Showing 27001 words to 30000 words out of 103342 words
Chapter 10 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
Haleema tayi kukan kura ta kai mata chakuma (kamar zakaru na fada) suka fara bige-bige
da naushe-naushen juna su kuwa 'yan matan amaryar sun kai su shabiyar a dakin harda Asnart
a ciki amma ba wace tayi yunkurin rabawa. Haka dai suka ci gaba. Saukar bulalin da suka fara
ji kamar daga sama yasa suka dan saki juna ko wacce idan ta cike da kwalla. Jin an dakata da
dukan nasu kamar hadin baki suka kara cakumar juna. Wani Razana nan kara ne ta cika dakin
wanda suka rasa daga ina ya fito. "Kaaaaaa!". Nan fa suka saki juna suka durkushe ko wacce
ta rufe kunnuwan ta domin karar yayi yawa. Haka 'yan matan amarya ma gaba dayan su kowa
ya rufe kunne suna raraba ido. "Kuuuuu taaaashiiii tsayeee". Wata murya ce wacce in kaji ta kai
kanka sai ka firgice gata da karfi ga tsoratar wa. Haleema da Nasmat tsatsaye suka mike ko
wacce karkarwa take kamar su ruga su bar dakin. Haka yan matan amarya wasu suka shige
cikin (wardrobe) wasu suka haye kan gado suka rufe da blanket kowa dai da wajen da yake
nufa neman mafaka. Asmart kuwa kofa ta nufa da gudu nufin ta ta bude ta gudu. Tsawa aka
daka mata. "Keeee inaaaa zakijeee". A wajen ta fadi ta fara zubda hawaye "Ba ko ina".
Ta fada murya na karkarwa cike da tsoro. Tana waige-waige saman Silin ta kalla da taga kamar
wani baki baki ta wutsiyar ido. Ihuu! Ta kurma hade da Runtse idanu tasa hannaye ta rufe
kanta. Kan mace ne a yanke gashi buzu-buzu fuskarta babu kyan gani abun tsoro. Kan reto
yake a sama shine ke maganar. Su Nasmat koda suka daga kai suka kalle ta sai tsoran su ta
karu ba wacce ta sake yunkurin Motsi da kanta balle ta kalli sama. "Watooo kuuuu waiii
gabaaaa kuuuuukeee yiiii tsakaaaa niiiin kuuu koo?". Cikin sauri suka hada baki gurin cewa.
"A'ah". Cikin tsawq "Ku rufe min baki marar kirkin banza da akayi kuna 'yan uwan juna kuma ku
musulmain ne amma kuke gaba da junan ku. Ku rungumi juna daga yau kar in sake ji. Ko bayan
auren haleema ne". Cikin sauri suka Rungumi juna suna karkarwa. Hahahhahhhah! dariya
ce mai firgitar wa ta kaura de dakin. "Sauran kuma in sake samun labarin kuna gaba. Sannan
Kar wacce ta yarda ta fita daga dakin nan a cikin ku in dai ba lokacin kai amarya ne yayi ba
kuna jina?". Wannan karan har 'yan cikin Durowa (wardrobe) sai da suka amsa da karfi "To".
Bat! aljanar ta bace.
Tsakar gida gaba daya ya hautsine tun daga farkon layin zaka iya juyo masu ihu nayi masu
kuka nayi haka ma masu karatu addu'o'i nayi. Kofar ta kulle har yanzu kuma zanar su ake ba'a
dai na ba. Fatima kanta ta tsorata da gudu ta tashi rike da yar babyn ta nufi wani keji ta shige ta
boye dan gudun kar a banke ta. Kafin kace me Mata wajen biyar ne suka shiga keji dan ce tan
kansu. fatima kam matse ta akayi gam. Macen da ke bakin kofar Kunama ta gallawa cizo ihu ta
kwada ta fita a guje tana Soshe-soshe. Gida gaba daya ya hargitse kowa ta kansa yake yi.
Abincin ma tuni an zubda shi an tatake. Ga kofa ta kulle taki buduwa. 'Yar tsohuwar nan ce ta
bayana a sama kamar tsutsuwa fuska a murtuke. Wata tsawa ta daka wanda tasa gaba ki
dayan gidan ya kara hargitse wa. Ba abunda ya kara haddasa cin kosan gidan sai falo da shima
yaki buduwa.
Mata kam wasu ban daki suka shige harda masu shiga cikin tukunya dan tsoran bulalar.
