Showing 27001 words to 30000 words out of 108932 words

Chapter 10 - DAN TAKARA COMPLETE BOOK Maman Nurul Huda .pdf

tunani da cewa"Ashnoor an Kai Miki ruwan bathroom "

Tace"ok kamar ko kin San jikina tayi tsami bugu na Sha kamar jaka wallahi Allah dai ya isar
min"

Inna tace"Amma ya dace yau kiyi using ruwan zafi ko zaifi"

Yatmusa fuska tayi tana kallon hanunta me ciwo ta girgiza Kai tace"bana sonta ne Inna nafi
Gane ruwan sanyi "

Inna zatayi magana ta katseta da cewa su wa'yanan Kuma daga Ina sun tsayaMana a gida ko
gulmar be kare bah ne...ta Kare da murgud'a Baki "

Dariya ce ta sub'uce masa Wai sune masu gulma yayi saurin gimtsewa ya Kau da Kai dan in
har ya cigaba da kallonsa toh wallahi zai iya rungumeta

Inna zatayi magana incharge ya kwad'a sallama me amo da yasa su kalli kofar

Da yike incharge ba mutum bane me natsuwa sai ya shigo da gudu da dai kamar zai zauna a
kafar mudi sai Kuma ya koma gefe ya saki kuka kamar wani d'an jinjiri Yana face majina Yana
cewa wayyo duniya Ina Zaki damu duniya budurwar Wawa yau Fahad ya tafi ya barmu

Kallon dukkan yaran gidan tayi saiko ta gan babu Fahad zuciyarta na bugawa ta kalli
incharge tace"me kake nufi?"

Tsam Aslim be ji dadin wanan abinda incharge yayi ba ya so sai Ashnur din tayi wanka ta ci
abinci ta huta sai a sanar dan shima gawar yake jira a kawo ayi Masa sallah sanan ya tafi tunda
Jamal yaje d'auko gawar

Kukan da ta gan hafsat keyi yasa ta karasawa ta Kama hijabinta tace"Ina Fahad?"

Sai kawai kuka me karfin ya kwacewa Rabi'a shaheeda na kuka tace"Ashnur kiyi hakuri
tsautsayi tayi sanadin Fahad "cikin kuka ta kwashe komai ta fad'a Mata

Incharge ya yage Baki ya saki wani irin kuka me ban haushi,yes me ban haushi domin
incharge is annoying shi ya kamata ya lallashesu amma yake rusgar kukan iya shege

Zaman dirshen yayi a kasa yayi tagumi yana sakin kuka cikin yararruka da shi kadai ke
fahimta

Duk Babu Wanda ya lura da Ashnur tayi baya sai Aslim da yike shikuma aikin nasa na
kallonta ne da sauri yayi hanzarin kamata

Cikin tashin hankali yayi ta Kiran sunanta Amma Ina ta sume

D'aukarta yayi gaba dayanta yayi gate duk yaran dake kuka Suka bi bayanshi

Mudi na kokarin Bude mota ya fisge key....abin mamaki da kanshi yayi driving Kuma ya
hana kowa binsa

Incharge yace"jama'a kuyi taimako shi ya mutu,itakuma za a gudu da ita anfa kashe kudi
Alan yariyar Nan shiyasa fatanta kamar glass

Motarsa na fita a layin na Jamal na shigowa da ambulance hakan yasa ma su din kin binsa
shiko mudi ya mutu da mamakin maigidan nasa dan tunda suke be tab'a ganin yayi driving ba

Private hospital ya kaita aka Bata taimakon gaggawa ganin Yana ta jiran likitoci su fito
Basu fito ba gashi an Kira sallah yasa shi tafiya massalaci Dan baya hada ibadansa da komai

Koda ta farfado da sunan Fahad ta farfado ta saki kuka tana Kiran sunansa

Duk inda likitocin Suka so calming dinta down gagara abin yayi saima fisge Karin ruwan tayi ta
fita da gudun ta bar asibitin

Dawowa yayi daga massalaci yana tafiya a natse saidai Yana shiga ciki ya samu labarin ai ta
gudu ranshi ya mugun b'aci ya kalli likitoncin kamar zaiyi magana sai Kuma ya juya ya fita but
su kansu sun tsargu dan ganin b'acin ransa karara

Komawa ophanage yayi Amma Bata dawo ba tare da mudi akayiwa Fahad sutura duk
gidan sai yayi shiru

