Showing 99001 words to 102000 words out of 103342 words
Chapter 34 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
Nan ya karkace hula ya fara zabga musu karya wai
ai Aljanu ne sukaci addu'ar da yayi ne ya manta baiyi bismillah ba shiyasa wai Aljanun da suma
zo ci basu makale ba. Su Asmart najin haka suka kyal-kyale da Dariya. Su mama Asiya suka
tambaya me suke wa Dariya. Basu bada amsa ba suka ci gaba da dariyar hakan yasa Zuwaira
taji haushi ta kora su da gudu suka koma falo suna daria. Nasmat taks cewa Asmart ita gaskiya
bata yarda da mutumin nan ba.wai tana zargin ko ba malamin gaske bane. Asmart kam cewa
tayi, "Au ke ashe zargi ma kike?. Kina gani fa gashi kiri-kiri ya maka karya. Wai yace Aljanu
sukaci abincin bayan kuma mu muka ci". Nasmat ta kyalkyale da Dariya Dariya tace,"Watakil
mune aljanun". Asamrt tace,"Yanzu mu rufa mishi asiri ne ko kuwa?". "Kyale shi muga iya
gudun ruwanshi tukun. Ba dai yace zai cire Aljanun Fatima ba yau". Dariya Asmart tayi hade da
cewa."Ai kuwa dai mu rufa mai asiri zuwa goben mu gani"._
_Acan kuwa su amam asiya suka cewa malam ya yake ganin za'ayi. Ce musu yayi shi yasan
yanda zaiyi wai in ya kama aljanun Fatima zasu kawo mai sauran. Falo suka dawo aka kawo
mishi abinci nan ma yace ya koshi wai Aljana ta kawo mishi yaci. Fatima yasa aka kawo mai
gaban shi nan yata tofe ta da miyau kallan shi kawai take yi tana hararen shi ba tare da tayi
magana ba. Da abun ya bashi haushi sai ya fara kashe ta da mari yan cewa tayi magana. Su
mama asiya suke cewa mai yasa yake dukan ta. Sai yace musu ba ita yake duka ba Aljanun ne
wai dama yasan sai sun mishi garda. Nan yata jifgar Fatima amma taki cewa ko uffan!. Wajejan
karfe goma na dare Aliyu yace a kai Fatima daki domin a can zaiyi aikin kuma yace a daren duk
tauri kan aljanun sai ya cire su. Daki aka kai ta ya shiga ya kulle bayan yace wa kowa ya shiga
daki ya rufe. Bayan Ya musu gargadin kar wanda ya fito ko da fitsari ne. Gado ya dale abu shi
ya kalle Fatima dake tsaye tana zare mai idanu yake ce mata in kinga dama ki zauna ko ki
kwana a tsaye ma ni ba ruwa na. Barci yake abun shi har da munshari. Can cikin barci yayi
mafarkin wasu mugayen halitu masu ban tsoro gasu da girma sukata tsorata shi suna firgiya shi
daga karshe suka kai shi wajen wata yarinya da ba kai a jikinta sai iya gangar jikin. Hannun ta
rike da wuka._
_Ko da yaga haka sai tsoro ya kara kama shi. Wannan halittun suka kai shi gaban ta bata jira
komai ba ta daga takobin ta jaka mai a ciki. Da cakawa ya farka firgigita. Ya tashi da ihu mai
makon yayi addu'a. Fatima ya gani tsaye yanda ya barta lokacin da ya kwanta har yanzu haka
take bata ko motsa ba. Kasancewar dakin da hasken dake akwai nepa. Ya kalli agogon dake
makale a bangon dakin yaga karfe biyu. Ya juya gax. Fatima da niyar yi mata magana. Wayam
yaga wajen ba kowa. Dube-dube ya kamayi. Ya sakko kasa yan kiran sunanta dake yaji an
fada mai. Ya duduba duk inda yake tunani bai ganta ba. Sai karkashin gado. Yana lekawa da
nufin yaga ko ta na nan yaji an rike mishi kai. Ihu! Ya farayi yana neman agaji. Jan kan nashi
ake shima yana iya kokarin shi yana neman ya kwace amma ya gaza. Sai da yasha wuya sosai
tukun aka sake shi. Da sauri ya yashi ya koma kan gado ya lulube da bargo yana lumfashi
day-day. Dif! Yaga wutar dakin ta dauke. Nan take kuma yaji dakin ya gauraye da wata
ibilishiyar dariya wacce kunnuwanka bazasu iya sanar da kai inda take fitowa ba. Domin in kaji
Dariyar sai kace gaba daya ma dakin ne da kanshi yake dariyar. Ga dariyar ba dadin saurare.
