Showing 78001 words to 81000 words out of 103342 words

Chapter 27 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

Advertisement

kingboy   

08 Jul 2025

5161

Mukhtar din. Ta shiga gidan bata iske murja a tsakar gida
ba hakan yasa ta wuce daki. A zaune fake Mukhtar din ya iske Murja a bakin gado da gani ranta
a bace yake. Yana shigowa ta fara binshi da harara. Shima martani yake mayarwa. Takardar ya
fiddo daga aljihun shi ya mika mata. "Sauran saki biyun ne wannan ki hada da na farko na sake
ki saki da uku". Karbar takardar tayi ta lunkuma a baki ta tataune tukun ta bushe da dariya
daga bisani ta bata rai ta tashi cikin tsiwa da bala'i. "Kai Mukhtar To bari kaji karyarka tasha
karya wallahi.baka isa ba wannan sakin bai saku ba. Ni da kai mutu ka raba ba inda zanje".
Mukhtar yace "Ki tatara ya naki-ya naki kiyi gagawar barin gidan nan tun kafin jikin ki yayi
tsami". Yar dariya tayi irn ta raini wayyo hade da cewa, "Ayyiriri iyye nanaye. Kai baka ma ji
kunya ba da ka fadi haka?. Waye zai karya ni kai ko kuwa wani?. Na ma ga alamun dukan
kake so dan haka bari kaga". Juyawa tayi da sauri waje taje ta daukko tabarya ta nufi Mukhtar
tasha mamaki ganin ko motsi baiyi ba duk da kuwa a haukace ta taho da niyar buga mishi. Tana
kawo tabaryar yayi charf! Ya rike hade da wanka mata wani wawan mari wanda sai da ta gigice
bata ma san lokacin da ta saki tabaryar ba ta fadi kasa. Belt Mukhtar din ya daukko ya fara
bulalata tana ihu! Bai sasauta mata ba duk sai da ya farfasa mata jiki tana ihu! Da jan jiki ta fito
daga dakin kafin ta tashi ta fita a guje bata ko sake wai-wayo baya ba. Safuratu tace "Yar nema
gobe ma ki kara"................................................_


� Murja yar masifa yau anji jiki �


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy

��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 87-88


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*

_*THIS PAGE DEDICATED TO ELOQUENCE ASSOCIATION*_

ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION

� *MUSA MELODY, AUTA* �
_(Autan Eloquence)_

� *MUHIEVERT INDIA* �
_ єя ιи∂ια Er love)_

� *SHAMSIYYA SALIS* �
_(Autar Eloquence)_

� *BASIRA N. DABO* �
_(Basira)_


Kai dama duk members wanda ban sani ba. Ina muku Fatan alkhairi. Allah ya kara daukaka.

Allah ya kara muku basira da Hazaka.

*ZAMANAWA*
Nayi muku fatan alkhairi ❤❤



*A PAGEN DA YA GABATA CIKIN LITTAFIN ALJANAR FATIMMA*
~Belt Mukhtar din ya daukko ya fara bulalata tana ihu! Bai sasauta mata ba duk sai da ya
farfasa mata jiki tana ihu! Da jan jiki ta fito daga dakin kafin ta tashi ta fita a guje bata ko sake
wai-wayo baya ba. Safuratu tace "Yar nema gobe ma ki kara".~

_*S*afuratu ta bayyana gaban su Mukhtar dake zazaune a tsakar gida hannun ta rike da wasu
daurinan kudi. "Mukhtar na kori Murja kuma ina kyautata zatan bazata sake ma irin rashin
kunyar da take ma da ba". Daurin kudi ta mika wa Umar da Mukhtar kowa daya-daya hannun
har karkarwa yake wajen amsa. "Wannan kudin da kuke gani kar kuyi tunanin a banki na sato
ko kuma kudin wani. Aa kudina ne mallaki na inada dukiya mai yawa a boye a inda mun biye su
ne a wani waje wanda mu biyu kadai muka sani daga ni sai Ummana. Wacce yanzu ita bata
raye. Dubu dari-dari ne ku samu koja jari da shi domin neman na kanku. Sallama nake muku
sai kuma wani jikon. Umar karka yarda inji ko inga kawa matar ka wani abu makamancin wanda
kake mata a baya. Dan in na kama ka da hakan bazaka ji dadi ba. Idan ta tashe kuce mata ni
na tafi sai Allah ya sake hada mu". Tana kaiwa nan ta bace bat!. Godiya suka kamayi mata
kala-kala suna murna. Mukhtar tunowa yayi bata bashi makulin napep ba. Har ya fara rudewa
da tunanin ina zai ganta kuma sai ya hangi keys din a kan tabarma. Da safe da suka gayawa
Rafy bata ji dadi ba sosai. Har hawaye tayi tana fadar Safuratu bata kyauta mata ba. Ya zata tafi
basuyi bankwana ba. Umar kuwa lalashin ta yake yana cewa ai zata dawo tace......_
______________________

