Showing 108001 words to 108932 words out of 108932 words
Chapter 37 - DAN TAKARA COMPLETE BOOK Maman Nurul Huda .pdf
deputy
Satinsu biyu taji garau Suka dawo Nigeria wani irin security aka karawa Villa Nan za ayi suna
watoh taron Mata but Aslim zaiyi taron suna maza a gidansa Kamar inda Abba shima Abba
zaiyi su ko suna Abuja sai bayan arbain
The fowwing akayi suna ban mamaki namiji babban sunan Abba aka sa Masa watoh
Kamal na biyu Kuma sunan kawu watoh kabiru...na ukun Wanda yafi Kama da Aslim da Adeel
sunan mudi aka same watoh Mahmud macen anyiwa marigayiya hajiya hajarah takwarah ana
Kiransu Babban da annur sai abnur sai Kuma Anwar sai Nuriya duk Rabia ta musu wanan Al
kunyar sunane na bugawa a jarida Aslim ya Zo Suka Sha anko aka tafi hall
Yaran Dole aka had'a da Basu Madara ana Gama suna da kwana uku kowa ya watse ummi
ta cigaba da gyaran yar'ta saf ta gyareta ciki da waje Daman Kuma ba wani budewa tayi ba Dan
aiki akayi Mata kwanansu hamsin suka dawo a ranar ko hajjah sai da tayi fad'a an bar Mata
jikoki suna tsala ihu sun kulle daki sosai tajj kunya ta d'au nuriya da Abba beson ganin laifinta
tace nasan kece Kika Tona mana asiri Dan babana baya Kuka Haka Kuma kawu da alhaji mudi
ma haka ke ba Dana a barki da nanny shikenan ki Hana mutane sakewa
Aslim yace"zamu Bata in kina cin zalin salihar y'ata
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya nigerlite na alfari da samun Aslim da deputy dinsa a matsayin
gwamna domin Yana shimfid'a ayyuka ba ruwansa ga matarshi ma tana tallafawa rayuwar Mata
A Haka Sukayi 8years dinsu da Abba saidai Abba ya tsayar dashi a Dan takarar shugaban
kasa dukda beso ba Haka ya amince kasancewar anji dadin mulki Abba Kuma ansan shi ya
tsayar da Aslim din Kuma wasu jihohi najin inda yayi transforming Niger sai ko aka zabesa sai
ya zamto Suna barin government house sukayi Villa direct ummi Kuma sun koma babban
gidansu hankali kwance Yan hud'u a gunsu suke tun yaye Dan bayansu Ashnoor tayi Yan biyu
duk maza yanzu ma tana da wani ciki su hafsat nada Yara biyu biyu wasu nada cikin na uku
Rabia itama tayi Yan biyu
Rayuwa tayi musu Dadi girma ya zo suna rayuwa kamar Yan uwa ga ophanage Yara suna
samun ingantaciyar illimi da Kuma abinci da lafiya kullum cikin kawo Yara Mara galihu ake Lada
na kaiwa hajarah da mummy a duk inda suke
Da dadewa an Yankewa su anty amarya hukuncin life in prisoment alhaji Bala kuwa da duk
wani abokan harkarsa an musu d'aurin Rai da rai
Shekara takwais cifff Aslim yayi ya sauka da mutunci domin yayi aiki kamar inda sirikinsa
Kuma ubangidansa yayi a lokacin yaran duk sunyi girma mudi yanzu shi ya fito takarar gwamna
Kuma Aslim na bashi goyon baya
Ba abinda ya rage musu domin dukkanin burikansu ya cika ba abinda suka rasa sai Suka
shimfid'a rayuwar me Dadi da Kuma kyautatawa juna yanzu Haka hafsat commioner ce mijin
Rabia Kuma yayi governor a lokacin da Aslim ke president a garin bauci Babu Wanda zaiyi
tunanin marayun da suka Sha fafatawa da rayuwa ne Suka Zama Haka sun inganta rayuwar
marayu da dama Maryam da Ashnoor sun Zama kawaye domin Maryam ta Kara aure itama dan
siyasa ta aura itace ta uku bisa kawance data kulla a Dole da Ashnoor sai ya zamto Ashnoor na
Bata shawarwari sai a lokacin ta yarda tayi wauta a baya sai gata itace star a gidan mijinta
sosai kawancensu tayi karfi ga yaranta baka sanin ba ashnoor ta haifesu ba har gun ummi suke
zuwa hutu sunyi girma Dan duk suna jamia yanzu ya'yan Ashnoor bakwai haihuwa
uku..Maryam ta sake haihuwa biyj da sabon mijinta hankalinta kwance Dan ba a had'a musu
gida ba Kuma tana gudun sake kuskure ta Kama mijinta gamm
Rayuwa ta cigaba da tafiya abubuwa da Dama sun faru me Dadi da marasa Dadi ciki harda
rasuwar Innah hajjah ko ta tsufa yanzu rigima take zubawa na tsufa...soyayyar Ashnoor kullum
sai girma take karawa a zuciyar Aslim
Yanzu ma duk sun Tura Yara hutu Abuja su adeel suna gun ummi little twins kuwa suna gun
Rabia a bauci autar Ashnoor little hajjah tana gun hafsat Dan sunfi shiri
Tsaye take tana feshe jikinta da humra a gaban madubi sai murmushi take ya shigo ya
rungumeta ta Baya murmushi ta sakar me tace"Kai baka tsufa ne"
.dariya yayi yace"na fiki yaranta in fad'a Miki
Ya Kare da kissing dinta yace"I love you Noor"
Tace"I love you too dan Takara "
Jan hancinta yayi tare da kaita gado
Sai'dai mu ce Allah ya Kara dankon kauna inda nayi kuskure Allah ya yafe min ayi amfani da
darasin dake ciki ayi wasi dana banza
Ina mugun yin ku masoya I love you all thanks for your love and sopport maman Nur na yinku
over
Mu hade a littafi na gaba January inshallah
Special group na sauke hakkinku kudinku yayi expire
Special thanks wa Wanda sukayi sponsoring Dina thank you very much for sopporting me
AMEENA 24 HOUR'S HAUSA NOVEL DOCUMENT for more information contact on +234
7014979567 What apps only