Showing 75001 words to 78000 words out of 103342 words

Chapter 26 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5028

kalle ta a zuciya yace " Wai wannan mata ta ce. Bata ma lura
da irin halin da nake ciki ba". Hawaye ne suka gangaro mai a fuska. Murja ganin taji shiru yasa
ta kalle tana ganin hawaye a fuskar shi cikin kwaratsi tace. "Dole ka zubda hawaye. Wai ance
Saurayin budurwarka ya mutu. Kukan munafurci kenan ma to wallahi baka isa ba malam. Yau
naga sadodo wai harda kirkirar hawaye, Eh lalai Malam Mukhtar zaka iya film daga bani kudina
sai hawaye to a nufin ka. In durkusa gabanka ina share ma hawayen ina baka hakuri ince
kabar kudin ko yaya?. To Wallahi bari kaji yau in baka bani kudina ba bar ganin dare yayi
wallahi sai na dauki wani abu naka wanda yayi kudina na sayar na dauki kudina". Mukhtar
magana kasa-kasa yace "Haba murja me yasa kike haka ne. Baki san damuwar mutum ba kizo
ki kara mai wata damuwa. Ko so kikr hawan jini ya kamani ne in fadi in mutu". "Wannan kuma
kai ta shafa. Ni kudina kawai nake bukata in baka bani ba kuma kaga tashin hankali harda
rufu'a Wallahi". Muktar yace "Murja An sace napep din da na daukko sojan haya". Murja ta
dan sasauta murya kamar abun kirki. "Kaico! Napepk din aka sace ashe ai ni baka gaya min ba

tun da wuri in maka jaje. Allah yasa a ganta ya tsare gaba. In ba'a ganta ba Allah yasa mai ita
ya maka afuwa". Mukhtar yace "Amin yanzu abun..". Kafin ya karasa ta taryi nunfashin sa. "To
an sace napep nayi maka Jaje kumaa gode wa Allah da ba kudina ne a ka sace ba. Da danaji
kana zancen sacewa har gabana ya fara dukan uku-uku na dauka kudina aka sace. Tunda
basu ne ba Alhmdulilah. bani kudina in adana kar suma garin sakaci irin naka kaje a sace. Atoh!
Wanda ya bari aka sace napep ai kudi bazasuyi wahalar sata a gunsa ba. Bani kudina malam"._






_Maganar tayi mugun bata wa Mukhtar rai ji yake kamar ya tashi ya hauta da duka. Matsalar
daya yasan ba abunda zai dauka a jikinta. In ma fadan ne bata kashi za'ayi. (Ragas).A
zuciyarsa yake tunani cike da tsanar murja "Wannan wai wace irin mata ce. Anya kuwa Murja
ba shedaniya ce ba. Kai ai ko shedan ne ke bina kudi na gaya mishi abunda ya faru ya daga
min kafa...". Shirun da taji yayi yana tunani ta wani daka mishi tsawa. "Kai malam ka bani
kudina wallahi tun muna sheda juna". Nan ma shiru yayi dan yama rasa abunda zaice mata.
Kukan kura tayi ta chakumi wuyan rigar sa. Ta fara magana dan masifar kamar mai shirin yin
kuka gashi da karfi take maganar. "Mukhtar yau fa ba mutun ci Wallahi sai ka biyani kudina. A
take a nan ko kuwa yanzu in maka lahani Wallahi". Mukhtar kokarin kwacewa yake daga
shakar da tayi mishi amma ya gaza. Murya a makure yace. "Sakarni ni yanzu ba ko kwandala a
jikina in na saaamu zaaan baaki". Maimakon ta sake shi sai ma ta kara shakar shi. Nan shima
ya fara kokarin shake nata wuyan jin tana kokarin ta kar shi. Amma ina ya shaketan amma a
banza. Ihu! Ya fara kugawa. Wani makwabcin su ne ya shigo sa gudu yazo yaga abunda ke
faruwa dakyar ya kankare mukhar a hannun Murja. Nan ya tambayi murja me ke faruwa ta gaya
mishi. Tambayarta yayi nawa ne kudin tace dubu biyar. Da sauri Mukhtar yace karya take hudu
da dari biyar ne. Ibrahim ya zaro Dubu biyar ya mika mata. Yana bata Mukhar yace "An biya ki
kudin ki to na sake ki saki daya. Zama dake ai bala'i ne". Murja cikin nuna rashin damuwa ta
wani jujuya kudin dake hannunta tayi guda yiiiriiyirri. "To dan ka sake ni sai me. Kai ne a kasa
wallahi domin nice rufin asirin ka kuma dan kaji in gaya ma saki daya ba inda zani. In ka cika
dan halak ka karashe biyun". Mukhtar har ya daga baki da sauri Ibrahim ya rufe mishi baki da
hannun yaja shi waje. Nan suka bar Murja nata masifa. Duk abunda ya faru Umar na gani sai
dai bashi da ikon rabawa ko magana domin yana cikin plan din Aljana._


