Showing 84001 words to 87000 words out of 103342 words

Chapter 29 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5034


Haka kuma kwanakin nan da yayi duk lokacin da yunwa ta takura mishi sai ya dinga tunowa da
almajirai masu zuwa wajen shi, Abunda yake zuwa mai a rai shine suma fa haka suke ji yayin
da suke jin yunwa. Mukhtar a zuciya yake kudurtar niyar bazai kara hakan ba. Yau aka cike
kwanaki bakwai cik! Da kawo Muktar daji. Tun da safe Safuratu ta bayyana mishi nan ta zaunar
da shi yana ta tuba yana neman afuwa. Tace "Muktar ya zuciyar taka tayi sanyi ne ko har yanzu
cike take da rashin imani da gurin cutar yar da take a matsayin sana'ar ka. Rufin asirin ka".
Muktar da yake durkushe gwiwowin sa a kasa. Harda hawaye, Cikin kuka yace, "Dan Allah dan
annabi kiyi hakuri dan Allah ki ceci rayuwa ta ki fitar dani daga wannan wahalar._



_Nayi miki alkawarin cewa bama Maryam ba in sha Allah duk wani wanda yake neman taimako
zan taimaka masa gwargwadan iyawata". Safuratu tayi mai wani irin kallo na tuguma, Kafin
tace "Na saba dajin rantse-rantse daga bakin ire-iren ku na karya. To ka sani cewa in har baka
daina cutar da maryam Allah, Allah kaji na rantse ko. To gaba daya sai na amshe duk dukiyar

ka ka dawo kamar dai da yanda kake a lokacin da ka karbe musu kudi. Zanje kuma in nemi
mutumin kirki in bashi amanar Maryam. Da wannan karon ma abuna nayi niyar yi kenan. Kuma
in kana ji wasa to ka sake kwatanta Rashin imanin da kake"._





_Muktar ya sauke ajiyar zuciya yace, "Na rantse miki har da Allah na canzu zaki same ni ba
kamar da ba. Domin wannan horan da kika min ya ankarar dani abubuwa da dama. Dan haka ki
taimaka ki mayar dani gida. Nayi kudirin ko da kuwa kin kwace Maryam da dukiyar ta daga
hannuna bazan fasa wannan kudirin ba. In sha Allah zan taimaka wa duk wanda ke da bukatar
in taimaka wa". Wasu kaya Safuratu ta mika mishi tace yaje ya saka su. Ba dade ba sai gashi
ya sanyo su. Makulin shagon ta bashi kafin kiftawar ido sai ganin shi yayi a kofar daki. Dake ya
saba da shiru na cikin daji yanzu duk sai yaji hayaniyar nan ba dadi. Bankwana Safuratu tayi
mai hade da kara nanata mishi cewa ya kula ya canza hali. Safuratu yau din nan ta tashi ne da
tunanin Fatima kuma zuciyar ta na raya mata ba lafiya ba. Hakan yasa ta tashi da niyar
komawa bauchi yau._

_____________________

_A bangaren Fatima kuwa bayan kwana biyu da tafiyar Safuratu Zuwaira da Hauwa suka taso
ta gaba wai su sai sunga abunda mama Asiya ta gaya musu ko gaskiya ne. Ai kuwa suka fara
takura wa Fatima tun suna zaginta har suka fara dankwashi. Ganin ba abunda ya faru ne yasa
suka kara kaimi wajen cin zalin ta. Daga karshe ma a gaban jama'a har da kuwa Mama Asiya
hauwa da Zuwaira suka karbe yar babyn Fatima sukayi gutsun-gutsun da ita. Nasmat, Asmart,
Ameera, da Mama Asiya duk sai suka fara tausaya wa su Zuwaira a kan abunda suka wa yar
babyn dan a tunanin su Aljanar in bata kashe su ba sai ta kusa. Su kuwa su Hauwa hankalin su
ko tashi baiba._




