babu abinda ta saka a gabanta..."


Kuka Fadwa ta fashe dashi ta ɗago tana kallon Ya'u, wanda ya kauda kai da sauri yana watsa mata harara.
Hannunsa ta kamo cikin sanyin jiki tana faɗin "Dan Allah idan akwai abinda nayi maka da yasa kake da niyyar azabtar dani da irin wannan wulaƙancin, kayi haƙuri ka yafe min ba dan halina ba na tuba ka gafarceni..." Ta faɗa lokaci ɗaya tana jin taruwar wasu zafafan hawaye a idanunta, jikinta kuwa sai faman rawa yake da kakkarwa, dan zuwa yanzu ji take tamkar tai ta ihu da ƙarfi ko zataji sauƙi da sassaucin baƙin ciki da tashin hankalin dake azalzalar ruhi da zuciyarta.
Bai tanka mata ba ya raɓa ta gefenta ya wuce ɗaki, haka ta zauna ta ci kukanta har ta gaji ta share hawayenta, sannan ta miƙe ta cigaba da aikin girka tuwon daya sata a matsayinta na amaryar da aka kawo gidan miji jiya, wacce ya kamata iyanzu ace tana cikin ɗaki akwance tana hutawa, amma saboda rashin gata yasa babu yadda ta iya dole ta fito, tayi abinda ya sata.




Bayan Kwana biyu


Zaune take a ɗan filin tsakar ɗakinta wanda babu komai a cikinsa sai tarkacen kayan robobin cin abinci da tukunyar da take dafa musu abinci sai bunbun zuba ruwan sha, wanda kuma ko arzikin ledar tsakar ɗaki ɗakin bai samu ba, sai wata ƴar yaloluwar katifar da suke kwanciya akai wanda ko arzikin zanin gado itama bata samu ba, sai kuma wani ɗan ƙullin kaya da aka ɗaure a ɗankwali wanda shine a matsayin filo.
Tsuru tayi kawai tana kallon ko'ina a cikin ɗakin kafin a hankali ta kai bayan hannunta ta goge wasu sababbin hawayen da suke ƙara zubo mata.


Wanda kuma tun da take bata taɓa shiga tashin hankali irin wanda take ciki a yanzu ba, duk wani abu da take tunani kuwa ada lokacin da take gidan Ya Azeez sai ta tarar na yanzu yaci ubansa.
Dan tun da take da Ya Azeez bai taɓa zagin iyayenta ba koda wasa, kuma kullum burinsa shine yaga ya kyautata mata, bai taɓa barinta cikin damuwa, kuma koya ta nuna tana son abu ko mene ne shi kuma koda yafi ƙarfinsa ne sai ya nemo mata koda kuwa zai takura kansa ne sai yasan yadda yayi ya samo ya kawo mata.
Bai taɓa barinta tayi aikin komai indai har yana gida, ko girki shi ke yi mata da kansa ya kuma bata taci, amma bai taɓa nuna gajiyawarsa ba, hasalima a kullum burinsa shine yaga ya faranta mata rai ya mata abinda takeso.
Amma wannan kam yau kwana uku da kawota gidansa har ta fara tantance tsakanin aya da tsakuwa.
Allah sarki Ya Azeez, ashe akwai ranar da zataji kewarsa a ranta har taji dama ace tana gidansa bata fito ba..?
Lallai sai yanzu take ƙara yarda da maganar Abbanta, inda yace yayi matuƙar baƙin cikin rabuwarta da Ya Azeez kuma ya tayata baƙin ciki domin da wuya ta ƙara samun kamarsa, kuma haka zatai ta kokawa rashinsa a rayuwarta.
Saboda shi ɗin na musamman ne kuma samun irinsa a wannan lokacin zaiyi matuƙar wahala.
Kuma gashi tun kafin aje ko'ina da rabuwar tasu abubuwa sun runcaɓe mata.


