Showing 87001 words to 90000 words out of 103342 words
Chapter 30 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
"Bani waje
in wuce". Fatima ta fada cikin kagara. "Iyeee! Lalai Fatima arzikin rashin kunya yaci uban na
da.Har ni zaki iya kallan kwayar idona kice wai in matsa ki wuce. Bari ki karbi hukunci tukun sai
ki wuce ko da jan gindi ne". Kokarin ajiye ruwan take. Ai kafin ta ajiye wata irin bangaza da
Fatima tayi wa Zuwaira can ta fadi kasa bokitin ruwan yayi sama ya fado duk ya jijika Zuwaira
da Carpet din falon. Wata mahaukaciyar dariya hauwa ta kwashe da ita. Har da rike ciki hade
da hawayen dariya._
_Zuwaira tace "Hauwa wai Giwa ce ta bangaje ni ko Saniya ko Rakumi?". Hauqa kara
kwashewa tayi da Dariya. Cikin matsanan ciyar dariya tace, "Duk ba ko daya a ciki". "To dan
Allah jirgin kasa ne ko mota._
_Domin kuguna ji nake kamar ya karye bani iya tashi yanzu". Hhhhhhhhhhhhhhh Dariya kamar
zata kashe ta. Karar dariyar ta ne ya tashi Mama Asiya dake can sama tana barci. Da sauri tayo
Downstairs tana "Lafiya-lafita mi yake faruwa ne?". Falan taga kaca-kaca Can an watsar da
shinkafa da miya. Nan an kwarayar da ruwa. Hauwa ta kalla dake ta faman Dariya. "Ke kuma
wanne irin iskanci ne zaki bata mana falo haka. Nan fa ba falon ki bane ke kadai balle kiyi mana
kazanta". Hauwa ta dan rage dariyar kadan tace "Aunty Asiya Wallahi bani bace aikin Fatima
ne". "Kuturun kareee! Wace Fatimar?". "Fatima tamu ta nan gidan mana". Cikin fusata Mama
Asiya ta nufi dakin su Fatima tana fadar. "Ina take dan ubanta Wallahi sai ta gyara dakin nan
tsaf!"................................................_
*Wayyo cikina* _HAUWA DOLE IN TAYA KI DARIYA. SU ZUWAIRA MADARA ANJI JIKI,
SAI KUMA A TASHI AJE AYI JINYA_
_*KU BIYO NI ZAI-ZAI DAN WANNAN KARAN WANDA AKAYI BABU SHI BAI MORI LITTAFIN
BA*_
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA.
SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN
KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 97-98
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
DAN KADAN NE DAI. KUNSAN ANCE *"DA BABU GWAMMA BA DADI".*
*DEDICATED TO*
*BIGBOY ISAH FANS*
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*GIDAN MARAYU FANS CLUB*
*3STAR HAUSA NOVELS*
GODIYA TA MUSAMMAN GARE KU TARE DA FATAN ALKHAIRI. BANI DA KALAMAI KO
AZANCI DA ZAN IYA MUKU GODIYA DA SHI. SAI DAI KAWAI ALLAH YA BAR MU TARE.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~MUN TSAYA A INDA HAUWA TACE, "Aunty Asiya Wallahi bani bace aikin Fatima ne".
"Kuturun kareee! Wace Fatimar?". "Fatima tamu ta nan gidan mana". Cikin fusata Mama Asiya
ta nufi dakin su Fatima tana fadar. "Ina take dan ubanta Wallahi sai ta gyara dakin nan tsaf!".~
_Mama Asiya na shiga ta iske Fatima zaune a gefan gado ta juya mata baya. "Fatima!