_Daga karshe ma tatara yar babyn sukayi suka kone ta rumus a tsakar gida. Fatima ta fara
kuka ai kuwa suka same ta suka ta narka taci duka har sai da ta gode wa Allah. Bayan kwana
daya-biyu su Mama Asiya sunyi mamkin ganin ba abunda ya faru da su Zuwaira gashi kuwa
kullum cikin duka da zagin Fatima suke. Hakan yasa suma gaba daya gidan suka koma ruwa.
Wato kowa ya koma kamar da zalluncin da ake wa Fatima har ya kusan linka na da ma. Haka
abba yanzu kusan kullum sai ya daki fatima ko ya aike ta gu mai nisa. Fatima na shan wuya
sosai. Dan ko yau haka ta tafi makaranta ko guntun biredi bata ci ba. Safuratu na isa gidan tace
ta duba dakin su Fatima bata ganta ba. Shiyasa tayi tunanin ko tana makaranta ne. Sai dai
kuma ta duba inda Fatima ke ajiye babyn ta amma bata ga komai ba. Hanyar makarantar ta
nufa. Dan daga nan har sai da ta shiga gidan Umar. Kallo daya tawa Rafy ta gane cewa tana

cikin farin ciki. Domin sai aikin gida take hankalin ta kwance tana wake-wake._




_Nan dai ta bayyana suka gaisa take tambayar Rafy ya zama gidan. Rafy tayi mata godiya tace
ai yanzu suna zaman lafiya sosai da mijin ta. Hamdalla Safuratu tayi nan dai suka hau hira.
Safuratu kam hankalin ta duk yana wajen Fatima. Lokacin ta so su Fatima nayi tayi sallama da
Rafy ta fito ta taryi Fatima. Tafe take tana wani rangaji kamar zata fadi, sai zubar hawaye take.
Ba komai akayi mata ba yunwar ce kawai ke cinta domin bata saba kai war haka bata ci komai
ba. Daga nesa Safuratu ta hange ta. Karasa wa kusa da ita tayi tana kare mata kallo. Irin
ramar da Fatima tayi ne abun ya tsorata Safuratu. Domin in ba kayi wa Fatima kwakwaran sani
ba. Bazaka iya gane ta ba a yanzu. Dan duk kashin wuyanta ya fito ta rame sosai.
Tangal-Tangal din da Fatima keyi har idanta na rufewa hakan ya shedawa Safuratu Fatima najin
matsanan ciyar yunwa._






_Sharf! Fatima ta fadi kasa Safuratu na ganin haka tayi sauri ta shiga jikinta. Mutane har
sunyo kanta da niyar agaji kuma sai sukaga Yarinya ta mike. Karasowa sukayi wasu na kakabe
mata jiki suna mata sannu. Idanun Fatima suka kara zarowa daga ka ganta zaka ga ba kamar
da ba. Yar ledar littatafan Fatima ta dauka ta nufi gida. Kwan! Kwan! Kwan! Kwan! Da karfi
Fatimar ke buga gida. Mai gadi najin haka ya taso a rikice yana fada yana fadin "Waye wannan
yake mana irin wannan buga gida kamar tashin duniya". Buga gidan bana wasa bane domin da
karfi Fatima ke bugawa. Har mai gadi yazo yana kokarin budewa amma bata dai na bugawa
ba. Yana budewa yaga itace. Ya tsaya tsabar haushi har karkarwa yake. Dan ji yayi kamar ya
mare ta duk da tana yar gidan. Fatima ganin mai gadi baya da niyar matsawa. Fuuu! Ta bangaje
shi ta wuce can ya fadi kasa a gigice. Domin irin bangajewar da Fatima tayi mishi ba karamin
kato bane zai yi masa ita har ya fadi. Yayi mamaki sosai. Tashi ya kakabe jiki ya juya yana
kallan Fatimar domin ya kara tabbatar da ita din ce ko wata.






