Showing 57001 words to 60000 words out of 103342 words
Chapter 20 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
tunda kai jarumi ne ko muje in kwatanta
maka inda kudin suke ka daukko". Da sauri Mukhtar yace "Kaiii! Amma kama raina min wayo
waye zai yarda ya koma hannun Aljanar can. Kaga tashi muje in ara maka kudin kawai". Tashi
sukayi suka hau mota basu zame ko ina ba sai wani kauye gida daya-daya. Tun daga farkon
gari su Umar suka fara jiyo garaya kidan 'yan bori na tashi. Gidan suka nufa suna shiga suka
iske masu kids daban masu rawar bori mata da maza daba. Sarkin borin wani dan gajeren
mutun ne baki_
_Wani dan baki dashi sanye yake da wasu jajayen kaya jikin sa duk layoyi da guruka. Ga wata
hular gashi da ya da ya saka a kai sai ta kara mishi muni. Duna kenan sarkin 'yan bori na
wannan yanki. da ganin su ya daga wa masu kidan Hannu duk sai suka dakata. "Mai ke tafe da
ku?". Ya tambaya yana zazare musu idanu. Mukhtar ne ya dan Risina ya dan kirara shi tukun
yace "Mun kawo karar wata shedaniyar Aljana ce da ta takurawa wannan bawan Allah. Nine na
bashi shawarar mu zo gurin ka nasan kai ne kadai zaka iya maganin ta. Aljana ce ta shiga jikin
matarsa sai azbtar da shi take yi". HHHHHHHHH Sarkin borin ya kece da mahaukaciyar
dariya sai kawai suma fadawan sa suka fara yi sai da yayi mai isarsa su dai su Umar tsaye
kawai suke suna kallan ikon Allah. "Shegiya 'yar mintsila tayi kamu".inji sarkin bori. Ya hade gira
yace "'yar mintsila ce wannan aikin ku mai sauki ne bama sai naje da kai na ba yara na zan
hada ku da su suje su fatatake ta. Ko jiya mun fitar da ita daga gida uku da take kokarin raba
aure. Fatan a shirye kuke?". Mukhtar yana dan murmushi yace "kwarai kuwa a shirye muke
Sarkin bori". Kudin aljihunsa ya fiddo ya ciri dubu biyar yaje ya ajiye agaban sarkin bori.
HHHHHHHHHH Duna yayi dariya tukun yace Lalai wannan ashirye kuke. Da mutane Biyar ya
hadasu masu kida guda biyu 'yan bori uku. Nan suka hayo mota suka nufo gidan Umar. Tun
daga zaure masu kidan suka fara kidan Su kuwa Masu borin kamar da gaske suka farayi sai
hauka suke wai su gasu sunzo gida mai aljanu. Shugaban yan borin da aka hado su da shi ne
yace wasu umar su kulle gidan. Ai kuwa suka fita daga gidan daga waje suka garkame gidan da
padlock. Safuratu abun mugun dariya ma ya bata ganin wannan mutanan masu hauka wai sun
zo wai su ita suka zo fitarwa. Fitowa tayi daga cikin dakin da sufar Rafy Sai dai idanunta
Tsanwar shar._
_Ta kuma murtuke fuska ba abunda take bisu da shi sai harara. Da ganin haka masu ku kidan
suka kara kaimi haka masu borin ma kara haukata sukayi har kusa da ita suke zuwa. Sun dade
suna yi amma shiru basu ga wani sauye ba domin tsaye take cik! Sai zuba musu idanuwan ta
masu abun tsoro. Ganin rainin wayan su yana yawa yasa ta nuna daya daga cikin matan 'yan
bori. Wani iska ne ya fito daga hannun nata ya kwashi matar yayi sama da ita......................_
*SU MUKHTAR ABUN HARDA MUGUNTA A KULLE 'YAN BORI DA ALJANA A GIDA*
*MAMA ASIYA YAU AN ZAMA SOJAN SAMA*
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 67-68
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
