Showing 45001 words to 48000 words out of 103342 words
Chapter 16 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
to muje". Fitowa sukayi suka nufi gidan yayan baban nata Safuratu tayi kamar yanda ta tsara
suka ci sa'a kuwa ya amince ya karbi Rafi'at. Safuratu kuwa ta fito ta koma gidan a matsayin
Rafy din...._
*________________*
_Su Asmart suna ganin an kusa zuwa makaranta sai suka kunce wa Fatima 'yar babyn daga
bayanta suka bata a hannu. Nasmat tace "Yauwa 'yar kanwata kinga daga yau 'yar ki zata iya
karatu. Yanzu muna shiga cikin makaranta ki Je ki kaiwa malam ita kice karatu za'a koya mata
kinji". Murmushi Fatima tayi wanda ya fito da gibinta ya kara bayyana kyawanta. "To aunty
Nasmat amma Dai A kusa dani zata ringa zama ko?". Asmart tace "Eh mana ai a ma kan
cinyar ki zata ringa yin karatun". Su nasmat Tare suka shiga makarantar. Suna shiga suka jiyo
sautin karatun malam din a Aji na 4. Ajin su kenan Asmart tace, "Yauwa Fatima kinji Malam can
a jinmu dan tsaya anan ki bari muna shiga muka zauna sai ki kai mai kinji?. "To". Fatima tace
nan ta sama waje ta dan zauna. Tana wasa da yarta. Su Asmart gaba suka yi suna dariya harda
rike ciki. Nasamt cikin dariya tace "Har naga ana yin sama da malam ana bugawa da kasa,
domin nasan sai ya daki Fatima ko yayi wa 'yar babyn wani abu". Asmart tace "wannan ai a
zaune take ke dai muyi sauri muje yanzu zaki sha kallo. Bayan sun shiga sun zauna ba'a dade
ba sai ga Fatima ta shigo ajin da sallama tana murmushi, hannunta rike da 'yar babyn. Malam
ya jawo wata aya yaje rabi kenan ya tsaya cik! Yana kallan Fatimar. Haka gaba dayan 'yan aji
zurawa Fatima ido suka yi. Wasu suna tausaya mata domin sunsab yau ta banu tunda ta shigo
wa da malam har cikin aji da 'yar tsana. Fatima kuwa tafiya ta fara ta nufi
ind.……………………………………………………_
*MUGAYE SUN HADA MATA BOMB. ALLAH YASA MA YA TASHI HAR DA SU.••••*
*DOMIN SAMUN FARKON LABARIN DAMA WASU LITTAFAN. SHIGA CIKI BLUE DIN NAN,
KA/KI YI LIKE NA PAGE MU, TUKUN KA/KI DUBA KASA.*
*Fb.me//Zamaniwritesassociation*
Ko nan
*Fb.me//Bigboyisahfans*
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 55-56
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
*WANGA PAGE SADAUKARWA NE GARE KI AUNTY NA. 'YAR MUTAN KATSINAWA.*
*FATIMA MAMAN ALI*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Haka gaba dayan 'yan aji zurawa Fatima ido suka yi. Wasu suna tausaya mata domin sunsab
yau ta banu tunda ta shigo wa da malam har cikin aji da 'yar tsana. Fatima kuwa tafiya ta fara ta
nufi ind.~
_»»Malamin Fatima ta nufa tana murmushi, sai da taje gabansa tukun ta tsayar da 'yar babyn
da kafafun ta ta kalli malam da ya murtuke ya bata Rai yake kallanta. "Ina kwana malam, dama
'yar babyn na kawo a ringa koya mata karatu ta iya Surutu karatu ne kawai bata iya ba. Kuma
so nake ta ringa yi". Kafa yasa yayi Ball da 'yar tsanar da karfi ta bigi jikin bango ta fada kasa
tum!. A fusace ya juya ya kalli 'yan aji "Ina nasmat da Asmart?". Gamu nan suka fada a tsure.