_"Tabbas Fatima ce, to amma ina ta sama wannan karfi haka". Shi kadai yake kallan ta yana
magana shi daya. Kofar falo Fatima ta ja da karfi kamar zata ballata. Yanayin yace labulan
kadai kai in ka gani kasan bana arziki ba. Hauwa ce kadai a dan ringeshe kan sofa tana tauna
Cingum tana daddana waya. Tana jin shigowar Fatima ta tashi zaune. Ita Fatimar ta nufo. Ita

kuwa wani matsiyacin kallo take bin Fatima da shi mai dauke da harara._





_"To shegiya har an taso daga makaranta wato za'a zo a ishi mutane da kuka. To kafin ki fara
komai ajiye kayan makarantar ki shiga dakina kiyi mopping dinshi ki gyara komai kafin kizo in
fada miki next work naki". Fatima kam tsaye take ta kafe Hauwa da ido bata ko giftawa. Hauwa
ganin Fatima taki wuce wa tayi abunda tasaka ta tace. "Ke dan uwarki ba kiji abunda nace kije
kiyi ba. Yar buhun uba kin wani tsare ni da wannan shegun idanun naki. Ko dai na jaki kike so
yan...". "Ina abincina?". Shine abunda Fatima ta fada hakan yasa Hauwa bata karashe
maganar da ta fara ba. "Iyee Fatima ni zaki wa rashin kunya?. To bari kiji dan ubanki ko langen
taliya bazaki ciba yau a gidan nan. Oh! Baki ji abunda aunty zuwaira tace ba ken...". Cikin
tsawa da kagara Fatima ta kara fadar, "Ina abincina na ce?". Abun ne ya fusata Hauwa hakan
yasa ta daga hannu da zafin ta da niyar wanka wa Fatima lafiyayan mari. Charf! Fatima ta rike
hannun hade da Wanka wa Hauwa mari da dayan hannun ta................................._

� *MU GYARA ZAMA KENAN SAFURATU TA SHIGA JIKIN FATIMA KOWA ZAICI
UBANSHI* ���

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy






��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 95-96

© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*


���� *KU KARANTA KU TAYANI DARIYA. FATIMA TA FARA ZAMA ABUN GUDU* �

DUK DANIN PAGEN SADAUKAR WA NE GARE KU
_*NERBEELERT LADY NOVELS*_




_INA MAKU FATAN ALKHARI... DAN ALLAH MASOYA KUYI HAKURI_



_KOMAI ZAI DADI A DUNIYA BAIYI MASOYA BA.... SO YAYI MIN RANA DAMA DA BAZARKU
NAKE TA RAWA KUNA INA?.._

_WANI TAMBURAN GIRMA NA BUGA DOMIN MASOYA NA. DA BAZAR KU NAYI RAWA
AN MIKA HANNU A HANNU NA. MAMAN HANAN TA NUNA LALI KUNA SONA. MAI ZAN
MUKU IN RAMA._ _A RAI NA INA SAKA. INA MASOYANA?._ _KU FITO_

_*NERBEELERT LADY NOVELS*_
SAKONIN KU YA RISKE NI. HAKIKA KU MASOYA NA NE. INA MATUKAR JIN DADI.
SANNAN INA MUKU FATAN ALKHAIRI DAGA ADMINS HAR MEMBERS NA WANNAN GIDA
MAI ALBAKA. *ANA TARE*



*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Cikin tsawa da kagara Fatima ta kara fadar, "Ina abincina na ce?". Abun ne ya fusata Hauwa
hakan yasa ta daga hannu da zafin ta da niyar wanka wa Fatima lafiyayan mari. Charf! Fatima
ta rike hannun hade da Wanka wa Hauwa mari da dayan hannun ta.~

_*G*alala Hauwa ta saki baki tana kallan Fatima cingum din da take ci ma bata san lokacin da
ya fado ba. Rike kunci tayi tana jin radadi a zuciyar ta tana fadar "Anya wannan Fatima ce?".
Hannu Fatima ta sake dagawa da nufi mari "Ina abincina nace?". Da sauri Hauwa tace "Bari in
daukko bari in daukko miki". A tsorace ta mike ta nufi kitchen din Fatima na binta da wani

