Showing 3001 words to 6000 words out of 103342 words
Chapter 2 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
ko zaiji karar ya ragu amma ba alamar raguwar. Ga zafin ya fara cin
karfinsa ya fara magana cikin murya irin ta mai kuka ko gunguni. "Haba wllh fita zanyi bazan
tsaya zafi ya kashe ni a banza ba. Wallahi fati zanyi ko me zai faru ya faru. Juyawa yayi ya
dauki makulan shagon bai ko tsaya debe kudinsa ba. Ya fara yunkurin tsallakowa bayan ya
tsallako ne ya bi a hankali kamar munahiki ya leko shagon ta bangaren da yake jin karar.
Leka warsa keda wuya sai yaji kamar an dauke wuta dif! Karar ta dauke. Hakan ya bashi dama
da karfin gwiwa na fitowa da sauri ya garkame kofar shagon yanufi hanyar gida da gudu-gudu
sauri-sauri takun da yayi bai wuce 15 ba sai gani yayi wutacen nan gaba daya sun dauke dif!.
Al'amarin da tasa shi yayi tsaye cik kenan. Kamar walkiya haka yaga wani farin abu ya gifta ta
gaban shi duk da duhun amma yaga abun kamar mutun lokacin tsoro ya kara rufe shi, Suman
tsaye yayi a gurin tsabar tsorata da yayi.
Sanda aka shafe kusan mintuna 10 yana wajen a tsaye ya rufe idanu alamun haske ya gani
hakan yasa ya bude idanunsa ai kuwa sai yaga wutar ta dawo. Nan fa ya ranci ta kare ya zura a
guje kamar wanda zai tashi sama. Yana wuce wani mangwaro yajiyo dariya a saman shi, a
cikin gudun ya wai-wayo abunda ya gani ne yasa shi har saida yayi tuntube karfin gudun yasa
har sai da ya wuntsila yayi kungun bala. Yarinyar nan ya gani kamar dazun duj jini na fita a
jikinta kuma itace ta dage kai sama tana gagaba dariya marar dadin ji.
Bai kula da ko yaji ciwo ko baiji ba. Ya tashi ya ruga a guje yana ihu. Bai daina ganin yarinyar
na fito mishi a sifofi na ban tsoro ba har ya kawo gida. Da shigar sa gida ko tsayawa sa kubobin
kawai banka kofar yayi. Dake yasan kyauran mai jamlock ne.
Da gudu ya fada daki UⓂⓂEIY ZEEY
(matarsa) na kwance a kan gado tana barci. Yabi ta kanta ya tsallaka dayan gefan tuni ya ja
(blanket) bargo ya rufa duk zafin da ake fama da shi. Nauyin sa ne ya tayar da Ummiey daga
barci waigawa tayi dan ganin waye sai ganin shi tayi ya kudun-dune cikin bargo yana sauke
nunfashi day-day tayi mamaki mutumin da baya san zafi ko kadan kullum in yazo sai ya mayar
da fanka ta bangaransa amma yau gashi ya shiga bargo lalai ba lafiya ba.
"Mai gida-Mai gida baban HAWWER-baban HAWWER lafiya kuwa?" Haka ta dinga jero mishi
tagwayen sunaye hade da dadabarsa tana tambayarsa. Karkarwa taga duk jikinsa ya hau yi.
Domin shi kam abunda yake ji yayin da yake ji bashi take fada ba kuma ba muryarta yake ji ba.
Domin wata murya yake ji mai abun tsoro tana fadin "Mu...ktar...m..u..ktra" a slow muryar ke
tafiya.
Ummiey ganin karkarwar da yake tayi yawa ta dan daga murya "Baban Hawwer lafiya kuwa".
Yayin da shi kuma yaji an daga mishi tsawa da wata muryar mai razanarwa ance, "Kai muktar
magana fa nake maka". Firgigit ya tashi zaune. Maimakon yaga matarshi ummiey. Yariyar nan
ya gani kamar yanda take dazun dan yanzu ma tafi ban tsoro domin dogon gashin kanta
mai-makon ya zuba a bayanta sai mikewa yayi tsaye cir! Yayi wani irin fadi A sama. ('Kai duk
wanda yayi arba da wannan yarinya ala dole hantar cikinsa ta kada dan tsoro, In ma bai sume
ba')
Muktar kuka ya farayi yana ja da baya-baya yana bata hakuri a haka har ya surmuyo kasa daga
kan gado bai ko jira kuma ba yaci gaba da ja bayan. Ummiey na gannin mai gidan nata ya fado
daga kan gado yana kuma kallonta yana kuka ta tabbatar da ba'a hayyacinsa yake ba. Hakan
yasa ta matso daga kan gadon ta sakko a hankali take binshi tana tambaya. "Baban hawwer
wai me ke damunka ne?, ka min magana mana".