A Haka dai rayuwar Fadwa ta dinga gudana a gidan Ya'u mai kifi.
Inda a cikin kwana huɗu zuwa biyar duk ta rame ta jeme kana ganinta kasan tana cikin matsananciyar damuwa.
Shiko Ya'u a cikin ƴan kwanakin har wata ƴar ƙiba ya ƙara yayi kyau abinsa yay ɓul, alamar dai bai da wata damuwa, dan tunda akai auren bai fita wajen suyan kifi ba, koda yaushe yana nan naniƙe da ita a gida yana gurzarta kamar tuwo ko gajiya baya yi.
Gaba ɗaya Fadwa ta gama galabaita irin muguwar galabaitan nan duk ta fita a hayyacinta, wanda kuma a cikin kwanakin duk wanda ya ganta da wuya ya iya ganeta, saboda wata iriyar muguwar rama da tayi ga wani uban baƙi da tayi kullum ita kenan baki a bushe ƙayau gwanin tausayi.
Allah ya sani ta kasa sabawa da yanayinsa gabaki ɗaya, amma ya kasa tausaya mata.
Gashi babban abinda yake matuƙar ɗaga mata hankali kullum shi kenan aikin abu ɗaya, ba dare ba rana.
Wanda kuma a gidan Ya Azeez sam bai saba mata da hakan ba, gashi kwata kwata shi bai iya tarairaya da lallashi da tausasawa ba.
Saɓanin Ya Azeez ɗinta dake komai cikin nuna tsantsar kulawa da soyayya uwa uba kuma tausasawa da lallashi, ga tarairayarsa mai matuƙar tsayawa mutum a zuciya, wanda kuma a lokaci guda sai yasan yadda yayi ya fitar da kai daga hayyacinka ya ɗaukaka maka tsananin so da shaukin kasancewa dashi cikin kowanne irin yanayi a lokacin.
Saɓanin wannan kuma da kullum burinsa kawai ya hayeta ya biya buƙatarsa babu ruwansa da wani lallashi ballantana wata tausayawa, shi dai kawai yaji ya gamsu kuma buƙatarsa ta biya shikenan zai tsallake ya barta.


Wannan yanayi yana matuƙar yiwa Fadwa ƙunci da baƙin ciki, tana matuƙar azabtuwa domin ta riga ta saba da yanayin Ya Azeez ɗinta cikin watanni taran da sukayi tare, gashi tun tafiya ba tayi nisa ba har ta fara tsanar kanta da nadamar abinda ta dinga yiwa Ya Azeez wanda a lokacin idan yazo mata da buƙatarsa bata saurararsa sai dai tai ta kawo masa uzururrukan ƙarya ƙarshe kuma ta nuna masa bata ra'ayi.
Shi kuma dake yana tsananin gudun ɓacin ranta a lokacin sai ya haƙura koda kuwa zai cutu ne ba zai taɓa takura mata ba.
Amma wannan tana ji tana gani kuma ko tana ra'ayi ko bata yi, haka zai zage ya sasiƙeta iyakar son ransa, wata rana kuma yana yi yana zagin mahaifiyarta haka zaiyi ya gama kuma ya tsallake ya barta nan.






*************




Bayan Sati Ɗaya


Acan Kano kuwa tuni shirye shiryen bikin Shatu da Ya Azeez yake ta ƙara kankama, Shatu da ƙawarta Husna Baita kuwa tunda bikin ya ƙarato kullum cikin zirga zirga suke basu nan basu nan, dan har gidansu Ummi taje ta roƙi mahaifiyar Husnan akan a barta ta zauna a gidansu har sai an gama biki, dan ita kanta Zahra bata samun zama yanzu kullum tana kan hanyar zuwa kasuwa yin siyayya.
Haka a ɓangaren Ya Azeez kuwa shima yana cikin tsananin farin ciki, shirye shirye kawai suke shi da Fahad da sauran abokanansu.
Biki ne kuma suke shiryawa na kece raini irin na manyan ƴaƴan gata.






