Aliyu yasa hannuwa ya toshe kunnuwa hade da kara dukun-kunewa. Kiii! Yaji an kama kafar
shi an jawo shi kasa cikin duhu ya mike tsaye yana lalube-lalube. Can yaji ya dafo wani abu
kamar mutum mari aka dauke shi da shi wanda karfin marin yasa har sai da ya wuntsila. Ihu!
Ya kwalla mai uban kara ya fara bada hakuri. Wata dariyar ta kara kaurade dakin. Ba tare da
hasken dakin ya dawo ba ya kara mike wa tsaye. Kamar iska ya kwashe shi yaji an maka shi
da bango. Kafin ya yunkura ya dawo yaji an kara fisgar shi an maka da kasa. Ji yayi kamar
bayanshi ya karye. Ihu ya fara kwallawa va kaf!-kaftawa su Zuwaira na dakunan su sai da karar
ihun ya tashe su. Su kuwa basu kawo a ransu cewa malam ne ke ihu ba. Su wai zatan su aljanu
ne. Hakan yasa suke kara dukunkunewa.........................................................._
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA.
SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN
KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
*Before last Page 112-113*
© *KING BOY ISAH* ✍
. .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍ *®Z.W.A* .
. .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
_*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
_*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_
Zamaniwriterassociation@gmail.com
❤ DEDICATED TO MASOYAN LABARIN *ALJANAR FATIMA* ❤
Kun taka rawar gani a yaba ba kadan ba. Masu bibiyar labarin nan. Dole nayi jinjina na
kuma yi muki fatan alkhairi masoya na. Hakika in baku bazan iya ba. Allah shi bar kauna.
Safuratu na bankwana *HAUSAWA NA CEWA A JURI ZUWA RAFI. WATARAN TULU YA
FASHE.*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ihu ya fara kwallawa va kaf!-kaftawa su Zuwaira na dakunan su sai da karar ihun ya tashe su.
Su kuwa basu kawo a ransu cewa malam ne ke ihu ba. Su wai zatan su aljanu ne. Hakan yasa
suke kara dukunkunewa.~
_Haka Fatima taci gaba da tsorata malam Aliyu tana bashi wahala. Kafin safe sai da ta sumar
da shi.Har Waje-jen karfe bakwai su mama Asiya basuga malam ya fito ba balle suji ya akayi.
Nan wasu ke cewa aje a bude a gani. wasu kuwa cewa suke abar shi watakil aikin ne bai gama
ba. Suna zazane a falo bayan sun karya sai ganin Fatima sukayi ta fito daga dakin ranta a
bace. Fuskar ba wal-wala. Batayi wa kowa magana ba. haka kuma ba wanda yayi mata
magana, Taje ta shiga dakin su jimawa kadan sai ta fito. Tana zuwa ta makore wuyan mama
Asiya da karfe. Ba tare da tace mata komai ba. Mama Asiya tayi iya kar kokarin ta ta kasa
kwabcewa. Sai da ta nemi agaji tukun da kyar sauran jama'ar suka kwace ta. Ana kankare ta
daga nan ta sake shake wuyan Hauwa nan ma da kyar aka kwace ta. Nan fa ta shiga layi daga
an rabata da wannan sai ta malale wa wannan. Kuma shakar da take bana wasa ba._
_Dan ji zakayi kamar wani Rikakken gardi ne ya shake ka. Kuma kafin a kwace kaji jiki. Da gudu
su nasmat suka fita waje aka nemo mutane. Aka daure Fatima da kyar. Domin su kansu masu
daure tan sunji jiki. Wasu duk tajiji musu ciwo. A nan falo aka hadata da karfen jikin Matatakala
(Stairs) aka daure ta. "Duk sai na kashe ku ranar da na kunci". Abunda ke fita daga bakin
Fatima kenan. Bayan hankalin yan gidan ya dan kwanta ne. Su mama Asiya suka tuna da aliyu.
Da sauri suka nufi dakin kwance suka tarar da shi har lokacin a sume. Aka kawo ruwa aka
yayafa mishi a firgice ya tashi yana raraba ido. Yana mikewa ya zabga a guje Kamar wani
sabon mahaukaci. Ana kiran shi ko waigowa baiba. Da ya isa falo yaga Fatima a daure na
hararen shi sai ya kara kaimi wajen guduwa. Asmart da Nasmat dariya kawai suke su. Zuwaira
ta daka musu tsawa take tambayar su miye na dariya. Nan suke gaya wa mutane cewa Da gani
Aliyu malamin karya ne. Nan suke fadar cewa su suka ci abincin da Aliyu yace Aljanu ne suka
ci. Sallalami su Asiya suka kwasa. Zuwaira ke cewa in kuwa haka ne sai sunyi maganin Nafisa.
