Showing 63001 words to 66000 words out of 103342 words

Chapter 22 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5029

shegiyar fatim...". Da sauri ta rike bakin ta. Kafin sunan ya idasa fitowa. Dum!
Taji dundu a bayanta mai karfi. "Munahika ke wato kamai na gidan nan 'yar marainiyar nan kike
likawa ko. To naji ita ta bata gun ni kuwa nace kije ki sa soso da sabulu ki wanke bango ya fita
tas!". "Aummm! Ummmm Naaaan Ceee baaaaaa". Inina ta fara yi cike da tsoro domin jin uban
aikin da aka tsiro mata da shi, wanda ita kuwa bata saba da wahala ba. Nan dai take tsaye, Ita
kuwa matar ta bace. Mama Asiya ta kalli bangon wajen da dan tsayi ji tayi kamar ta fashe da
kuka. Cikin gunguni take cewa. "Shikenana yanzu rayuwa ta zama abunda ta zama. Duk
wanda yaga ya fika karfi sai yata zaluntar ka. Wallahi ni dai Allah,..". Cikin wata tsawa wacce
sai da cikinta ya kada. "Keeee wai ba aiki na saka ki ba". Haba da jin hka mama Asiya ta rude.
Da sauri ta nufi wajen tanki ta dauko boki ta cika da ruwa Dubi-tubi ta kai wajen bangon ta ajiye.
Mai gadi na daga can kan dan benchin sa kallanta kawai yake, sai tunani yake ya gaza gano
me hajiya take shirin yi. Mama Asiya taje ta daukko wani dan karamin bokitin tasa soso ta kada
kumfa duk abunda take 'yar babyn Fatima na goye a bayanta. Sosan ta dora jikin bango ta fara
gogawa. Da ganin haka mai gadi ya taso da gudu yana fadin "Dakata Dakata hajiya". Tsaye ta
mike tana aika mishi wani mugun kallo ranta a bace. Yana kara sowa gurin ta ya fara cewa
"Hajiya me kike shirin yi ne haka. Naga dai alhaji yana iyakar kokarin shi kusan ko wacce
shekara sai ya canza fenti yanzu haka ma nasan yana gaf! Da canza wa..." Hannu ta daga
mishi hade da dan juya mai fuska "Ya isa haka dan Allah. Ko na kira ka ne da zaka zo ka fara
jawo min wannan doguwar aya da tun kafin ka shigo gidan nan na harda ce ta harar yafi a
kirga?. Malam koma kayi aikin dake ganka ka barni inyi nawa aikin"._




_Da gama fadar haka ta tsoma soso cikin kunfa ta juya taci gaba da dirzar bango. "Haba Hajiya
ko dai aikin nan ya zama dole ne ai bake ya kamata kiyi shi ba tunda gamu a gida". Bata ko
kula shi ba sai kara da dagewa tayi ta kara kaimi wajen dirzar bangon ta. Mai gadi ya kara
matsawa domin ya karba yaci gaba. Wani wawan duka ta kawo mishi, Takuwa ci sa'a ta same
shi a wuya gata dama abu ga mai jiki. Mai gadi ihu ya kwada ya nufi cikin falo yana fadar
"Jama'a gida ku fito Hajiya ta haukace". Juyawa tayi ta harare shi tace, "Shege dan sa ido
kadan nayi ma. Allah yasa ka kuma dawowa". Hauwa Zuwaira da sauran 'yan kananan yara
duk akayo waje. Su hauwa abun Dariya ya basu amma sai suka basar. "Haba Aunty Asiya miye
kike haka kamar wacce ta sama tabuwa, Bango ne fa kike wanke wa". Zuwaira ce ta fadi haka
lokacin da ta dan matsa kusa da Asiya din. Mama Asiya ko kallanta batayi ba kawai aikin ta
take tukuru. Hauwa'u ta kalli Zuwaira tace "Gaske fa aunty wannan ba abun kyale wa bane kina
ganin fa abun yaci gaba, Mama Asiya hauka kawai take a yi gagawar nemo malami y duba
ta...". Sakin aikin da take tayi ta nufo Hauwa tana nun mata yatsa. "Inji uban yace na haukace,
Gaya min ko kuma ke ma yanzu inyi kasa- kasa dake a nan wajen". Da sauri Hauwa ta boye
bayan Zuwaira tana bada hakuri. "To kiji in gaya miki lafiya ta garas ki ganni nan nama fiki