"Kowa ya tsaya kar ya matsa a inda yake". Aljanar ce tayi magana cikin daga murya abunda ya
tsayar da guje-guje da ake faman yi kenan. "Wato ku marar imani ga abinci a gaban ku ba na
uwarki ba bana ubanki ba almajira tayi bara harda masu daga sauti gurin bada hakuri. Ke kuma
Waccen 'yar lukutar matar (Ta nuna Mama asiya da yatsa) kece muguwa har da bani abinci mai
gishi ri nayi magana kika ta so baki ga girma na ba a haka kamar zaki bige ni ko?". Mama
asiya jikinta ne ya hau bari murya na rawa "A'a dan Allah kiyi hakuri bansan ke aljana bace,
wallahi dama taimaka miki ne zanyi dan na.....". "Rufe min baki, (Aljanar ta daka mata tsawa)
Makaryaciyar banza, Ku kuma abunda yasa nayi muku wannan hukuncin dan ku kiyaye gaba
ne. Ni Aljana ce ba mutum ba. Da mutum ce da kun wulakanta banza kenan. Wai ace a cikin ku
kuna ganin wannan matar zata ci min mutunci ba mai bada hakuri ko dakatar da ita sai ma
dariya. Kunci sa'a ni musulmar aljanah ce ba muguwa ba amma da yau sai nayi muku tatas a
gidan nan duk da sai na farfasa muku jiki".
Shiru sukayi babu mai ko motsawin kirki kowa a tsora ce yake. "To abunda nake so da ku yanzu
shine Ga mai gidan nan da 'yan anguwa a kofar gida sunzo jin me ke faruwa, kar wacce ta
yarda ta bude baki ta fadi abunda ya faru, Duk wanda aka tambaya yace ba komai. Sannan
baku ba fita daga gidan nan sai bayan an kai amarya. Duk wacce tayi yunkurin fita kuwa zata
hadu da fishina". Tana gama fadar haka ta bace bat! Kofar gidan kuwa da su Alhaji ke faman
ballawa ta bude wayam. Shigowa sukayi suka ga gidan yayi kaca-kaca nan suka hau tambaya
me ya faru kowa sai dai yayi shiru da bakin sa. Masu dan kokari da rashin tsoro ne ma suke
cewa babu komai. Nan dai su Alhaji suka gaji da tambaya sukayi fushi suka bar gidan suka
koma harkokin su na shirye-shirye daurin aure.
Tsakar gidan tsitt! Kake ji babu mai wani kuzari duk sun jigata marar dauriya ma daga cikin su
kuka suke wasu kuma na Soshe-soshen inda suka sha bulala. Wata Yar siririyar mata ce ta
mike tana fada. "Wallahi ni sai na fita na tafi gida. Sai dai in kashe ni zata yi ta kashe kawai dan
zalunci daga zuwa wajen biki a tsare mu kamar wani gidan maza". Jakar ta ta dauka tasa
takalmi ta nufi kofa buzun-buzun da niyar wuce wa. Har ta kusan kai wa kofar gida, taji an kama
kafarta ta baya an wani warto....................................
*TASHIN HANKALI*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 35-36
NA. ✍KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
DEDICATED TO YOU:
☺ *SISTER NA HAFSAT IBRAHIM* ☺
NAGA DOGON COMMENT, NAJI DADIN ADDU'O'IN KI DA FATAN ALKHARIN DA KIKA MIN.
NA GODE KUMA KEMA ALLAH YA BAKI DUK ABUNDA KIKA ROKAR MIN. (Ana tare)
_All my fans thanks 4 You love and supported. Allah ya bar zumuncin. Ina ji da ku sosai da
bazar ku nake rawa._
_*WATO YAU INA TYPING INA DARIYA BAN TABA DARIYA GURIN TYPING KAMAR
NA YAU BA. UHMMM BA SAI NACE KOMAI BA KU KARANTA TUKUN. NAJI DAGA GARE KU
MY FRIENDS I LUV U OLL*_
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL
ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
----
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Jakar ta ta dauka tasa takalmi ta nufi kofa buzun-buzun da niyar wuce wa. Har ta kusan kai wa
kofar gida, taji an kama kafarta ta baya an wani warto.~
```»» Kafarta ta fadi Janta akayi kiiii! Tana ihu hade da wuntsile-wuntsile, Zaka ga ana janta
amma idanunka baza su gano maka mahalukin da ke jan kafar tata ba. Sai da aka kai ta can
gaban mutane sannan aka barta, Zaune ta tashi tana kuka tana wage-wage, jama'ar wajen
wanda basa da jumurin dariya har sun fara gagaba ta. Suka ji wata tsawa wacce tasa kowa yayi
tsi!. Gidan shiru kake ji ko fitsari ba wanda ya yarda ya tashi yara da manya, haka suma can
saman beni suna cikin daki sunyi tsi! Sunyi zugum suka ji ana Kwankasa kofar daki. Wasun su
