Showing 9001 words to 12000 words out of 103342 words
Chapter 4 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
ki karo min ruwa wllh sai kinyi sawo
uku nan gaba". Rushewa tayi da kuka "wllh ni dai na gaji wajen yayi nisa aunty ki tausaya min ki
deba a can". Wani tankin ruwa ne ta nuna da yatsarta ya cika sai zuba yake ma. A lokacin
Safuratu ta gane cewa ba rashin ruwa yasa aka tura fatimar ba mugunta ne kawai.
"Kan uba! Iyee fatima ni zaki dinga fadawa kin gaji in aike ki kice kin gaji?". Kwashe ta da mari
tayi dan karfin marin har saida ta kusan faduwa. Wani sabon kukan ta dora dashi mai karfi. Da
gudu naga wata budurwar ta fito daga falo tazo ta kama fatima tana kalan waccan, "Haba
ameera wai miyasa ke muguwa ce bakya jin tausayin yarinyar nan ko kadan shin so kike ki
kashe ta ne?. Kin turata debo ruwa dan iyayi bayan ga ruwa nan yanzu kuma kina dakar ta
gaskiya karki kara dukanta".
"An daka din kiyi abunda zaki yi bari ma ki gani inci ubanta a gaban ki inga ubanda ya isa ya
hanani". Fatimar ta nufa ta daga hannu zata kara marinta da sauri Wacce ake kira Iddau charaf!
ta rike hannun, "Ameera wllh bazaki dake ta ba a kan me wato ita batada gata ko?". Ameera
tace, "Sake min hannu, sakar min hannu". "Anki a saki ki kwace in kina da karfi". Haba wa ai
kafi ta rufe baki tuni Ameera tayi kukan kura ta chakume ta, nan fa suka hau kunce harda
naushe-naushe. Safuratu na tsaye tana kallan ikon allah abun ya fara rikitata.
Wasu yan mata ne a daki su biyu kusan kansu daya da kadan dayar ta dara daya Zan iya cewa
daya shekarar ta 12 dayar kuma 14. Daga ganin su kaga mararsa jin magana ta kwaliyar da
sukayi ma kadai ta isa ta sheda maka hakan ba kauya wa day ba wannan kwaliyar taci uwar ta
kauyawa day a hauka. Kamar ance wa mai suna Asma'u ta kallo waje ta window. Wani dan
kara tayi na jin dadi nan da nan ta mike.Yawa bigi ciki aunty ameera, karki bari ta kada ki aunty
iddau". (fiddausi suke kira da iddau) koda jin haka naga dayar ta bar abunda take da gudu tazo
ta haye kan gadon itama ta fara leke. Tsalle tsalle suke suna dunkule hannu suna fadin bamu
rabawa saidai mu kara zugawa bigi cikin dan bari bakin. Maganar da suke tana kaiwa har
kunnuwan masu fadan amma basu bari ba sai ma kowacce ta kara dadagewa. Su kuwa su
Asma'u komawa sukayi Kamar dai supports a filin Wrestling ko wacce ta zaba wacce take
so............
Mujee zuwa.
Autan writers nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 11-12
NA. KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
*IN DEDICATION TO YOU OUR NASMAT* _Ina ji dake wllh in kikayi fushi dani ina zan
saka kaina Da bazarku nake rawa ZAMANI You're my blood body Au!_
I love you all my fans
Even if you haven’t found your love yet, don’t worry, with time comes a lover!
```FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----```
*Afuwan Readers nayi amfani da SUFURATU Maimako SAFURATU a farkon pagen baya.*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
Maganar da suke tana kaiwa har kunnuwan masu fadan amma basu bari ba sai ma kowacce ta
kara dadagewa. Su kuwa su Asma'u komawa sukayi Kamar dai supports a filin Wrestling ko
wacce ta zaba wacce take so...»Wata mata ce mai jikin sosai da gudu ta fito tana "kai kai ku
bari mana" Da kyar ta samu ta raba su a cikin su kowacce taji jiki. Sai Huci suke suna hararen
juna. "Me ya hadaku kuke fada ku da kullum bakwa rabo da rigima kamar Ba yan uwa ba".
"Momy wai dan na daki waccan shegiyar yarinyar shine tazo wai zata rama mata". Ameera ta
fada tare da nuna Fatima dake tsaye gefe tana hawaye. Harara matar ta galla mata tare cewa
"muna fuka ai kinga ta koma gefe tana hawayen munafurci, ke kuma Fiddausi wllh hawainiyarki
ta kiyayi ramata, in badan iskanci ba saboda ta dake wannan Yarinyar zaku kama fada da yar
uwarki".