lafiya". Ta fadi hakan ne cikin daga murya a fada ce. Harda dakar kirji ya bada sauti Dum! Dum!
Ta wani gir-gir za. Zata kwaso wani zancen ta hangi wannan Aljanar a bayan mai gadi ta nufo
su. Haba ai kuwa da sauri ta koma bakin aiki ta. Wayar Zuwaira ce tayi ringing da sauri ta
daga. Abba ne dan Mama Asiya. Wato yayan Ameera. "Hello Mama Zuwaira wai lafiya na kira
wayan maman mu shiru, Dama ina so in sheda mata ne gani nan a hanya". Zuwaira tace, "Eh
to da sauki dai, Dan Allah kayi sauri ka karaso". Da fadar haka ta tsinke wayar suka ci gaba da
bawa Asiya baki wai tayi hakuri ta daina Wankin bango. Amma ko sauraren su taki tayi._


^^^^^^^↓


_Ameera, Nasmat, da Asmart ne suke tafe jere an taso daga islamiyya. Asmart tace, "Yau bari
muje gida nayi target din duk abunda Fatima zatayi mu. Domin wallahi ba sasauci". Nasmat
tace,"Ke dai bari, Ni ai nafiki tsara mugunta a kanta. Kinga yau sai nasa ta share duk gidan nan.
Sai nasa tayi mopping din duk dakunan gida. Kaya na ma wajen sat 5 sunyi shegen datti amma
sai nasaka ta wanke su, Ke in gaya miki da ace ni nake girki da ita zansa tayi duk wani abu da
nasan zai ban wuya". Dariya asmart ta kwasa, Kafin tace "Gaskiya ke babbar muguwa ce".
Ameera da jinsu kawai take sai yanzu tayi magana cikin murya kasa-kasa. "Kai Wallahi ku
kiyayi kanku da wannan yarinyar in kuwa ba haka ba zaku ci uban ku". Cikin hadin baki suka ce
"Saboda me". Ameera kamar munafuka ta kalli gabas ta kalli yamma, Cikin rada tace "To in
gaya muku wannan 'yar babyn ta Fatima Aljana ce". Da jin haka suka bushe da Dariya. "Ashe
ke sai yanzu kika sani?, ai mu in gaya miki ni da Asmart tuni mun san da wanna. Kawai
mugunta ne ya hana mu fada muku". Suka kara sakin wata Dariyar. Asmart tace, "Yanzu ma
kuma abunda yasa muke tsara wannan muguntar saboda mun san an yanka 'yar babyn ne jiya
a Islamiyya". Ameera tace "Aiho! Kuma fa haka ne, ai kuwq nima sai na dauki fansar abunda
Aljanar tayi min ranar nan". Lokacin suka karaso kofar gida. Da sallamar su suka hangi su
Zuwaira sai fama da Mama Asiya suke suna so su hanata wankin bang amma taki hanuwa.
Suna karasawa wajen Zuwaira tace wa nasmat tayi sauri taje gidan ASP ta kirawo shi tace
Aljanu sun kama Mama asia. Da sauri Nasmat ta juya data falla a guje bata tsaya ko'ina ba sai
gidan ASP. Da shigar ta kuwa batayi birki ba har cikin falo. Ta shiga Ko sallama babu, A falo ta
iske su shida matar sa. Cikin shigar kayan aiki da alama ma tafiya zaiyi. Nasmat daga ka ganta
kaga wacce take a rude. "ASP, ASP kayo taimako gida mu ba lafiya". Asp cik da san yaji me ke
faruwa yace, "Ke miye akayi". Cikin rudu Nasmat kamar uwar da danta zai mutu take fadar
"Dan Allah ka taimaka ASP kataho mu tafi, Banda bata lokaci karsu kashe ta". Lokacin da
Nasmat ta kama hannunsa tana kokarin jawo shi. Shi kuwa sai kara tatogewa yake. Da sauri
cikin hadin baki shida matar sa suka ce "Suwa?"._




