Showing 24001 words to 27000 words out of 103342 words

Chapter 9 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5109

ta amsa "Eh zanyi hakan aunty
aljana". Nasmat ta fada murya na karkarwa. 'Yar tsanar tasa dan guntun hannunta ta wanke
Nasmat da mari. Da sauri Nasmat ta dafe kunnu domin zafin marin. Kuka ta fara wii!-wii! Harda
hawaye. Tsawa aljanar ta daka mata. " Rufe min baki, Ki kira ni da *SAFURATU* KO
*ALJANAR FATIMA* In kuwa ba haka ba zaki san da sani". Gum Nasmat ta kame baki duk da
kukan yaci karfin ta sai dai ba yanda zata yi aljana ta saka ta gaba. Hawaye ne kawai ke zuba a
idanunta. "Muguwa ashe mugunta ba dadi kuke cutar marainiyar Allah kaf! Gidan nan banda
alhaji da fiddausi ba wanda zan saurara wa sai na dauki mumunar mata ki a kanku. Sannan
yanzu abunda nake so shine. Bayan kin kaiwa Fatima ni ku wuce gidan baki da ita kina jina"?.
"Eh", farin ciki ne ya ziyarci zuciyar Nasmat domin kuwa abunda take so kenan Taji maganar
mugunta. Aljanar tace sai taci uban kowa a gidan. Daukar 'yar babyn Nasmat tayi ta fita da ita
anyi sa'a kuwa lokacin mai gadi ya dawo, Wata muguwar harara ta galla mishi lokacin da ta zo
giftawa. A zuciya tace "Mugun mai gadi ko hada kai ma aka hada baki, Wai dan kuu... Uba sai
yanzu zai dawo bayan na shiga tarkon Aljanah".




Kwance suka Tarar da Fatima a kofar gida sai sharara barci take ta gaji da kuka. Nasmat rike
da 'yar tsana a hannnu wacce duk sanda ta kalle ta bata marmarin karawa don irin hararen da
take aiko mata. A hankula ta tayar da Fatima ko ita Fatima tayi mamaki abunda bata taba gani a
gun aunty nata ba kenan. Ko Nasmat taga mamaki a fuskar Fatima a zuciya yace "Yarinya
wuya ce mai saka kafuri sallahr dole". Kallan Fatima tayi Cikin fara'a "Fatima Ga 'Yar babyn ki
dama fa wanka ne zanyi mata. Yanzu tashi zakiyi mu tafi gidan biki". Fatima cike da Zumudi ta

karba "Na gode aunty na tayi kyau sosai. Amma mama asiya tace baza'a je dani ba".
Murmushi Nasmat tayi, "Karki damu baza ta ce komai ba ai dani za'a je". A zuciya kuwa tace
"Yarinya ai ko Mama Asiya taga bala'in da na gani dole ta tsure ta amshi duk wani umarni ko da
ta san bazai yuyu ba". Fatima tace to "muje muyi wanka ko Ko aunty?". Nasmat kallan Aljanar
tayi irin kallan da babyn ta watso mata ya nuna mata alamun bata yarda da wannan ba. "A'a
'yar kanwata ai sai mu makara tashi muje nima ko uniform bazan cire ba". A hakan kuwa
Nasmat ta tsayar musu da napep suka hau. Har yanzu jikin Nasmat bai daina Rawa Ba.
Allah-Allah take su sauka ta bace musu a gidan biki ta rabu da bala'i. Ba'a jima ba suka isa
kofar gidan. Nasmat ta shiga gida kenan domin ta karbo wa mai Napepk kudin sa ta bar fatima
nan rugume da babyn ta.
Wasu 'yan mata ne suka zo wuce wa, Idan daya ya kyalla kan yar babyn Fatima hakan yasa
tace wa abokiyar tafiya. "Laaaa! Kawata dubi wata 'yar tsan mai kyau muje mu ganata". Suna
karasa wa gurin hadiza ta warci yar babyn ta maka ta da kasa tasa kafa ta taka. "Haba kawata
wannan gunkin abunda Allah ya tsine wa mala'iku Ma basa zuwa gidan da ke d..,.". Tasss!
Tasss, Taji saukar tagwayen marika a kumatun...........................



Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks




Autan writers nee king boy




��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 31-32

NA. ✍KING BOY ISAH


✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍



*WANNAN PAGE IN SADAUKAR WA NE GA LITTAFIN

‍♂ *'YAR AIKIN GIDA NA* ‍♂


*SHAZEE* Allah ya karo basira Aljanar Fatima taji dadin kyautunan pages da kike bata hakan
ma yasa ta tasa ni gaba a kan sai na baki wannan. Yauwa kuma ina so muyi sirri a bani
number hafsat zan aike ta wajen BOKA MAI KWARAN GWAL! � .lolz


*BADA HAKURI*

Masoyan littafin nan ina baku hakuri bisa rashin jina da kuka yi jiya. Naga sakonin ku da masu
kira na. Na gode � I luv yhuu All my fans.





