Showing 1 words to 3000 words out of 119425 words
Chapter 1 - RUWA DA KANKARA Book Complete by Hadiza D Auta.pdf
مس.>
*______________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈⛈*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The notion}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________________*
*PAGE ONE*
*********************
Wani dattijo ne tafe akan keken shi, da ciyawa a bayan kariyar sa wadda ya daure da igiya,
yana ta sauri saboda yana so ya k'arasa gida, saboda hadarin dake barazanar tasowa, ga wani
duhun damana da ya mamaye fadin sararin samaniya.
Aiko duk saurin shi na son yaje gida kafin afara ruwan, sai da suka fara sauka tareda wani iska
mai karfi dake kadawa, ya karawa keken shi gudu yana tafe yana sharce ruwan dake zuba
akan fuskarshi.
Tun daga nesa yake jiyo sauti kamar na kukan jariri, acikin al'jabi ya k'ara kasa kunnuwan shi,
saboda yana so ya gasgata abunda kunnuwanshi suka jiyo masa, acikin fargaba yake tafiya
saboda jin kukan yana k'ara kusantoshi, sai raba ido yakeyi domin ya ganema idanunshi
abunda zuciyarshi ta tabbatar masa.
Karaf idanunshi suka hango masa wani k'aton kwali dake ajiye acikin ciyayi, inda ko tantama
babu acikinshi ne wannan kuka na jariri yake fitowa.
Gabanshi ya k'ire ya fad'i, ba shiri ya tsaida keken shi ya sauko, tareda furta kalmar:
"INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN YA HAYYU YA KAYYUMU BI RAHMATIKA
ASTAGISU, A'UZU BI KALIMATILLAHIT TAMMATI MIN SHARRI MA KHALAKA"
Bai tsaya anan ba har saida yayita jero addu'o'i yana shafe jikin shi, sannan ya tunkari inda
kwalin yake ajiye, acikin jarumta ya saka hannu ya bud'e kwalin bakin shi d'auke da bismillah,
da sauri yaja baya ganin abunda ke ciki, alokaci d'aya aka tsuge da ruwan sama masu k'arfi,
har ya juya acikin sauri da nufin yaja keken shi ya bar dajin.
Aiko jinjiri ko jinjirar dake cikin kwalin ta kara k'wallah wani kuka saboda ruwan saman dake
sauka acikin kwalin suna jik'a masa/mata jiki, da sauri dattijon ya waigo yana k'ara maimaita
addu'a acikin zuciyarshi da bakin shi.
Da hanzari ya dawo ba shiri, ya k'ara zurawa jinjirin/jinjirar idanu, alamu duk sun nuna a
bayyane cewa mutum ce/ne, amma ganin farin da tsantsar kyawon halittar ya sakashi jin tsoron
kar fa ace diyan aljanu ne, azuciyarshi yace:
"Nayi niyyar taimako don Allah koma menene Allah Ubangiji ya kare ni da sharrin dake ciki"
Aikuwa duk wani tsoron da yake ji ya gushe azuciyarshi, acikin kuzari, yayi bismillah ya saka
hannu ya d'auko abunda ke cikin kwalin, ya aza akafad'arshi, ba shiri jinjirin/jinjirar yayi shiru
tareda sauke wasu ajiyar zuciya ajere da juna.
Yana kai idanunshi acikin kwalin, yaga kud'i ajere k'asan kwalin, sanadiyyar towel d'in dake
shimfid'e aciki da ya janye a gefe d'aya yayin d'auko jinjirin/jinjirar, da sauri dattijon ya maida
jinjirin/jinjirar acikin kwalin ya rufe, aiko ba shiri ya k'ara k'walla wani kukan, jiki yana rawa
dattijon ya kinkimi kwalin ya azashi agaban kekenshi sannan ya gyara mata zama ya fara lula
gudu, duk da k'arfin ruwan dake sauka, acikin k'warewa yaketa balbala gudun, hannunshi d'aya
rik'e da kwalin d'aya yana tuk'a keken, wanda har izuwa lokacin jinjirin/jinjirar bata daina kukan
ba.