tuni sun kankame juna kowa na ihu yana kiran momynsa. Shiru ba wanda ya sama damar bude
kofa hannun mace suka gani ya zuro ta jikin kaure ya murda key nan take ya bude. Nan fa
tsoran su ya karu ba abunda ya kara tsorata su sai ganin wata kyakyawr zankadediyar budurwa
fara ce tas!. Sanye da doguwar farar riga daga ka ganta kaga balarabiya. Wannan ya tabbatar
musu da ba mutun bace aljana ce domin basa da alaka da Larabawa. Hannun budurwar rike
take da Wani dan karamin akwati mai marika. Nufo su tayi tana murmushi. "Ina Amaryar ta so in
miki makeup". Ta fada lokacin da ta durkusa tana kokarin bude dan akwatin. Haleema da
Nasmat kamar ba abokan gaba ba domin haleema makal-kale Nasmat tayi Nasmat kuwa
kokarin raba ta da jikinta take domin karta jawo mata. Aljanar ta tsaya tana kallan su gaba
dayan 'yan matan amaryar kokarin turo haleema suke gaban aljana ita kuwa tana kara make
wa. Sakin baki aljanar tayi tana kallan su ganin haleemq bata da alamar tahowa. Tsawa ta yi
musu wanda ya rikita dukan su kanta ya fara futar da hayaki. Gaba daya sun firgice jikin halima
na rawa ta taho tana wani kwabe fuska jiki na rawa. Daga tayi tako daya sai ta tsaya ta wai
waya baya kamar ta ko ma. Aljanar ce ta wani harari kawayen amaryar da idanunta wanda sukq
fara komawa ja. Da sauri mutum uku suka turo haleema da karfi. Ta fada jikin Aljanar ta dan
rungume ta "Haba 'yar uwa ta ya kike tsoro na bafa cutar da ke zanyi ba". "To", din karfi da yaji
Haleema ta fada jiki na bari. Nan Aljanar ta zaunar da ita ta fara Gyara mata fuska. Wasu
kayan shafe-shafen ma kai baka taba ganinsu ba. Sai da ta gyara mata fuska ta fito fes! Tayi
kyau sosai, Aljanar ce ta juwa musu fuskan Haleema "Tayi kyau kuwa 'yan uwa". Da karfin su
kamar hadin baki ba wacce aka bari wajen cewa. "Eh tayi kyau". Duk tsoro suke ji. Sai da
Aljanar ta gama gyara ta sosai har gwagwaran sai da ta sake hada mata mai kyau. "Kuta shi
mu fita yau kowa sai yawa amaryar nan huduba. Cikin hanzari suka tashi saboda tsabar tsoro.
Gaba Aljanar
Amaryar na binta baya sai 'yan matan amarya da suka rufo musu baya. A tsakiyar falo Aljanar
ta zaunar da haleema ta ce su dakata ta kira wo muta nan. Ba garda ma duk suka ce "To". Fita
tayi waje mutane anyi Tsuru-tsuru kowa sai tunani yake, wannan gidan biki baiyi dadi ba.
"Sannun ku da hutawa uwayen amarya ko?, To ban ware kowa ba ku shigo ku mata hudu ba".
Kamar daga sama suka jiyo maganar da sauri suka waiga duk wanda ya kalle ta ya san Aljana
ce hakan yasa duk a tsorace suka tashi dan bin umarnin ta har rige-rigen shiga daki ake. Kuri
sukayi wa amaryar inda ita kuma Aljanar ta tashi sama tana kallan kowa. Jin sunyi shiru sun
saka amarya gaba kowa sai raraba idanu yake Ta daka musu tsawa. "Kuyi mata hudu ba nace
ba ku sata gaba ku kalla ba". Kafin kace me dakin ya cika da hayaniya kamar makaranta
haya-haya wani bai ma san abunda ke fitowa a bakin sa ba, kawai tsabar tsoro ne. Jin sun cika
mata kunne ta kara musu wata tsawar wacce tafi ta farkon kara da ban tsoro. Da yawa sun
zabura koya ya kama bakinsa yayi tsitt!. "Au! Dama haka ake huduba a garin ku?. Oya daya
bayan daya zakuyi" mama asiya ta nuna da doguwar yatsa. "Ke fara". Mama asiya na
karkarwa. "To, Amarya kina jina ki bi mijin ki sau da kafa kiyi masa ladabi da biyaya banda Rai
ni shi shugaba ne a gare ki. Banda daga mishi murya duk abunda ya saka ki kiyi". Shiru ce ta
biyo baya. "Au! Shikenan kin gama?". "Eh, A'ah" ta bada amsa. "To duk ke kina wa mijin ki
hakan?". "Eh ina mishi mana". Ta fada tana murmushin dole. "Shikenan zan bibiyi rayuwar ki
idan naga akasin haka to ke ma kin san sauran". Cewar Aljanar bata tsaya sauraran amsar
ba.cikin daga murya ta nuna Zuwaira Da yatsa ke da kike noke-Noke oya saura ke". Zuwaira a
firgice kamar ta saki fitsari ta fara karkarwa tsabar tsoro. "Too too niii dammmaa abuuu!!!...".
