Showing 33001 words to 36000 words out of 103342 words

Chapter 12 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5055

wani jirge share gudu, Hancin ta a wani tabe yake. Idan
kawa Aljanar nan kallo guda baza kayi marmarin karawa ba. Ko asmart kauce kai tayi da taga
hakan. "Lalai samun waje wato kece yau har kike ce min Muguwa ko Asmart?". Da wata iriyar

murya Aljanar ke magana wacce tasa Asmart cikin tsoro da fargaba. Duk rawar kan da take da
farko yanzu ta daina karkarwa ma ta somayi. "Sunana Safuratu Ko kice *ALJANAR FATIMA* ko
kadan bani bari ayi zalunci balle ni inyi. Ko da yake inayin zalunci sosai ma amma fa a kan irin
ku azzalumai, Yarinya ce 'Yar karama gaba daya kun fita do wai me ta tsare muku miye abun
zaluntar ta in baku taimake ta ba marainiya ce fa". Murya na rawa Asmart ta daga baki da niyar
magana. "Baaa.....". Tsawa Aljanar ta daga mata "Me zaki ce min baki da abun cewa Kalmar *YI
HAKURI* Kuwa ke ma baki dauke ta a komai ba yayin da kika tashi zaluncin ki, Dan haka nima
yanzu dole in zalunce ki ba sani ba sabo". Aljanar na rufe baki ta nuna Asmart da yatsa. Sai
gata tayi sama tana ihu! Tana harbe-harben iska Da kafa. "Hahhhahhhhahhahhahah. Yanzu
kuma kinsan me zanyi?, Kasa zan sake ki kanki ya daki Dutsen can ya rabe biyu kinga an rage
mugun iri". A smart ihu! Ta fara tana bada hakuri hade da rantsuwa baza ta kara zaluntar
Fatima ba.





Kafin ta rufe baki tuni Aljanar ta sake ta kasa tayo tana ihu!. Ganin ta kusan zuga kasa gashi
saitin dutse ne, Ta rintse idanu ta sadaukar. Ji tayi ta fado a katifar ta. Abunda yayi matukar bata
mamaki kenan. Tashi tayi da sauri tana waige-waige cikin dakin abun ya daure mata kai,
Tunanin da take wannan mafarki ne ki gaske. Ganin ba kowa a dakin yasa tayi magana a
bayyane. "Shegiyar Aljanar muguwa yar...". Kafin ashar din da tayi niyar fada ya karasa fitowa
taji wani abu ya diro a kanta ta baya. Ihu ta fara yi "Wayyo Allah na na shiga uku na lalace Dan
Allah dan annabi kiyi hakuri Wallahi bazan kara ba". Da karfi Asmart din ke magana. 'Yar babyn
ce ta diro gabanta. Tana mata dariya.




Mai wani irin siririn sauti. "Dama zuwa nayi in gaya miki wannan abun da ya faru a tsakanin mu
ni dake in kika 'yarda kika fadawa wani Ke ma kinsan sauran". Tana fadar haka ta bace bat!.
Asmart na ganin haka ta Tashi ta fito da gudun tsiya daga dakin. Nasmat na zaune a Falo ita da
Ameerah suna kallo sukaga Asmart ta wuce a guje tayi waje. Nasmat ta tashi ta bita a guje tana
wai-wayen kofar dakin. Haka ameera ma ta biyo su. A tsakar gida Asmart ta tsaya tana Maida
nunfashi. "Ke uban miye kika wani rugo da gudu. Kin tsorata mutane". "Kyankyaso ne". Asmart
tace wa Ameera. "Asmart Wallahi in kika kara mana wannan iskancin san naci ubanki. Ya zaki
ringa fitgita mutane?.




Ameera na fadar haka ta juya ta koma ciki. Asmart tsuke baki tayi tana kwaikwayan maganar
Ameera din. Nasmat ce ta Dan dake ta. "Ke gaya min me akayi ni dai nasan yanzu ba