_A zabure tace, "Aljanune suka cika gidan mu gasu can kuma sun kama mama Asiya sai
azabtar da ita suke". Da fadar haka ASP yasha jinin jikinsa. Domin shi in dai harka ta aljanu ce

akwai shi da tsoro ta bangare. "Aljanu?". Ya kuma maimata maganar. Nasmat tace
"Eh".Zainab matarsa tace, "Mai gida ya naga kamar ka tsorata ne daga yin maganar Aljanu".
Wani shegen yak'e yayi, "Haba ke kuwa Zainab kamar baki sanni ba. Kamar ni jarumin jarumai
A duk cikin 'yan sanda kice wani ina tsoro?. Haba dai". Ya kalli Nasmat yace, "Ke yi gaba gani
na tahowa bari inje in daukko bindiga ta. Kunsan ko Aljanu tsoran bindiga suke yi". Asp ne ya
fadi haka yayin da ya juya ya nufi dakin sa. Zuciyar sa sai sake-sake yake yanda zai tsere.
Domin Allah ya gani bazai iya zuwa gidan ba. "To ni in naje ma uban me zan musu?". Ya
tambayi kansa. "Kai alquran bazan je ba". Ya fada cikin dan daga murya............................._


☺ ```Wayyo mama Asiya nayi miss dinki � yau kam kina gasuwa. Ai gwara ki dinga irin
wannan aiki ko jikin ki ya sabe. yau duk wanda yaje kusa da mama Asiya zaici ubansa. Dan
na lura neman wanda zata huce haushi a kansa take. � Haba asp karka ba maza kunyi mana.
I love All my fans. I'm back``` �




Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy




08144420347





��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 73-74


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*

���
*ZAMANI WRITERS* _*SUNAYEN KU A RUBUCE SUKE DAYA-BAYAN-DAYA A
ZUCIYATA. BANSAN YA ZAN BAYYANA IRIN KEWAR KU DANAYI BA.*_ _*KULLUM
TUNANIN KU NAKE. NAKAN CE "Ah Duniya kenan, kamar jiya ne nake tare daku yau gashi
rashin ta ya nisanta ni daku". SAI DAI INA MAIYI MUKU ADDU'AR DAUKAKA KUYI KWARI
KU ZAMA GANJI, DUK BAKIN CIKIN MASASAKI SAI DAI YA SASSAKA YA BARKU.*_
_*ZAMANI WRITERS ALLAH YA SAKA HASKE A RAYUWAR MU ALLAH KASA MU RINGA
RUBUTA ABUNDA ZAI AMFANI JAMA'A.*_

�Dan autan ku ya dawo. A dora daga inda aka tsaya


_MARUBUCIN KWARE BABBAN BURINSA SHINE YA RUBUTA ABUNDA ZAI AMFANI
AL'UMARSA, KO BAYAN RAISHI. SHI BA GORIN SHI YA TARA MAGOYA BAYA DA DUMBIN
MASOYA BA._