"Oya ku fito nan". Sumi-sumi suka tashi suka je gaban sa suka durkushe. "Kune manya ku
zan wa hukunci domin ita yarinya ce bata san komai ba. Me yasa kuka bar Fatima ta taho
makaranta da wannan Tsinannan abun?". Cikin hadin baki suka ce "Wallahi Malam ba tare
muka zo ba". Karya kuke tare da ita kuka zo mana". Rantse-Rantse suka hau yi wai su
alambaran ba tare suka zo da Fatima ba. Da malam yaga suna so su Bata mishi lokaci sai ya
juya ya kalli Fatima. "Ke Fatima fada min gaskiya in kuwa kika min karya sai na yanka ki. Tare
kuka zo ko A'a?". Su Nasmat ta kalla ko wacce a cikin su Uwar harara yake Tillo mata hade da
gatsina duk dan karta fada. "Eh Malam wallahi tare muka zo". A fusace ya juya gare su. "Da
Ni zakuyi wa karya ko Dan uban ku?. To ku jira hukunci kar wacce ta motsa daga nan". Hakuri
suka shiga bashi shi kuwa bai ko tsaya sauraren su ba. Ya fita waje bai jima ba ya dawo
hannunsa da wuka. 'Yar babyn ya dauka a yaje saitin gaban allo, "Kai ina so duk ku saurare ni,
daga yau duk wanda ya sake yin ganganci ya shigo cikin makarantar nan da 'yar tsana, Kai
bama a makaranta ba Ko a hanya na hadu da mutum da ita wallahi sai jikinsa ya gaya masa._
_Ya kalli su Nasmat tukun yaci gaba da cewa, "Sau nawa ina yi muku bayani ina fada muku
Mala'iku na rahama basa zama a wajen da wannan gunkin yake, mu kuwa so muke mu
kasance da su a ko da yaushe. Dan haka in kunje gida ku gaya wa babban ku na kwace 'yar
babyn Fatima". Yana gama fadar haka ya sa wuka ya yayanka 'yar tsanar har gida shida.
Tukun ya kwashe ta ya fitavda ita ya watsa saman soro. Dadi da farin ciki ne suka ziyarci su
Nasmat. "Shikenan malam ya jawo wa kansa yau zai gane kurensa". A cewar Asmart, Nasmat
tace "Ke ni fa tsoro nake ya zo ya dake mu wallahi". Ya daka din mana ai ba komai ni kam
bazan ji zafi ba ko ya bige ni domin kuwa nasan shima yau zai bugu kum...". Bata karashe
maganar ba Sai ga malam ya shigo hakan yasa ta garkame bakinta tashi shiru. Yana zuwa
kuwa ya dauki bulalar sa sai da yayi musu goma-goma da karfi tukun yace su koma mazaunin
su Fatima ma yace ta koma Ajin su. A cikin su Nasmat ba wacce tayi kuka Dan farin ciki ma
suke yi wai yau malam ya tabo Alkakai._
*_______________*
_Umar kuwa yana fitowa daga gidan ya nufi gidan iyayensa ya gaida su dauki mashin dinsa ya
fito bai zame a ko'ina ba sai wajen abokinsa mujaheed bayan ya parka mashin Ya sauka
fuskarsa dauke da murmushi yaje ya mika mashi hannu suka gaisa shima yana kallansa yana
'yar dariya. "Abokina ashe kana gari shiru kamar kayi tafiya baka ko lekowa mi gaisa kai da
kake da mashin". Umar sai da ya sama waje ya zauna tukun yace, "Haba mujaheed ya za'ayi
in ki zuwa gurin ka da gangan, Wallahi kawai ayyukan ne sai a slow". "Gaskiya ne abokina to
me ke Going?. Tun da naga fuskarka dauke da murmushi nasan a kwai labari". Hhhhhhhhh
Umar yayi Dariya, "Gaye shiyasa nake san zama dakai Wallahi, domin kai din akwai kwalwa.
