Showing 30001 words to 33000 words out of 108932 words

Chapter 11 - DAN TAKARA COMPLETE BOOK Maman Nurul Huda .pdf

ba iya magani Mata kadai ba tana da sabulai masu gyara fata tayi kyau da
sheki zaku samu Kaya kamar haka

1 gumba kwakwa da madara,wanan gumban in kika cishi toh a ranan sai kin rufewa oga Baki
domin kappp Yan unguwaku sai ya tada su daga bacci (lol)

2,original tsumi tab'ani kaji ruwa,wanan shi ake Kira fadama oga bashi da matsala ta fanni
ruwan dadi,Kuma tsumin Bata da wani d'aci ko bauri ko da biredi zaka ci abinki

3,original tabaje wanan ba a cewa komai domin bajewar da zakuyi ya wuci tunanin Mai hasashe

4sweetner powder wanan hakki ne me Kara dadi oga yaji zakwat

5 sweetner milk

6 dilka soap,in kikayi wanka da sabulun nan Zaki koma fresh skin d'inki tayi kyau

7 snow whitening soap wanan Kuma na Kara haske ne ki Zama lantarki a gidanki ko ba light

8.morroccan whitening soap shima zai saki kiyi sheki ga Karin haske

9*pure shea butter Mankadai me kyau ba algus ga Sanyi ta zo a siya a Shafawa kafafu saboda
kaushi Yana Hana kaushi

10 special yaji...Mai kyau da dadi,da sauransu,duk kayayyanki mu are 100%pure babu algus
zero side effect

Kuma duk mun sauke farashin muna end of the year bonanza buy 3 get 2 original karku Bari
wanan damar ta wuce ku ku tuntubi wanan number ta Yar gidan Tafida b b watoh Maman
mufeeda domin suyan naku
O90 32036606

Last free page
3️⃣5️⃣-3️⃣6️⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim

Tace"mun shirya"

Ya d'ago ya kalleta yace"a Hakan Zaki meeting din ai sai mutane su gudu ke hafsat je ciki
d'auko min powder ta shafa ko tayi daraja in kin je a tsiyace a tsiyacen zasu sallameki but if you
act big zasu natsu"

Cikin yanayi Dake nuna alaman Bata son surutu tace"please iam not in the mood allow us to
go"

Ganin zainab Taki zuwa ya daka Mata tsawa daya girgizata da gudu tayi ciki zuwa d'auko hodar

Tana dawowa ya bude powder ya d'au delop ya Fara Shafa mata a takaice Saida ya sa Mata
powder sanan suka bar gidan

Suna zuwa gidan woman leader din suka tarar da jama'a duk matane wanda babu budurwa
sai matan aure ne su Ashnoor ne Yan Mata da wata Rashida

Zama sukayi asnoor tayi ta bin mutane da kallo domin sun burgeta meeting din akwai displine
gashi komai well organize

Basu daman su gabatar da kansu akayi ta mike ta Fadi sunanta su zainab ma Haka aka tafi

Woman leader ta cigaba da bayanin akan an kawo musu president domin tayi karatu

Tafawa Sukyi Ashnoor na mamakin an Bata chairperson zainab Kuma sec

Babu b'ata lokaci ta tashi tayi godiya da jawabi daya shiga jikinsu akan ruko da
amana....tace"abinda ke rike kungiya shine gaskiya da amana,dayawar kungiyoyi sun mutu bisa
zalunci shugabanin saboda haddama da babakere da yayiwa shugabancin yawa a bada Abu
Dan bawa al'uma Amma su danne toh ita bazata yarda da wanan d'abi'a ba
Tafawa akayi ta amshi takkadar minute din meeting din ta bi activies din tana going through
Kuma taji dadin komai Domin a natse suke komai

Woman leader tace"chairperson gobe muna da meeting yau zamu je mu samu Wanda zaiyi
Mana hanya mu gan d'an Takarar Nan Aslim

Jinjina Kai tayi tace" da karfe nawa zamu??"