Asama'u da Nasima (Suke kira da nasmat) Ba karamin haushi sukaji ba ganin mama asiya taje
ta raba fadan. Mtseewwww! A tare suka ja tsaki, "Wannan mama Asiyar gaskiya mu dai bata
gyara mana ba wallahi allah ya isa". Cewar Nasmat. Asma'u taja tsaki mtswww!, "Ni har ta
bani mugun haushi wallahi Duk da tana momy na. ta wani taho tubur-tubur da ita kamar kaza
buloras irin lutayan nan kinsan fa basa iya tafiya sosai in suka girma bari kiga irin tafiyar maman
mu".
Nan fa Asmart ta sakko ta fara nuna kalar tafiyar, harda irin Dafe kugu yanda yan lukutaye suke
in sun gaji. Da sauri nasmat ta sakko "dallah malama ba haka take ba bari kiga ni". Itama
kwakwayan tafiyar mama asiya ta shiga yi. Bayan tayi tafiya mai dan tsayi Asmart na tsaye na
kallo da gudu ta dawo tana fadar "kuma bari kiga yanda take in taci ta koshi ta kasa tashi daga
kwance". Kwantawa tayi Rairan a kan katifa tukun ta fara wani jujuyawa tana irin juyin nan da
karfi abun in kagani dole kayi dariya. Asmary ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya. Daga
bisani kuma ta dan tabe fuska alamun tayi fushi. Kulli ta kaiwa asmart a baya "Dan ubanki ki
bari mamana ne fa". Asmart ta mike tsaye dariya ta kusan kubuce mata, matawa nayi kuma ai
ke kika fara. Gaba daya suka saki dariya har suna rike ciki kamar mahaukata.
Fiddausi ta tace "Haba mama asiya ya za'ayi.....". Tun kafin ta idasa maganar mama asiya ta
daka mata tsawa "Ke rufe min baki wallahi ko in gwab gwabje ki yanzu a gurin nan, marar
kunya" Fiddausi tafiya tayi tana bubuga kafa tana gunguni. "Ke me kike cewa. Zagina kike
ko?". "Ni dai bance komai ba". Kunnan fatima mama asiya ta kamo hade da jawota gabanta.
"Munafuka ke kuma zo nan uwar iyayi, wato dan an dan bige ki ne kike wa motane kuka ko, to
na kori mai rama mikin muga kuma uban da zai ramamiki yanzu".
Dankwashin ta tayi a kai hade da cewa "Ameera gata nan ki mata abunda kike so inga wanda
ya isa ya hana ki ko uwarta tazo nan bata isa ba balle ma tuni ta bar duniyar". Tana gama fadar
haka ta tura Fatima ta fada jikin Ameera ita kuwa ta koma falo. Koda jin mama asiya ta fadi
haka Sai ran Safuratu yayi mugun bace tuni idanunta soka koma jajur kamar garwashi,
"Wato.marainiya ce shiyasa kuke gana mata azaba ko to kunyi na karshe". A cewar Aljana
Safuratu tana maganar ne a kusa da su amma su ko kadan basa ji.
Ameera ta dauki bokitin ruwa ta kara dorawa Fatima a kai maza wuce ki debo min Ruwa wllh
sai kinyi sawu uku ko mutuwa zakiyk ba kuka ba". Fatima tana kuka abun tausayi ta kama
hanya ta koma debo ruwa, bayan taje ta debo a gajiye ta kawo amira ta juye ta kara bata bokitin
wai ta koma. Fatima ta fashe da wani kukan domin ji take kafafunta kamar zasu tsinke dan
gajiya, amma ba yanda ta iya dolenta ta karba ta tafi tana tagal-tagal mai gadi shi kanshi ya gaji
da bude mata kofa, tuni ta bata mishi rai shi ba abun ya bigeta ba yayi ta aikinsa domin yasan
yanda take a gun alhaji Fatima na tafiya a gajiye jiri ya fara debarta nan take ta fadi kasa a
galabaice. (Wayyo Rashin uwa)
Wani alhaji ne yake tafe a cikin wata dan kareriyar mota tun daga nesa da ya hange ta ya fara
cewa "Wa nake gani haka kamar mama ta?. Bai tabbatar da itace ba saida ta tafi faduwa, ai
kuwa yana ganin ta fadi ya danno motar kamar wanda zai tashi sama dan tsabar gudu. Aljana
Safuratu tayi niyar taimakawa fati kenan taga motar nan ta dirfafo gare su hakan yasa ta koma
gefe.
Wani mugun birki yaja ji kake kiiii! Kafin motar ta karasa tsayawa ya fara kokarin fitowa.
