Showing 54001 words to 57000 words out of 103342 words
Chapter 19 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
to yau dai Allah ya toni Asirin ki kashin ki ya bushe. Umar ne ke fadar haka lokacin
yana kokarin saka kwado ya garka me dakin kwadan ne yaki rufuwa dan haka ya saka kubobi
kawai ya barshi. Haka tagar ma. (Window) ya rufe ta. Juyowa yayi ya nufi Rafy da har yanzu
tana kan gado duk abun da yake yi ido kawo take binsa da shi, Duk wanda yasan Rafy in yaga
ta yanzu yasan idanunta sun kara girma. Bai yi wata-wata va ya fara zura mata bulala. Yana
dukan nata da karfi yana fada._
_Yayi mata kusan bulala goma amma yaga shiru ne domin ko motsawa batayi ba In banda
manyan idanun ta da take binshi da su ga ta wani daurw fuska. abun ya daure mishi kai sai
ganin iri dukan da yake mata ko icce ne sai haka. Umar na waje jira yake kawai ya fara jin ihu!
Rafy amma shiru. Mujaheed ya daka iccen dake a matsayin bulala zai narka mata kenan, cikin
hanzari ta mike saurin su irin na Aljanu ta kwace icen ta bace da shi. Mujaheed waige-waige ya
kamayi a cikin dakin yana neman ta. Hihihihihihhi-hihihihi. Wata siririyar dariya ce ta fara cika
dakin. "Waye? Waye waye mai dariyar nan? In ba tsoro ba fito mana. Ni fa nan da kike gani na
a shirye nake ba raggon namiji bane". Aljihu Umar ya laluba ya dauko wata laya ya rike a
hannu yaci gaba da cewa ta fito mana. Ta baya yaji an turo da karfi ya nufi bangon dakin kafin
ya isa bangon yaji an tare shi da hannu ba tar da yaga wanda ya tare shi din ba. Mari fasss!
Fasss! A duk kumatun nashi biyu, Rike kumatun yayi kamar yayi ihu kuma sai ya yi tsoran kar
abokin sa yaji ya kunyata. Ji yayi an dan dadabe shi. "Kaaaa!" Yana juyawa baiga kowa ba sai
saukar wasu tagwayen marukan. Wayyo! Mujaheed ya fada a hankali ba da karfi ba ya dafe
kumatun sa. "Muguwa kawai wannan tsoro ne ma. Ku fito fili mana mana ayi ga da ga, in ba
tsoro ba". Mujaheed ke maganar ya dunkule hannu kamar dan dambe sai juye-juye yake so
yake kawai yaga ta bullo._
_Dariya yaji da karfi a bayan sa. Hahhahhhhhhhh! Yana juyawa kuwa abunda ya gani ya
tsorata shi sosai. Wai katan dodo ne mai bakin gashi buzu-buzu ko'ina jikinsa gashi ne.
