Showing 30001 words to 33000 words out of 103342 words
Chapter 11 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
asiya Har karo suke yi ita da kishiyoyin ta wajen fita. Har anzo tsakar gida tukun
Aamart tace "Nasmat wai miye ake wa gudu?". Tambayar da sukaji Asamart tayi ne yasa duk
suka ja birki suka tsaya. Nasmat cike da mamaki tace "Me kika gani a bandaki kika yi ihu!?".
Kyankyaso na gani mana, Shine na tsorata ke kuma sai naga kin rugo ai na dauka wani abun
ne kika gani". Dogon tsaki sukaja kusan tare, kowa na haki tukun suka fara wa junan su
dariyan. "Kaga 'yan iskan yara kun tsorata mu ai mun dauka Aljanar ce ai ta biyu mu har gida".
Inji hauwa. Komawa sukayi cikin gidan gaba dayan su a tsorace suke ga barci ga gajiya amma
ba wacce take da karfin halin shiga dakin ta ita kadai. fatima ita kam tuni har tabi lafiyar gado
tun shogowar su ta farko. Suna nan zaune a falo har alhaji ya dawo. Da ya dawo suka tayar
mishi da rikici domin ko wacce sai da ya rakata daki sai ta rufa da bargo tukun yake fitowa.
Fiddausi kuwa sai wajen karfe sha daya angon haleema ya zo tukun tace gida zata. Da kyar
suka lalaba ta ta yarda zata kwana a dayan dakin sai safe ta tafi.
Yau kusan kwana Biyar da faruwar hakan, kusan kullum sai Nasmat ta hadawa Asmart tarko
domin ta taba Aljanar ko fatima amma har yanzu shiru kake ji. Abun na matukar cin ran Nasmat
domin tasha zuga Asmart ta ci uban fatima ko kuma ta yiwa 'yar babyn wani abu amma ba
abunda yake faruwa. Suna zaune a tsakar gidan kan but din motar baban su Fatima ta zo wuce
wa Rike da 'yar tsanar ta. "Ke dan ubanki zo nan". Cewar Asmart, Fatima ta zo. "Muga 'yar
babyn nan kullum kina tare da ita kamar mayya". Fatima bata so ba dan gudun kar a dake ta,
ta mika wa asmart 'yar tsanar. Nasmat a tsorace take tun da Nasmat ta zo shiyasa ma ko uffan
bata ce ba, Yanzu ma badan ta so take zaune a gun ba kawai dan mugunta ne, So take kawai
asmart ta tsokalo wa kanta. Asmart na karbar 'yar tsanar ta juya ta ciki da bai, tana kare mata
kallo. "Fatima naji ance wai babyn ki na magana ko?". Cikin fara'a Fatima tace "Eh mana tana
cin abinci ma kuma idan aka bige ta ko na barta ita kadai har kuka take yi". Asmart ko da jin
haka sai ta buga 'yar tsanar da kasa da karfi Tum!. Fatima sai binta kawai tayi da kallo. Asmart
ta wani dauke Fatima da mari har sai da ta fadi nan take ta fara kuka. "Shegiya ma karya ciya
kince tana kuka idan an dake ta to yanzu me ya hana tayi kuka?". Asmart ce ke fadar haka
lokacin ta diro daga kan bayar motan. Taje ta dauki 'baby Doll din ta kama kan ta murda da iya
karfin ta, da mugunta so tayi ta cira kan amma yaki cire wa. Fatima kuwa kuka take tana fadin
"Aunty dan Allah karki kashe min babyna". Nasmat har yanzu zaune take kan mota sai kallan
drama take, Cikin ranta farin ciki cike fal! Dariya ce ta mugunta ta kamata lokaci guda ta fara
kyal kyalata. Suna hada ido da 'yar tsanar tayi gum baki. Domin gani tayi kamar hararen ta take.
Asmart kuwa 'yar babyn tayi a kasa ta fara tataka ta tana tsalle tana dira a kanta. "Wato har rai
ne da ita da kike cewa karna kashe miki ita kenan, To gashin nan ta mutu". Wani tsalle da tayi
gefan takalminta ya dan Daki gefan gashin kan 'yar robar wanda har wani dan guntun gashin
ya tsinke daga kan. Fatima na ganin haka ta kara fashewa da kuka. Da sauri taje tana kokarin
kwatar 'yar ta tana cewa. "Dan Allah aunty kiyi hakuri kinga har kin fara tsinka mata gashi".
Asmart ta sunkuya ta dauki diyar "Au! Ashe fa gashi gare ta aunty yolash! Kenan, amma fa idan
aka dan rage wannan gashin zata fi kyau dan haka bari inje in mata aski". Tana fadar haka ta
nufi falo da gudu Fatima kuwa ta bita tana kuka tana cewa ta bata diyar ta.