"Ke ki natsu kiyi mana magana sak!, In ba haka ba yanzu in mayar dake Mage". Hannu
zuwaira ta dora a kai. "Na shiga uku dan Allah kiyi hakuri karki mayar ni kyanwa.
Haleema ki tsaya kiyi tunani yanzu kin girma kin zama cikakar mace ki natsu ki zabi kawayen
kirki masu nuna miki hanyar tsira karki dauki masu Janki juwa hanyar halaka. Wannan wani
zama ni ne ya zo mana wanda shawarar kawaye ke bada babbar gudun muwa wajen kashe
aure. Ki tsaya ki natsu ki gane aure shine darajar 'ya mace ki zauna da mijin ki lafiya......". Taf!
Taf! Taf! Aljanar ta fara tafawa zuwaira da jin haka sau duk suka dau tafi..Aljanar tace kinyi
kokari. A haka aka tayi duk illahirin matan da suke dakin hatta kawayen amarya kowa sai da
ya to fa bakin sa ko baka da abun fada sai ka lalibo. In kaki kuwa sai dai kaga ta zuro hannuta
tun daga can sama ta wanke ka da mari. Haleema tun tana dauka har ta kai ga sai dai ta ce
"Eh", Kawai ko ta daga ma kai.
Wasa- wasa Dai abu har dare yayi anawa amarya nasiha. Dare nayi lokacin kuwa 'yan daukar
amarya suka zo ko ta kan Alhji yayi nasiha ba'a bi ba. aka dauka Kowa na zumudin aka basu
amaryar su.mata ko daya ba'a sama wacce ta tafi rakiyar amarya ba. Domin duk wacce ta fito
daga cikin gidan. Sai tace "Alhmdulilah". Ta ari ta kare ko mai wai-wayen gidan babu. Haka 'yan
matan amarya ma duk wacce ta fito sai ta ruga a guje ta nufi hanyar gidan su. Kamar dawa ki
haka mata suka cika layin da guje-guje. Ganin za'ayi abun kunya ba 'yan rakiyar amarya yasa
mama asiya da umma suka roki su Zuwaira da su taimaka a raka amarya. Su Fiddausi da su
nasmat sune a matsayin kawayen amarya su hudun su kuwa su zuwaira a matsayin manyan
mata. A tsorace suka kai amrya gidan ta suna kai ta kuwa kowa sauri yake ya fito. Ganin suna
shirin tafiya su kyale ta ita kadai gata itama a tsara ce take. Kuka ta saki ta biyo su tace wallahi
sai dai a koma tare baza su barta ita ka dai ba. Ganin da gaske take da kyar Fiddausi ta ce tayi
hakuri su zauna har angon ya zo. Nan ma da kyar ta yarda. Su mama asiya ansha bulala duk
jiki sai radadi. Ana tafiya a mota sai cewa direba (Driver) yayi sauri take. Kowa a tsora ce yake
sai da suka karasa gida tukun hankali ya dan kwanta. Su Juwaira a kujerun fali suka zube kowa
najin jiki hade da tsinewa gidan bikin. Nasmat da asmart Dakin su suka nufa domin suyi fitsari
dan ya matsi ko wacce a ciki. rige-rige suka fara da gudu wajen shiga dakin. Sai da aka . kusan
zuwa toilet din Nasmat ta tuno da macijin nan na dazu. Birki taja a gurin tayi baya. Taki fada wa
Asmart dan mugunta. Asmart na bude bayin ta kwala uban ihu! Ta juyo a guje. Nasmat na
ganin haka itama sai tace kafa me naci ban baki ba. Da gudu suka fita falo. Su mama asiya na
ganin su a wannan hali basu tsaya tambaya ba ko wacce ta tashi a guje aka nufi hanyar fita
a............................```
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 37-38
NA. ✍KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
DEDICATED TO YOU, BIEBOH habibalo. 2mro is ur bazday
happy birthday to You Ni ne na farko ♂.
*Note* BA SABODA *SURBAJO* KADAI AKAYI WANNAN BA, DAN HAKA BA KO
WANNE NOVEL DA AKAYI AMFANI DA WANNAN ZAI ZAMA NATA BA. ABUN KAWAI
RA'AYI NE KUKAN JAKI.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Taki fada wa Asmart dan mugunta. Asmart na bude bayin ta kwala uban ihu! Ta juyo a guje.
Nasmat na ganin haka itama sai tace kafa me naci ban baki ba. Da gudu suka fita falo. Su
mama asiya na ganin su a wannan hali basu tsaya tambaya ba ko wacce ta tashi a guje aka
nufi hanyar fita a.~
»» Su mama