~Ganin rainin wayan su yana yawa yasa ta nuna daya daga cikin matan 'yan bori. Wani iska ne
ya fito daga hannun nata ya kwashi matar yayi sama da ita...~
_*D*a ita ya dawo da ita kasa tum!. Sannan ta mika hannunta ya zama wani zakalele ta
daukko abun da ake kidan duk ta farfasa su. Da ganin haka duk suka rude. Rafy bacewa tayi ta
koma daki taje ta daukko dorina. Suna tsatsaye kowa yasha jinin jikin sa sai gani suka yi bulala
ta fito daga daki ta nufo su ba tare da sunga mai rike da ita ba. Nan fa bulalar nan ta fara binsu
daya bayan daya tana zane wa nan da nan gidan yacika da ihu! Ba abunda kake ji sai ihun su
da kuma karar bulalar. Da gudu wani ya nufi kofa ya hau bubugawa yana cewa. "Ku bude, Ku
bude zata kashe mu". Saukar bulala yaji abunda yasa ya zabura kenan ya koma suka hau
zagaye-zagaye Gaba daya sun rasa maboya. Su Umar najin Mutanen na ihu! Amma suka ki
bude haka makwabta duk lokacin wani ya fito ya tmbaya lafiya sai suce mishi "Babu komai ana
dan wani aiki ne". Umar kalli Mukhtar yace "Abokina ni fa ina tunanin Aljanar ce take dukan
'yan borin nan. Kamar ihun bana mutum daya nake ji ba". Mukhtar ya kalli Umar yace "Haba
dai kamar dai wasu garori. Yo ai nake gaya maka wannan su aikin su kenan suna cire manyan
aljanu ko sunkai dubu ne ma balle wannan kwara dayar kuma ma mace". Umar dai baice
komai ba. Cikin gidan kuwa tuni tayi musu rudu-rudu wata mata ce daga cikin masu borin ta
sake komawa wajen kyauren da karfi take girgiza wa tana cewa "Dan Allah dan Annabi ku
bude karta kashe mu wannan Aljanar ko kadan bata da imani". Umar yace "kaji ko, To Wallahi
gwara mu bude kar muyi kisan kai". Mukhtar ya kalle sa yace "Kai dai Wallahi ka cika naci to
bari dai na bude ka ganwa idan ka, Ni dai nasan Aljanar ce ake suburbuda. Shine take neman
agaji". Mukhtar y fara bude kofa da cire kwado matar nan ta fito a guje kamar an harbo ta. Ai
kuwa duk da suna maza sai da ta bangaje su suka fadi har kasa. 'yan borin nan daya bayan
daya suka ringa bi ta kansu daga karshe dai da kyar suka samu suka tashi suka rufawa 'yan
borin baya. Wanda har yanzu dorinar bata dai na binsu tana Shadar su haka yansa basu daina
gudu ba. A kasa suka je har kauyen. Sai da Safuratu taga an kusan shiga kauyen tukun ta
shafa musu lafiya ta koma gida._
_Da gudu suka ringa fadawa gidan sarkin bori haba wa wasu daga cikin masu kidan da masu
borin duk wartsakewa sukayi suka fara zabgawa a guje ganin mutane na shigowa a jere. Shi
kanshi sarkin borin kadan ya hana ya tashi ya gudu kawai dan dai kar yaji kunya ne kuma yaga
iya mutanen sa ne. Har dubawa bayansu yake ko zaiga abunda ke biye da su shima yayi ta
kansa amma bai gani ba. Zubewa sukayi a gabansa sai huci sukeyi kowa yasha gudu hatta su
Umar sun galabaita. "lafiya-lafiya!". Sarkin bori ya fara tambaya ciki su ba wanda ya iya daga
baki yayi magana domin duk a wahalce suke. Sai zuwa can Mukhtar yace wa sarkin borin
"Wallahi Aljanar ce duk taci ubansu ta farfasa kayan su. Bama wannan ba har nan ta biyo mu
tun daga can a kasa muka zo tana basu kashi. Sai da suka zo bakin garin nan tukun ta koma".