malalacin kallo._




_Hauwa taje ta zubo mata abincin ta kawo. "Yauwa Fatima ga abincin". Ta mika hannun ta na
dan karkarwa. Fatima na amsa ta zauna a nan ta fara cin abincin hannun baka-hannu kwarya.
Juyawa Hauwa tayi da nufin haurawa upstair dakin ta. "Ina kuma zaki je dawo ki zauna". Fatima
ta fada ba tare da ta dago kai ta kalle Hauwa ba. "Umm umm da... Da.. Ma zanje ina... Jin
fitsari nee". Hauwa tayi maganar murya na karkarwa. Dan duk ta tsorata da Fatima tasan ba ita
kadai bace, Akwai lauje cikin nadi. "To ba yanzu ba dawo ki zauna". Fatima tace ba tare da ta
kalle ta ba. Hauwa har zatayi magana. Fatimar ta daka mata tsawa hakan yasa ta gimtse bakin
ta. Sumi-sumi ta zo ta zauna. Sai kallan Fatimar take wanda sai cin abincin take kamar wacce
tayi shekara bata ci ba. "Innalilahiwa'inailaihirraji'un 2×, Me zan gani haka". Zuwaira ce ka fadar
haka lokacin da take saukko daga kan matakalar tayo kasa._




_Da sauri ta karaso gurin ta tsaya kan Fatima tana zazaga masifa. "Hauwa haka mukayi dake
wato in kafa doka har kin isa kisa kafa ki shure ko?. Wato wuyanki yayi kwari, Ni dake waya fara
shigowa gidan nan ko da baki min biyayya a matsayin ki na kanwata wacce nafi shekaru ba. Ai
ya kamata kiyi min biyayya a matsayina na wacce ta riga ki shigowa gidan nan". Hauwa kallan
Zuwaira kawai take tana kallan Fatima dake faman dibar Shinkafa fara da miya. batace ko kala
ba. Zuwaira taci gaba da cewa "Sanin kanki ne nace yau yarinyar nan bazata ci ko kwayar
shinkafa ba a gidan nan amma gashi nan kin dauka kin bata. Wato ke uwar tausayi. Zanyi
maganin ki kuwa". Hauwa kallan Zuwaira kawai take tana mata wani kalan uku goma hudu
shabiyar. Kasan ranta kuwa addu'a take Allah ya kai damo ga harawa._



_Fatima ce ta mike rike da filet din abincin. Kamar jira take Zuwaira na juyawa kuwa ta yaba
mata shi a fuska. Bata jira komai ba ta juya ta nufi dakin su. Hauwa na ganin abunda ya faru ta
kwashe da dariya harda rike ciki. Zuwaira kuwa cik ta tsaya kamar wacce suka gasar tsayu ita
da gunki. Haushi ya kule ta can kasar ranta tunanin abunda zatayi wa Fatima take. Dan kakabe
jikin ta tayi miya duk ya bata mata kaya. In ka ganta sai ka rantse wasa da miya tayi. "Ni ni ni
Fatima tayi wa haka,_




_Lalai Yarinyar daga ni kuwa bazaki kara ba. Yau ko makiyin ki sai ta tausaya miki Fatima". A
fusace tayi waje, Nan take zuciyoyi suka shiga aikin bata shawarwari na mugunta wanda zatayi

wa Fatima. Dakin mai gadi ta zarce. "Fito-fito mai gadi, Ina wannan dorinar taka mai baki biyu?".
"Tana daki Hajiya". Har dan jijiga take yi dan kaguwa "Bani aranta yi sauri dan Allah". Kallan ta
ya tsaya yana yi "Hajiya wa kuma za'a daka da ita. Naga yaran duk suna makaranta?". Tsawa
ta daka mai, Nan da nan ya zabura ya shiga daki ya daukko mata. Yana bata ta nufi wajen
tankin ruwa ta debi ruwa a irin yan kananun bokitin nan. Ta nufi falo da shi. Fridge ta nufa da
sauri ta daukko kankara ta zuba a ciki tukun ta shiga tsiyayya ruwan sanyi. Ita kadai take
magana. "Dan ubanki ai yau kin shiga uku sai na jikaki da ruwan sanyin nan tukun in miki dukan
kawo wuka. Badai ni kika wa wannan wulakancin ba". Tana gana matse pure water mai sanyi
ta dauki dorinar da bokitin ruwan wanda zuwa yanzu tuni ruwan yayi mugun sanyi. Ta nufi dakin
su Fatima. Hauwa dai na zaune a falo ido kawai take binta da shi._