Woman leader da safe zamu inshallah da karfe 10

Tace"no problem Allah ya tashe mu"

Sun tautauna kafin a tashi taro sukayi gida


______

Ba karamin kewarta yayi ba kawai d'aurewa yake kasancewar yayi busy sosai da campaign
gefe d'aya Kuma maganar da Maryam tayi Masa na yaje ya nimi first lady ya tsaya Masa a Rai
Yana son ya nuna Mata shi dan halak ne Kuma namiji badai sakarya bace zai nuna Mata

Maryam ce zaune a falonta suna Hira da kanwarta

Nana tace"anty Maryam a gaskiya kin bani mamaki Allah ya baki miji Amma kike Wasa da
damarki first lady na jihar nan fah Zaki Zama ki tsaya Sanya bazaki tsaya Masa ya ci election ba
a gari bmmaganarku ake wasu na cewa kila baya kyautata Miki ne shiyasa Baki fito kin taimaka
Masa ba...wasu na cewa kila Yana da wata banzan haline maganganu dai iri iri na cin fuska
domin kowa yasan matar Yan siyasa suna taimaka ma mazansu please ki taimaka ki tashi tsaye
yaci wanan zaben mijinki kamilanle mutum ne...wallahi Yana sonki da badon Yana sonki ba
bazai jure lalacinki ba"

Yatmusa Baki tayi tace"nanah ni a rayuwata bana son stress me yake Nima a duniyar da Allah
be basa ba Yana da kudi,suna,asali da Kuma rufin asiri tun Kan ya shiga siyasa na fad'a me ba
ruwana ya nace yanzu house of reps be isheshi ba ya kakabo aiki har governor yaji dashi
wallahi,so kuke nayi ta yawo gari Dan yaci governor gashi in na dawo ba barina zaiyi ba da

jaraba da wanne zanji ku barni kawai anan

Baki sake nanah ke kallonta,Bata tab'a ganin wawiya irinta ba

Zatayi magana ta mike tace"kin gan mu kashe maganan Nan zani in . Huta ki gaida gida

Tana fadin Haka ta Haye sama nanah ta bita da kallo takaici a fusace ta mike Dan Bata Jin
dadin barinta a fili tace"Nan bada jumawa ba Zaki Sha mamaki ba ayiwa namiji Haka soon Zaki
Zama Yar kallo

Ta mike tana goyon danta sai gashi ya sauko cikin yadi me tsada anyi me d'inki zamani yayi
kyau ba karya hularsa tab'ani ka ji hadisi masu tsadar gaske ne kansa danshi irin hular da yake
son sawa kenan

Yace"au nanah kina Nan Ashe ya na gan ki ke kadai Ina take"

Tabe Baki tayi tace"ta sallameni,

Yaji b'acin Rai a maganarta be ce komai ba Dan shi mutum ne me matukar rike sirrin gidansa
Amma be ji Dadi inda tayi da Yar uwata ba

Ya saka hanun aljihu ya Ciro kudi da besan adadinsu 500note sabbi ya Bata yace"a gaida
gida"

Ta me godiya

Tana juyawa sukayi Karo da anty safiya Yar uwarsa ta shigo gaisawa sukayi a mutunce ta
amsa tana cewa badai tafiya ba

Nanah tace"wallahi uzurin gaggawa ne ya rikeni shiyasa

Anty safiya tace"toh a sauka lafiya ki kula

Nanah ta jinjina Kai

Murmushi ya sakarwa kanwar tasa itama ta maida me tace"ka gan manya kenan toh ya zirga
zirga

Yace"alhamdullilah lil ya yaran,

Side hug tayi me ta koma ta zauna tace"Ina hajiyar gidan Yar mulki"

Yasan gatse tayi masa yace"tana ciki "

Tace"ai sai ta fito mu gaisa ko,Bari in Kira servant din gidan Nan su kirata"

Talatu!Talatu!!talatu!!!

Da gudu talatu ta fito tace"au anty ne a gidan namu?"

Murmushi tayi tace"eh wallahi Yi min sallama da hajiyar ku"

Dan jimmm talatu tayi har anty safiya ta kalleta tace"ya dai??"

Cikin Sanyi tace"jiya ta Mana gargadi akan in tana baccin safe mu daina tashinta Wai is
important to her "

Anty safiya ta tafe hanun tana kallon Aslim da idanunsa ke waya kamar baya jinsu nan ko
Yana Jin komai....ta kuma tafe hanun tace"soko(Allah)wanan wani irin matsifa ce ta
bacci....Yaya nifa tunda Nike ban tab'a ganinta zaune ba sai a kwance Amma Kai kana ganinta
zaune kuwa?"
Daure fuska yayi dan be kasance cikin maza masu fidda sirrin gidansa ba ko Kuma aibata
matansu he feels ko menene tsakaninsu ne,Amma yasan halin safiya indai sauran kannesa ne
ba zasuyi magana ba Amma ita akwaita da bin didigi da iyayi