Tofa dandano daga abunda ke cikin littafin:
*RUWA DA KANKARA*
Akafta
Nice dai taku har kullum :
D/Auta
مس. الله رلا نمح رلا ميح
*______________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The notion}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________________*
*ASSALAMU ALAIKUM DA FARKO INA MIKA SAKON GAISUWATA AGAREKU TAREDA
SAKON TAYA JUNA BARKA DA SALLAH ALLAH YA MAIMAITA MUNA*
*PAGE TWO*
********************
Jiki yana rawa dattijo yakai k'ofar dan madaidaicin gidanshi,bayan waige waige da yakeyi don
yana jin tsoron tuhumar 'yan unguwarsu, ba shiri ya sauke ajiyar zuciya, ya godewa Allah da
wannan ruwa da ake tayi kamar da bakin k'warya, wanda k'arar saukar ruwan ya hana ajiyo
sautin kukan jinjirin/jinjirar.
Abakin k'ofar gidan ya ja burki, Wanda a kallo d'aya zaka gano gidane irin na rufin asiri, amman
fa akwai babu a gidan, duba da yanda k'ofar shiga gidan ta kasance ta langa langa duk ya
hunhunde ya taso wanda idan bakayi a hankali ba yayin shiga gidan tsaf langa langar zai yage
maka kayan dake jikinka.
Da dubara ya sauko hannushi d'aya rik'e da kwalin da jinjirin/jinjirar yake ciki wanda duk ya jik'e
sharkaf, saboda ruwan da ake ta tsulawa har izuwa lokacin, yayinda shima jaririn/jaririyar har
izuwa lokacin bata daina kukan ba, amman ga dukkan alamu daga yanayin kukan da yake ko
take ta gaji sosai, saboda tasha kuka har muryarta ta dusashe.
ya samu ya jingine keken, sannan ya ciro kwalin dake gaban keken ya rungume da hanzari ya
fada gidan a sukwane kamar anjefo shi.
Kai tsaye ya wuce wani d'an madaidaicin d'aki, yayin da iya kulu dake baiwa akuyoyinta k'asari
ta bishi da kallo baki asake, tana mamakin kukan jaririn da tajiyo, haka kawai zuciyar ta tabuga
ba shiri, da sauri ta d'auraye hannunta ta nufi d'akin da taga ya fad'a, jin sautin kukan jaririn
muraran ya k'ara kid'imeta.
Ba shiri ta afka d'akin ko sallama babu domin ta ganewa idanunta abunda ke faruwa, da sauri
wata tsohuwa dake zaune tayi tagumi tareda wannan dattijon suka bita da kallo.
Ido abud'e iya kulu tace:
"Malam me nike shirin gani?"
Da sauri tsohuwar ta katseta da cewa:
"To tonanna maza kiyi sauri kiyi shela har mak'ota su ji, tunda ke ba'a sirri dake"
Jiki asanyaye iya kulu ta rakub'e gefe tareda tsurawa masu kallo in ta kalli malam ta kalli Dada
'yar tsohuwa, tanason taji ba'asin abunda ke shirin faruwa.
Dattijon nan mai suna malam wanda ga dukkan alamu, wannan tsohuwar itace mahaifiyarshi,
duba da yanda kamar su ta fito abayyane.
Ya saukar da ajiyar zuciya tareda cire tagumin da yayi, ya duk'a ya d'auko jinjirar dake cikin
kwalin ya rungume ajikinshi, tareda sauke ajiyar zuciya, jinjira kam saboda sanyin da ya ratsa
jikinta, da sauri ta ratsa kuka, ba shiri Dada ta karbeta hannunu malam ta janyo zane ta goyeta
tana jijjigata tana bubbuga bayanta, tun tana kukan har taji gumin goyo tayi bacci.