*KARSHEN PAGEN BAYA*
~"Haba kawata wannan gunkin abunda Allah ya tsine wa mala'iku Ma basa zuwa gidan da ke
d..,.". Tasss! Tasss, Taji saukar tagwayen marika a kumatun.~

»»Dafe kumatu tayi, "Kai! Kai! Kai! Kut...uba yau za'ayi bala'i a wajen nan wato dan na yarda
wannan tsinanar 'yar tsanar shine zaki mare ni ai kuwa bazan taba yarda ba". Kafin kawar tata
tayi magana tuni hadizar ta wanka mata mari. Nan fa sukayi hau kunce. Fada ya kace ba. Duk
abunda yake faruwa a kan idan Nasmat Ita kuwa tasan abunda ya hada fadan hakan yasa ta
kyalkyalewa da dariya harda rike ciki. 'Yar tsanar ce ta mata wata iriyar harara wacce tasa bata
shirya ba ta dakata da dariyar. A hankali taje taba wa mai adai-daita kudinsa tace wa Fatima
"kinga dauko 'yar babyn ki mu shiga ciki". Da sauri Fatima ta share hawayen da suka fara zubo
mata. Ta dauko 'yar Nasmat ta kama hannunta suka shiga ciki. Safuratu ganin sunki rabuwa da
fadan ne. Ta zo ta fara kan uwa da wabi. Mari sai dai kaji kara tass! Tass an rasa daga ina yake
fitowa. Ba arziki suka rabu da gudu suka bar wajen domin sun maru ba laifi. Da shigar su
Nasmat falon. falon suka iske mata ne damkam a ciki su mama asiya suka fara wurgo mata
harara,

Umma ce ta taso wacce itace mahaifiyar Haleema da ake wa auren kuma yayar Mama asiya
ce. Yanayin jikin su da na asiya duk daya itama yar lukuta ce. "Nasmat ke wacce irin doluwa
ce?, Da zaki taho mana da wannan marar jin yarinyar. Ko zaki zo ai bai kamata ki zo mana da
wannan ba, Ke kinsan cewa jina na ko kadan bai hadu da wannan kazamar yarinyar ba".
Umma ce ke fadar haka. "Umma ni gani nayi an barp ta a gida ita kadai shi yasa ma nace ta
taho mu tafi. Mama asiya ce ta taso tubur! Tubur! "Kanwar uwarki ce ita din da zaki ji ba dadi
dan an baro ta a gida. Dallah fidda muna ita waje kuna ji daga shigowar ta har ta dumame falon
da wari". Umma tace "Zo nan kawo 'yar babyn nan dan ubanki daga yau ta zama ta khaleel".
Warce diyar tayi ta mikawa wani marar jin yaron ta dan lukuti. Fatima kuwa ta fashe da kuka ba
komai yasa ta kuka ba sai kwace mata 'yar baby da akayi. Wani mugun dadi ne ya ziyarci
zuciyar Nasmat ganin abunda su Umma suka aika ta, domin yau cikin mugunta take. Waje
Fatima ta koma ta sama wani waje ta zauna ta saka kanta tsaka nin kafafunta tana kuka a
hankali. Nasmat kuwa tasan amare suna sama kuma tasan Asmart ma na can amma ta tsaya
kawai so take ta ga abunda zai faru. Khaleel ana bashi 'yar tsanar waje yayi da gudu. Wajen
wasu marar jin abokan nashi yaje. Suna ganin ta kuwa wani daga cikin su ya rugo da gudu ya
dau ki wuka wai yanka ta zasuyi. Sai da aka kwantar kamar dan akuya wukar kawai zasu dora
nan take ta fara girma kafin su ankara tuni ta koma make kiya abun tsoro. Rugawa sukayi da
gudu khaleel ne rike da wuka sai ya daga kai yake kallanta shi yaki rugawa. "Yanka ni mana
khaleel". Abunda take fada tana mai-mai tawa kenan nan take tsoro ya ziyarci khaleel din
karkarwa ya fara bai ankara ba yaji saukan bulala.