_Gidan shiru kake ji ba hayaniya hakan ya nuna cewa yara sun tafi makaranta kenan. Zaune
suke sun tattara hankulan su gaba li daya sun mikawa TV dake makale a bango. Mama Asiya
ce ta shigo itama ta sama waje ta zaune hade da cewa "Sannun ku". "Yauwa suka amsa
gabaki daya". Kafin Zuwaira tace "Aunty Asiya tun washe garin ranar da abun nan ya faru
nake tambayar ki me yasa kika yi duk wannan abubuwan harda goya babyn Fatima amma kinki
bamu labari". Asiya ta waiga hagun da dama tace "Yanzu zan fada muku amma abun sirrine
dan haka ku dawo nan". Tashi sukayi gaba daya suka koma kan sofa chair din suka hada kai
da ganin kasan abun munahinci ne. Mama asiya tayi kasa da murya ciki-ciki tace "Wato ni kaina
ina so in sanar daku abunda ke faruwa to sai dai duk lokacin da zan fada muku sai inga wannan
shegiyar Fatima. Sai inyi shiru. Shin ko kunsan wannan yar babyn ta hannunta Aljana ce?".
Kallan juna Zuwaira da Hauwa sukayi cikin rashin fahimta "Bamu gane ba aljana kamar yaya?".
Mama Asiya ta lumfasa tace "Kwarai Aljana nima ban zata ba sai ranar. Duk abubuan nan da
kukaga inayi to ita take saka ni. Har bullo min take a cikin wata irin suffa abun tsoro".
Kwashewa sukayi da dariya gaba dayan su harda ma rike ciki. Hauwa tana fadin "Wai Aljana sai
mu zauna ki mayar damu aljanu ai". Zuwaira tace "Heheheheh!, Kinji fa dama na gaya miki ai

motsa jini ne take ba komai ba. Shine zaki bige da ce mana wai Aljana ce..."._

_Asiya ce ta mike a fusace. "Dariyar ta iska haka kuma in kuma mutum bai bari ba Wallahi
yanzu zan narki kayan banza. Aa kaji mun yan rainin wayo. Ni dai na gaya muku kuyi hankali da
Fatima. Dan yanzu ba ita kadai bace ba kamar da bane da muke mata duk abunda muke so. To
yanzu in mutum ya zalunce ta akwai ma rama mata. Dan haka kuyi hankali. In kunne yaji to jiki
ya tsira". Tana fadar haka tayi gaba ta nufi dakin ta. "Ni dai cikin abubuwan da nake wa Fatima
ba abunda zan fasa sai ma karawa da zanyi Wallahi. Bari ma ta dawo inci ubanta sai muga
Aljana. Hhh kawata wai kinji mu za'a mayar Aljana". Zuwaira ce mai wannan maganar. Asiya
kam bata ko juyo ta kalle su ba ta shige abunta._



_Safuratu na dawowa gidan taga Fatima bata nan wannan ya tabbatar mata tana makaranta
ne. Jikin yar Babyn taje ta shiga. Lokacin tasowa Fatima Nasmat, Da Asmart tare suka shigo
gidan sai wasa suke a tsakanin haka ya tabbatar wa da Safuratu cewa Fatima bata cikin wani
damuwa._






_Kwana biyu nan Zuwaira da hauwa suna so su taba Fatima su gani kuma suna tsoro. Dan kar
suje abunda Asiya ta gaya musu gaskiya ne. Haka shima bangaren abba kullum cikin target
yake na yanda zai yiwa Fatima mugunta wacce zai huce haushin marin da mama Asiya tayi
mishi a kanta. Safuratu kuwa da taga kwana biyu hankalin Fatima kwance ranar nan tana
zaune sai ta tuno da su Kamal da matar sa Khadija hakan yasa tace bari ta nufi can taga irin
halin da ake ciki ga Muktar ma._
**************
_Zaune yake a tsakar gidan yana goge takalmin sa da alama fita zaiyi. Yarinyar ce cikin
uniform dinta na makaranta tazo ta durkusa ta gaishe shi ciki-ciki ya amsa mata rai a bace.
Kamar dai ta bari kuma sai tace "Baba bani naira hamsi". Cike da masifa da hargowa yace
"Kinci ubanki ke da hamsin din kaji marar kunya marar tunani yanzu duk halin babu da ake ciki
ke baki gani da zaki ce wani wai in baki Hamsun to ko kwandala bazan bayar da. Bace min da
gani ko in make ki". Hannu ya daga kamar zai bige ta. Da ganin haka ta tashi ta ruga a guje
tana kuka. Ummiey ce ta fito Cikin nuna bacin rai tace "Baban Hawwer gaskiya abun da kake
baka kyautawa ko kadan. ko dan kaga Aljanar nan bata dawo shiyasa ka fara wa yarinyar nan
rashin mutunci?". Muktar ya dago cikin fushi "Ummiey bana san haka fa. Miye ruwan ki in ma
Aljanar ta dawo nasha dai ba wajen ki zata zo ba ko?. Kin anta irin gatan da na nuna wa
wannan yarinyar ne?. Ai ko hawwer ban mata abunda na mata ba. Na mata ada lokacin da
nake tunanin Aljanar nan zata dawo. Yanzu kuwa tunda naga bazata dawo ba, Ai sai in sakata