Gashi dai har ka gano ni". "Eh mana bani nasha". "Kasan dai zance gizo baya wuce na koki,
Maganar shawarwarin da kake bani ne kai gaskiya abun nayi min dadi, Yanzu gidana sai
abunda nace ayi shi za'ayi Rafy gaba daya tsorona take ji. Yanzu fa idan na ajiye kara baban ta
ma ya ajiye mu kowa yace karta tsallaka to Wallahi a yanda take jin tsorona idan nace ta
tsallaka na baban ta sai ta tsallaka wallahi"._
_Dariya sosai Umar yayi yace "Gaskiya ne abokina ai nake gaya maka mace kullum kana bude
mata hakora kuna wasa da ita wallahi gaba daya raina ka zatayi ta ringa ma abubuwan da taga
dama, amma idan ya kasance tana jin tsoran ka, Haba Malam a nan zaka ji dadin rayuwa. kai ni
fa yanzu haka maganar nan da muke yi gidan nan haka na fito ban bata ko kwandala ba kuma
nace Dambun nama nake so da gasasar kaza. Dan tsabar tsoran da take min har russuna wa
take tana godiya tana cewa an gama mai gida. Yanzu nasan ko bata da kudi sai ta ara ko kuma
ta sayar da wani abun nata taje ta sayo min kafin in dawo". Duk maganar da yake Umar sakin
baki yayi kawai yana kallansa. Dajin yazo karshen zancen umar yace "Kanbuhu! Ashe ni
wannan yarinyar rainani tayi. Ni fa nake gaya maka Yanzu Naira Hamsin ne na bata nace ina
san shinkafa da miya amma shine ta tsaya tana min surutai wai kudin ko cefane bazai isa ba
balle Ma a auno shinkafa ashe kawai dukan da nake mata ne har yanzu bai sa tayi hankali ba".
Muhajeed ya kama baki "Kai! Kai! Lalai kuwa bata horu ba. A hakan ma nake gaya maka dan fa
baka sakar mata hakoran dariya ne amma da farat! Daya ma cewa zatayi bazata yi ba". Daga
jin haka Umar ya mike jikinsa har rawa yake, Muhajeed yace "Abokina naga ka mike ina
zaka?"._
_"Hmm, abokina kenan ai mikewar nan da kaga nayi ba inda zani gida kawai zan koma. Domin
a yanda ka bani labarin matarka take ma in dai ba haka Rafy ta ringa min ba zuciyata baza tayi
sanyi ba. Kuma wallahi in taki min biyayya yau sai na sumar da ita dan ubanta". Yana fadar
haka ya mikawa Muhajeed hannu sukayi masabaha ya hau mashin dinsa yayi dogon ja.
Mujahedeen na ganin Umar din yayi nisa sai ya kalle shi ya kashe da dariya yace "Banza kawai
gara ka hadu da mace mai hakuri sai azbatar da ita kake. Uban waye zai wa matarsa duk
abubuwan da nake fada maka in ba irin ku dolaye ba. Shege ni dama KA SAKE TA NA AURA".