Tace"ohhhh ban tab'a gani ba sai ta koma yarensu watoh nupamci tayi ta maganganu
shidai bece komai ba

Tace"haura ki ce Mata na Zo"

Talatu batayi musu ba ta tafi saidai ko da taje ashar Maryam ta saki Mata ta rufeta da matsifa
harda barazanar zata koreta talatu ta saukok cikin tashin hankali tana rokar anty safiya tasa
Baki karta rasa aikinta

Anty safiya tace"abinda ban Gane ba anan kin sanar Mata nice na zo"

Tace"eh "

Anty safiya tace"Yi tafiyar ki "

Talatu ta wuce tana godiya

Bàyan ta wuce anty safiya ta maida dubanta ga Aslim tace"Yaya zuwa nayi muyi magana a
gaskiya abubuwa basa tafiya inda ya kamata ya kamata a ce kana da matar da zata tsaya Kan
harkokin ka I mean governor kake nema ba class rep ba

Sai yanzu ya d'ago ya kalleta ta tsuke fuska tace"ai dai gaskiya ne mutane gari nata magana
gaskiya ka Kara aure

Mikewa yayi ya dan duka yace"Ina yini hajjah"

Kumbura fuska tayi tace"ai gaskiya ne"

Wucewa yayi ta mike ta bishi tana sake jaddada me ya Kara aure

__________
Washe gari tsaf Suka shirya zuwa gun wanda zaiyi connecting dinsu da Aslim Yana ganin
tsaleliyar budurwa ya rude tare da musu alkawarin zasu Fara shiga ko wani program na Yan
siyasa ba b'acin lokaci yayi Mata party membership card tare da musu register da door to door
campaign
Members sunji Dadi sosai mussaman da yayi ta musu alkawarin tallafi sai sukayi
exchanging number

Gida ta koma cike da fargaba domin yau take sa ran zuwa government official domin yau ne
last date dinsu saidai tana zuwa ta gansu gindi bishiya hankali kwance da lafiyyayen abinci
Wanda da alamu take away ne

Incharge ba kunya godai godai ana yagan kaji

Yana ganinsu da zainab yace"ku Zo ku Zo ai mu Kam siyasa tayi Mana Rana da me muka
tsaya yine"

Kallonshi tayi tace"a Ina kuka samu wanan ,

Shi ko kulata beyi ba sai exther tace"wani ne ya kawo musu

Kallon shaheeda tayi,shaheedsh tace"wasu ne Suka kawo Mana

Zama tayi tace Ina namu,

Amsa tayi ta Fara ci zainab ma Zama tayi incharge ya kalli hafsat yace"wanan dan sanda dake
Mana sintiri a gidan Nan injin dai lafiya,Dan wallahi bazan bawa talaka ba sai me kudi nayi
wahala daku yanzu Dadi Nike ji,,ke Kuma Ashnoor ya kamata ki fidda miji fahhh na gaji da
ganinki Haka gauzakau"
Ashnoor tace"Ni nace maka zanyi sure ne?"

Yace ikon Allah toh in bakiyi aure ba me zakiyi?"

Tace"Kai dai ba ruwanka da rashin aurenah

Yace" ke Baki ganinki wata jibgegiya ki rufan asiri kiyi aure dan iskanci Baki son aure kike
karanta littafin hausa....kullum ke cikin Barbara kike toh waye zai barki ki zame mishi matsifa"

Tace"ai gomma ni wallahi a karatun littafi na Kare na fika zauwrawa nawa ka Nima ka
auresu ne?sai sun yarda da Kai ka ci musu kudi ka barsu in kana bacci har..... "
Ganin zasu Fara fad'a yasa innah cewa"ya Isa haka bata son jin komai

Hakan yasa sukayi shiru Daman ba Wanda ya tanka su Kar su zageshi Dan da alamu Ashnoor
din rainon incharge din ne halinsu d'aya

Bayan kwana biyu sosai Suka samu cigaba a harkar kungiyarsu suna zuwa ganin manya
sosai

_______

Shikuma Aslim yayi busy mussaman akan maganar su jiddah da yasa a nimo su a b'oye a b'oye
ana binciken case din ba tare da sanin alhaji Bala ba sai ya dauka an watsar da zancen ne
shima busy yayi sosai da sosai kammm

__________

Yau da wuri Suka tashi Dan zasu campaign,Yan kungiyarsu an Basu slot na mutane uku Wanda
zasu tarbar Dan Takarar shugaban kasa ta jam'iyar su Aslim kasancewar member din matar
aure ne su uku ne kawai Yan Mata yasa su ukun ne zasu ciki harda zainab sai wata Rashida