Nasmat na ganin haka ta kyalkyale da dariya harda rike ciki tace "Asmart yau zaki ci ubanki, kin
dauki ruwan da zai dafa ki". Haka su asmart suka wuce su mama asiya a falo da gudun tsiya
fatima na binta tana kuka. Asmart na shiga dakin tayi sauri ta rufe dakin tana dariya. Fatima nan
ta tsaya tana kuka tana faman bu buga kofar. "Ke fati uwarki nace, ko baki ji ba". Hauwa ce ke
maganar. "Kaji 'yar iskar yarinya mutane na zaman su suna hutawa zaki zi ki ishe su da kuka".
"Mama hauwa aunty Asmart ce ta kwace min babyna". Fatima ta fada tana kara rushewa da
kuka. Afusace hauwa tayi kanta tana mata fada har da duka ta kora ta waje. Asmart na shiga
dakin ta wullar da 'yar babyn a kasa hade da taka ta ta nufi wajen kayan kwaliyar su tana
neman reza ita da gaske iski zatayi wa 'yar tsanar. Wani dan tsalle tayi na jin dadin ganin rezar
nan fa ta zo ta zauna ta aske wa
'Yar tsanar kanta tas!. Tana kallanta ta kyalkyale da dariya, "Amma fa kinyi kyau sosai yar
yarinyar fatutu, bari in ma kan nan kiss". Ta fada cike da zolaya ta manna wa kan 'yar babyn
kiss. Uhhhmmahhh, Ai kuwa taji bakinta da kan kamar ansa gam an like. Jatayi da niyar raba
bakin ta da kan 'yar babyn ai kuwa yaki rabuwa bakin nata ya manne Tun tana daukar abun
wasa har ta kai ta ga fara kuka tana jan kan ki!ki!-ki!ki! Amma yaki fita. Hawaye shabe-shabe ta
tashi ta nufi kofa tana kuka tayi-tayi ta bude kofa taki buduwa. Ihuu! Ta farayi tana neman dauki
amma shiru gidan kamar ba kowa.Hannu tasa ta kama gangar jikin 'yar babyn taja da karfi sai ji
tayi ta fizge ta. Ai kuwa ta wullar da ita can jikin bango a tsorace tana mai da nunfashi
daya-daya. Fitsarin wuya taji da sauri ta shiga ban daki lokacin taji harda kashi ma. Tana
tsugune ta fara jin wata 'yar siririyar dariya na fitowa daga dakin. tun anayi a hankali har aka
fara da karfi abun yayi matukar tsorata ta domin bata san mai kalar dariyar nan ba a gidan.
Wani hayaki kuma taga ya fara shigowa ta kasar kofar toilet din. Bata gama ba ta wanke a
hankali ta dan bude kofar a tsora ce. Hayaki ne cike da dakin baka iya ganin na gaban ka ga
kuma dariyar har yanzu yi ake. Mamaki da tsoro suka kara ziyartar Asmart a lokaci guda. Wajen
da take jin dariyar ta nufa tana tafe a hankali duk da ba wani ganin gabanta take sosai ba. Tana
tafiya taji tayi karo da wani abu tana kallan kasa taga wani abu ne lulube da Bakin zani kuma
daga ciki dariyar ke fitowa. Karkarwa ta farayi tana tunanin ta daga ko ta barii.......................
*Kuyi hakuri kadan neee*
Ni kuwa Idan nice Asmart sai na daga naga ko ma miye. Kai/ke fa???. Lolz
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 39-40
NA. ✍KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
*DEDICATED TO YOU, ZAINAB ZEE*
*Hip hip hip hurray, Happy birthday to you*
*ZAINAB ZEE*
And
*BIEBOH*
*Ina taya ku murnar zagayowar haihuwar ku. Allah ya karo wasu shekarun masu amfani. Ya
yafe zunuban da kukayi a shekarun da suka wuce. Ya kuma linka ladar* It's you day.
~Tana tafiya taji tayi karo da wani abu tana kallan kasa taga wani abu ne lulube da Bakin zani
kuma daga ciki dariyar ke fitowa. Karkarwa ta farayi tana tunanin ta daga ko ta barii.~
»»Hannu na karkarwa cike da tsoro ta kama dan bak'in mayafin ta fizge karfi. 'Yar babyn ta gani
kwance rufda ciki itace mai dariyar. "Aikin banza ashe wannan abarce ma har na tsorata".