*Ya Allah ka gafartawa mahaifina da sauran Musulmi baki ɗaya🤲*
*WADATAR ZUCCI*




*Wattpad: Aishaalto09*






3️⃣6️⃣




A haka shirye shiryen bikin yake ta ƙaratowa, gashi har yau saura sati biyu, shirye shirye kuwa kota ina yinsa akeyi, ta ɓangaren gidan su Shatu kuwa suma suna ta yin nasu.
Haka a ɓangaren gidansu Ya Azeez suma duk da Umma ba a garin take ba, amma Abba yaba Mami manyan kuɗaɗe ita ta shige gaba akan komai kamar itace uwar angon, domin shi kansa uban gayyar yana daga ɓangaren Mamin da ita yake dukkan wasu shawarwari da shirye shirye, hatta da kuɗin kayan lefe da komai da komai kuwa ita Ya Azeez ɗin ya turawa ta account ɗinta bayan kuma wanda Abba ya bata shima ta haɗa, suka je Dubai ita da Basma da wata ƙawarta Hajiya Turai suka haɗo komai.
Ɓangaren gidansu Shatu ko suma suna can suna ta nasu shirin bikin na kece raini irin na ƴaƴan manyan mutane.




*********


Zaune take a saman kujera mai cin mutun uku dake cikin falonsu, wayarta ce a hannunta suna video call da Ya Azeez, wanda baya gari yau kwanansu uku kenan a Lagos shida Fahad, sunje siyo motoci, inda kuma sati ɗaya zasuyi acan kafin su dawo.


Sanye take da wata doguwar rigar jallabiya baƙa, wacce ta dace da kyakkyawan surar jikinta, kanta kuma kitson kalaba ne ƙanana ƙanana da Husna ƙawarta ta kama mata, gyalen jallabiyar ne a kanta wanda ya zame kaɗan, sai hakan ya baiwa lallausan baƙin gashin dake gaban goshinta damar bayyana gashi kalaban ya kamu sosai gashin kuma yasha gyara sai sheƙi yake, fuskarta tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tai ba, sai ƴar hoda kaɗan da lipstick da ta ɗan goga, amma fuskarta tayi kyau matuƙa sai sheƙi take.


Daga tsakiyar falon kuma Husna ƙawarta ce zaune a saman kafet ɗin dake shimfiɗe a falon ta tanƙwashe ƙafafunta ta jingina bayanta da jikin kujera tana ta faman latsa wayarta.


Shatu kuwa sosai tayi nisa ta shagala da video call ɗin da sukeyi da Habibyn ta, sai zuba masa shagwaɓa take tana wani narke masa wai ita ala dole nan tayi missing ɗinsa, shi kuma duk ya wani susuce mata sai lalaɓata yake yana lallashinta.


Ƙara gyara zama tayi tana kwaɓe fuska cike da wani irin salon shagwaɓa da sangarta, wanda har gyalen kanta ya zame gaba ɗaya kalaban kanta ya bayyana.


Daga can ɓangaren Ya Azeez kuwa dake kwance a saman wani makeken Royal bed dake cikin wani katafaren hotel da suka kama a garin Lagos, juyi yayi yana ƙara ƙanƙame filon dake rungume a ƙirjinsa ya tsura mata ido ta cikin screen ɗin wayar kafin yace "Pls Eishatuna ki ɗan sassauta min kar ki zautani in kasa aiwatar da abinda ya kawo ni..." Ya faɗa cikin wata irin kasalalliyar murya dake bayyana tsantsar shauki da muradin da yake ciki, kana yana wani lumshe manyan idanunsa yana sakin numfashi.


"Ni kuma Habiby..."
Ta faɗa a sanyaye tana karyar da wuyanta gefe a sangarce.


Saukar muryarta a kunnuwansa da yadda tayi maganar da wani irin daddaɗan salo ne kuma yasa shi jin wani irin yanayi mai cike da shauki da muradi mai girma na sauka da yawo a cikin jikinsa.
Wanda kuma hakan yasa a hankali ya rungume wayar a ƙirjinsa kana ya ɗago lokaci ɗaya yana ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo ta cikin screen ɗin wayar, kafin kuma ya kwaɓe fuska cikin wani irin salo na musamman yace "Pls ki barni haka Eishatuna, zamuyi waya anjima, yanzu Fahad na jirana zamuje wani guri dashi idan na dawo zan kiraki..."