T-shirt aka Basu me d'auke da hoton Aslim da Dan takarar shugaban kasa watoh kamaludeen
sai pcap an rubuta Aslim 2022

Fitowa tayi daga wanka zindir kamar inda ta saba,hafsat dake kwance tana karatun
English book tace"kedai Baki da kunya

Ko kulata Batayi ba ta shafa cream sanan ta saka wando matsetse

Bra ta saka katin ta saka t-shirt din Saida tayi ta shafawa hoton presidential candidate din
sanan ta saka t-shirt din Kamar ko an gwada ta yayi Mata kyau

Tace"ai sai ki sauko ki gyara min gashi tunda hanun bashi da ranan kwancewa

Murmushi hafsat tayi ta diro ta d'au comb ta Fara gyara Mata gashinta

Tace"hafsa Baki mamaki har yanzu goverment officer Basu Zo ba shiru fah Kamar an d'auke
ruwa

Hafsat tace"ai nasan tunda kikayi tozali da Dan Takara matsalan mu ya Kare"

Tace"ban fahimta ba,


Hafsat tace"ai bazaki fahimta ba my sis"

Gyaran gashin da hafsat tayi Mata tace"tsam be Mata ba saidai ta dagoshi saman Kai

Hafsat ta kwance ta Kuma gyara

Fitowa sukayi suka tarar da incharge zaune Yana Shan iska

Zainab tace"mu zamu wuce "

Yace"ku dai anyi Yan kauye ko dan hodar Nan da ake muksikawa bazaku sa ba

Daure fuska Ashnoor tayi yace"yauwa Ashnoor da kinje ki saki Rai Dan nasan ki da mugun
zuciya Allah ya baki sa'a shugaban kasar yace" Yana sonki"

Tsaki tayi ta Kama hanun zainab suka tafi

Kamar inda ta kwana jiya tana shafa hoton dan takarar shugaban kasar jikin rigarta Haka tayi
a napep ta rasa me take ji akan hakan har suka Kai airport

Airport suka je tarba aspirant kamaludeen

Mutane ne makil a airport din kowa da uniform dinsa da pcap wasu Kuma da antamfar
jama'iya mata sunfi yawa

Ashnoor tana tsaye baki sake tana kallon jirgin da suka sauka domin yau airport yayi aiki

Daman tashi shine matsala sauka na zuwa da sauki

Jirgi ya d'auke mata hankali ji take kamar taje ta shiga

Shigowa yayi Yana tafiya cikin takunsa na maza masu ji da lokaci da Kuma naira

Ihuuuu da akayi ana sai Aslim yasa ta firgita taje juyawa dan in ta Zo irin wurin nan tsoro

yake bata Dan ba wuya Yan daba sunyi fad'a Kuma Bata so a illahta

Kafarta gurdewa tayi dutsen da yayi wadging ya gangara dole itama tabi dutsen tana
gangarawa Dan gun akwai dutu

Ta sadakar zata ji ciwo Kuma Dole tayi kasa

Ta rintse Ido kenan taji ta jikin mutum

Hanunshi na kugunta d'ayan na bayanta idonta a rintse shiko fuskarta yake kallo ta bude Ido
ta kalleshi hararanshi tayi ta Fara kokarin janye kanta Amma yaki Bata Daman Haka

Ta kalli hagu ta kalli dama ta gan dayawar mutane su suke kallo

Gyara Mata tsayuwa yayi cikin basarwa ya Kai kanshi wuyarta da stlye inda ba za a fahimceshi
ba

Kasa kasa yace"me kike anan?"

Fisgewa tayi tace"wanan ba business dinka bane D'an Takara"

Murmushi yayi Yana Kau da Kai ya hango mudi na fad'a da wani ya karasa gun yace"meke
faruwa "

Mudi yace"hoto yayi muku nace ya bada camera "

Gayen yace"Ni ba wani hoton da nayi muku wallahi muna hotone da friends Dina yaji karar
camera shine ya nace in bashi don't we have freedom again
. Aslim yace"kyalesa Mahmud"

Mudi be so ba he feel gayen Nan is upto something domin ya gan lokacin daya turo ashnoor ta
gangaro

Mudi yabi bayansa Yana cewa oga gayen Nan fa shiya turo anty akwai abinda yake so
Daman dai hoton yake so ya yada a ce akwai wani Abu a tsakaninku

Cikin ko in kula

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login