kyankyaso bane. Tunda naga baki fito da 'yar babyn ba". Wata muguwar harara asmart ta
dakawa Nasmat. "Yar banza ni ai ba ruwa na dake ke dama ashe kinsan abunda ake ciki shine
kika min shiru inawa aljanar tambada. Waii!! Ai yau naga ta kai na. Al'quran har na fidda rai!".
Labarin abunda ya faru da ita taba wa Nasmat tace harda targa de. Sai dai tana duba wa kuma
taga babu. Abun ya bata mamaki matuka. Nasmat ce ta fara gagaba dariya mai makwan taji
tausayi dariya harda rike ciki. Sai da taba wa Asmart haushi ta cika tayi fam! Kamar wacce zata
fashe tsabar zuciya. Sai da Nasmat tayi dariya mai isarta tukun ta tsagaita ta bawa Asmart
labarin abunda ya faru da ita ranar Biki ta kara da cewa "Zuwan da nayi Gidan bikin ba dan
Allah bane Aljanar ce ta tilasta ni tasa nayi mata wanka harda kwaliya". Hahahhahhahahhaha
Asmart ta fara gagaba dariya ta rike ciki. Nasmat ta bata rai "Bansan iskanci fa Asmart kinsan
dai ni yayarki ce". Hhahahhahh "Sorry ni kinsan abunda ya bani dariya ma wau da Kika mari
fatima kan ya guntule kuma ta dauko ta biyo ki da shi zan so inga ya kika yi a lokacin.




"Nasmat ta danyi murmushi Sannan tace "Hmm ai ranar naga tashin hankali wallahi. Kai a
yanke fa ya biyo ni yana magana". Asamrt tace "Ai kinyi kokari da nice da suma zanyi a gun".
Yatsa Asmart ta dora a kan habarta alamun tana tunani. Can kuma sai tace "Nasmat ni kuwa
inaga mun sama hanyar da zamu ringa yin mugunta a sauka ke". "Ban gane ba me kike nufi?".


"Yanzu zan fahimtar dake, Sa nin kanki ne gaba daya mutanan gidan nan mugaye ne ga
Fatima, abu kada take musu su hauta da duka ko Zagi. To kinga kuma a yanzu daga an taba ta
aljanar ke rama mata". Tsallan murna da jin dadi Nasmat tayi"Shegiya Asmart kanki yana ja
sosai. Kinma san me na tuno da kika fadi wannan maganar. Wallahi sai na tuno malamin
islamiyyar mu shi ya kamata mu danawa bomb". Hahhahaha "Kyale mugu Ai mu shikenan mun
sama hanyar mugunta kum....". Fatima ce ta Rugo da gudu hannunta rike da 'yar baby, ta nufo
su tana cewa "Aunty 'Ya ta na kuka wai madaya take so". Su kuwa suna ganin ta suka yi waje
da gudu..
_____________________

Kullum tunanin su Nasmat a kan yanda zasuyi su hada malamin su da Aljana ne. Yau ma zaune
suke su biyu a falo asmart ce tace. "Ni Wallahi bana so mu fara yin muguntar nan a kan kowa
sai malam, Wai shi mugu zai ga mugunta ai. Yanzu dai hanyar da zamu bi dan mu hada su fada
ya kamata mu nema". Nasmat tayi tsaki, "Ni fa tsoro ma nake aje yafi karfin ta kinsan fa duk
karfin aljani malami in dai mai tsoran Allah ne sai yaci ubansa". Hahhaha Asmart tayi dariya "To
ai kinji yanda kika ce in mai tsorab Allah ne, kin manta irin zaluncin Malam habib Jifa dan yana
san wannan tsigai din duk wanda ya ko harare ta ne sai ya dake sa. Wani lokacin ma fa ba'ayi
mata komai ba sai ta hada mutum da malam dan mugunta". Nasmat tace "Zainab ba, Ai ni
haushin ta nake ji Allah yasa Aljanar ta hada har ita yanda take 'yar siririyar nan kuwa zatayi
gudu". Dariya suka yi gaba daya. Suna cikin dariyar sai ga Ameera ta shigo hannunta rike da

leda baka. A yangace ta zo ta zauna a gefe daya ko kallansu batayi ba. Su kuwa tun da ta shigo
ledar suke kallo sun san saurayin ta ne ya kawo mata wani abun.





Tana bude ledar kamshin soyayar Kaza ya daki hancin su kamar wanda aka kira suka zo suka
zauna a gefanta suna Lasar harshe kamar mayu. Kaza ce dankwaleliya da Robar Madara
katuwa mai sanyi. Muguwar harara Ameera ta wulla musu hade da tsawa. "Nasmat Asmart
ku kiyaye ni Wallahi zanci uban yarinya. Kaji yara kamar mayu daga ganin abu sai ku wani taso
kamar an kira ku". "Haba auntynmu ai gani mukayi kayan Allah na Annabi ne". Cewar nasamt
"Kaji uwar iyayi wato duk zaman mu dake ban isa a ce min aunty ba sai yau dan an ganni da
dan abu na ko. To wallahi ba wanda zan bawa". Zumbur Asmart tace "al'quran sai munci".