Ba komai ke tab'a mutane ba inda harya koma ga mahallicinsa besan asalinsa ba

Da Aslim aka sallacesa ana kokarin fitar dashi zuwa makabarta ta shigo gidan Kamar
mahaukaciya Babu ko takalmi balle d'an kwali a kallo d'aya zaka fahimci she looks pale and sick

Da gudu ta Karasa ta rike makarar tana kuka tana Kiran sunanshi har shidewa take ,su
zainab sunyi iya kokarinsu na ganin sun riketa Amma Taki sauraransu

Incharge ya koma gefe yayi tagumi Dan duk gidan baya son ganin b'acin ranta dukda dai beda
abokin fad'a sai ita Amma yana Mata soyyaya ta daban domin ita din tana da Shiga Rai Kuma
kallon ya' yake Mata

A hankali Aslim ya Karasa inda take tana kuka ya d'ago Kanta

Kallota yake cikin ido itama ta dubeshi kamar wata wacce ta Saba dashi ta kalli gawar Fahad ta
sake kallonshi.....zata saki kuka ya girgiza Mata Kai tare da bude hanunshi ta fad'a ciki tana
sakin kuka me tsuma jiki

Wani Abu Aslim yaji daga kansa har tafin kafarsa ya lumshe idanunsa Yana buga
bayanta....bema lura da Yar jaridan da Suka shigo ba suna haskasu Wanda Abdul ya kirasu ba
tare da sanin kowa ba dan Yana son duniya tasan abinda Sunday ya aikata na zalunci yasan in
aka haska komai toh fah za a shigo lamarin har manya ngo
Flash din camera ne ya sashi janye jikinshi da sauri saida Kash Yan jarida sun karkata ne
akanshi kamar saboda shi aka kirasu,madadin su maida hankalinsu Kan gawar

Hotunan sunyi yawa har Saida mudi ya tsawarta da k'yar Suka tsagaita shi Kuma yaja
maigidansa barin gidan dukda be so wucewa ba Amma sanin fah Yan jarida kiris suke jira yasa
yaji maganan mudi

Alhamdullilah ankai Fahad makaucinsa na gaske Wanda is unfortunate he died without
knowing his root it so sad that he died that way but God knows best

Ranar gidan shiru kowa ya Kama Kansa da kyar da taimakon likitan da mudi ya Zo dashi
akayiwa Ashnoor da ta firgice allurar bacci Aiko tayi baccin

Washe gari sai Kuma ta tashi da wata damuwar ta rashinsu Jiddah kasancewar incharge na
gari tasan shi da kansa zai tashe yaran sallah asuba shiyasa Koda sukayi sallah kwantawa tayi
a gadonta tayi ta kallon silin ba komai ya firgita ba sai inda Fahad ya bar duniya ba tare da ya
San iyayensa wanan abin na Mata ciwo yau sai ta ji tafi ko wacce Rana kewar iyayenta,sake
juyawa tayi ta goge hawaye ta rintse Ido da kyar baccin wahala ya Kuma d'auketa

_______

Rai ba Dadi ya Isa gida ya tarar da Maryam a falo cikin doguwar Riga Kai ko Dan kwali t tana
waya da alamu siyayya tayi take sake tabbatarwa hajiya turai a turo mata kayan gobe

Wani haushine ya dibesa ganin ko kulasa batayi ba ta ci gaba da wayarta hankali kwance
shifa ya duba ya hango be gan abinda yayiwa Maryam to deserve this Ill treatment ba...Yana
kokarin ganin ya faranta Mata but ita ba ruwanta da farin cikinsa

Adeel ne ya sauko da gudu ya Haye jikinta tureshi tayi yaron zai Fadi ya taro yaron sai
ranshi ya Kuma b'ace sosai

Ya dubi yaron yace"jeki sama kayi Wasa

Yaron zaiyi magana ya katseshi da daka me tsawa yace nace ka jeki

Juyawa yayi ya bar falon shi Kuma ya kalli Maryam da ta Gama waya tana latse wayar

Yace"Maryam what are you good at??"