********************
_Lokacu misalin karfe takwas na dare ne amma shiru kake jin dajin in ba kukan tsuntsaye ba
shima ba sosai ba. Kasancewar ba farin wata rudum! Wajen yake duhu in kana tsaye bazaka
ga abunda ke kasa ba. Muhisan da rafson ne jingine da yar kurkurar ba abunda suke sai busa
sugari. Can kuma Rafson ya kalli Muhisan yace "mu tafi yanzu mana". Muhisan yac "Kai
mahaukaci ne naga alama. Yanzu fa dare baiyi ba bar ganin duhun nan sauyin yanayi ne yanzu
haka ko tara batayi ba". Shiru Rafson bayi magana ba. Daga cikin Napep din Aka zuro hannu

aka dan ja kunnen Muhisan. A fusace ya juya ga Rafson yana mishi jaraba wai ya daina kama
mishi kunne. Shi kuwa yace baima san anyi ba. Kafar Rafson yaji anja daga kasar napepk din
da sauri ya janye kafar hade da cewa "Baabah akwai matsala fa. Kafata naji ana ja daga
karkashin nan". Muhisan yace "Kai dallah can rufe muna baki to me kake nu..". Kafin ya rufe
bakin yaji anja tashi kafa"Kuturun uba! Bari inga uban miye ke ja min kafa". Durkusawa yayi da
nufin lekawa Wani abun kulli aka mai a duron baya wanda ya bada sauti Dum!. "Kai! Kai! Yau
banga mai hanani inci kut... Ubanka ba a jejin nan. Me nayi ma da zaka min dundu"?. Muhisan
ne ke fadar haka yana dagowa ya wanka wa Rafson mari shima kuwa ya rama nan fa suka hau
kunce. Shuuuuuuuuuu! Sukaji wata irin kara mai karfi ta nufo gunsu. Tsayawa sukayi da kuncen
suka fara waige-waige_



_Ji sukayi an watso musu wani abu kamar ruwa. "Kai waye ke watso mana ruwa?". Suka fada
cikin hadin baki. Muhisan yaji abun da dan danko hakan yasa ya fiddo leta ya danna. "Jinine
yaseen". Abunda ya furta kenan. Da sauri Rafson ya matso kusa. Yana ganin jinin sai suka hau
dube-dube wata kururuwa sukaji marar dadin ji a bayan su da sauri suka waiga gefan. Wani
katan abune ga dukan alamu baki ne. Idanunsa kawai suke hangowa masu kamar singnonin
mashin abun ya durfafo su yana wani irin gunji. Da gudu suka fada napepk nan fa sukayi
sukayi ta tashi amma taki. Ga abun na kara kusantowa karar shinna cika musu kunne. Da dai
sukaga bazata tashi ba sai gaba daya suka fita suka runtuma a guje._