Fatima!2×". Shiru fatima ko waigowa batayi ba. Kara matsawa wajen ta tayi "Ke dan iskanci da
rainin wayo kinaji ina kwala miki kira amma kikayi banza dani. Zonan dan ubanki". Gashin kan
Fatima ta kama ta jawo ta kiiii! Har cikin falo, "Maza jeki daukko kayan mopping kizo ki tattara
shinkafar nan da kika zubar ki wanke wajen miyar nan da kika zubda. Sannan in kin gama ki
daukko tsumma kizo ki matse wannan carpet din da kika zubda ruwa a kai". Harara kawai
Fatima ke binta da shi. Hauwa da Zuwaira dake zaune kan armchair tana wash-wash ba
abunda suke sai kallan Mama Asiya da fatima. Zuwaira fatan da take shins Allah yasa Mama
Asiya tayi ganganci wa Fatima._
_Duk maganar da Mama Asiya take Fatima ba abunda take mata sai mugun kallo. Mama Asiya
da ta gama jawabin nata ta juyo taga Fatima na hararen cikin fada tace "Ke Fatima ba magana
nake miki ba. Wallahi tallahi in raina ya baci bazaki ji dadi ba. Dan ba wanda ya isa ya kwace ki
a gidan nan...". Duka ta kaiwa Fatima dim! "Ni kike wa gatsine da uban ki. Bari ki gani".
Juyawa tayi ta dakko dorinar wajen Zuwaira. Fatima na ganin haka ta kyalkyale da dariya lokci
daya kuma sai ta hade girar kasa da ta sama. "Zaki iya duka na da bulala. Na baki offer nan.
Amma ki sani cewa duk bulala daya idan kika min ni goma zan miki". Mama asiya bata dakata
ba ta nufo Fatima tana zuwa ta lafta mata balula. "Wuce kiyi abunda na saki". Wani malalacin
kallo Fatima tsare mama Asiya da shi. Dan bulalar da aka mata sai ka rantse ba jiki aka daka
ba domin kuwa ko motsi batayi ba. Mama Asiya ta kara buga mata bulalar tana nuna mata
hanya da hannu._
_}"Ki wuce kiyi abunda na saki nace ko?". Zata kara mata ne Fatima ta rike bulalar. "Bulala
ashirin ya ishe ki dan wannan jikin naki ba lalai ya dauki talatin ba". Tunanii mama Asiya ta
shiga yi nazari take akan maganar da Fatima ta fada. Domin ita bata gane nufin ta ba. Tana
tsakar tunani sai ji tayi Fatima ta fisge bulalar daga hannun ta ta Zura mata._
_"Wai-wai wai.. Fatima ni kika dak..". Ai kafin ta rufe baki ta kara jin saukar wata bulalar. Hakan
yasa ta nufi Fatima da nufin ta kwace bulalar. Da gudu ta shige ta. Hakan yasa Fatima tayi
saurin gocewa kuma tasawa Asiya kafa. Rigijimmm! Kake ji ta Fatima. Su Zuwaira in banda
dariyau ba abunda suke yi. Sai dai kuma daga Fatima ta harare su sai kowacce ta matse bakin
ta. Fatima kan Mama Asiya taje tana Maka mata bulala tana kirge. "3..4..5..6..". Mama Asiya na
tashi ta kara nufar Fatima a fusace. Tana Zuwa kusan ta Fatima ta kara sa kafa ta hangiza ta
baya._
_Tagal-tagal ta tafi zata fada kan Coffee tabal din dake tsakar falo. Ganin in ta fada kanshi ya
gama aiki dake na Glass ne da sauri Fatima ta rike hannun ta. Ta mike tsaya. Ko da taga ta
mike sai taci gaba da dukan ta. Wannan karan Asiya da gudu ta hau zagaye falon tana neman
dauki. Fatima na binta tana zana. Duk wacce mama Asiya ta nufa. Hauwa ko Zuwaira sai su
arce a guje. Sai da Fatima tayi mata bulala ashirin cik!. Tukun ta zauna kan kujera tasa Mama
Asiya tayi Kneltdown a gabanta. Dage kai tayi gefe ta fara wa mama Asiya magana kamar
yanda tayi mata dazun._
_Cikin gadara fatima tace, "Maza jeki daukko kayan mopping kizo ki tattara shinkafar nan da na
zubar, ki wanke wajen miyar nan da kika zubda. Sannan in kin gama ki daukko tsumma kizo ki
matse wannan carpet din da kika zubda ruwa a kai". Jikin Asiya har yana rawa tace "To to an
gama ranki shi dade". Zuwaira da Hauwa sun jin haka suka nufi Hanya zasu tsere._
_Kan Fatima a kasa ba tare da ta dago ba tace, "Ku muna fukai na baku damar tafiya ne?".