Asiya tace "Ai ba wani ba wata zuwa zamuyi ta biya mu duk kudin da muka kashe kawai"._
_Zuwa sukayi suka same ta da masifa. Da kyar suka kankaro dubu uku a gunta. Haka Fatima ta
kasance a gun a daure abinci ma hanata suka ringa yi sai dai fiddausi ta bata a sace. Abba
kuwa har yanzu hannnun shi daya a makale. Sunyi-sunyi Fatima taki gyara mai hannu. Su
Asiya duk a tsorace suke kullum fargabar kar Fatima ta kunce suke. Dan suna shan barazana
da kashe di a gunta. Domin cewa take in dai aka kunce ta sai ta kashe mama Asiya Zuwaira da
Hauwa. Hakan yasa ma suka gagauta kiran alhaji. Cewa yayi sharri suke mata. Hankalin shi bai
tashi ba yaji ya matso ya dawo gida sai da yaji sunce sun daure Fatima. A lokacin ne yaje ba
abunda yake so sai gida. Yau take juma'a ranar da Alhaji zai dawo. Tun da safe akata
shirye-shirye aka gyara gidan tsaf!. Safiyanu da matar shi da yaran su uku sunzo. Haka ma
Yusuf shida matar shi. Kowa yaci kwalliya in banda Fatima dake daure. Su Safiyanu da basu
san me ke faruwa ba sai a lokacin suka tambaya mama asiya ta zauna ta shirya musu karya da
gaskiya._
_Abba murna yake sosai domin yasan in dadyn su yazo dole Fatima ta mikar mai da hannu.
Tun wajen sha biyu su Safiyanu suka yafi airport domin tarbo Alhaji. Sai wajen karfe uku jirgin
su ya karaso. Suka runkuto a mota suka taho gida. Ba abunda yake tambaya sai Fatima. Haka
da suka shigo gida duk iyalai sun fito kofar gida cik da farin ciki. Shi kanshi yaji dadin irin taryar
da aka mai a tafiyar yan watanni kamar yaje yayi wani shekaru. Abunda ya rage mai farinciki
shine kawai da baiga Fatima ba. Aliyu da Abdul suka shiga jidar kayan da Alhaji ya kawo suna
shiga da ita. Alhaji na shiga falo sukayi ido hudu da Fatima dake daure jikin karfe. Ta fashe da
kuka hade da fadin "Dady kaga yanda suka daure ni ko?". Hankalin shi a tashe ya nufe ta
tausayi ya kama shi kamar ya fashe da kuka. Nan take yaji wani irin haushin su Mama Asiya.
Kunce ta yaje ya farayi. Mama Asiya Zuwaira da Hauwa. Hankalin su yayi matukar tashi ganin
abunda Alhajin ke shirin yi. Asiya da sauri tanufo shi tana hada shi da Allah karya kunce Fatima.
Tsawa ya daka musu hade da cewa "mutanan banza marar tausayi. Wato abun naku har ya kai
ku daure ta dan kunga uwar ta ta mutu ko?". Zuwaira da hauwa suma magiya suke binshi da shi
akan ya hakura karya kunce Fatima ya saurare su amma. Yaki. Yana kunce Fatima ya warware
mata igiyar dake jikin ta. Nan take suka rungume juna. Alhaji Salim tsabar tausayi sai da ya
zubar da hawaye. Safuratu na ganin an kunce Fatimar sai ta koma jikinta. lokaci daya Alhaji yaji
Fatima ta zabura ta kwace jikinta daga jikin shi kamar wacce aka tsinkula. Nan take idanunta
sukayi jajur kamar wacce ta kwana tana kuka. Da gudu ta nufi kitchen kamar wata
mahaukaciya. Bata jima ba akaga ta fito hannunta rike da wukA._
_Da gudu ta nufi su mama Asiya. Sa ganin haka sukayi waje da gudu. Fatima ta bisu. Alhaji
Safiyanu da yusuf da sauran matasan da gudu aka bi su. Sai da kyar aka samu aka rike Fatima
su mama Asiya kam har sun kusa fita daga layin sai da sukaga lala-lalai an rike ta an kwace
wukar tukun suka juyo. Kusan karti biyar ne ke rike da Fatima amma sai juyasu take kamar
wanda suka rike giwa. Hankalin Alhaji a tashe yasa aka nemo masu Ruq'yah. Bai wani bata
lokaci ba malamin mai suna Bashir Halilu Tabiyyah. Ya karaso. Yana shiga ya tarar sai fama
ake da Fatima ana rirrike ta. Kai tsaye ya nufi gunta ya tofa mata wasu addu'o'i. Yace su sake
ta. Ba tare da gardama ba suka sake ta. Sunyi mamakin ganin ta tsaya cik ta natsu. lokacin su
mama Asiya suka shigo. Kukan kura tayi ta warci wuka ta
nufe............................................,..................._
Komai yayi farko zaiyi karshe ♂♂
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA.
SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN
KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
*THE END*
© *KING BOY ISAH* ✍
. .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍ *®Z.W.A* .
. .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
_*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
_*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*JIJINAR BAN GIRMA GA MAKARANTA LABARIN NAN. KAMAR YAU NE NA FARA DA ONE
PAGE YAU DAI GANI A END*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ba tare da gardama ba suka sake ta. Sunyi mamakin ganin ta tsaya cik ta natsu. lokacin su
mama Asiya suka shigo. Kukan kura tayi ta warci wuka ta nufe.~
_Su Mama Asiya. Da gudu suka koma. Malam yayi caraf! Da Fatima. Nan take ya fara tofa
mata wasu addu'o'i shiru tayi tana kallan mutane. Malam ya mata karatu cikin kunnenta na
hagun. Tukun ya dafa kirjinta yaci gaba da karanta ayoyin ruk'yah. Ji sukayi ance "Dakata
malam ni ba azzaluma bace". Cikin bacin rai malam yace, "Ke kuwa ce azzaluma tunda gashi
kin shiga jikin yar karamar yarinya kina kuma yunkurin kashe wasu". Aljanar tace, "Kwarai na
shiga jikin Yarinya kuma hakan kariya ne daga wadancan azzaluman matan ubanta. Domin in
ban kashe su ba su zasu iya kashe ta ita". Tsuru aka zurawa Fatima ido da bakinta ne kawai ke
motsi amma ba ita ke maganar ba. Alhaji har rawar jiki yake domin sosai yake san Fatima. Nan
malam yasa aka kirawo su Asiya a tsoarace suka zo suna baya-baya da Fatima wacce sai
hararen su take kamar idanun zasu fado kasa. Malam yace wa Safuratu me su Asiya sukayi wa
Fatimar na zallunci. Bata boye komai ba duk ta kwashe abubuwan da su Asiya da 'yav'yan
sukayi wa Fatima ta fada. Malam ya juya gare su ya tambaya haka ne. Jiki a sanyaye ta amsa
cewa eh duk abunda ta fada gaskiya ne. Alhaji a zuciye ya nufi Asiya da niyar ya dake ta yana
fadin "Amma Asiya kin cika macuciya maciya amana. Amanar ma ta marainiya kuma yarinya".
Ba dan malam ya dakatar da shi ba kuma ta gudu da sai ya ji mata ciwo. Nan malam ya
kwantar mishi da hankali ya kuma ga Safuratu yake tambayar ta ta yaya akayi ta zo gidan har
take taimakawa Fatimar. Bata boye musu komai ba ta sheda musu cewa wannan aikinta ne. Ta
dade tana irin taimakon nan da sasanta matsalolin ma'aurata. Gaba dayan falon sunyi mamaki
malam yake tambaya. Shin a kwai irinta ne dama a cikin Aljanu. Tace ita dai bata sani ba amma
tasan cewa. Ba duka aka zama daya ba._
_Malam ya tambaye ta a kan me yasa take irin wannan taimakon. Tace "Dogon labari ne amma
dai bari in baku shi a gajarce yanda kuma zaku fahimata. Uwata da ubana mutanen kirki ne a
cikin mu aljanu tun kafin a haife ni a kasarsu wani babba daga cikin aljanun shi ne abun bautar
su. Wata rana sai sani Aljani wanda shi ya kasance musilmi ne. Yaje garin bisa batan hanya. Da
yaje kasar kuma mahaifina ne mutum na farko da suka fara haduwa da shi. Kuma shi ya sauke
shi a agidan shi. Ko da lokacin sallah yayi. Ya tashi yayi su sai suna kallanshi ba tare da sun ma
san ko me yake ba. Bayan ya gama sallar yaga sun tsura mai ido basu tashi sukayi sallah ba.
Da ya tambaye su sai suka nuna basu ma san me yayi ba. Nan suke fada mai su ai shugaban
su suke bautawa. Natsuwa yayi ya musu bayanin Islam sosai kuma suka fahimata suka