Yayin da shi kuwa yarinyar yake gani tana tunkaro shi hakan yasa ya kara sauri wajen jan
gindin da yake yana yin baya yana fadin. "Na shiga uku yau naga ta kaina, dan allah kiyi hakuri
karki kashe ni shin dan naki taimaka miki shikenan nayi laifin da za'a azftar dani har haka.
*DAGA TAIMAKO* dan allah karki kashe ni".
Ummiey da jin wannan kalamai na fita a bakin mijin nata sai tayi tsaye cik! Tana kallon shi cike
da mamaki tana cewa "Lalai baban hawwer yau ba lafiya kake ba. Yanzu ni din kake cewa zan
kashe ka ni?".
Yayin da shi kuma yake jin wani abun daban sabanin abunda take fada. Domin shi yarinyar
yaga ta tsaya tana gagaba dariya kafin ta fada da murya mai fitowa bibiyu. "Kai muktar ka sani
ka debo ruwan dafa kanka, a cikin kifayen da kake kamowa yau ka kamo ajali ka. Nan take
yaga wata wulshe-shiyar wuka ta bayyana a hannun yarinyar.
Ihu! Ya fara kurmawa yana fadin "Wallahi na tuba baran kara ba, dan allah ki yafe min duk
abunda kike so zan baki. Duk lokacin da kikaji yunwa ki dinga zuwa ina baki abinci ko da kuwa
zakiyi ci Goma ne a rana amma dan allah ki taimaka kiyi min rai karki kashe ni". Ummiey taga
abun da mijin nata yake ya fara yawa harda ihu nan ta fara tunanin ko ta leka ta kirawo
makwabcin su ne. Kuma sai dai tace bari ta karasa gare shi. Tahowa tayi cikin sauri ta mika
hannunta zata taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya zube kasa sumame. domin shi
yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi................
Mujee zuwa.
Autan writers nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 5-6
NA. KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
THIS PAGE DEDICATED TO YOU.
NASMAT
ASMART
MARYAM AMIN
SIS HAFSAT
MMN AFNANN
KHADIJA BABY
KHADIJA
KHAIRAT
MMN SADIQ
KAMALA MINNAH
Love is my everything. It’s everywhere. It’s in the messages you send me, it’s in the words you
say to me and it’s in your eyes when you look at me. Love is in my heart and in my thoughts.
Love is you and me. I love them ☺
FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----
*Karshen pagen baya...*
Tahowa tayi cikin sauri ta mika hannunta zata taba shi. Ihuu! Ya kurma mai razanar wa kafin ya
zube kasa sumame. domin shi yarinyar ya gani ta zo kanshi ta daga wuka zata caka mishi»
Ummiey gaba daya ta firgice kamar ta kurma ihu! Itama. Ganin mai gidan nan nata a kass
sumame. A rude tayi waje tana zubda hawaye. Da sauri taje ta bude randar kasar ta wacce
ruwan ciki yayi sanyi sosai kamar ansa kankara tasa moda ta kwalfo tayi cikin daki da gudu.
Tana zuwa batayi Wata-Wata ba ta kwaraya mishi gaba dayan ruwan da ta debo. Firgi-git ya
mike zaune yana nishi yana yan waige-waige kamar wanda yake neman wani abu dayan
hannun sa kuma goge fuskarsa yake domin ruwanda Ummiey ta kwaraya mishi. Ganin baiga
abun da yake zatan gani ba yayi saurin mikewa ya nufi kofar daki a guje ya rufe ya sakala
kubobi biyu yana fadin.
"Ummiey wllh kashe ni zatayi taimaka ki kama a jawo wardrobe din nan a kara rufe dakin".
Ummiey kam tsaye tayi ta saki baki tana kallansa yanda duk yabi ya rikice yake abu kamar
mahaukaci. "Baban hawwer wai lafiyar ka kalau kuwa? Ya kake wasu irin abubuwa ne haka
wanda ban taba ganin kayi kwatan-kwacin kalar su ba?".
Tsawa ya daka mata kamar yanda ya saba dama baya jiya mata dadi, ba dan Ummiey mai
hakuri ce ba da tuni ta bar masa gidansa to amma sai akaci sa'a irin matan nan ne masu hakuri
tayo gadon gidansu dake babban ta shine limamin masalacin juma'ar anguwar kuma baban
malammi ne masani. Itama kuma haka tayi sauka har biyu. Zabura tayi tsawar da ya daka mata. "Nace miki kizo ki kama wannan wardrobe din mu kai mu
rufe kofar aljana ce in ta sake shigowa kashe ni zatayi".