HHHHHHHHHHHHH Duna Sarkin bori ne ya ke ta kyalkyala dariya. Zuwa can kuma kamar
dauke war nepa dif! Ya dakata da dariyar ya murtuke fuska. Mikewa tsaye yayi ya fara magana.
"Shegiya 'yar mintsila, Ashe tasan wasa ma guri gare shi. Tasan da ta karaso nan. Kai da ta ma
karaso garin nan da kwanan ta ya kare kenan bama wahalta ta zanyi ba, Yaseen da kashe ta
zanyi, Yo me ake da masu irin halinki 'yar mintsila". Gatsine-gatsine ya fara yi kamar wani
mahaukaci. Mukhtar ya kalle shi yace "sarki yanzu miye abunyi?. kaga dai wannan bawan Allah
'yar mintsila ta hana su sakat! Ta hana su wali shi da matar sa...". "Dakata malam". Cikin daga
murya sarkin bori ya fadi hakan. Shi kadai ya yata magana "To, Naji, Aa, Baza a kara ba, Sunyi
kadan ko, hihihihihi, Zanja musu kunne". Duk maganganun da yake shi kadai ne idanunsa
kuma rufe._
_Bude idanu yayi fuskarsa a murtuke ya gallawa Mukhtar harara yace "Aikin banza, ai duk
abunda yafu kune kuka ja domin kudi kadan ka bayar, Wannan dalilin ne ma yasa sarkin aljanun
da muke aiki tare da shi yayi fushi lokacin da na aika yara na yaki ya bisu, Dan haka sai kun
karo kudi yanzu ni da kaina ma zanje in furtume ta, Mintuna 5sunyi yawa tabar gidan". Mukhtar
ne ya kalli Umar da alamun yana so ya tambaye shine ya kara ko kuwa?. Umar da ya fahimci
haka tun kafin Mukhtar yayi magana yace, "Sarkin bokaye in dai kudi me ba matsala. Mu dai
gurin mu ta bar gidan". Naira dubu biyar Umar ya karba a gun Mukhtar ya kara musu. Amma
sarkin bori yace Sai dai Goma. Ba yanda suka iya dubu goma suka kara mishi kudin wajen sa
suka zama 15K. Shiri sosai sarkin bori yayi layoyi da turaren magani. Ha tayar da mutum
Kusan goma daga cikin yaran shi Masu Kida da masu borin. Duk da yasan wajen akwai nisa
amma da isa da takama da nuna shi sarkin borin ne a kasa ya taho. Mutum biyu rike da kasko
hayaki na tashi daya bayanshi daya a gabanshi. A haka suka nufi gidan umar........._
___________________
_Mama asiya da sauri ta karasa ban dakin ta. Ta farawa 'yar baby wanka. Tana cikin gurza mata
soso kawai sai kan ya kille. Mama Asiya juyawa tayi gabas da yama kudu da arewa bata ga
Aljanar ba ga kuma kan 'yar babyn a hannunta. Tsoro ne duk ya kamata tama rasa abunyi nan
ta fara kokarin mayar dashi amma daga ta lika sai ya fado. Suuuuuuuuuu! Taji wani kara hade
da iska a bayanta a tsorace ta juya. Tsohuwar nan ta gani tsaye cikin wata doguwar jan riga
yanzu tama fi muni ga abun tsoro idan nata sunyi wani kwala-kwala gasu jajaye farin ba yawa.