_Gudu suke sosai a birjin hasken da suka ga ya nufo su a baya yasa su juyawa. Napep din ce
ta nufo su ba kowa a ciki. Da ganin haka suka kara kaimi wajen gudu. Basu ankara ba sai gani
wannan Bakin Aljanin ya duro a gaban su kamar an cillo shi yana musu wata iriyar dariya mai
karfi ga rashin dadin ji a kunne. Wata uwar turjiya suka ja gaba dayan su sai da suka fadi domin
tsayuwa ce bata san rai ba. Sunyi yunkurin tashi kenan sai ganin wanna aljani sukayi a gaban
su. Abunda ya kara tsoratu su kenan. Cikin murya marar dadin ji yace. "Kuje ku shiga mu tafi".
Tashi sukayi suka shiga napepk din jiki na karkarwa. Ba tare da sunga mai tukin ba sukaji anja
napep din a guje. Ihu! Suka fara yayin da wata murya ta mace tace "Kuyi mun shiru barayin
banza". Shiru sukayi haka napep tata shara gudu har suka kusan isowa gari inda suka tarar da
wani gate na yan sanda masu binciken motoci a hanya. Haka suka bi layi ana ta bincike ana
zuwa kansu dan sandan yaji ance. "Barayi ne na kawo muku ku hukunta su". Dan sanda ya
bata rai hade da cewa su Rafson kai ku fito dan ubanki. Fitowa sukayi ya ja su har wajen
ogansu dake can zaune kan benci. "Yallabai ga wasu yan iska nan. Wai mu suke cewa su
barayi ne. Wasa suke da hankalin police sir!". Ogan harara ya gallawa su Rafson yace "yan
iska dama daga ganin ku yam shaye-shaye ne dan...". "Nice nan na kawo chu bachu chuka
kawo kanchu ba". Wata yar Yarinya ce wacce bazata wuce shekara 4 ba ta bayyana a gaban
su sanye da bakaken kaya idadun ta manya sun wuce kima. Gata baka. Ai kafin ta rufe baki
tuni Ogan yan sanda ya wuntsila daga kan bencin yayi kundunbala ya tashi ya zabga a guje

haka suma duk sauran yaran shi da su Rafson kowa ya kama
gabansa........................................._


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy






��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 85-86


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*

� DEDICATED TO YOU �

My Dear �� *Queen Hauwa Haucy* ��

Na yabba da kaunarki gare ni. Bansan da wanne irin kalamai zanyi amfani wajen yaba miki
da godiya a gare ki.

Sai dai ince Allah ya barmu tare Allah kara basira da daukaka na gode matuka da irin Kaunar
da kika nuna min. ☺

*A PAGEN DA YA GABATA CIKIN LITTAFIN ALJANAR FATIMA. LOLZ* �
~Wata yar Yarinya ce wacce bazata wuce shekara 4 ba ta bayyana a gaban su sanye da
bakaken kaya idadun ta manya sun wuce kima. Gata baka. Ai kafin ta rufe baki tuni Ogan yan
sanda ya wuntsila daga kan bencin yayi kundunbala ya tashi ya zabga a guje haka suma duk
sauran yaran shi da su Rafson kowa ya kama gabansa.~