"Mamana! Mamana!" (Sunan da yake kiranta da shi kenan dan sunan kanwar mahaifiyarsa
kenan wacce ta rike shi)
Tashi mamana me ya same ki, da sauri ya dauke ta yasa ta a mota sai ma da zai shiga mota
tukun ya hangi dan bokitin can a gefe Ya kuma dubi jikin fatima ya ganshi a jike "tabbdijam Lalai
Asiya baki so zaman lafiya ba". Abunda ya fada kenan ya shiga motar ya fara tafiya. Sanyin
AC ne ya farfado da Fatima daga yar guntuwar sumar da tayi.
"Oyoyo dadyna Yanzu kazo?. Abunda ta fada kenan lokacin da ta kara matsawa jikinsa ta dan
jingina da shi. "Mamana me ya sameki ne na ganki a nan a kwance kuma da bokiti kusa da ke
ga jikinki a jike ina zaki?". Shiru tayi na dan lokaci tukun tace "Baba ruwa naje debowa zanyi
wanka". Hararar da ya daka mata tasa tayi saurin cewa "Aa baba ba wanka ba wanki zanyi".
Kalansa tayi taga ba annuri a fuskarsa nan take ta sake canza magana "Baba dama shukoki ne
zanba ruwa basa san ruwan gidan mu". Tsawar da ya daka mata ta firgitata abunda abbanta bai
taba mata ba kenan nan take ta fashe da kuka. Rai a bace yace, "Mamana ban sanki da karya
ba karya ba halin mutanan kirki bane shin waya koya miki karya, in kuwa kika ce karya zaki
dinga min to wllh kinji na rantse bazaki sake ganin hakoran dariyana ba".
Cikin kuka tace,
"Dady kayi hakuri wallahi zan fada ma Aunty Ameera ce tace sai na debo mata ruwan wanki
wannan sawuna na uku kenan gashi na gaji amma taki ta hakura ta barni in huta". "What!
Yanzu duk kankartar ki ameera ta aike ki dauko ruwa?". Kai ta daga mishi "A ina kike dibo
ruwan?, Su Asma'u basa gidan ne?". "A can wajen makarantar mu ne. Dady suna gidan mana
a daki suke ma".
"Innalilahi!". Ji yayi kamar ya fashe da kuka domin allah ya gani ko shi bazai iya sawu biyu ba
daga gidansa zuwa can balle ma wai ace wannan yarinyar kuma harda ruwa a kai. Ranshi ne
yayi mugun baci Fatima sai surutu take amma saidai ya kada mata kai dan ko maganar ji yake
bazai iyaba.
Da gudu ya karasa kofar gidan ko daga odar da yake ya isa kasan ya dau zafi, dan in kana
kusa da shi sai ka rufe kunnuwa, da gudu mai gadi ya zo ya bude yana shiga ya parking din
motar ya futo a fusace ya nufi Garzali mai gadi baisan hawa ba baisan sauka ba yaji saukar
mari a kumcinsa. "Garzali ashe kai aikin banza ne ban sani ba ashe a banza nake biyanka
kudina in wata yayi". Cikin murya mai rawa "Afuwan ranka ya dade bansan laifin me nayi ba".
"Au bakama san miye laifinka ba ko uban wa yace ka budewa Fatima kofa yanzu in diyarka ce
dan gidan ku zaka barta taje debo ruwa ne. To daga yau wllh in na sake kamaka da irin wannan
laifin a bakin aikin ka". Fuuu!! Ya wuce kamar jirgi mai gadi ba abunda yake sai bada hakuri
harda durkusawa a gun. Bayan alhaji ya danyi nisa ya tashi yace a kan wannan yar banzar
yarinyar ana min barazana da aikina". "Me kake cewa?". Inji alhji "Aa Alhji cewa nayi ayi hakuri
zan kiyaye".
Tun daga kofar falo ya fara kwala kira "Ameera! Ameera!". yana janye da hannun Fatima. Nan
danan saiga ta ta fito Jikinta na rawa dan tasan abunda ta aikata ko kadan batayi tunanin abban
nasu zai zo war haka ba. "Dady gaaa..". Saukar tagwayen mari da taji ne ya hanata idasa
maganar sai ihuu! da ta kwada mai karfi! Kafin kace me falon ya kusan cika Da yara da manya
bansan haka gidan nan keda iyalai da yawa ba sai yanzu.
Asiya ce tazo ta rungume Ameera dake faman kuka. Alhaji ya fara magana.