Tsaye cik! Sukayi suna kallan juna. "Ku dawo nan ku tayata wannan aiki. Bari inje in siyo
halawa. Kuma saura inzo inga wata bata abun da na sata. Uhmmm Wallahi da jaki ma sai ya
tausaya mata". Fatima na fadar haka ta mike har ta nufi kofa kuma ta juyo. "Au! Ashe ba kudi a
guna". Kallan su tayi daya-bayan-daya Suma ita suka kwalalowa ido kamar wasu mujiyoyi. "Mai
nera dari ta bani kun wani kwalalo min idanu. To tubarkallah kuci kanku". Dajin haka suka shiga
raba idanu, Suna kallan junan su. "Kaaaaaaaaaaaaaa! Daku fa nake". Wannan muguwar
kuwwar ta daka musu wanda yasa duk sao da suka rufe kunnuwa. Dajin haka har rige-rige suke
wajen daukko kudin._
_Zuwaira ce ta fara kawo mata. Hannu na karkarwa kamar wacce ke rawar sanyi ta mika mata
hade da cewa "Gashi dari biyar ne ba canji". Wata muguwar harara Fatima ta bita da shi tukun
ta karbi kudin fuuuuuu! Ta wuce. Dai-dai lokacin Mama Asiya da Hauwa suka fito da sauri ko
wanne rike da kudi. Zuwaira ta juyo "kudin ku sun huta. ta ai ta tafi". Mama Asiya tayi ajiyar
zuciya hade da kallan su gaba daya "Shin mai kuka fahimta game da lamarin nan". Kamar
hadin baki su hauwa sukace. "Aljanar ce ta shige ta ba wani abu ba". Mama Asiya tace. "Haba
nima nayi tunanin haka. Ji yanda Yarinyar ta juye lokaci guda ta zama abar tsoro. Ai kuwa sai
munyi taka tsantsan domin Wallahi wannan zata iya sabauta mutum". "Ahh! Ni Zuwaira yau
naga tashin hankali. Gaskiya dole mu dauki matakin gagawa". Hauwa ce tace "Kunga Wallahi
gwara muyi abunda tace kafin tazo ta fatatake mu". Mama Asiya ce ta koma kan kujera ta
zauna._
_Da ganin haka itama Zuwaira ta je ta zauna. Hauwa tayi musu wani irin kallo a gantsare tace
"Shin me hakan ke nufi?. Ko kuna nufin bazakuyi aikin bane?". Su Mama Asiya kallo kawai suke
binta da shi. "Chabb! In kuwa haka ne Wallahi nima bazan yi ba. Gwara in Aljanar ta dawo tayi
mana koma miye a tare". Hauwa na fadar haka ta nufi wajen su ta nemi waje itama tayi
zamant...................................................._
Kuyi hakuri da wannan kuyi min afuwa. Wallahi sai da karume-karume nayi type din nan.
Sai na fara sai kawai wani uzurin ya zo. Yanzu haka wani abokina ne ya kawo min ziyara.
I'm busy
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA.
SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN
KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 99-100
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
_*WANNAN PAGEN NAKA NE AUTAN ELOQUENCE. ALEWAR KANKANA MELODY*_
_Ku bani kidan birthday a sama._
Autan- Eloquence, Kuce min Auta Eloquence Today is u birthday Today is you
birthday .