Ummiey sai yanzu ta gane mijin nata gamo yayi. "Baban hawwer wacce aljana kuma"?. "Oh!
My god ya fada. Tunda bazaki kama min ba baza ki taimakawa mijinki ba so kike ta halaka ni to
bari in kai ni ai zan iya". Kiki-kiki ya jawo wardrobe har kofar dakin ya danne kofar. Danne wa
keda wuya yaji an fara girgiza kofar dakin da gudu ya haye gado ya lulube. Ummiey ce tazo
kanshi ta fara tofa mishi addu'o'i har allah ya taimaka barci yayi gaba da shi.
Tunda asuba da ya tashi yaci gaba da zabur-zaburansa. Ummie na tofa mishi addu'a amma
taga abun yafi karfita hakan yasa ta dauki waya ta kira babanta tana kuka ta gaya mishi duk
abunda ya faru. Yace gashi nan zuwa. Mukhtar ba abunda yake sai surutai duk bayan yan
mintuna kuma sai ya dinga tsorata yana boyewa yana fadar "gata nan gata nan".! Ummiey ita
kanta ta shiga rudani.
Ba'afi mintuna 20 ba malam hamza ya karaso gidan koda Mukhtar ya jiyo sallamarsa da gudu
ya fito ya makal-kale malam yana surutai saida malam yayi da gaske tukun ya raba jiknsa da na
Mukhtar lokacin ya fara tofa mishi adduo'i tukun ya samu haukan da yake ya dan lafa malam
yasa shi ya zauna a tabarma da ummie ta shimfida. Bayan sun zauna ne malam ya fara karanta
ayyatul kursiyyu tare da sauran ayoyi masu karfi. Ba'a dade da fara karatun ba sai ganin
wannan yarinyar ta bayyana cikin kayan da Khadija ta saka mata. A gaban malam ta zauna
hade da musu sallama. Muktar har zai ruga malam ya zaunar da shi. Hatta ummie ta tsorata
domin ganin abun tayi kamar a mafarki.
Malam ya kalle ta yace "baiwar allah me wannan mutumin ya miki an bani labarin irin azabtar da
shi da kika yi jiya". Muryar ta ba dadin ji tace, "ka tambaye shi malam shi ai yasan abunda yayi".
Malam baiyi gardama ba ya juya ga muktar ya tambaye shi me ya mata. "A tsorace yac malam
wallahi ba abunda nayi mata shagona taje tana nuna alamun yunwa take ji a rana ta farko na
kore ta a rana ta biyu kuma ganin ta takura min na dake ta".
"Karya kake muna fiki azzalumi macuci, Ko daya ba dan wannan ne na shiga rayuwarka ba.
Wannan ma nayi ne dan in tabbatar da rashin mutuncin ka da mutane ke fada sai naji kai da
bakin ka ma fada kake. Malam muktar Shin har ka manta abunda kayi shekara daya da rabi
baya da suka wuce?. Yarinyar ta fada cikin tsiwa tana hararen shi. Nan fa kwakwalwarshi ta
shiga juya mai yana kokarin tuno wani abu. Ganin ya shiga dogon tunani ta sake daga mishi
wani tsawan wanda ita kanta ummie ta firgita kamar ta fada daki taji. "Kaaaai! Mugu wato har
ka manta yaron da ka kashe ka rabasu da dukiyarsu ka raba yaya da kanwa. a fadama ko?".
Dummm! Gaban muktar ya fadi jin ta tado zancen da a tunaninsa ba wanda ya san shi daga
allah sai shi sai kuma wannan yarinyar. (What!) "Yaron da ya kashe?". Ummiey da malam ne
suka fadi hakan a tare.
Bugun kirjinsa ne ya tsananta nan take jikinsa ya fara bari. Motsowa ya farayi gaban Yarinyar
yana fadar "Dama ke aljana ce ban sani ba. Don allah ki rufa min asiri karki tona wannan sirrin
duk abunda kike so zanyi amma ki taimake ni karki tona wannan sirrin...." Tsawar da ta daka
mishi ce ta tsayar da shi nan take ta wani bata rai fuska ba wal-wala. "Bani bace domin dani ce
da bazaka kwana ba a ranar. Ka basu labarin abunda ka aikata wa wannan yarinyar da kanka,
in kuwa ba haka ba yanzu ka gayawa yan garin ku". Ta karashe maganar cikin daga murya.