Iya kulu dai tana tsaye sai rabon idanu takeyi, Malam ya k'ara sauke ajiyar zuciya ya fara
yimasu bayanin yanda akayi ya tsinto ta.
Iya kulu ta rafka salati da k'arfi tace:
"Yanzu malam haka kawai kaga d'iya acikin daji an jefar kai kaje ka kwaso muna jaraba ka
kawomuna acikin gida, muna zaman zamanmu ka jaza muna hitina, yanzu in d'iyar aljanu ce
fa?, shikenan kasa mu shiga uku"
Dada saboda hararar da take yimata, kamar idanunta su fad'o, amman duk da hakanan sai da
iya kulu takai k'arshen maganarta, malam ya d'auke kallonshi daga kanta yace:
"Ko aljanar ce nayi niyyar taimako don Allah kuma bazan fasa ba, saboda bazan iya ganinta
acikin wannan halin ba, ace in kasa taimakon 'yar jinjirar Allah ba, bazan tab'a yafewa kaina ba,
idan har ban taimaketa ba, ki kwantar da hankalinki za'ayi cigiyar iyayenta, idan ansamesu sai
mu basu 'yarsu salun alun, don ga dukkan alamu wannan 'ya bata k'ananun mutane bace, duba
da yanayin shigarta, sannan da wad'annan mak'udan kud'in da na sameta tareda su"
Jiki yana rawa inna kulu ta zaro ido tace:
"Kud'i? Kud'i fa kace malam"
Malam ya tabbatar mata, sannan yace da ita ta bud'a kwalin ta gani, aiko jikinta yana b'ari ta
bud'a da sauri ta d'auki kwalin ta rungume baki har kunne tace:
"Bari inje in b'oye su malam tun kafin 'yan unguwa su gano munada wad'annan kud'ad'en a
gidanmu su samu abakin duniya"
Da hanzari Dada ta karb'e kwalin tace:
"Ta ina suka zamo kud'inmu?, waya baku?, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i, to gani
nan bari nan saboda bamuda hak'k'i da wad'annan kud'in har sai anje wurin mai unguwa
abunda duk yace shi za'a bi, saboda gudun abunda zaije ya dawo kafin agano iyayen yarinya
su karb'i 'yarsu"
Iya kulu ta b'ata fuska tace:
"Dada fa kowa ya samu ta kanshi yakeyi, yanzu saboda Allah sai ad'auki wad'annan
zundumayen kud'i akaiwa mai unguwa, haka kawai ya cenye su ya barmu sake da baki, kura da
shan bugu gardi da kwasar kud'i"
Dada ta rik'e baki tace:
"'yar kuluwa wallahi kiji tsoron Allah ki rage son kud'i, tun kafin su halako ki abanza"
Iya kulu ta fita fuu alamun ranta ya b'ace, don tasan k'arshen abun in ta biyewa Dada ranta ne
kawai zaiyita b'aci akan hakan, malam dai ya bita da kallo ya girgiza kai, saboda inda sabo ya
saba da ganin rikicin da yafi haka tsakanin Dada mahaifitarshi da Iya kulu matarshi.
Muje zuwa mutanena♀♀♀♀
Akafta
Taku ce har kullum
D/Auta
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: .مس الله رلا نمح رلا ميح
*______________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The notion}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________________*
*HAPPY EIDUL FIDHIR FOU YOU ALL MY FAN'S*
*PAGE THREE*
**********************
Malam ya maido da kallonshi akan dada yace:
"Idan an d'auke ruwa zamuje mu kaita wurin mai unguwa, domin abada sanarwa koda Allah
zaisa adace asamu iyayenta"
Dada tayi shiru na d'an wani lokaci, sannan ta sauke ajiyar zuciya tace:
"Ban tari numfashin ka ba, amman jikina yana bani wannan 'yar ba'a yankin nan namu take ba,
akwai lauje acikin nad'in da yayi jagora wajen ya rabata da mahaifiyarta, don ga dukkan alama
bawai gama garin yanda ake jefar da yara bace, akwai wata sark'ak'iyar da tayi tsanin wannan
bak'ar aika aikar, domin na tabbata duk inda iyayenta suke insha Allahu, suna cen acikin tashin
hankalin neman ta ruwa k'ok'o "
Malam ya nisa sannan yace:
"To ke Dada su nemeta akan mi? bayan sun nuna daman cen neman maraba sukeyi da ita,
idan akayi la'akari da kud'in da aka saka tare da ita, ana nufin an baiwa wanda ya tsinceta ladar
tsintuwa kenan?".