*HAPPY BIRTHDAY MUSA MELODY AUTAN ELOQUENCE*
_Happy birthday Melody wish you many more Albarkakun years head_
Allah ya yafe maka zunubanka na shekarun da suka wuce. Kuma allah ya baka wasu shekarun
Masu albarka
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~"Chabb! In kuwa haka ne Wallahi nima bazan yi ba. Gwara in Aljanar ta dawo tayi mana koma
miye a tare". Hauwa na fadar haka ta nufi wajen su ta nemi waje itama tayi zamant.~
_*M*ama Asiya na ganin hauwa ta zauna sai tace, "Haba hauwa wai ke a zatan ki bazamuyi
aikin bane?. Haba mu mun isa. waya isa yaki yi aljana ta zo ta karyashi. Kinga dama ni jira nake
ki daukko kayan ne fa". "Yauwa nima abunda na gani kenan". Cewar Zuwaira. Hauwa tace "To
ai da na dauka nufin ku bazakuyi ba ne". Fita tayi ta kwaso kayan mopping Har su tsintsiya da
abun kwashe shara. "To ku tashi gashi na daukko". Mika mama Asiya tayi "Wayyy! Wallahi ni
kam duk na gaji please dan fara. Kafin in taso". Zuwaira tace, "Ashe bani kadai ba gajiyar nan.
Kinji kuwa yanda kuguna yake kamar zai balle"._
_Cikin hantara "Dallah yi min shiru muguwa kawai. Ai ban taba sanin ku mugaye bane
azzalumai yan bakin ciki sai yau". Kallo suka tsare ta da shi, Yayin da ita kuma taci gaba da
magana. "In ba zalinci ba kunsan cewa Yarinyar nan Fatima ba lafiya lau take ba, Kuna ganin
zan mata ba dai-dai ba amma kuka ki dakatar dani...". Tun kafin ta krasa maganar Zuwaira ta
karbe ta da cewa "Wannan kuma Hauwa zaki cewa muguwa. Domin tun farko ita tasan cewa
Aljanu sun shiga jikin Fatima amma taki wa mutane magana".Yar dariya Hauwa tayi hade da
cewa, "Daga baya kenan. Ku tashi muyi aikin nan tun wuri Wallahi". Ganin basu da alamar tashi
ita ma hauwan ta zauna hade da cewa "Wallahi bazanyi sharar nan ni kadai ba. Gwara in ta zo
ko kashe wa zatayi ta kashe mu tare"._
_"Kanki ake ji". Cewar Zuwaira. Zaune suke kowa da tsoro a zuciyar shi, amma cikin su ba mai
so a gane yana jin tsoran. Karar bude kofa sukaji. Ai kafin kace kwabo, Tuni ko wacce daga
cikin su ta tashi da sauri ta dauki abun ta fara aiki. Su Asmart ne suka shigo gidan. Su mama
Asiya na ganin su. Kowacce ta yarda abun hannun ta ta koma ta zauna. Mtsweeee!
Mtsewwww! Mtsewww Sautin tsaki kawai kake ji yana tashi. Su Nasmat kuwa mamaki ne ya
cika su. Daga shigowar su sunji an tarye su da tsaki. Har sun nufi dakin su Zuwaira ta kira su.
"Kuyi sauri ku cire uniform din islamiyar nan kuzo ku share gurin nan". To suka ce ciki-ciki suka
wuce suna gun-guni. Bayan sun fito ne suka kama aiki, Fuskar su ba mai annuri kamar ta
shanu sai gunguni suke. "Wai daga dawowar mutum daga makaranta ko hutawa baiba a saka
shi wani shar...". Shigowar Fatima ya hana Asmart karashe maganar zucin da take._
_Lollipop ne a bakin ta yana tsotsa ga wani biscuit a hannunta. Su mama Asiya gaba daya sun
tsorace dan Zuwaira har yar karkarwa take. Nasmat tace "Wannan Yarinyar kuma uwar wa ta
bata kudi har ta sayi wannan katan biscuit din?". "Uwarki ce ta bata". Zuwaira ta bata amsa.