_*M*ukhtar da Ibrahim suna fitowa Ibrahim ya bada shawarar suje police. Haka suka dunguma
suka nufi police din suna cikin tafiya kawai Mukhtar ya hange napepk dinshi anyi parking dinta a
gefan tati. Da ganin haka ya ruga da gudu cike da zubudi yaje yana lalekawa yana fadar
"Wallahi itace"2×. Umar Safuratu ya ga ta leko daga cikin napep din tace ya shiga. Dajin haka
yaje ya shige napepk din. Mukhtar sai murna yake ya shiga gidan baya yana duduba wani abu
sai ji yayi anja adai-daitar a guje. Nan ya fara kwalla ihu yana neman agaji. Ba abunda ya kara
tsorata shi sai ganin ba driver napep din ita kadai kejan kanta. Ibrahim yayi kokarin ya sama
abun hawa ya bisu amma ina. Lokacin da ya samu ya tsayar da wani mashin su tuni har sun
bace mai baima san inda sukayi ba. Safuratu bata tsaya da napep din ba sai a kofar gidan
Umar da isar su ta sauya zuwa yarinya. Ta kuma bawa Umar wata koya tsanwa yana sha sai
gashi ya bayyana. Mukhtar tsoro ne ya kamashi dan ya gane Aljanar gidan Umar ce. Safuratu
tace mishi ya fito su shiga daga ciki nan fa ya fara kakafe wa. Umar yayi iya bakin kokarin shi
amma Mukhtar yaki yarda ya shiga gida. Abun ne ya bawa Safuratu haushi. Da hannu ta
nunashi sai ji yayi an daga shi sama ana nufar kofar gida da shi. Nan fa ya fara ihu yana bada
hakuri. Safuratu tace ba komai zasuyi mishi ba amma yaki yin shiru. Daga dayan hannun ta
wata wulfefiyar wuka ta fito taje ta tsaya saitin makogwaran Mukhtar Safuratu tace "kayi min
shiru ko in umarci wakar nan ta cire ma kai". Shiru yayi ko uffan bai kara cewa ba har suka
shiga gidan. Ba nefa gida duk duhu ne Safuratu ta kalle kwan nepar sai wani haske ya fito daga
idanun ta ya shige shi nan take gidan yayi hask fayau!._




_Nan suka zaunar da Mukhtar Rafy kam tuni ta gaji da jira har tayi barci. Safuratu tace "Zanyi
ma wasu tambayoyi. Amma kasan da sani in ka min karya zan gano ka dan haka gwara ka
taimaki kanka a fadan gaskiya". Mukhtar bakin shi na rawa yace "To, To zan fada miki
gaskiya". Safuratu ta kalle shi ta nuna Umar "Miyasa ka bawa Umar abokinka shawarwari na
banza. Wanda kasan kai ba haka kake wa matar ka ba?". Mukhtar yayi jim! Kadan tukun ya
nunfasa yace. "Hakikanin gaskiya na bawa Umar shawarwari na banza ne domin tun muna yara
mu abokai ne kuma na riga shi yin aure sai kuma naga ya fini jin dadin auren wannan yasa na
kirkiri hanyar da zata dakushe jin dadin nashi shima ya dawo kamar ni. Amma daga karshe nayi
nadama". "Karya kake mugu azzalumi macuci'. Umar ya taso mai da fada da niyar ya shake
shi. Safuratu ta miko hannunta ya zama xankalele ya shiga tsakanin su. Can Umar ya koma
yana hararen Mukhtar yana huci._

_Safuratu ta kalle Umar "Haba kai da nake ganin ka mai hankali shin bakaji abunda Mukhtar din
yace bane?. Kai yanzu bazaka tausaya mishi ba. Kalle fuskar shi ka kalle cikin idanunshi kaga
cike yake da nadama da tarin dana sani. Umar na kawo shi nan ne dan in muku sasanci ba
fada ba dan haka ka saurare mu kawai in bance kayi magana ba karka kara saka baki". Umar
jikin shi yayi sanyi da jin haka. Safuratu ta kalli Mukhtar taci gaba da magana, "Mukhtar amma
kai miyasa ka auri mata kallar wannan?. Shin auren soyayya ne ko hadi ne". Mukhtar yace
"Auren soyayya mukayi da murja sai dai tun tana budurwa ake fada min irin mugayen
halayanta. Amma nake kauda kai wasu abokan nawa har rikici muke in suka aibata ta a
gabana. Ni a ganina duk rashin kyan halinta ai ni bazata min ba tunda ni mijinta ne. Sai da na
aure ta tukun na karyata kai na. Domin kuwa abubuwan da murja take sam basuyi kama da na
mai neman gidan aljanna ba ita fa duniya kawai ta saka gaba. Kullum zancen ta kudi-kudi
lokacin da mukayi aure idan na bata kudin cefane sai ta murkushe rabi. Idan na auno shinkafa
ko Masara sai ta kwashi san ranta taje ta sayar daga nayi magana sai tayi fushi tace wai
zarginta nake yi. Da dai naga abun yayi yawa lokacin inada dan arziki na sai na hada yan
kudade kusan dubu dari da goma ne. Na bata nace taja jari ni a gani na ai rufin asirin ta nawa
ne kuma rufin asirina nata ne._