Gudu yake yana kuka hade da soshe-soshe yana kiran uwarsa. Daga ganin sa kaga wanda
ake bi ina zane wa sai dai in ka duba baya babu wani wanda yake biye da shi domin aljanar a
bace take. A million ya shigo gidan Nasmat na jin kukan sa a tsorace ta ruga a guje bayan
mama Asiya ta wani makal-kale ta. Khaleel ne ya shigo yana kuka Da sauri Umma ta tashi ta
tarye shi "Auta na lafiya, auta lafiya". Bayan ta ya boye yana nuna hanyar waje matan da ke
falon duk suka dubi gurin ba komai. Da sauri ta juya tana jijiga da gani kasa bala'i ya tashi.
"Waya taba min kai auta fada min ko uban waye wallahi sai naje naci mutun cin sa, fada min
waye". Cikin kuka yace "Yar babyn Fatima ce". "Kai bana san shirme fada min waya dake ka".
Amsar da ya kara basu kenan *"ALJANAR FATIMA* Ce". "Ok kwace ma tayi kenan bari inzo".
Buzu-buzu ta fita a waje ta sama Fatima rike da 'yar babyn mari ta wanka mata, "Ke dan ubanki
in bawa yaro na abun yayi wasa shine zak kwace, kawo ta dan uban ki" warce wa tayi ta koma
ciki Fatima kuwa kuka ta kama yi domin ita dai a iya saninta taga Khaleel ya wuce yana kuka
bai dade ba kuma taga ya fito ya kawo mata yar babyn ta da kanshi.

Umma na shiga da 'yar tsanar Nasmat tayi wani mugun tsalle a firgice ta fada bayan kujera A
tsorace tayi muky! Tana saurare su. Khaleel na ganin Umma ta shigo da yar babyn ya kara
fashewa da kuka ya ruga a guje ya makal-kale Mama asiya kamar zai shige jikinta. "Bana so!
Bana so! Karku kawo ta". Abunda khaleel din ke fada kenan ganin uwar tasa bata daina nufo
shi da yar tsanar ba ya sa ya tashi ya zuba a guje sama.




Rike baki Umma tayi "Ah! Ashe tsoranta ma yake har na wani bashi. Komawa tayi daga bakin
falo ta wurgawa Fatima 'yar tsanar "Dauki tsiyar ki gata nan tsoranta ma yake yi". Fatima cike
da farin ciki ta bar kuka ta dauki abunta ta rungume. Masu dafa abinci ne suke ta zuzubawa sun
karasa kowa sai dai ya zo ya dauki nasa da na 'ya'yansa Fatima najin yunwa tsoro take taje ta
dauka ga abincin a Take away amma tana tsoro a mata fada. Yunwa ta kai mata karo koma
taga har yara na zuwa dauka ba'a hana su hakan yasa itama ta tashi dugwi-dugiw ta nufi wajen
da aka jera take away din. Tasa hannun zata dauka kenan, taji an daka mata tsawa sai da ta
zabura firgi-git "Keeee! Dan ubanki waya baki izinin ki zo nan balle ma har ki dauki abinci?".
"Dama-dama yunwa nake ji mama asiya". "Kinci ubanki maza wuce idan anyin sauran abincin
shi za'a baki". Magana tayi wa masu dafa abincin tace kar wacce ta yarda ta bawa fatima
abincin in kuwa wata ta bata sai ta hadu da fishinta. Tana gama fadar haka ta dauki abincin
guda uku ta nufi falo. Gaba daya hudun ta saka gaba da niyar ci. Lomar farko ta na kai wa baki
ta zubdo da sauri. Nan take kowa da ya kai abincin baki sai ya zubdo saboda masifafan gishiri
da ke cikin abincin duk wanda ya kai baki sai yaji kamar dai gishirin ne yayi loma da shi. Ran
jama'a ya baci hakan yasa sukayi tururuwa suka wa masu aikin abincin caaa! Kamar zasu cinye
su dan masifa. Mama asiya ce ta juyo ta kalli Fatima mugunta ce ta motso hakan yasa ta dauki
abincin daya tana murmushi "Fatima to ga abincin ci ko". Da sauri Fatima ta karba domin
masifar yunwa take ji. Loma ta fara kaiwa hannu baka hannu kwarya. Gaba dayan matan gidan
kallanta suke suna dariyar mugunta, Ita dai fatima kallansu take ta rasa me yake basu dariya
domin kuwa ita lafiya lau take jin abincin da dadinsa. Wata tsohuwa ce ta shigo gidan bara
sanye take da bakar hijab doguwa har kasa, fuskarta duk a tatabe.



Bara tayi da farko suka ce hakuri kamar hadin baki. Ta kara nan ma suka bata hakuri. Kamar
bata ji ba a karo na uku ta sake yi musu bara. "Masu gida a taimaka min da abinci ko kanzo ne
ko saura in sama abunda zan zuba a ciki na rabo na da abinci tun jiya". Sauran muta nan ne
suka fara balbale ta da masifa Umma tana murmushin mugunta ta dauko abincin har guda biyu
ta sa tsohuwar ta zauna. Ta bata abincin suka koma gefe dan suyi dariyar mugunta. Lomar
farko tsohuwar ta zubdo tana kakarin amai.Dariya suka hau kyakyatawa kamar me. "Haba
bayin Allah ya zaku bani abincin da zai kashe ni wannan abinci ko gishiri". Asiya ta taso cike
da masifa kamar zata hade tsohuwar. "Kinga tsohuwa bama san ciki da rashin mutunci da rai
nin wayo, Dan kutu....uba ba sao da aka baki hakuri har sau biyu ba kika ki hakura kuma
yanzu an baki shine zaki wa mutane tsiya". Cike da Tsokala da tsiya mama asiya ta juya