MATSALAR DA TA AFKU KUKAJI NI SHIRU
*Makon da ya gabata lafiyan ta lau ina tsaye sai gani nayi ta fadi kasa kanta ya bugu da kasa.
Tayi tsalle ta kara mirginawa a galabaice. Nan take ni da wasu jama'ar wajen muka nufe ta dan
ceto rayuwar ta. Kafin mu karasa wajen har ta sume. Nan fa na shiga rudu da kidima. Wani
bawan Allah ya kawo pure water aka yayyafa mata amma shiru bata ko motsi balle ta bude ido.
Da ganin haka na kara tsurewa. Nan take na fara kuka ina rairawa baitotin kauna. Domin duk
wanda ya sanni ya sanni da ita. Duk wanda ya taba ta batawa nake yi da shi. Duk inda muke
tare ko barci baya raba mu. Itace abokiyar hira ta. Ba komai ne ke kara burgeni a game da ita
ba. Sai ilimin ta zakuyi mamaki idan nace muku duk yaren duniya tana jin shi. Takan koya min
karatu takan tunatar dani ta min nasiha. Ko kadan bata bari raina ya baci. Duk lokacin da
muke tare kuwa har mantawa nake da na kusa dani. Uhmm abun dai da yawa. Sungumar ta
nayi da gudu na nufi asbiti mafi kusa. Nan take akayi emergency da ita. Likitoshi gaba daya
sukayi kanta. Da kyar suka samu ta fara bude ido. In takaice muku labarin dai Sai jiya Dr. Tasi
ya samu nasarar ceto Rayuwar wayar tawa bayan jinya mai tsanani da tayi.*
���� Nayi missing dinta sosai

_ALHAMDULILLAH. ​YANZU DAI JIKIN NATA DA SAUKI. SAI DAI DUK TA RARAME. MUNA
KYAUTATA ZATAN ALJANA KURSIYYA CE TA SHAKE TA DAN HAKA MUKE CIGIYAR
SARKIN BORI EMERGENCY. WANDA YA GANSHI KO YAJI LABARIN SA_

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Asp ne ya fadi haka yayin da ya juya ya nufi dakin sa. Zuciyar sa sai sake-sake yake yanda zai
tsere. Domin Allah ya gani bazai iya zuwa gidan ba. "To ni in naje ma uban me zan musu?". Ya
tambayi kansa. "Kai alquran bazan je ba". Ya fada cikin dan daga murya.~

_*"M*ai gida tana jira fa" Zainab ce ta kwalo kira. Asp Abdul naji yace "gani nan bindigar ce ban
gani ba". Cikin dan daga murya. Ganin bashi da wani zabi ne yasa ya dauki bindigar ya fita.
Yana fita falon yaga Nasmat tsaye. "Au! Ke ba cewa nayi kiyi gaba gani nan zuwa ba?". Nasmat
tace "Dama kai nake jira ai mu tafi". "Kaji yarinya da rashin kunya wato ke dole sai mun jera
kugu, Tukun mun tafi tare?. Ai kuwa abunda bazai yuyu ba kenan, idan kina so inje to fa sai kin
fara yin gaba". Asp Abdul ne ya fadi haka lokacin da yake kokarin zama a kan armchair.
Nasmat da dai taga mutumin da gaske yake idan bata tafi ba bazai je ba sai ta juya tace, "Na
tafi to dan Allah brox kayi sauri karsu kashe ta Aljanun basa da imani". Da fadar haka ta juya ta
fita shi kuwa da ganin haka sai ranshi yayi fari ya tashi yace wa Zainab "Yau zan baki mamaki
zaki ji jarumtar mijin ki. In gaya miki aljanun ko irin na ranar nan ne sai na fatataki aniyar su. Sai
ni asp na Xainab ba gaba da gaba ba yiiiihuhu". Yayi dan ihu irin na kauraye. Zainab ba abunda
take bishi da shi sai "Allah mai gida". Daga karshe kuma ta bushe da dariya jin yayi ta kauraye.
Sallama yayi mata ya fita hade da cewa "Daga can bazan ko dawo gida ba wajen aiki zan
wuce". "Ok Allah ya kiyaye min kai ya dawo min da kai lafiya jarumina" shine abunda Zainab ta
fada. "Ameen godiya nake gimbiyar mata". Ya fada kafin ya fita har a zuciyar sa yaji dadin
addu'ar. Yana fita daga gidan ya kalli gabasa wato saitin da gidan su Nasmat yake. Wata
hayaniyar mutane yaji da dan karfi-karfi. Ji yayi kamar an cewa. "Kuyi sauri ku kira ASP din". Ai
kuwa dajin haka a zuciyar sa yace ai kuwa ko kurata bazaku samu ba. Yamma yayi a guje.
Kafin asmart da aka sake aiko wa ta fito tuni har ya sha kwana. Asmart ta koma gidan Asp tace
wa Zainab "Ance ASP din yayi sauri". Zainab tace ai ya fita yanzu-yanzu bai je gidan naku
bane?". "Eh kawai Asmart tace ta juya da sauri ta koma tacewa su Zuwaira ance ya taho nan._