Asmart kafa tasa ta dan buge ta abunda ta gani yasa ta fara ja da baya. Idanun 'yar tsanar ne
wani irin bak'in jini ke fita a matsayin hawaye ga wasu manyan hakora da suka zazaro waje
wani abu take taunawa tana dariyar kamar danyan nama hakan yasa bakin ta shima yayi ja
idanunta kuwa sun koma baki da ja. Sabanin bakin da fari. Heheheheheheheh, "Baki san nice
ba ko?. To da kin dauka wace a ciki?". 'Yar babyn ce take magana cikin wata 'yar siririyar
murya. Nan take jikin asmart ya fara rawa saboda tsoro magana na rawa-rawa, "Dan Allah kiyi
hakuri ki rabu dani Wallahi bansan ke aljana bace. Wallahi na dauka diyar roba ce".
HahahahHahhha "Wata dariyar mai karfin gaske 'yar robar tayi wacce tasa sai da Asmart ta rufe
kunnan ta. "Wato ke azzaluma ko kina zatan zan kyale azzalumai irin ku ne? Muddun da rai! Na
da lafiya ta bazan dinga sasauta wa azzalumai irin ku ba. Musamman masu cutar marayu.
Yanzu in kina so in hakura ba abu mai wuya bane kawai zo ki dauke ni ki min wanka ki mayar
min da gashi na". "To, To". Da sauri asmart ta fada, Lokacin taje da niyar Daukar 'yar babyn
amma tayi iya kokarin ta ta raba ta da kasa ma abu ya gagara. Ita kuwa aljanar sai gagaba wata
kalar dariya take marar dadin ji. "Oya daga ni mana ko so kike yanzu in fara taba lafiyan jikin
ki?". Dan Allah kiyi hakuri *Aljanar fatima,* wallahi nayi-nayi na kasa ne". Hihihihihihh. "To
tunda dai kika ce min Aljnar fatima naji dadi kuma na rage miki aiki amma da ko shekara zamuyi
baza ki iya rabani da kasa ba. Yanzu abunda nake so jeki ki tsinto gashina ki zo ki mayar min
abuna".
Asmart na karkarwa tace, "To ai dakin duk hayaki ne bana ganin gaba na. Tana rufe baki
hayakin ya dauke gaba daya taga kamar ba'a taba yinsa bama. Da sauri ta nufi wajen ta fara
tsinto gashin da ta aske a kan Aljanar 'yar babyn. Sai da ta tsinto gaba daya tazo ta mikawa
aljanar a tsorace tace "To gashi". "Au! Miko min kawai zakiyi? Zo ki mayar min kamar yanda
kika aske min in kuwa ba haka ba yanzu kiga karshen mugu". Da sauri Asmart ta matsa kusa ta
fara kokarin mayar da gashin da ta aske. Daga ta dora sai taga gashin ya fado, aljanar kuwa sai
dariya take. Asmart tuni ta gaji, ta kuma gaya wa aljnar itabkuwa tace dole sai ta mayar mata da
gashin ta kamar yanda yake a da. A smart taci gaba. Tana yi ta fashe da kuka da karfi.
"Keeeeeeee!!!". Wata muguwar tsawa aljanar tayi wa asmart tana yi kuwa dakin yayi duhu
rundum. Asmar bata iya ganin ko tafin hannunta balle aljanar da ke gabanta. A zuciyar ta tace "
wannan dama ce ta in tsere dan haka yanzu bari inyi nan nasan ta nan kofar fita take". A
hankali ta tashi kamar barauniya take sanda. Kafarta taji tana takawa kamar a cikin hakukuwa.
Abun ya bata mamaki ta fara zance a zuci, "To me ya kawo wannan hakukuwan cikin daki
kuwa?, dakin da ake share wa kullum. Ahhh! Wayyo Allah kafa ta". Asmart tace yayin da taji ta
taka wani abu kamar kaya ya kuma shige mata cikin kasa. Dake har yanzu mugun duhun na
nan bata san ko me ta taka ba. Kuka ta fara tana Yarfa hannu tama manta da Aljanar. A wajen
ta zauna sai lokacin ta tuno da ashe aljana na kusa. Hakan yasa ta rike baki ta gam. Rintse ido
tayi hawaye na zubowa ga radadi zafin da take ji. Bude ido tayi haske fayau sai dai kuma a
inda ta tsinci kanta ne abun yayi matukar girgiza ta da bata mamaki. Wani mugun daji mai wasu
irin itatuwa wanda bata taba ganin kalarsa ba ko a TV gasu dogaye ga kuma fadi. Duk sunyi
inuwa wa waje. Yanayin wajen kadai abun tsoro ne ko kukan tsuntsu babu balle kayi tunanin
zaka sama mutum. Wa-waigawa tayi ko ina iya ganinta bata hangi karshen dajin ba. Kuka ta
kara fashewa da shi, domin wannan ba karamin tashin hankali bane a gare ta. Sai yanzu idanta
ya kai ga kafarta da ke zubda jini ashe kaya ce ta taka. Kara rudewa tayi ganin jinin dake zuba
hannu ta dora kai ta fashe da kuka tana surutai na neman taima ko daga uwar ta da dangin
ta.Da dai taga kukan baya yi. Sai ta fara kokarin cire kayar, daga ta dan sai ta sai ta saki kara,
"Wayyo", Haka dai tatayi. "Kee! me kike a nan". Wata muryar ce katuwa ta fadi hakan, Kamar
daga sama Fatima taji maganar
A firgice ta juya firgigit!. Wasu irin mutane ta gani masu mugun abun tsoro. 'yan kanana ne
kamar yaro dan shekara 6 haka. Amma kawunan su a mulmule suke kamar kabewa Gasu
manyan idanunsu kananu 'yan mitsi-mitsi. Ko wanne daga ciki gashi ne buzu-buzu a kan ba
tsari. Asmart ihu ta kurma ta sa hannu ta fizge kayar ta tashi ta ari ta kare. Su ma kuwa sunkai
su goma suka rufa mata baya. Sa'arta daya basa da gudu domin kan yake rinjayar su. Suta
faduwa. Gudu suke cikin wannan kunkurumin daji asmart duk da tayi musu nisa bata tsayawa
wai waye. Sai da tayi gudu sosai tukun ta sama gidin wata bishiya ta jingina tana haki.