"Ke dan ubanki baki da hankali ne ya za'ayi ki aiki wannan yarinyar wai ta debo miki ruwa har
can wata uwa duniya baga kanan ki nan ba wanda suka fita me ya hanaki aike su ko zaluncine
kawai abun, to wai ma inace dazun nan da aka kawo wuta Nasa aka kunna soma?". "Haba
alhaji dubi fa yanda ka kunburawa yarinyar nan kumatu kamar dai ba yar uwarta ta aika ba,
kawai fa uniform dinta ne zata wanke kasan farare ne shine fa ta aiki Fatima ta debo mata ruwa
a can kasan yafi na nan haske". Asiya ce ke maganar lokacin da take lalashin yar tata.
"Asiya! asia! Sau nawa na kira sunanki,.?". 3 Ta bada amsa a Hatsale, "To wllh asiya ki fita a
idona zan miki rashin mutuncin da bakiyi zato ba wato duk ke kike daurewa yaran gidan nan
gindi suke abunda suka ga dama ko?. To bari kiji in gaya miki wllh duk wanda yake so muyi
zaman arziki da shi a gidan nan to karya ya taba mamana in kuwa mutun bai yarda ba ya
gwada taba ta yaga abunda zai farubda shi". Yana gama fadar haka ya kama hannun Fatima
ya nufi dakinsa. Ya fara tafiya kenan asiya ta fara gunguni kamar yarinya "Shikenan wato sai a
raba kan yara a hana su shakuwa da juna". Maganarta ce tamai zafi sosai yaji bazai iya
daurewa ba. Sakin hannun fatima yayi da gudu ya Nufe ta, Abunka da lukutar mata bata da
gudu ta ruga amma baisha wuya ba wajen kamota. Koda yaje sai yasa kafa ya kwalfe ta nan ta
fadi ta fara wash! Wash! Wayyo ya karya ni. Bai ko tsaya kallanta ba ya wuce ya dakinsa shida
fati.
Asmart da Nasmat ne suka kalli mama asiya tukun suka bushe da dariya ganin ta a kasa kamar
an zaunar da buhun masara. Kowa na gurin abun ya bashi dariya har kishiyoyin nata guda biyu
dake tsaye a gefe. Saidai kowa yasan jarabarta duk gidan dama ba wanda zai iya mata dariya
sai wannan biyun marar ji. Ai kuwa kafin kace me ta yunkura da kyar ta tashi tubur-tubur ta
nufe su wai da niyar ta kamosu ta daka, kafin kace me tuni sun ruga upstairs tana biye da su
koda tahau matakala na daya biyu sai sulbi ya kwashe ta ji kake tum ta fado kasa kamar an
yarda buhun masara. Kanta ne ya bugu da kasa. Su asmart da suka juyo sukaga abunda ya
faru sai suka dora da wata sabuwar dariyar.................
Hmmmmm Gidan nan za'a sha kallo naga alama.
Mujee zuwa.
Autan writers nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 13-14
NA. KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
THIS PAGE IN DEDICATED TO YOU
☘ *UMMU BASHIR* ☘
*ZAINAB YUSUF*
*HUSAINI ATK (80K)*
```FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----```
*KARSHEN PAGEN BAYA*
kafin kace me tuni sun ruga upstairs tana biye da su koda tahau matakala na daya biyu sai sulbi
ya kwashe ta ji kake tum ta fado kasa kamar an yarda buhun masara. Kanta ne ya bugu da
kasa. Su asmart da suka juyo sukaga abunda ya faru sai suka dora da wata sabuwar dariyar.
»» gidan ALHAJI SALIM S.O kenan babban gida ne dake cike da iyalai. alhaji salim mata hudu
gare shi saidai daya ta mutum yanzu uku ke a raye. Asiya uwar gida yaranta biyar biyu mata
sune AMEERA DA ASAMA'U. Maza uku SAFIYANU babban danta sai mai mishi YUSIF. Da
kuma yayan ameeera ABBA.
Mai biwa asiya ZUWAIRA 'Ya'yanta hudu FIDDAUSI. NASIMA. ABDUL Sai ALIYU. A yanzu
HAUWA'U Ce amarya yaranta biyu kadai kanana ILIYASU ABUBAKAR.
Shekarar hindatu (Mamar fatima) uku a gidan ta rasu sai dai ta mutu ta bar fatima tana yar
shekara biyu. Yarinyar fara kyakyawa a duk gidan tafi kowa kyau domin ita ta dara mahaifiyarta
ma kyau. Alhj kamal kuwa ya dauki duk san duniyar nan ya dora a kan fatima domin yana jin
tausayinta sosai kasan cewarta karama kuma marainiya hakan yasa ya dauki amanarta yabawa
asiya.
Irin san da yake nuna mata shi