_Tsuru su Zuwaira sukayi domin su kam sun rasa abun yi. Mama Asiya sai faman wankin bango
take, Duk wanda ya matsa kusa kuwa domin ya amshe sosan sai ta nufo shi da duka. Su
Nasmat kam abun tsokala ma suka samu. Domin da gangan suke zuwa suce ta bashi su tayata
dan ta biyo su ko ta xage su suta Dariya. Ana cikin haka sai ga Abba ya shigo jaye da akwatin
sa. Da ganin sa su Nasmat suka kwashi hayaniya "ga yaya Abba! ga Yaya abba!" Ihun da
suke ne ya tayar da Fatima da take can daki sai barci take. Da sauri Asmart ta karbi akwatin ta
tafi kai mishi daki. Shi kuwa mama Asiya ya nufa sai tambayoyi yake. "Momy lafiya-lafiya".
Bata ko kalle shi ba. "Mama Zuwaira me ya same ta ne haka take abu kamar na yara?" Abba ya
tambaya. Zuwaira tace "Kadai gani Wallahi tun dazun muke fama da ita ta bari amma taki,

Watakil dai iskokai ne". Dake Abba ya biyo jikin Asiya shima irin babbar jikin nan gare shi in ka
kalle shi a fuska ne zaka gane yaro ne. Baiyi shakka ko tsoran tunkarar Mama Asiya ba,
Hannuwanta ya rike yana mata magana cikin sanyi. "Haba momy miye kike yi haka?. Dan Allah
ki bari". Hararen shi tayi "Kai sakar min hannu ko inci mutuncin ka. Miye ruwan ka da abunda
nake yi". Abba yace "Momy bango ne fa kike wanke wa. Bayan kuma an kusa sake fentin ma
baki daya". "Ok wato kaima a mahaukaciya ka dauke ni ko? Kana nufin bansan me nake ba. Ai
nasan bangon ne"._




_Abba ya dan marairaice cikin shagwaba. "Please momy ki bani ni zan wanke gun. Ke muje ki
huta". Nan ma kin yarda tayi magiya kala-kala yayi mata taki yarda ta bari hakan yasa ya fara
janta da karfi. Ba yanda ta iya ganin zai kadata tace. "Abba nema kake ka balla ni ka cike naci.
To naji muje in huta amma fa sai na dawo na karasa aiki na". Abba.yace "Eh naji muje dai".
Haka suka runkuta Cikin falo su zuwaira, Hauwa, Nasmat, Da dai sauran su suka rufa musu
baya. Mama asiya duk ta gaji ji take kamar an bubuge ta. Domin aikin da tayi yau bata taba yin
kalar sa ba tunda aka haife ta. Fatima ce ta fito daga daki gaban tane ya fadi ganin Abba.
Shima kuwa yana ganin ta ya fara hararen ta domin ko kadan jinin su bai hadu ba. Cikin
hanzari Fatima ta dan rissina tace, "Yaya abba ina wuni?. Kazo lafiya". Maimakon ya amsa
sai ya murtuke fuska rai a bace yace, "Zo nan". Jiki na rawa ta fara matsowa gurin sa tafiyar
kamar wacce aka sawa Dabai-bayi. Tsawa ya daka mata. Hakan yasa ta karasa wajen nashi
da sauri. Tana isa bai ko dubi kankantar ta ba ya kwashe ta da mari da karfi. Dan karfin marin
sai da Fatima ta fadi. Ai kuwa ta fasa ihu!. Da faruwar haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login