Umar har ya kusa gida ya sama passenger nan ya tsaya ya dauke sa. Shine ya juya akalarsa i
zuwa cikin gari...._
*__________________*
_Mama Asiya, Zuwaira, Da Hauwa babu abunda suke yi in ba uwar hamma ba ta yunwa."mun
shiga uku wannan wanne irin bala'i ne to wai me ke faruwa a gidan nan ne. Dazun a gurin kari
Munzo mun iske babu Dan wake biredi a rube haka store ba komai. Gashi mun aika Mai gadi
sayan indomie babu yanzu mun aike shi sayan abinci Ya dawo nan ma babu. Gashi har Azahar
tayi gaskiya ni bazan iya jurewa zama da yunwa ba. Wallahi gidan mu zani ina dalili Azumin
dole". Kamar hadin baki suma sauran suka mike "Ai muma bamuga ta zama ba wallahi". Kowa
dakinta ta nufa ta daukko hijab kusan tare suka fito. Zuwaira ce a gaba ta nufi kofar fita a falo da
niyar bude wa. Tana bude wa ta zura kafa da niyar fita sai ji tayi an hankado ta baya, Haka tayi
baya ta fadi Tabar!, Dariya mama Asiya ta kyalkyala, "Saurin me kika haka harda faduwa?". Dan
mugunta Zuwaira taki fadawa Mama Asiya turo ta akayi. Ai kuwa Asiya na zura kafarta da niyar
fita. Da karfi aka hankado ta baya kamar buhun Hatsi haka tazo kasa Tum!. Badan Zuwaira ta
goce ba da a kanta zata fado. Zuwaira da Hauwa me zasuyi in banda dariya, Dariya harda rike
ciki Suna cikin Dariya suka ji kofar ta koma ta rufe da kanta da karfi. Hauwa taje tayi-tayi ta
bude amma ina..._
*_______________*
_A cikin islamiyya karatu ake amma su Nasmat hankalin su kan malam duk motsin da zaiyi
idansu na kanshi. Ko waje ya fita sai sun bishi wai su kawai sai sunga yanda zata kare shi da
Aljana. Bayan sun dawo aji an shigo littafan Fiqhu Malam ya kalle Nasmat "Ke Zanyi miki
tambaya a cikin littafin.Ahdhari (Ahalari) Minene farkon abunda yake waje ba ga Baligi?". Tsuru
Nasmat tayi tana zara idanu ta kalli Asmart cikin Rada "me zance?". "Oho alquran nima ban
sani ba". Malam ne ya daka mata tsawa "ke tambayar ki fa nake yi" A zabure tace "Malam
abunda ya kamata baligin ya sani shine Mahaifiyar sa da uwayen sa da kannansa da abokansa
da makwabtansa". Ta juya ta kalli Asmart "Dan Allah ko ba haka bane". "Haka ne mana"
Nasmat ta bata amsa a takai'ce. Gaba dayan ajin suka bushe da dariya. Malamin kansa yaso
yayi dariya kuma sai ya bata rai tsabar takai'ci bai kuma ce mata komai ba yace. "Maryam
minene farkon abunda ya wajaba baligi?". Mikewa tayi cikin zazakar muryar ta ta fara bayani._
*"Farkon abunda ya wajeba ga baligi ya Inganta imanin sa sannan yasan abunda zai Kyauta
farillan Ainihinsa kamar hukunce-hukuncen sallah Dana tsarki da azumi. Yana wajaba a gare
shi ya kiyaye hakokin ubangiji, Ya tsaga ga umarnin Allah da hanninsa, Ya tuba ga Allah (SWT),
Tun kafin yayi masa azaba".* _"Attakah biirrr". Malam ya fada gaba daya ajin aka kaurade da fadar "Allahu akbar!". Wajen
Nasmat ya zo ya mata bulala biyu, Hade da yi mata fada._
*______________*
_Tunda umar ya shiga gari bai dawo ba sai Wajen magariba. Yana fara'a amma da shigar sa
gidan ya wani daure Fuska. "Rafy! Rafy!" Kira ya fara kwallawa sai can tukun ta amsa ta fito
Tsaye kerere tayi masa. "Gani". "Ina abincin da na saki kiyi min?". "Banyi ba" ta bashi amsa a
hatsale Hannu ya daga da karfi Da niyar kaura mata Mari, Charaf! Ta rike
hannu........................._
*Tabb! Ramin mugunta su Nasmat a gina sa gajere*