Fuskar duk a jagule take abun tsoro da kyama. Mama Asiya karkarwa take domin ta tsorata
sosai. "Kiiii kii yi haaakuuurii Da dada dama". Matar ce ta daka mata tsawa "Munafuka ba
abunda zaki gaya min harda wani karkarwa. Ashe dama haushin Babyn nan kike ji ko? Gashi
kin dai cire mata kai da gangan". Da sauri Mama Asiya tace, "A',a Wallahi ina mata wanka ne
ya fita. Kiyi hakuri please". "Kina so in hakura?!. "Eh". Mama asiya ta fada da sauri. "In kina so
in hakura to ajiye 'yar babyn ki jiyo". Da sauri ta ajiye 'yar babyn a saman Bath din, ta juya suka
fuskanci juna da Aljanar. "Ba wani abu mai wuya bane kawai kuka da dariya nake so ki min a
lokaci daya. In bakiyi ba kuma yaseen sai na maida ki kuli-kuli"._
_Dajin haka mama Asiya ta fara. Hahahahaha wiiiiiii wiiiiiii hahahaha yiiii yiiiii Hahahahaha
Uhmmm uhmmm hahahaha. Ta dade tana yi Aljanar ce ta Wanke ta da mari Tats!! "Dan ubanki
haka ake kuka dama a garin ku ba hawaye?". Zafin marin da mugun takaici sune suka saka
Mama Asiya kukan gaske hawaye suka fara kwaranya. "Yauwa haba ko ke fa. Yanzu naga kina
kukan gaskiya sauran kuma Dariya". Mama Asiya da tuni kuka yaci karfin ta rasa ya zatayi
dariyar tayi. Hakan yasa ta kama Bude hakori tana yak'e. Da gani haka Aljanar tace "Wannan
ai ba Dariya bace maza yiwa kanki chakulkuli. Kiyi Dariya". Chakulkulo tahau yi wa kanta Ta
karfi da yaji sai da dariyar ta zo mata ta hada da kukan tana yi. Aljanar kanta abun ya bata
Dariya Hakan yasa tace wa mama Asiya "Oya yanzu na yafe miki kuma na gyara kan babyn
juya kici gaba da mata wankan". Da fadar haka ta bace, Ita kuwa mama Asiya ta juya taci gaba
da wa 'yar baby wanka. Safuratu a wani *KURMIN DAJI* ta bullo ba abunda take sai Dariya.
Mama Asiya bayan ta gama mawa 'yar tsanar wanka ta tsane ta tas!. Taje da ita gaban mirror ta
fara mata kwalliya. Irin kwalliyar da Asiya ta tsaya ta tsara wa 'yar babyn ko ita kanta bata taba
yin ta ba._
_Ji tayi kawai 'yar babyn tace "Daukko zani ki goyani". Da sauri Mama Asiya ta bude wardrobe
ta daukko zani tazo zata goya ta kenan taji tace, "Yaseen kin ma mugun Rainani, Da wannan
tsohon zanin zaki goyi gimbiya guda?. Maza ki daukko sabo". Komawa tayi ta daukko sabo a
cikin kayanta wanda bata ko taba sawa bama, Tazo ta goya 'yar habyn da goya ta kawai sai ji
tayi ta kama kuka. Mama Asiya tsuru tayi jira kawai taji me yasaka ta kukan. Wani mugun
tsunkuli taji an mata wanda har sai da tayi 'yar kara. "Shegiya muguwa wato kina ji ina kuka
shine baza ki ringa jijiga ni irin "yanda ake wa jariri ba ko?. Maza fita dani ki ringa jijiga ni ko
nayi shiru". Da fadar haka 'yar babun taci gaba da kuka. Ai kuwa mama Asiya ta hau jijiga da
lalashi kamar ta sama jaririn gaske. Su Zuwaira na falo suna hira. Kawai sai ganin Mama Asiya
sukaye ta fito daga dakin ta goye da 'yar baby Sai faman jijigata take tana fadar "Yi shiru- Yi
shiru. su basa ko jin.........................._
*Yaseen na gaji
MAMA ASIYA *RENAN DOLE YA SAMU...*
*SARKIN BORI DUNA*
An nufo gidan Umar. Allah yass kai ma a raka ka har gida kamar yanda akawa yaranka
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 69-70
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
*BADDEEYERH*
Written; *BEAUTY QUEEN*
_JA MUJE GWANA TA. ALLAH YA KARA BASIRA DA FASAHA. KINYI ABUN A YABA.