Tace"what do you mean"

Zama ya gyara yace"I mean you are not a good mother to your children...nima mijinki ba dadin
Zama dake Nike ji ba toh miye Kika sa a gaba that makes you neglect your duty....you are the
future first lady of the state inshallah but you are not sopporting me on this the critics are using
you to tanish my image you are not helping the needies.....something happen today da matar
politicians Suka tashi tsaye wajen taimako ke kina gida you don't even watch TV what sort of
woman are you in nace Zan Kara aure yanzu za a ce na zalunceki I made someone else first
lady"

Wani murmushi tayi na ko a jikinta she feels Kamar he is just threatening her with kishiya
ne ita daman Bata wani son first lady bazatayi stressing kanta ba gaskiya ta sufa da bautar
takakawa

Tace"nidai a rayuwa takura ce bana so nifa ban so ka nimi wanan governor din ba dan nasan
fad'a zamuyi tayi ne wallahi Kai kasan ni tun day one bana son stress bare in yi ta bautawa
talaka gaskiya zaifi ka nimi watan tayi first lady din as long as I will have peace is not my
problem gaskiya
Wanan maganar tata ya firgitashi how can a wife bazata so progress din mijinta
ba....kenan bata sonshi ne take wanan maganar

Shi ba mutum bane me son hayaniya mikewa yayi ya bar Mata falon ranshi ba Dadi

D'akin adeel ya tafi saida ya lallashesu ya leka leesat a Nata d'akin sanan ya tafi d'akinsa ya
zauna Bakin gado ya rike Kai


Muryarta yaji tace"toh damuwar ta menene toh ba gani ba ai sai in maka first ladyn in shine
matsalan bana son kana sanyawa kanka damuwa

Dariya yayi yace"and nasan you will be the best first lady in the history of Niger love"ya Kare
da Bude Mata hannu yace"Zo taho gareni "

Make kafada tayi sai yayi murmushi yace"toh Bari Ni in taso

Tashin ko yayi Yana karasawa ya gan wayam

Dafe kanshi yayi Dan is as if he is loosing it,he is mad abinda ke basa mamaki shifa ba yaro
bane why all this feelings

Murmushi yayi Jin b'acin ransa ya ragu ya shige toilet cike da tunanin ya take yanzu

Washe garin ya tashi ne da farin ciki saboda mafalkin ashnoor dinsa ya basa farin ciki

Yana dawowa daga sallah ya koma bacci

Hayaniya da yaji tana tashi ne ya sashi farkawa Jin muryar ummansa Rai bace ya sashi
mikewa ya saka jallabiyarsa ya sauko da sauri

Maryam ce zaune ta d'aure fuska rike da news paper itakuma umma na cewa kin kyauta
kenan a ce Yana dake ana Masa gorin matar aure, wallahi ki canza hali

Karasawa yayi da yike sun gaisa da umma tun dawowarsa sallah asuba yasa basu wani ja
gaisuwar ba

Ya dau paper headline din ya karanta Wanda ya nuna magana ce akansa domin cewa akayi
shin Aslim Yana da mata kokuwa dai tuzuru ne ko kuwa akwai abinda ake b'oyewa al'uma
domin be tab'a zancen matarsa ba bare Kuma ta fito ta taimaka
Shi kansa abin ya dakesa Amma ganin Maryam din Bata nuna damuwa ba sai ya kalli hajjah
nashi

Yace"kiyi hakuri ummata za a nimo mafita "

B'acin Rai ya hanata sake magana shi kansa yasan halinta maganar ya Bata Mata Rai ne
shiyasa ta saka Baki Amma Bata da wanan matsalar ita

Hajja na fita Bebi ta Kan Maryam din ba ya koma ciki


________

Yau dinma Haka Suka wuni ba hayaniya incharge din nema ke tunanin akan nimo su jiddah ga
Yan sanda sunce a Basu lokaci saukinsa d'aya Markus da Sunday suna tsare

Bayan sati d'aya,kamar inda dai rayuwar take duk inda ka Kai ga masoya a duniya in ka
mutu zasu cigaba da rayuwarsu ba Wanda zai kashe kansa dan baka Raye but inka samu na
kwarai memories dinka na brain dinsu Kuma zasu bika da addu'a toh hakan ne ta kasance ga
Fahad sai memory ya bar mush Wanda bazasu manta ba ko daina Masa addu'a
Su Ashnoor data Sha zazzabi sun hakura da mutuwar fahad Amma Basu manta ba....tun
wanan ranan Aslim be Zo gidan ba domin gudun media ya Lura kiris ake jira ayi rubutu a kansa
shiyasa yake taka tsantsan Amma tunaninta na azabtar dashi

Ashnoor Bata San ma yanayi ba ita ta manta wani Aslim ko da yike Bata masan da zamansa ba