Hannunsa kuwa wasu mugayen farcina ne masu kaifi, Girman abun ya kai A hade Mujaheed
biyu ko uku. Babban abun tsoran shine kan Rafy ne, Idanun ta sun juye sunyi baki. A haka take
nufo inda Mujaheed yake tana dariya, Duk lokacin da ta wangale bakin ba abunda zaka hango
ciki sai wasu rubabbun hakora. Duk jikin Mujaheed ya fara rawa mugun tsoro ya kama shi,
faduwa yayi kasa yana ja da baya yana bata hakuri cikin kuka kuka."Dan Allah kiyi hakuri,
Wallahi bazan kara ba, kuuuummaaaa maaa..." Ya fara magana karkarwa ganin abun ya kusan
iskoshi. Daga waje yace Umar yace "Abokina wai ya dai naji shiru ne har yanzu bata fara ihu
ba, Nafa gaya maka karka raga mata kaci ubanta sosai ni na saka ka". Cike da takaici
Mujaheed yace "Ka yanzu zakaji ihu na ni...". Kafin ya rufe baki yaji an shaki wuyansa kamar
wani zakara an daga shi sama Ihu! Ya fara "Wayyo! Allah na Wayyo! Wayyo!". Da karfi yake
ihun! Fitsari ne ya fara zuba shaaa! Wulli tayi da shi ya maku jikin bango. Sa'ar shi Daya ba kan
shi ya budu ba._
_Tashi yayi a guje ya nufi wajen kofa, ai kuwa wutar dakin ta dauke duf! Baka iya ganin komai
ko'ina duhu ne. Inda ya nufa ya azo kofa zai ji, Kawai sai yaji yaci karo da mutum haka kuma
aka dalla mishi mari, Wani bangaren ya sake nufa nan ma yaji saukar mari. Ba abunda yake in
banda kuka da ihu! Yana neman agaji domin yanzu abun yayi yawa mari da duka ta ko'ina kawo
mishi ake. Umar daga waje ihun yake ji kamar na matar shi haka yasa ba abunda yake yi sai
murna yana fadin "'yar banza gobe ma ki kara". Mujaheed ya daku sosai dan fuskar sa har sai
da ta fara kunbura. Yana nan duke ya rufe kanshi da hannnuwa dan dukan shi da ake. Ba
abunda yake sai ihu da neman agaji. Tsik! Yaji an dakata da dukan nashi, a hankali ya fara
bude ido yaga ashe haske ya dawo. Yana bude idan ya ga ashe tsugunne yake gaban gado
Can kuma kan gadan rafy ce ke kallan sa tana murmushi. A tsorace yaja da baya. "Dan Allah,
Dan annabi kiyi minn Rai ki barni in tafi gida ki yafe min Wallahi ko can dam ni wa'azi nazo in
miki kibi mijinki...". Tsawa ta daka mishi wanda sai da yayi muguwar zabura. "Wa'azi kazo ko
dai kara rikita al'amura?, Ashe dai dama kai ne muna fuki wanda ka raba su da farin ciki da
shawarwarin ka na mugun ta da ke ta. Umar Ya dauke ka tamkar dan uwa ne komai zaiyi sai ya
sanar da kai amma kai gurinka ka na ya za'ayi ka saka su cikin damuwa ne shida matar sa
ko?"._
_Duk hawaye ne da majina da a fuskan sa. Da sauri yace "Aa Wallahi ba haka ban...". "Rufe
min baki ko in kara maka dukan da ya fi na dazun". Hannu yasa ya kame bakin sa. Aljanar taci
gaba da cewa "Tunda kai ne wanda ya jefa su cikin wannan halin to Wallahi kasan yanda zakayi
ka dawo musu da farin cikin su. Daga yau zuwa gobe na baka. Sannan kuma ina so in gaya
ma karka yarda ka fadawa Umar cewa na dake ka". Wani zane ta wurgo mishi tace "Oya goge
hawayen da majinar. Ka fita a hankali kana murmushi". Da sauri ya dauka ya gogo ge. Tashi
yayi zai fita alamun tsoro ta gani a fuskan sa gashi har yanzu yana 'yar karkarwa. "Kai dawo ka
fita kana Murmushi nace ba karkarwa ba". Wani mugun yake yayi tukun ya juya ya fara cire