Malam ya k'are maganar acikin jin haushin, wad'anda sukayi wannan ta'adi, tareda janyo
kwalin kud'in ya fara fiddo dasu awaje, saiga wata farar takarda aninke, ta jik'e sharkaf da ruwa
tayi laushi, da sauri ya d'auko ta ya fara bud'a ta da dubara, don gudun kada ta yage, sannan
'ya harhad'a d'an guntun bokon shi na yak'i da jahilci, ya fara karanta abunda ta k'unsa
abayyane domin Dada taji yace:
"Assalamu Alaikum
Wannan jaririya ayau kwana hud'u da haifuwarta, diyar sunnah ce gaba da bayanta, ga kud'i
nan a kula da ita sosai arik'eta amana.
Bakin dada yana rawa tace:
"Maganar ka gaskiya ce Ayuba, don haka dole ne mu kaita wurin mai unguwa domin mu cire
kanmu a zargin 'yan wannan gari namu, sabo.... "
Kafin ta k'are maganar jaririyar ta fara mutsu mutsu tana son tayi kuka, da sauri Dada ta kwanto
ta daga goyon da tayi mata, aiko yarinya ta fara saka hannu abaki tana tsutsa tana bud'ar baki
sannan ta saka kuka, Dada ta kalli malam tace:
"Nono take nema kuma gashi ana wannan ruwan ina za'a je asiyo mata madara?".
Malam ya shafa goshin sa sannan ya tashi tsaye jikinshi yana rawa yace:
"Bari inje in gani in d'an liti yana shagon shi in siyo mata madara sai abata"
Dada tayi hanzarin fad'in:
"Wannan madara ba itace ake baiwa jarirai ba, ka jira zuwa gobe idan Allah ya kaimu, sai kaje
birni ka siyo mata, saboda madarar da ake baiwa jarirai daban take, na ganta ana baiwa yaran
gidan Alhaji murtala, don kasan uwar batada isashen nono"
Malam ya dawo ya zauna acikin damuwa yace:
"To yanzu Dada me zaa bata tasha ne?,tunda gashi tana jin yunwa?"
Dada ta yunk'ra ta tashi tsaye tana girgizata sannan tace:
"Akwai yanda za'ayi, kira man 'yar kuluwa, tazo ta tatso muna nonon Akuyarta da tayi sabuwar
haihuwa, sai abata, amman yanzu idan kace kaje birni a yanzu to yaushe zaka dawo ne?,
gashi yamma tayi sosai, gara dai abari gobe ido yana ganin ido sai kaje ka dawo a mutunce"
Malam ya zaro ido yace :
"Dada yanzu kina ganin ba wata matsala, a nonon akuyar idan an bata?"
Dada tayi murmushi tace:
"Da akwai matsala da tuni kai ne ka fara fuskantar ta, saboda kai ka fara sha kafin ita, gashi
kuma Har yanzu ba abunda ya sameka"
Malam yayi murmushi sannan yafita yana cewa:
"Yau tsohon tarihin ya tashi kenan?"
Dada tana dariya tace:
"To wa ya janyo tashin ba kai ba"
Malam ya fito yaje rumfar da akuyoyin iya kulu suke ad'aure, sannan yace da wani yaro wanda
bai wuce shekara takwas ba yace :
"Kai garzali je kira man iyarka"
Aiko saigata ta fito tana cin magani sai kumbure kumbure takeyi, malam ya kalleta yace:
"Dauko man kofi mai kyau ki kawo, zan tatso nonon akuya ne abaiwa yarinyar"
Iya kulu ta washe baki tace:
"Yawwa malam na nawa kakeso in tatso maka?"