Shiru tayi tana kallan uwar tata da duk ta lura da yanayin ta a tsorace take. Asmart tace "Ke
Fatima zo nan dan ubanki ki share wajen nan kal!, ki goge". Da sauri Mama Asiya tace "Sai dai
ni uwar ki in share". Da fadar haka su Asmart suka fara tunanin akwai lauje cikin nadi. Fati dake
bin su Zuwaira daya bayan daya da harara sai yanzu tayi magana tace wa su Asiya "Ku ku tashi
ku tafi abun ku". Har rige-rige suke wajen tashi. Zuwaira har ta kusan zuwa Stairs ta juyo.
"Uhmmm! Fatima chanji na fa". Cikin gadara Fatima tace, "Na bawa almajirai sadaka. Ko da
magana?". "Aa"._
_Zuwaira tace ta wuce sama da sauri Fatima rufe ido tayi kamar me gyangyadi. Cikin tsawa
Asmart tayi magana "Ke Fatima in kika yarda na karaso wajen ki wallahi sai kin raina kanki".
Shiru bata bude ido ba balle tayi magana. Nasmat dake kallan tace, "Ke wai ba magana ake yi
miki ba?. Kin wani rufe ido kamar kazar dake gwaida". A fusace Asmart tayo kanta da nufin ta
dake ta._
_Fatima na bude ido tayi turus! Asmart taja birki tayi baya a guje. Haka itama Nasmt bata san
lokacin da ta tsallake kojera ba ta wuce. Kofar dakin su sukaje zasu shiga kenan sukaji an turo
kofar da karfe. Ba komai ne ya tsorata su ba. Idanun Fatima ne suka koma baki kirin gashin
kanta ya wani mimike tsaye. "Ku dawo ku share gun nan. Ina zaku?". Suna karkarwa hade da
kankame juna suka juyo. "ba inda zamu". Cikin tsawa tace suzo su share gun. Da sauri suka
taho suka hau aiki. Rufe ido Fatima tayi ta sake bude wa nan take kuma idanun ta suka dawo
Normal. Su Asmart sai shara suke suna goge carpet ita kuwa Fatima ta mike kan Sofa Sweet
take sha abunta tana wasa da Biscuit dinta. Abba ne ya shigo yana jin waka._
_Ganin su Asmart na aiki Fatima a kwance ya daka mata tsawa wai ta tashi ta taya su aikin.
Fatima ko kallon shi batayi ba. Su Asmart ne suka ce yaje ba komai zasu karasa aikin. Washe
gari da safe. An zuba wa kowa abun kari Indomie da biredi sai tea. Asmart da Fatima gefan su
guda. Fiddausi da amira ma. Haka suma yan kanana yaran. Sai abba da ya dawo falo ya zauna
a nan yake break din. Fatima ce ta fito daga dakin su ta nufi Dinner. Bata wani tambayi ina
abincin ta ba taje ta dauke Tea da indomie na gaban Mama Asiya. Da ganin haka Abba ya daka
mata tsawa. "Ke dan ubanki sa'ar kice da zaki daukar mata abinci". Wata muguwar harara ta
watsa mishi. Hade da murguda baki "Nata nake so kuma shi zanci in ka isa ka hana. Kuma ko
da naka naga damar ci shi zanci". Fatima ke kallan shi tana maganar. Tashi yayi ya nufi dinner
din a fusace._
_Mama Asiya kamar ta dakatar da shi kuma wata zuciyar sai ta bata shawarar cewq ta barshi
watakil Aljanun Fatima mata kawai suka raina. Abba yana zuwa ya daga hannu ya kai mata
mari, cikin