"Nifa Habiby ban gaji da jin muryarka ba, pls kace masa ya tafi shi kaɗai, ya barni in ɗan ƙara ganinka kaji..."
Ta faɗi maganar cikin sigar shagwaɓa, tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.


Tausasan laɓɓan nata ya kalla, still kuma yana ƙara jin wani irin abu nayi masa yawo a cikin jikinsa yace "Idan na dawo zan kiraki ai, bazan daɗe ba kinji...?"


"Uhmm..."
Ta amsa masa a hankali tare da ɗan tsura masa ido ta cikin screen ɗin wayar tana kallon kyakkyawar fuskarsa, kafin ta ɗaga masa hannu alamar bye, kana kuma ta katse kiran.


A hankali ta ɗago kai tana murmushi karaf kuwa idanunta suka sauka a cikin na Husna dake ta galla mata harara, ganin irin kallon da take mata ne yasa ta zamewa ta kwanta a saman kujera tana faɗin "Kyaji dashi dai..."
Ta faɗa tana wani lumshe idanunta a hankali tana sauraran yadda zuciyarta ke bugawa da tsananin son Ya Azeez da ƙaunarsa.


Husna kuwa ganin sharetan da tayi ne yasa ta miƙe tsaye tana faɗin "Idan kinga dama sai ki tashi mu tafi dan wlh idan kika bari na kwanta duk nacinki babu inda zanje, sai dai ki tafi ke kaɗai ko ki haƙura da fitar sai gobe, amma idan na shige na kwanta kuwa ba inda zanje na rantse..."


Kanta ta ɗan dafe a hankali kana ta tashi da sauri saboda tunawar da tayi cewa Basma na can na jiran zuwansu domin su tafi kasuwa suyo siyayya.


A hankali ta miƙe tsaye tana ɗaukar wayarta kafin tace "Muje ni karki cinyeni da baki, almasifatu..." Ta faɗa tare da yafa gyalen jallabiyar a kanta, kana taja hannun Husnan lokaci ɗaya suka fice daga falon.


A farfajiyar gidan suka ci karo da Ummi da ƙawarta Hajiya Zakiya da tayo mata rakiya, suna ta hira taƙi ƙarewa tun daga cikin gida.
Cikin natsuwa suka ƙaraso kusa dasu suka rusuna suna gaishe da Hajiya Zakiyan, ta amsa musu fuska a sake kana tana kallon Shatu cike da tsokana tace "Ƴata amarya lallai har kin fara kyallin goshin amarci, wannan irin kyau haka sai ina kuma da yamman nan...?"
Shatu tai murmushi tana sunne kai, Ummi ta harareta cikin wasa tana faɗin "Ina zasu kuwa daya wuce kasuwa yo siyayyar biki, ai kinsan ƴaƴan yanzu ba kunya ce dasu ba, ko irin ƴar kunyar nan ma su basu ji kawai shirye shiryen su suke tayi da kansu babu abinda ya damesu, marasa kunya kawai..." Ta ƙarashe maganar tare da zafgawa Shatun hararara.
Da sauri Shatu ta kamo hannun Husna suka wuce da hanzari suna dariyar maganar Ummin.
Hajiya Zakiya kuwa kai ta kaɗa tana dariya kafin tace "A'a barsu suyi Hajiya Khadija lokacin su ne, Allah yasa ayi taro lafiya a tashi lafiya..."
Ummi tace "Ameen ya Allah Hajiya..."
Daga haka suka ƙarasa inda direban Hajiya Zakiyan yayi parking motarta ta buɗe gidan baya ta shiga, kana suka ƙara yin sallama da Ummi, direban yaja bayan maigadi ya buɗe musu gate ne kuma suka fice daga cikin gidan, yayinda direbansu Shatu shima ya rufa musu baya suka fice daga gidan a tare.




Washegari


Ranar ta kama saura kwana sha ɗaya dai-dai bikin Ya Azeez da Shatu.