_Taja jari kuma sana'ar ta karbe ta tana sayar da fulawa. Man kwanti. Shinkafa. Da dai sauran
kayan miya. Kwanakin baya sai aka kore ni daga wajen aiki na dawo zaman gida. Duk da ni na
bata jari amma kullum bata da abun yi min sai gori wai na zama mijin hajiya ita take cida ni. Da
abun ya bani haushi sai naje nace ta bani kudina dubu dari dana bata jari. Nan fa tace ta cinye
kai tsaye. Abun yayi kamari har ta kai mu ga dambe. Nayi mamakin karfin murja dan dagani tayi
ta ringa nunawa mahalicci tana bugawa da kasa. Da dai naga tana neman jinyata ni sai nace
na hakura. Bayan kwana biyu sai na sama wani mashin din ina achaba. Mun dade a haka ina
ciyar da ita duk da ta fini samun kudi. To ranar sai mai mashin din ya sayar da shi. Nan na sake
komawa gidan jiya kekenapap din nan itace ake bani duk sati to kinga kuwa ko ni kadai ne
baxata iya rike ni ba balle ma harda mata ta. Wannan yasa na fara cin bashi a gurin domin ita
bazata bada ba sai bashi a haka har na tara kudade da yawa. In kinga irin rashin mutuncin da
take min a kansu bazaki taba cewa ni mijin ta bane". Safuratu taja dogon nunfashi tace,
"Tabdijam kaga irin abunda ake gaya muku. In kun tashi aure ku nemi mace mai hankali tausayi
da sanin ya kamata. Amma sai ku bige da neman mace Fara kyakyawa doguwa. Baku ma
damu da kalar tarbiyar ta da halayyarta ba. Hmm in kuwa kuka cigaba da haka lalai zaku ta
tsintar kanku cikin irin wannan matsala Mukhtar. Umar abunda nake so daku shine ku yafi juna

nasan duk hassadar da yake maka sharrin shedan ne". Umar ya sauke ajiyar zuciya ya kalle
Muktar yace "Ba komai abokina na yafe maka Allah ya rabamu da sharrin shedan kuma". "Na
gode abokina ameen Allah ya saka da alkhairi". Umar yace mu duka Safuratu ce ya kamata
muyi wa godiya. Muna matukar godiya Safuratu. Hakika da za'a samu irin ku a cikin al'umar
aljanu da wasu abubuwan sun saitu a cikin mu mutane". Murmushi tayi kafin tace. "A komai ai
ana samun na gari ta yuyu bani kadai bace ma. Yanzu Mukhtar ya zakayi da matar ka?".
Mukhtar ya bata rai yace "Ni fa na sake ta saki daya. Amma kuma tace bazata bar gidan ba".
Dariya Umar da Safuratu sukayi.
Safuratu tace "Ji shegiya kamar gidan ubanta. Bari inje in korar maka ita". Mukhtar yace "Jira
bari in karashe sauran saki biyun su zama uku domin na tsani murja gaba ki daya bazan iya
zama da ita ba". Takarda aka samo mishi ya idasa sakin Safuratu ta amsa ta bace. A kofar
gidan Mukhtar ta bayyana cikin sufar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login