kubobin. Yana ganin daki ya bude haba wa sai ya kwasa a guje kamar bai ji duk abunda ta fada
mishi ba. Safuratu ta girgiza kai tace "Hmm yaro bai san wuta ba aka ce sai ya taka". Umar na
tsaye yaga mutum ya wuce a guje kamar wanda aka harbo. Ai kuwa ya rufa mishi baya. Sai da
sukayi gudu mai nisa. Duk wanda ya tambaya lafiya Sai Mujaheed yace "Aljana! Aljana! Haka
ya ta tsorata wasu suna rugawa suma. Sai da ya gaji da gudu tukun ya tsaya ya zauna a wata
inuwa duk jikinshi yayi sharkaf da fitsari ga Gumi ga hawaye. lokacin bai ko san Umar na biye
da shi ba. Da karasowar umar da zai tashi da gudu sai kuma ya tsaya da yaga Umar ne._
_Umar na zuwa ya fara tambayar sa "abokina wai ya haka naga ka fito a guje bayan dazun naji
tana ihu". "Dallah can ni rufe min baki ta gama ihu ko na gama ihu!. Ashe kasan haka matar
ka take da kartin Aljanu shine ka hadani da ita". Umar yace "Abokina sai fa dana fada maka
wannan matar Aljanu ne da ita kaki yarda. To yanzu miye abun yi danni gaskiya tsoran komawa
ma nake yi". Mujaheed yace "In dai kana da kudi wannan ba matsala bane akwai wasu 'yan
bori da na sani aikin su kenan fidda aljanu nake gaya ma fit! Daya zasu fidda wannan Aljanar
karamar kwaro ce ai. Dan ko ni nan abunda yasa taci galaba a kai na ban shiryo bane........_
: _________________
_Mama Asiya zaune take suna hira ta fara jin wata murya na kiran ta. "Aaaaasssssiyyyyaa!"
Da sauri ta waiga baya wayam ba kowa. "Aaassiyya". Ta kara juyawa ba kowa. "Wai dan
Allah bakwa jin ana kiran sunana?". Ta tambaya gaba daya suka ce su basuji ba. Tashi tayi ta
nufi dakin ta wanda daga nan guraren ne take jin kiran. Da bude kofar da wartar ta ciki duk
daya. Duk kibar ta kiiii!! Taji an jata bata ganin mai jan nata. kasa kofar kuwa ta koma ta rufe
gam! Jikin bango aka makata. Wash! Ta fada. Wutar dakin ta fara rawa zuwa can kuma wata
iriyar dariya marar dadin ji ta kaurade dakin. Ahhhhhhhhhh! Mama Asiya ta saki ihu! Mai karfi
hade da rufe kunnuwan ta. An dan dau lokaci a haka ta rufe idan ta gam ta kuma toshe
kunnuwa da hannaye. Zuwa can taji an tsaya da dariya wani abu taji na jika ta. Kamar ruwa.
Da sauri ta bude ido. Ahhhhjh! Ta kara sakin Ihu! Jini ne gaba daya ya malaye dakin tashi tayi
tsabal!-tsabal tana taka kafa cikin jinin ta nufi kofa da nufin ta gudu. Har ta kusan zuwa taji
kamar an jawo kafafun ta shuuuu! Sulbi ya kwashe ta ta koma. Hahahahaha! Taji dariya hade
da wani irin gwalan gwalantu na fitowa daga Cikin wardrobe. Karkarwa take duk ta rude kayan
jikin ta sun koma jawur kamar wacce ta fito daga kwata. Tashi tayi ta nufi wardrobe din hannun
na karkarwa ta bude. Ihu! Ta saki mai shegen kara Ahhhhhhjjhhhhjhhhhhhhhhh!. Su mammiya
ta zube a gurin..........................._
*MUJAHEED*
Karfin hali sata a jikin gawa. Wato baka ma daku ba kenan. Ai kuwa in dai Safuratu ce zata yi
maganin ka...
*MAMA ASIYA*
Allah yasa yau ki daku ki kusan zaucewa ma
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 65-66
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
*GODIYA NAKE MASOYA*
JINJINA GA ALL MEMBERS NA
*ANSHOLLY NOVELS*
✍ *KING BOY ISAH NOVELS*
_Na yaba da kaunar ku gare mu_
*HADIZA TUNAU(.*
Na ga sakoki Allah ya saka.