Nan take tsoran Mukhtar ya karu. "To-to bari in fada amma dan allah karki min komai".
Malam da diyarsa ba abunda suke sai kallo da sauraren ikon allah. Ummiey tunani take shin
wannan wane BOYAYYEN AL'AMARI ne? Wanda bata sani ba game da mijinta. Ita dai bayan
mugun halin sa da kowa yasan da shi bata kuma san da wani ba. Mukhtar ganin kowa yayi
shiru shi ake saurare ga kuma wannan aljanar da ke mishi wani mugun kallo mai tsoratarwa. Ya
shiga basu labari..............................
Mujee zuwa.
Autan writers nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 7-8
NA. KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
THIS PAGE IN DEDICATED TO YOU.
_*QUEEN HAUWANCY AUTAR MARUBUTA*_
_I love you to the moon and back, and you know that. I will never let you down, even if you
make me mad, you can always ask me advice, I will never leave you._
```Duk illahirin yan writers na zamani suna ji dake yar auta kaman yanda nake ji dake
nima ☺ kina sakamu nishadi Da Littafin ki ILLAR BASHI Ni ban taba
jin irin wannan gidan sunan ba hatta ruwan da za'a sha ma bashi mai ruwan ya zuba Dan
akuya za'a yanka shima bashi Abincin gidan bashi Kayan miya bashi Ba beauty bama
koni bazan tsaya ba ♂
Kina wuta ina binki da fetur yar kanwata Allah dai ya kara basira```
FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----
*KARSHEN PAGEN BAYA*
Mukhtar ganin kowa yayi shiru shi ake saurare ga kuma wannan aljanar da ke mishi wani
mugun kallo mai tsoratarwa. Ya shiga basu labari
» Ya fara da cewa Kimanin Shekara daya da rabi baya da suka wuce, lokacin ba'a fi watani uku
da yin aure na da Ummiey ba. Lokaci ne da na shiga mawuyacin hali talauci ya min dankar
kazar uwar ba'u. Ba komai ne ya kara zafin talaucin ba sai matsalar da muka samu da ogan
gare jin mu na bar aiki.
Nayi buga-buga na shiga na fita domin in sama abun yi amma abun yaci tura, duk inda na nema
aiki bana samun aiki. Ranar wata laraba da naga abinci sakawa a baki ma yana shirin gagarar
mu, Hakan tasa na shirya na dauki gatari na nufi jeji domin nayo itace na sayar. Hanya nabi ina
tafe ina tunanin yanda rayuwa duniya tamin tutsun jaki lokaci guda na surmiyo kasa. Rashin sa'a na ya tsananta ni kam bansa yama zanyi ba domin ko faskaran ban iya ba.
Naje ratsa wata fadama naji kamar maganar mutane a cikin wani dan lungu ina lekawa naga
wasu yara ne guda biyu na dan tsorata da ganinsu kamar yanda suma suka frigita yarinyar ta
kankame na mijin wanda ya kasance yayanta ne. Bayan yan tambayoyi da nayi musu suka bani
amsa nan na dan saki jiki da su. Nace su fito muka sama waje muka zauna na tambaye su me
sukeyi a nan. Namijin ne ya kalli kanwarsa hade da cewa "Rasheda in fada mishi". maganar da
Yarinya tayi ya tabbatar min da yarinya ce mai wayo da hankali. "Eh yaya na ganshi da manyan
kaya ina ganin kamar mutumin kirki ne ba irin su kawu mansur ba". Yaron yace "To amma
amana". Na kallesa nace mishi "yaro ka yarda dani bazan cuce ku ba. Saidai ma in taimaka
muku".
Kwarai a lokacin da tausayin su a raina.
Yaron ya shiga bani labari kamar haka: Yace mahaifinsa mai kudi ne duk anguwar babu
kamarsa a dukiya. Yana da kani daya yaya daya. kawu abba da kuma kawu Mansur kawo abba
shine karame wato kanin babanmu saurayi ne kuma shi mutum ne mai tausayi sabanin kawu
mansur wato yayan su shida baban mu. Kawu abba yana san mu sosai mun shaku da shi
sosai dake a gidan mu yake da zama shima yana da dakinsa daban. Hatta makaranta shi yake
kai mu.
Ranar wata alhamishi ce mun dawo daga school muka tarar da abban mu da kuma kawu
mansur suna rikici cacar baki abun kamar a buga. bamu san me ya hada su ba, koda ganin mu
sai kawu mansur ya nufo hanyar fita wajen har ya kusan zuwa kofa ya juyo yayi bakaken
maganganu hade da barazana wa baban mu, sannan ya fice baban mu yaji haushi sosai