Jikinta yana rawa ta d'auko kofin ta fara tatso nonon har saida yayi rabin kofin sannan ta rufe ta
mik'a masa baki har kunne tace:
"Kawo hamsim na raga maka don sani da sabo"
Malam ya karb'i kofin kota kanta bai bi ba ya koma d'akin dada ya kai mata, aiko tasa d'an
k'aramin cibi ta fara bata nonon, yarinya kam sai sha takeyi har sai da ta k'oshi sannan ta
b'ingire tana ta baccin ta hankali akwance sai maida numfashi takeyi acikin natsuwa, Dada ta
maida ta abaya ta goya, ta d'auko towel d'in da aka tsinto ta dashi ta lullub'eta, sannan ta janyo
zanenta da take yafawa ta yafa ta kalli malam tace:
To yanzu muje wurin mai unguwar tunda ansamu ruwan sun tsaya kafin su dawo"
Malam ya d'auko kwalin suka fito, iya kulu tana barandar ta atsaye taga fitowar su, da sauri ta
k'araso awurinsu tace:
"Yanzu da gaske kai kud'in zakuyi?, munaji muna kallo ayi muna sama da fad'i dasu?"
Dada ta galla mata harara sannan tace:
"A'a barmaki za'ayi ki tusa su agaba kiyi ta kallo tunda gadon gidan ku ne"
Iya kulu ta b'ata fuska ta kalli malam tace:
"Nidai bani Hamsin d'in kar ka mance"
Malam ya kalleta don baya buk'atar tada jijiyoyin wuya yace da ita:
"Kin biyoki"
Suka fita suka barta, sai ga garzali aguje ya biyosu yana fad'in:
" Baba ina zakuje?, ina zuwa"
Dada tace:
"Zo muje shalelena, inda dai wancen mai kan mangwaron ne da ko k'ofar takashi bazanje dashi
ba, halin uwarshi kaf shi ya kwashe"
Tofa ita iya kulun
Akafta
Taku ce har kullum
D/Auta
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: .مس الله رلا نمح رلا ميح
*______________________________*
*RUWA DA KANKARA⛈*
*NA HADIZA D/AUTA*
☀ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer's of The notion}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsap
p
*________________________________*
*BARKA DA SALLAH MY FAN'S ALLAH YA MAIMAITA MUNA*
*PAGE FOUR*
******************
Dada yar tsohuwa agaba malam da Garzali suna biye da ita suna tafe suna tattauna matsalar
har k'ofar gidan mai unguwa.
Ba tareda b'ata lokaci ba suka samu damar ganin shi, bayan sun k'are gaisawa ne, malam ya
fara koro jawabin abunda ke tafe dasu, gabaki d'aya d'akin kowa jikinshi yayi sanyi k'alau, da
jin wannan badak'alar da ta faru acikin garin nasu, mai unguwa yayi gyaran murya sannan yace:
"Ina jaririyar?"
Dada ta ta ciro yarinyar daga goyon da tayi mata, wanda sai alokacin duk wad'anda ke d'akin
suka gano da d'iyar abayanta, saboda baccinta takeyi sharkaf,har da su ajiyar zuciya alamun
taji dad'in goyon.
Malam ya karb'i d'iyar ya mik'awa mai unguwa, Mai unguwa ya k'ura mata kallo na tsawon
lokaci yana nazari, sai ga hawaye suna kwaranya akan fuskar shi, saboda ta bashi tausayi
sosai, kasancewar shi mutum mai tsananin tausayi, saboda yanda ya ganta fara jajir babu
d'igon baki ajikinta kyakkyawar yarinya son kowa k'in wanda ya rasa, don rashin imani irin na
mutanen mu, ace ad'auke ta akaita daji a yadda, tamkar an yaddo kashi, afakaice ya