Aunty Salma kuwa takanas ta ɗauko wata mai gyaran jiki da tsumi tun daga ƙasar Niger, wanda kuma ba ƙaramin kuɗi aka kashe ba wajan zuwanta nan ɗin.
Koda ta iso kuwa wani lafiyayyen ɗaki na daban aka ware musu a cikin gidan, baka jin komai kuwa sai ƙamshi, gadon da aka ajiye domin baccinta kuwa tamkar anyi ɓarin turare akai.


Kullum da safe za'ayi mata turaren jiki dana tsugunno dana wanka, sosai ake gyarata ciki da wajenta.
Ga haɗin kayayyaki kala kala, tun daga kan na gyaran jiki har na turaruka da kayan mata.
Haɗi akayi mata na musamman irin na amaren zamani.
Tsumi ne na musamman irin na buzaye akewa Shatu, gyara ciki da wajenta dashi, sai tsumata ake, yanayin turaren da ake turara mata jiki da tufafi dashi kuwa lokaci guda wani daddaɗan ƙamshi ya soma bin jikinta duk inda ta gitta kuwa ƙamshi take bari awajen.
Kullum mai yi mata dilka da halawa sai tazo, ga wani sihirtaccen kyau data ƙara, haskenta ya ƙara fitowa fuskarta ta ƙara wani fresh tai kyau gwanin ban sha'awa.


Yayinda kuma a kullum Aunty Salma da kanta take sakata gaba tana bata haɗe haɗen da Hajiya Mariam Buzuwa ta haɗa mata, wanda kuma saboda tsabar son zaƙinta bata taɓa yi mata musu, haka take karɓewa ta shanye abinta tass hankalinta kwance.
Wanda hakan yasa a wuni sai ta canza pant uku, saboda yadda take tsiyaya, sakamakon gyaran ya kamata sosai.


Ana saura sati ɗaya biki kuwa su Mami da wasu manyan ƙawayenta suka kawo akwatuna guda goma sha biyu cif shaƙe da tsadaddun kaya ƴan gasken na kece raini.
Sannan kuma Fahad ya bada makullin danƙareriyar mota ƙirar Ferari fara sol wacce aka zubo kayan akwatinan acikin yace kyautarsa ce a kawowa amarya.
An karɓe su hannu bibbiyu domin ƙawayen Ummi manyan mata sun cika gidan, ga kuma tawagar Aunty Salma suma dan haka akayi musu tarba ta mutunci da karamci.
Sosai suka ga kara da karramawa, sai yamma liƙis sannan suka koma gida bayan an cikasu da abin arziki har da tukuicin kuɗi mai tsoka.


Inda kuma ana saura kwana uku ɗaurin aure ne Umma da Imaan suka zo daga Kaduna, nan gidan iyayen Fahad ɗin dai suka sauka, wanda kuma ta ɓangaren ango a nan ne za'ayi komai na taron bikin.


Ɓangaransu Shatu kuwa yau ne suka fara gabatar da events ɗinsu wanda kuma gaba ɗaya duk na mata zalla ne babu namiji ko ɗaya, wanda kuma yanzu tsakanin Shatu da Ya Azeez waya ne kawai ke haɗasu sai chat, saboda an hanata fita sakamakon gyaran da ake mata.
Shiyasa sosai suke kewar junansu, ba kamar Ya Azeez da yake cike da tsananin ƙaunarta da begenta, haƙuri kawai yake yana daurewa saboda babu yadda zaiyi, amma ji yake kamar yayi shekaru ne bai ganta ba.
Ranar da akayi Bridel Shower kuwa wasu ƴan uwan Abbie dana Ummi suka iso, washegari kuma akayi buɗan kai da kamu wanda idan ka kalli Shatu kuwa a ranar saika ƙara kallonta saboda tsantsar kyawun da tayi, kuma a ranar ne ƴan uwan Abban Ya Azeez dana Ummansa suma duk suka iso garin.


Sai ana gobe ɗaurin aure ne suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login