_"Ayi dai mu gani in tusa tana hura wuta". Inji Hauwa ta fada da dan karfi. Zuwaira taji ta amma
bata kula ta ba. Dashigar ta dakin ta fara kwallawa Fatima kira. "Fatima! Fatima! Fito dan
kut...uban ki. Yau ai sai kin raina kanki". Shiru bata ji ko motsi ba. A tunanin ta Fatimar na ban
daki. "Ki fito na gaya miki dan Wallahi in na iskeki a bandakin nan bazamu kwasheta da kyau
ba. Sai nayi miki jini da majina Wallahi". Nan ma shiru bata ji an tanka ba. Bulala da bokitin ruwa
ta dauka buzun-buzun ta nufi ban dakin da zuwa tasa kafa ta haura kofar da karfi. Kofa na
budewa taga wayam. "Shegiya asbe ta gudu daga dakin". Falo ta fito "Hauwa ina wannan
shegiyar Yarinyar ta nufa da ta fito?". Hauwa ta kalli Zuwaira Mamaki karara a fuskanta. "Au!
Fatiman fitowa tayi ne?". "Kina nufin baki ma ga wucewar ta ba?. Fatima zaki gama guje-gujen
ki kidawo ki iske ni har gida". Zuwaira ta fadi haka ta ajiye bokitin da bulalar a gurin, ta nufi
Upstair da niyar taje dakin ta canja kaya._




_Da bude daki ta tsaya cik! Tana karewa tsakar dakin kallo Fatima ce gaba daya ta bince ke
wardrobe din da su kabbet duk ta wurwatsa kaya a tsakar daki. Yanzu ma sai bincike take tana
bubude lokoki. "Aunty Zuwaira jan baki nake ta nema tun dazun a ina kika ajiye shi". Wani
kululun bakin ciki ne yazo wa Zuwaira makogoro. Nan take ta kai dubanta Mirror ta hangi duk
kayan kwaliyar ta har da jan bakin ma a wajen, "Wai amma dan rainin wayo wannan yarinyar
tace wai jan baki take nema. Kai kawo dai wani tashen iskanci da rainin wayo ne. Amma bari
inyi maganin ki yanzu". Jawo dakin tayi da sauri ta koma falo da gudu ta daukko bokitin ruwa da
bulala. Tana dawowo ta bude daki kuma sai gani tayi wayam! Ba kowai sai tilin barnar da
Fatima tayi mata. Domin shirya kayan da Fatima ta warwatsa kadai jarabar duniya ne. Gashi
wasu kayan a goge ma suka amma Fatima ta kara tattake su. Hauwa na zaune a falo taga
Fatima ta fito daga saman beni bayan ita kuma bata ga fitowar ta daga dakin su bama. Abun ne
ya kulle mata kai. Fatimar tafe take hannun ta rike da dan karamin mirror na kallan fuska dayan
hannun kuma jan bakine da take ta faman Gogawa a lips inta. Tsaye taje tayi a kusa da Hauwa

tana shafa jan bakin. Zuwaira tun daga sama kake iya jiyo jarabar ta. "Yarinyar kamar
Aljana,yanzu nan fa na baro ta a dakin nan wai amma bata nan. Hmm dani kike zancen
Fatima._




_Ai Wallahi in dai kere na yawo zabo na yawo wataran a hadu. Wai ni ta...". Bata karashe fadin
abunda tayi niya ba hango Fatima da tayi a falo. Nan take ta fara sauri tana kokarin sakkowa.
Fatima hanyar dakin su ta nufa. Zuwaira dake rike da bokiti da bulala a hannu da gudy taje
tasha gaban Fatima. "Ina zaki munafuka Allah ya kama ki. Yanzu zan chaskwala ki".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login