Da safe incharge ya Tara su a reception inda yayi serious yasa duk Suka natsu suna kallonsa
domin sun San he is always not serious shiyasa duk sanda zai nuna serious suke natsuwa

Yace"nasan dukkanin mu musan gwamnati ta sake kawo notice kwana uku ya rage mana ko
Kuma gidan Nan ta koma hanun gwamnati

Ashnur mummy ta bar Miki gidan Nan ne dan ki cigaba daga inda ta tsaya ki ma inganta
rayuwar ya'yan Nan fiye da inda tayi buri ta Zama babban uwar marayu but unfornately sai ya
Zama bayan mutuwarta mun Gaza cika Mata wanan burin...bana manta kalmanta na karshe
tace"Kabir ka inganta rayuwar marayu ku cigaba da kula da wanan gidan mu samu Lada baki
daya,yanzu a Nan gidan yaushe rabon da a kawo maraya gidan Nan? Yaushe rabon da mu
d'auko maraya Koda an Kira mu abinci na gagarar mu...abin takaici mun kasa Basu ilimi da
lafiyar gasu kwance ba lafiya......abin takaici sanadin sakacin mu biyu sun b'ata Wanda hakan
be faru ba lokacin mummy

Kuka Ashnoor ta fashe dashi

Yace"yanzu a cikin kwana ukun Nan Ina son muyi Duk inda zamuyi mu cika muradin gwamnati
in akwai Wanda take da idea inda zamu dinga samun donations ta fad'a Mana"

Hafsat ta mike tace" a tunanina me zai hana mu shiga politics I have been thinking Kuma
na gano a rayuwa ba abinda ke kawo kudi yanzu sai politics shine me kawo kudi..in mukayi
la'akari da lokacin da mummy ke Raye itama siyasar take shiyasa tasan manya har ake taimaka
Mana bazamu zauna mu saki Baki ba tashi zamuyi kungiyoyin anguwa duk mu shiga har mazan
Ina son mu tsayawa Kan mu bawai muyi ta jira a kawo ba domin me kawowar sai ya d'ibi
rabonsa zai kawo Mana akwai tallofofi dayawa da akeyi a gari Kuma ana anfana Kuma nayi
bincike na gano anan saman mu akwai kungiyar mata na Yan siyasa luckily I was told tun
4years back mummy ce ta tsaya musu suka kafashi nayi magana da woman leader ta nuna min
suna bukatar me ilimi ya jagorancesu domin dukkaninsu Basu da zurfi a karatu Dan Haka ana
cutarsu suna niman Yar boko,,,,sai na shigar da Ashnoor Kuma sunyi buying idea din sosai
sunce zuwa 4 ta yamma ta shigo zasuyi magana da ita

Incharge yace"dadina dake kanki na ja wanan shawarar tayi "

Hafsat tace"kaima akwai na maza sai duk nu shiga dasu Fahad a had'a karfi da karfe nasan a
Sannu zamu cinma burinmu "

Jibrin yace"inshaallah"

Ashnoor bata so ba itafa siyasa Bata sonsa domin tana cikin masu yiwa mata Yan siyasa kallon
Yan iska yau gata zata Shiga

Dan farin cikindu da ganin ta cika wasiyar mummy zata amince kodan su samu rayuwa me
inganci

Da wanan taro ya watse da yamma bàyan tayi sallar la'asar ta saka wando cinoz da Riga
me totle neck duk jikinta a Sanyaya in ta tuna a baya ta tab'a gwada shiga siyasa Amma Bata ji
dadinshi ba saboda inda maza da sun haife kakanta suke niman su Kwana da ita that makes
her hate politics but yanzu she has no choice
Fitowa tayi dasu Rabi'a suka hango incharge a gindin bishiya karasawa sukayi suka

Maman Nur
*_D'an Takara_*

By maman nurool
HudahWanan littafin na kudine 300 ne for regular vip 600 via 2378022567
Aisha Mohammed
Zeinth bnk,for more information message me watsaap 09090112846

❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Promo!promo!!promo!!!
Buy 3 get 1bonamza

Yar gidan Tafeeda pure kayan Mata ta Zo muku da alkhairi
Ina kuke Mata Yan kwalisa Mata da suka amsar sunansu Mata ba muna Mata ba...macen
da tasan kanta Bata boranci...toh ki Zo mutuniyar taku Yar gidan Tafeeda me son ganinku cikin
farin ciki a gidanjen auren ku ta Zo muku da ingantancen maguguna Mata masu inganci
100%pure ba algus

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login