Bata fi mintuna biyar ba taji wani irin gurnani a bayanta. A hankali take juyawa a tsorace. Wata
bakar damusa ce mai jajayen ido. Sai bude baki take yi tana lasar harshe. Mugun tsurewa
asmart tayi, da baya-baya ta fara tafiya damusar na kara matsota. Saurin da damusar ta fara
ne yasa asmart ta juya ta runtuma a guje tana ihu! Da musar kuwa tace dake aka hada mu.
Gudu take iya karfin ta tana waige. Wani makeken gida taga ya bayyana a gabanta. Batayi wani
tunani ba ta Afka! Ciki ta rufo kofar, gida ne makeke mai kayan kwaliya da filawoyi iri-iri sai dai
bata ga kowa a cikisa ba. Sannan ba dakuna sai daki daya wani wangame me wanda yake a
bude sai wani jan labule dake sanye a kofar dakin shi ya hana aga cikin dakin. Asmart tunani
take taje ko kuwa ta tsaya nan. Daga karshe dai ta yanke hukuncin gwara ma taje in ma kashe
ta aljanar nan zata yi gwara ta kashe ta ta huta. Gadan gadan ta nufi dakin ta yace labule cike
da jarumta tana shigewa Kyauren dakin ya rufe gam. Can Asmart ta hango wata mata tsaye
Sanye da riga baka doguwa. Gashin kanta dogo ne shine ya barbazu ya hana q ga fuskarta.
Cikin Masifa da daga murya Asmart tace "Ke.............
Yaseen na gaji. Kuyi hakuri da wannan.
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 41-42
NA. ✍KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
*DEDICATED TO YOU*
*Mzz Dady*
*Rabi'atu Shua'ibu*
*Layuza*
*Phateema*
*Teemah*
*Maimunat (Aunty maimuna)*
*Ummu Azza..*
Thanks d luv an supporting This book❤ Duk masoya na Ana mugun tare ♂
*YAU TAMBURAN GIRMA NA BUGA DOMIN MASOYA NA,* ☺
*INA MASOYA NA?. KU FITO*
*INA MASOYA NA?. KU FITO*
*INA MASOYA NA?. KU FITO*
*INA MUKU FATAN ALKHAIRI,* *DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI* ☺
*INA MUKU FATAN ALKHAIRI,* *DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI* ☺
*INA MUKU FATAN ALKHAIRI,* *DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI* ☺
Dan Allah masoya Kuyi hakuri
Dan Allah masoya kuyi hakuri.
M INUWA 2
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Gashin kanta dogo ne shine ya barbazu ya hana q ga fuskarta. Cikin Masifa da daga murya
Asmart tace "Ke....~
"Ke wai wace ce, me kika zo yi gidan mu?, Ke wacce irin muguwa ce?". Cikin karfin hali Asmart
ke watsawa matar ta tsaye wacce ta tabbatar da itace Aljanar. Duk yanda ta ci cije ta kafe ta
cire tsoro. Dariyar da aljanar nan ta bushe da ita sai da ya tsorata Asmart din dan sai da taji
kamar ta ruga. "Keeee!". Aljanar ta fada lokacin da ta dago kai da karfi gashin kanta ne ya wani
mi mike tsai-tsaye idanuwanta jajawur Wasu ba kaken abubuwa kamar tsutsotsin suna yawo a
ciki. Fuskar tata a tabe take bakin ya