TABBAS MUTANE ZASU KARU DAKE SOSAI. KICI GABA KUMA KI MAIDA HANKALI WAJEN
ZAKULO IRI-IREN MATSALOLIN NAN DAKE ADDABAR MU A WANNAN ZAMANI. HAKIKA
DA YAWA ZASU HANKALU TA DALILIN LITTAFIN_
*ZUBAR HAWAYE*
Written by. *ZEETTY*
Cogrt Sis kinyi rawar gani, Kinyi abun azo a gani. ZUBAR HAWAYE.
BABBAN DARASIN DA KE CIKI.
_GARE KU SAMARI MAYAUDARA. FATAN IN KUKA KARANTA LABARIN NAN ZAKU
HANKALU KU GUJE YAUDARA. SHIN KUNSAN YAYA TA KWASHE DA AHMED AMARYARSA
DA FEEDO?_
_MASU SOYAYYAR_ SHAN MINTI. _KU BAKU TUNANIN NAKU YAN UWA MATA IDAN
KAGA ANAYI DA KANWAR KA ZAKAJI DADI?. KUMA MATA AI DA LAIFIN KU SHIN IDAN
KIKA KI AMINCEWA ZAI MIKI DOLE NE? IDAN KUMA YA DAI NA ZUWA GURIN KI RASA
MIJIN AURE ZAKIYI NE?. UHMMM ZEETTY TAYI KARIN HASKE A LITTAFIN NAN NATA
ZUBAR HAWAYE_
ZAMANI NA ALFAHARI DA KU. MUNA JIRAN SABABBIN LITTAFAN KU
KU BANI KIDAN BIRTHDAY A SAMA
MASU GUDU SU GUDU
YAU BIRTHDAY QUEEN NE MUKE KU SANI
MASU GUDU SU GUDU
BIRTHDAY HAUSY FA DAN KU SANI
MASU GUDU SU GUDU
DUK ZAMANI MUNA MURNA
MASU GUDU SU GUDU
NI NE RARA NAZO IN FADI
MASU GUDU SU GUDU
ALJANA TA ZO BIRTHDAY, KUJI YA
MASU GUDU SU GUDU
*HAPPY BIRTHDAY TO YOU MY QUEEN HAUWA HAUSY*
*Ina Wishing u More Albarka Years Ahead Dear.*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Kawai sai ganin Mama Asiya sukaye ta fito daga dakin ta goye da 'yar baby Sai faman jijigata
take tana fadar "Yi shiru- Yi shiru. su basa ko jin.~
_Tafe yake jama'ar na binshi baya har da su Umar sune masu gwada mishi hanya. Har kofar
gidan, Kaskon Hayakin ya karba ya fara shiga gidan sannan yaranshi suka rufa mishi baya, Su
Umar kam a tsorace suke sai da suka bari kowa ya shiga tukun da labe-labe suka shigo a
hakan ma suka tsaya a bakin kofa. Sarkin bori tsaye yayi a tsakar gidan yana wani zazarr ido
yana waige-waige cikin tarwatu Da gagautawa ya fara cewa yaransa "Kuyi sauri ku kukuna
hayakin nan ga shegiyar nan tana fama ta gudu, Kuyi sauri, Kuyi sauri". Da sauri yaran nashi
suka daukko wani kullin magani suka zuba a kaskwayan kusan guda shida aka kunnawa wuta.
Ai kuwa hayaki ya cika gidan ba abunda kake ji sai tarin su, Gaba daya har sarkin borin. Su
Umar kuwa dajin haka sukayi waje nan makwabta 'yan gaf! Da gidan su suka fara fitowa suna