♂ *Umar kuwai baisan Aljana bace, Pls aci gaba inji ya zasu kare*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 57-58
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
*DEDICATED TO MY JIGO ZAMANI WRITERS ASSOCIATION * IN san duk masoyan wagga
kungiya
✈❤ *JIRGIN ZAMANI* ❤✈
*Mun hau mun shillah Ahhha ha* *JIRGIN SO ZAYA TASHI KU KADAI MUKE JIRA 'YAN
GATA DUNIYAR SO KUNE DA SARAUTA.*
☺ _Ku na gano da ku nake san rayuwa._
_Naga kuna da tausayi kunyi a rayuwa._
_Zanen dutse hali kuce bashi goguwa._
___
_Tarbiya ko a harshe ashe akan gane mai itta littafan ku da kansu sun nuna._
_Nayi dare ku ban masauki gidan ku in kwana._ _Kuzo ku shigo har abinci zamu
muku kwadan rama_ ZAMANI WRITERS ASSOCIATION ❤ *WE LOVE U ALL ZAMANI
WRITERS FANS*
'YAN PHAREEDAH KHAMSHI NOVELS KUYI HAKURI WALLAHI PAGES DIN NE YAKE TSAYI
IDAN NAYI COMMENTED SAI SU NUNA YAYI NAUYI. TO KAFIN RABASHI BIYUN SAI WANI
UZURIN YA FIZGE NI. PLS
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kira ya fara kwallawa sai can tukun ta amsa ta fito Tsaye kerere tayi masa. "Gani". "Ina
abincin da na saki kiyi min?". "Banyi ba" ta bashi amsa a hatsale Hannu ya daga da karfi Da
niyar kaura mata Mari, Charaf! Ta rike hannu.~
_»»Gam ta rike hannun, Umar yaja-yaja ya kasa kwace hannunsa hakan yasa ya kara kai
dayan hannun ds karfi da niyar ya dake ta shima rike shi tayi. Yayi juyin duniyar nan ya ware iya
karfin sa domin ya kwaci hannun sa amma ya gaza hakan yasa ya bar kokarin kwatar hannun
ya wani bata Rai!, "Sakar min hannun" yana fadar haka ta sake shi, Tsayawa yayi a gurin yana
kare mata kallo har haske ta yayi da Torch ya tabbatar kums matar shi ce. A zuciya yake fadar
"Anya kuwa wannan Rafy ce?. Dama Rafy na da wannan karfin take bari ina jifgarta?". Juyawa
yayi ya kara kallan ta. "Bakiyi ba kika ce saboda me to kika ki yi?". A fada ce yake maganar
"Saboda baka bar min kudi isasu ba mana". "Au! Kuma dan na baki kudin da basu isa ba shine
ke baza ki cika ba kiyi yanda matan Kirki suke yi ko?". Da sauri ta bashi amsa "Sana'ar me
nake yi?, ko kuma kana bani kudinka ne?. Kare mata kallo yake sama da kasa Mamaki ne yake
karuwa a gare shi. Shi badan ma ya haskata kuma yaji muryar matar shi ce ba da sai yace ba
ita bace, Domin yanda yasan Matarshi a kwana nan mugun tsoranshi take yi. Yanzu tsoran
dokan ta yake tunda yaji Wani sabon karfi a gunta. Juyawa yayi ya nufi kofa da niyar fita. Ai
kuwa ta baya ta kama rigar shi ta jawo shi kamar wani karamin yaro "Ina zaka je baka bani
abinci ba?". "Sakar min riga malama masallaci zani". Murmushi tayi tukun tace, "To mai gida a
dawo lafiya. Amma maganar abincin dare fa?". Bata rai yayi "zan sayo na kawo". Yana kokarin
tafiya tace "To naji amma fa wallahi in ka dade sai na saka hijab na bika na lalubo duk inda
kake". Bai ko saurare ta ba ya kada kai yayi gaba Sai sake-sake yake a ranshi._
________________
_Fatima tunda taga an yanka mata 'Yar baby an jefa sama take kuka. Gaba daya yau batayi
karatu ba kuka kawai take malamin ajin ya dake ta amma take yin shiru Haka lalabo ma ba
wanda baiyi ba. Ita kuwa taki. Ba yanda ya iya dole ya korota waje. Waje ta samu ta sauna ba
abunda take sai kuka tana kallan saman soron da aka jefa mata 'yar baby. A haka har aka tashi
gaba daya makarantar,Fiddausi ce tazo da kyar taja ta