*IDDAH*
*MEERAH DANFODIO*
*MISS PRETTY*
*ZAYYNERB*
*SUWAIBA*
_Allah bazan iya lisSafo ku ba._
♂ *king dai Nata dago hannu masoyan Aljana wanda na sani dama wanda ban sani ba.*
Ana mugun tare
♂ _KUYI HAKURI DA DAN WANNAN PAGEN NIMA KAI NA NASAN YAYI KADAN. WAYAR
TAWA CE YAU KAMAR TA SHA GIYA SAI YANGA TAKE_
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Karkarwa take duk ta rude kayan jikin ta sun koma jawur kamar wacce ta fito daga kwata.
Tashi tayi ta nufi wardrobe din hannun na karkarwa ta bude. Ihu! Ta saki mai shegen kara
Ahhhhhhjjhhhhjhhhhhhhhhh!. Su mammiya ta zube a gurin.~
_Ta dan dade a suman zuwa can ta farfado. A kwance kan gado ta tsinci kanta idanta a rufe sai
kanta da take jin yana mata zogi. Har zuwa yanzu bata bude ido ba kan ta dan dafa wash!
Wash.Tana Bude ido ta saki wani kara Ahhhhh! Da sauri ta mike ta sauka kasa. Wata tsohuwa
ce ta gani kwance a gefan ta tana mata murmushi fuska duk a yamutse. "Wace ce ke?". Mma
Asiya ta tambaya. Tsohuwar ta tashi zaune ta kalli Mama asiya ta wangale baki tayi mata
dariya sai yanzu munin ta ya kara bayyana domin hakoran gaba duk babu su sun zube. Ga
bakin jajur da shi kamar wacce taci danyan nama. Duk zaman da nayi gidan nan baki sanni
ba?. Amma anyi yarinyar banza makaryaciya nasha dazun kika wullani saman soro, To ni
Aljana ce sunana Safuratu".
_Karkarwa Mama Asiya ta farayi baki na rawa "Daddadda dan Alllllah ki yyiiii hakkkkuurrrri
karkiiiii ki kashe ni". Kwashe wa da dariya Aljana tayi tace "oh! Baki so in kashe ki ko?". Da
sauri Mama asiya da haryanzu ko'ina jikin ta karkarwa yake ta daga kai alamun eh. "To
shikenan kinyi alkawari duk abunda nasaki zakiyi a wunin yau?. Wannan shine zai kubutar dake
kar in kashe ki". Mama Asiya ta zube kasa "Eh Wallahi na yarda duk abunda kika ce komai
wuyar shi zanyi in dai bazaki taba min lafiyan jikina ba". HHHHHHHHH Aljanar tayi dariya "To
yanzu tashin farko maza tashi kije ki hau kan Soro ki daukko wa fatima 'yar babyn ta. Dama
kince kiga uban da zai daukko ta to ba ubanda zai daukko ta sai ke maza tashi". Aljanar ta
karashe maganar cikin tsawa ta kuma murtuke fuska. A razane mama Asiya ta tashi da sauri
tubur-tubur da ita tazo ta wuce Su Hauwa dake falo. Zuwaira na ganin Mama Asiya a haka tace
"Aunty Asiya lafiya kuwa?". Juyowa tayi tace "Ina fa lafiya, ku dai da kuke lafiyan kuna da
amm...". Aljanar taga ta bayyana a Kan sofa kusa da Juwaira. Haba ai kuwa bata karashe
maganar ba tayi waje a guje. Da fitar ta ta fara kira maigadi yana daki ya fito da sauri. "Yauwa
aiken ka zanyi dan Allah jeka gidan Alhaji mudi ka karbo min aran kuranga. (Tsani)". "To" ya
fada da sauri ya juya ya fita nan ya barta sai bari take ta kasa zama gu daya. Kai ta daga ta kalli
gurin taga da dan nisa. "Kai amma fa hawa can gun zai min wuya anya kuwa zan hau". A fili
take yin maganar Wannan tsohuwar taga ta bullo "Bazaki hau ba kenan". "A'a ni nama isa
dama kawai fada nayi". Ta danyi murmushi mai wuyar gane ma'ana._
_Mai gadi ne ya shigo ba kuranga. Mama Asiya na ganin sa bata ma tsaya jin ta bakin sa ba
kawai ta hau shi da masifa. "Kai dai musa mugun mashiririci ne. Ban ma taba ganin mai gadi
irin ka ba, To ina abunda aka aike ka ka kawo din?. Ka wani dawo wa mutane hannun bibiyu
baka san abun Emergency bane". Shiru yayi har sai da ta kai aya tukun yace "Hajiya wai cewa
sukayi An amsa aro ne sai dai wai muje gidan Naseer mu daukko". "Ah! To me kake jira kuma
da bazaka je ka daukko din ba". "Hajiya gaskiya ni kam bazan iya daukko wannan kurangar ni
kadai ba. Tayi min nauyi". Aljanar ta bayyana bayan Mai gadi tana hararta da sauri tace "Maza
muje in kamo ma mu daukko". Mai gadi yayi mamaki sosai shi tunani ma yake, ko mi za'ayi
da kuranga bayan yasan ba wani gyara za'ayi ba yana san tambaya kuma yana tsoran masifa.