"Jama'a ku karo mata Takeaways uku ta kara ta kai wa jikokinta". Gaba dayan gidan dariya
suka hau yi mama asiya harda dukawa tana Rike ciki. Dagowar da zatayi taji saukar mari ya
bada sauti. Tasssss! abunda ya dakatar da dariyar jama'a kenan. Hannu Daya mama asiya
tasa ta dafe kumatu, ba abunda ya bata mamaki da tsoro sai ganin ba komai a gurin tsohuwar
ta bace.Saukar Bulala taji a bayanta...................
....


Yau wasu sun dauko ruwan dafa kansu.

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee king boy









��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 33-34


NA. ✍KING BOY ISAH


✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍

*WANNAN PAGE IN SADAUKAR WA NE GA MOMCY DIN MU. MUNA SANKI MUNA
KAUNAR KI. MUNJI SAKON KI A BAKIN 'YAR UWAR MU,
QUEEN MEARYAM ('YAR MAMARMU)*

We love you too♥
BY ALL ZAMANI WRITERS.

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Hannu Daya mama asiya tasa ta dafe kumatu, ba abunda ya bata mamaki da tsoro sai ganin
ba komai a gurin tsohuwar ta bace.Saukar Bulala taji a bayanta...~

»»Da sauri ta fara so sa baya tana ra raba ido.wata bulalar aka zubga mata wacce tafi ta dazun
ma zafi abunda yasa ta rugawa tubur-tubar cikin jama'a tana ihu! Kenan duk. Aljanar binta take
tana zane wa tuku ta koma kan uwa da wabi, domin kowa duka take ai kuwa gida ya hargitsa
mutum.na tsaye ko yana gudu sai dai yaji saukar bulala. Haka suka fara rantar ta kare suna yin
kofa, Nasmat na jin gida ya hargitse ta kwashe da dariyar mugunta domin tasan (A rina, wai an
saci zanin mahaukaciya) Wata mata ce aka biyu da gudu ta shigo dakin, karan bugo na tashi
amma ba ka ganin mai dukan. Nasmat na ganin haka tayi wani juyin da bata shirya ba. Da gudu
ta nufi saman bene (upstairs) ai kuwa matar ta biyo ta tana ihun neman ce to. Nasmat na ganin
haka ta kara wuta. Tana karkarwa ta fada dakin da amaren suke ta turo kofa, Tayin saurin Saka
kuba. Ta jingina baya tana haki. Gaba dayan 'yan matan ne suka hayaya ko mata kamar zasu
cinye ta danya. "Ke wace iriyar ce da zaki shigo wa muta ne ko sallama babu kin tsorata muta
ne". Wasu 'yan mata uku ne suka fadi hakan cikin daga murya. "Kuyi shiru Aljanu ne aljanu".
Haleema ce ta taso cike da masifa. "Kutumelesi Lalai yau zakiyi bayani wato ke dan rashin
kunya har kika iya tako kafarki zuwa wajen biki na oya to wallahi kama hanya in ba so kike
yanzu mu kwashi 'yan kallo da ke ba.



Bar ganin ina amarya wallahi sauke gwa-gwaran nan zanyi inci ubanki". Duk da Nasmat taji
haushin zancen Amma sai ta basar domin jin Matar nan ta zo bakin kofa sai bubugawa take
tana fadin "dan Allah ku ce ce ni ki bude zata kashe ni". Karkar wa Nasmat ta fara yi tsoranta ya
karu abun ya zame mata biyu ga masifar haleema ga kuma wacce aljana ta biyu. "Sister
Haleema dan Allah kiyi hakuri zan fita, Wallahi nima ba da gangan na shigo ba aljanu ne a
gidan yanzu ma aljanace ta biyu mu ni da wata kinji ta nan tana bubugawa". Wani dogwan tsaki
amaryar taja tare da kama hannun Nasmat tana kokarin bude kofa ta tura ta. "Aljanu ko to
wallahi sai dai su kashe ki amma sai kin fita. Ke sunci kut.....ubansu ma aljanu". Kafin ta rufe
baki taji saukar wani lafiyayen mari wani har sai da taga taurari. Juyo wa tayi, "Kai kai kai kika
mare ni Nasmat. to wallahi yau banga mai raba ni dake ba a gidan nan". Nasamt kafin ta bude
baki ta ce l ba ita ta mare ta ba.

tuni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login