in wala". Ummiey Tace "To ai ita wannan dukiyar ta ce. Sannan kuma kaga tunda Allah ya karbi
Hawwer bai sake bamu wata yar ba. Ya kamata mu rike maryam kamar Yar mu hawwer Domin
ni jinta nake sosai a raina kamar yar dana haifa". Mtsww.. Muktar yaja tsaki tare da sa takalman
sa yace "Naga alamar maganar kike so to ai ga bango nan sai kiyi da shi. Nasan bazai taba
gajiya ba. Ni dai na tafi". "A dawo lafiya". Shine abunda Ummiey ta fada bai ko amsa ba yayi
gaba. Safuratu da duk abunda ya faru a gabanta ya faru kai ta girgiza "Lalai wannan ashe
bakayi hankali ba. Zamu hadu da kai"._






_Gaba dayan unguwar an taru sai kallan masu jigilar watso kaya waje. Ba mai bada hakuri balle
a hana. Wani mutum mai sanye da Jacket ranshi a bace sai cewa yake "Yauwa ku fito da su
bana so inga ko cokalin su a gidan nan. Yau yau nake so su tashi su bar gidan nan". Can gefe
kamalu ne zaune yayi tagumi yayi wani tsamo-tsamo kamar bera ya fada ruwa an fiddo shi.
Gefan shi kuwa Khadija ce ba abunda take sai kuka tana zubar hawaye. Tana tunanin irin
wannan bakar rana wai yau sune ake watso musu kaya a kan titi. Kaddara kenan. Safuratu na
ganin haka ranta yayi mugun baci. Nan take ta Juye suffarta zuwa wani saurayi mai kwarjini.
Tsakiyar mutane ta ratsa ta fara bin masu fiddo kayan tana Fasfaska musu mari tana fadin "Ku
mayar da kayan nan kafin Rai ya baci". Ai kuwa basuyi gardama ba suka fara dibar kaya suna
mayarwa. Daga baya wannan mai sanye da jacket ya fara bala'i ya nufo Safuratu. Yana zuwa
ya duma mata kulli. Da juyowar ta ta shaki kwalarsa da hannu daya ta dage shi sama. Kafafun
shi na reto...................................................._



� *NAN FA AKE YINTA*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy

��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 88-90


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*

*WANNAN PAGEN NAKU NE MASOYAN LITTAFIN ALJANAR FATIMA A DUK INDA KUKE*

_A KULLUM FARIN CIKINA DA JIN DADI BAYA MISALTUWA IN NA TUNO DA KU
MASOYA NA. INA JIN DADIN _COMMENTS NAKU KUNA A RAINA._ COMMENTS NAKU
NADA MATUKAR MAHIMMAN CI A GARE NI. KO BA KOMAI ZAN KARA SAMUN KWARIN
GWIWA._

� _*DAN HAKA YAU DUK WANDA YA KARANTA BAITI COMMENT BA SAI NASA
SAFURATU TA SAKO MAI DUTSE A KAI*_ �

Luv u oll supporting ❤���
Har Unsupported din ma �


*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ai kuwa basuyi gardama ba suka fara dibar kaya suna mayarwa. Daga baya wannan mai
sanye da jacket ya fara bala'i ya nufo Safuratu. Yana zuwa ya duma mata kulli. Da juyowar ta ta
shaki kwalarsa da hannu daya ta dage shi sama. Kafafun shi na reto.~