Ko gyale Mama Asiya bata sako ba a haka suka je har can suka daukko kurangar sai wani sauri
take saka shi, Bayan sunje aka aza kurangar a saitin gurin da zata hau din. Mai gadi ganin tana
shirin hawa yace "Hajiya me za'a daukko miki bari in daukko miki". Ta juyo kenan suka hada
ido da Aljanar "A'a bari". Ta fada lokacin ta fara hawa kurangar a hankali take tafiya gata lutuyi
ba dan kurangar karfe bace da ta ballata dan can kake hango ta tuli guda. Har tayi dan nisa ta
waiwayo kasa. Tsoro ne ya kama ta ta fara karkarwa ji kakae ratsatsam! Suka zubo kasa tare
da kurangar. Mama da jin haka sai gaba dayan mutanan dake cikin gidan suka fito. "Lafiya!
Lafiya" ake ta tambaya "Lafiya lumi". Ta fada lokacin da ta mike ta fara kokarin mayar da
kurangar. Mai gadi dake tsaye Dariya taci karfin sa tun yana matsewa har ya fara saka ta fara
fitowa fili. Yana 'yar dariyar ya nufo ta lokacin tana kokarin hawa. "Hajiya na gaya miki kinyi
nauyi bazaki iya hawa ba bari in hau in dauko miki. Kama jaki haka Mama asiya ta harb mishi
kafa ta kuwa ci sa'a ta same shi a baki ba wanda baiyi dariya ba a gun. Mama asiya a hankali ta
hau har can ta ta daukko 'yar tsanar har da jakara._
_Bayan ta sauko tace wa Mai gadi ya mayar ma da masu kuranga abunsu. Aljanar ce ta bullo
"Kinyi kokari sosai, yanzu abunda nake so dake shine ki Je kiyi wa diyar nan wanka ki mata
kwalliya mai kyau irin ta amare in bakiyi ba kuma sai naci abunki". "To". Kawai su Zuwaira suka
ji mama Asiya tace ta nufi daki da sauri rike da 'yar baby su dai basu ga wanda take magana da
shi ba._
_____________________
_Umar ya kalli Mukhtar yace Abokina yanzu dai bani da kudi a jikina amma idan kana da su ka
ara min muje a daukko yan borin nan gwara a fidda Aljanar nan ko na sama zaman lafiya".
Mukhtar yace "Ai kai ba a baka Rancen kudi ba ka ki biya da wuri amma ga kudi nan wurina
kudin uwar gida ne dubu 20 Zan sayo mata fulawa da mai, kasan sana'ar ta kenan". Umar yace
"Haba abokina ai ka sani bama 'yar haka da kai Wallahi ina da kudi a gida yanzu haka ba dai
ina tsoran Aljanar nan ba da munje na daukko. Amma