_*H*arbe-harbe ya kamayi yana neman kubucewa amma ina rikon da tayi mai ba na wasa
bane. Wulla shi tayi ya fadi kasa. Da ganin haka wasu yan kallon suka fara sabe wa suna
guduwa. Masu fito da kaya kuwa suka kara azama wajen mayar da kayan cikin gida. Mutumin
da Safuratu ta koma shi ya nufi Mai jacket din nan a jiki. ya fara da cewa. "Lalai kai ka cika
marar imani da tausayi da har zaka sa a watso wa da mutane kayansu tsakiyar titi. Wannan

wane irin cin mutunci ne?. A kan kawai basu biya ka kudin hayaba ko mai?. Shin kai baka
tunanin in kai ne ake wa hakan baza kaji dadi ba". Mai jacket din ya mike yana kaka be jiki,
kafin mutumin ya karaso gare shi ya nuna shi da yatsa. Yace "ba dai ni kawa haka ba a bainar
jama'a. to ina tabbatar maka da cewa sai kayi nadamar abunda ka aika ta min. Domin alhaji
dayyabu sam! Bazai rabu da kai ba dole ya dau kwakwaran mataki a kanka". Da fadar haka ya
juya ya tafi. Safuratu kuwa tace, "Ina nan ba inda zani ina jiran alhji Dayyabun. Ko uban waye
yazo inaji dashi. Banza wanda bai san mutuncin dan adam ba". Mai jacket din wanda ake kira
da Dan ladi na alhaji Dayyabu. Ya juyo ya kalle Safuratu. "Alhaji kake zagi?. Lalai yau mai
kwatar ka a hannun alhaji sai Allah". Juwaya yayi ya hau mashij dinsa ya buga ya tafi a guje._





_Kamalu ne ya taso yana mishi godiya. Safuratu tace "Ba komai ai yi wa kai ne". Kamal fuskar
shi cike da damuwa yace "Mun gode da abunda kayi mana, Kuma naga abunda ya faru dan
haka nake rokon ka da ka bar gurin nan domin alh. Dayyabun nan da kaji ana fada hatsabibin
mutum ne. Yana da kudi sosai shi yasa yake takada duk wanda yaga dama. Yanzu nasan in
yazo ya tarar da kai a nan sai ta Allah. Dan Allah ka taimaka ka bar nan". Safuratu dake suffar
namiji tace "To wai wannan gidan nashi ne. Haya kuke a ciki ne?". Kamal ya kama hannun
mutumin suka shiga daga ciki dan ganin mutane na kallan su. Khadija ma tashi tayi ta bisu.
Bayan sun zauna kamal yace, " Wannan da kake gani. Gidana ne kwanakin baya wata kaddara
ta fado mana matata ta kamu da wata cuta. Asibiti suka nemi kudi million daya da rabi. Na hada
jarina gaba daya Dubu dari hudu ne.Na nemi taimako wajen masu kudi da dangi amma ban
samu ba. Gidan nan shi kadai ya rage min. Kuma Allah ya gani a kan matata ba abunda bazan
iya yi ba. Da har nayi tunanin sayar wa sai wani abokina ya bani shawara inje wajen Alh.
dayyanu yana bada aro amma ya shaida min cewa, Baya ba mutum aran kudi sai ya tabbatar
da mutum nada wata kaddarar da tafi abunda ya ara. Yace mutumin baya da mutunci idan kuka
sa lokaci baka kai mishi kudin sa ba. To zai zo ya sayi gidan ka ko mota ko wani abun yanda
yaga dama ya cika ma kudin ya kuma kore ka. Da naji haka da har nace ban amince ba. Koma
sai na canza shawara na amince. Naje na aro million daya da dubu dari na cika da kudin gurina
na kai asibiti akayi wa matata aiki. Bayan ta sama lafiya da wata daya alh. Ya fara aiko min dan
ladi shine wannan mai jacket din da ka gani._







_Hakan tasa ni dole na saiyar da gidan kuma shi Alh. Dayyabun shi na sayar wa.
Da sukaga watan ya shude ban kai musu kudin su ba shine Alh. Ya turo wasu matasa yan daba
suka dauke ni, Suka kai ni wajen sa. Nan yake gaya min tunda naki bayan kudin sa to ya saya

gidana. 1.5 million. Yanzu zai cika min dubu dari hudu. Da na nuna rashin amincewa sai yace
wa da yan daban nan suta duka na har sai na amince. Nan fa suka fara jifga ta da dai naga
suna neman hallakani sai nace na amince. Nan yayi dariya ya kawo dubu dari hudu ya bani.
Wannan abun da nake gaya ma ya faru shekaran jiya ne. Yace in tattara kayana in tashi daga
gidan in ba haka ba ya min korar kare. Nace to, jiya nayi neman duniya in sama gida ko na
hayane in biya shekara amma abun ya gagara. Shine fa yau tun safe ya turo dan ladi da
wannan matasan suka zo suka fara watso mana kaya waje. Mutumin ya ja dogon nunfashi
yace "Lalai wannan mutumi ya cik...". Hayaniyar da sukaji a kofar gida ce ta tsayar da mutumin
bai karashe magana ba. Kamal jiki na rawa yake cewa. "Wallahi Alh. Ne kaga sai da nace ma
ka gudu-ka-gudu amma kaki, to yanzu gashi nan ya debo yan daba". Mutumin hankalin shi
kwance yace "Abunda nake so da ku yanzu shine kuyi sauri ku shige daki kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login