"Sai kunci saiku.....". Ameera jin wayar ta na kara ta tsaya da maganar da ta dauko, Ta kara
wayar a kunne. "Hello Habibina, Ok in fita?. To gani nan. (Just 5mints). Tana fadar haka ta
tatara kayanta ta tashi cike da zumudi ta nufi dakin su. Kallo kawai su Nasmat suka bita da shi.
Tana shiga dakin taga Fatima a kwance rungume da 'yar ta sai barci take. Da har tayi niyar
tayar da ita kuma sai ta fasa a cewar ta idan ta tashe ta Fatima ma cewa zatayi sai ta bata
namanta. Bayan ta tabbatar da ba kowa a dakin su nasmat basu biyo ta ba kuma. Karkashin
gado ta tura ledar ta lulube da bedsheet ta fita da sauri amsa kiran masoyin ta dake kofa yana
jira. Su Asmart kamar jira suke ta fita da gudu har rige-rige suke wajen shiga dakin. Bincike
suka farayi da kyar suka gano ledar a karkashin gado. Kamar kazar ta uwarsu ce, Kowa ya ciri
cinya daya-daya da sauri suka cinye abu ga marar gaskiya. Yegot din kuwa kowa korba
Uku-uku suka yi suka hakura. Dariya Nasmat tayi na mugunta can kuma tace "To yanzu ya
zamuyi". Dan jum kadan

Asmart tayi tukun ta kyalkyale da dariya. Nasmat tace "Miye?". "Kinga kalle ni dai kawai samin
ido". Inji Asmart tana fadar haka kuwa ta dauki ledar naman taje ta ajiye a kan gadan Fatima da
take ta barci ba ruwantan mai ta goga mata a hannayen ta Sannan ta shafa mata abun madara
a baki da kagani kace ita tasha. Tana ganin haka ta...................................


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy

��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 43-44


NA. ✍KING BOY ISAH


✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍


*DEDICATED TO YOU* �

*HASSAN ATK TANKO*

*HUSAINI ATK TANKO*

*UMMU BASHIR*

*BEAUTY QUEEN*

*SAMEE KHAIRAH NOVELS*
_Jinku nake a can karkashin Zuciya na_

*PHAREEDA KHAMSHI NOVELS*
_Kuna sani inji kamar ni King din gaske ne_ lolz

*BIGBOY ISAH FANS*
_Kukan na daban ne banda kalaman da zan yabe ko ko gode muku sai dai ince. Allah ya saka
muku Allah ya barmu tare_

*KINGBOY ISAH NOVELS*

_Kun riga da kun zama 'yan uwa na jinku nake kusa da Raina. Auntys da sisters king dai na ji
daku Allah ya bar zumunci_

� Thanks d luv an supporting This book❤ Duk masoya na Ana mugun tare ‍♂



*KARSHEN PAGEN BAYA*
~"Kinga kalle ni dai kawai samin ido". Inji Asmart tana fadar haka kuwa ta dauki ledar naman
taje ta ajiye a kan gadan Fatima da take ta barci ba ruwantan mai ta goga mata a hannayen ta
Sannan ta shafa mata abun madara a baki da kagani kace ita tasha. Tana ganin haka ta.~

»»Kara bushewa da dariya. Da sauri suka fita daga dakin suka koma falo suka zauna suka ci
gaba da tadin su kamar basuje ko'ina ba. Ameera na dawowa dakin ta shiga a bakin kofa tayi
birki tana kallan kan gadan Fatima. Murje idanu tayi domin ta tabbatar da abunda idan nata ke
hangowa gaskiya ne ko kuwa. "Kutu...". ta kawo ashar ta maka yayin da ta nufi wajen Fatima
din a masifance. Dim! Dim! Ta hau ta da kulli baji ba gani, bata ma da kuka ta farka bata sana
hawa ba batasan sauka ba sai duka kawai da taji. "Wallahi, yau sai naci ubanki a gidan nan
wato har ni zan ajiye abu ke munafuka ki dauko ki ci min". 'Yar babyn ta dauka tayi tulli da ita a
bango sannan ta kama Fatima da hannu biyu ta daga chamak!. A falo ta dire ta ta dauki wayar
charger ta fara bulala ta. Kuka sosai Fatima tak tana fadin "Aunty me nayi miki?, me nayi
miki?". Ita kuwa baji ba gani kawai dukanta take, Fiddausi na kitchen tana jin kukan Fatima ta
fito a guje tana zuwa kuwa ta dauke Ameera da mari. Dafe inda aka mare ta din tayi "Kanbuh!
Ni kika mara". "An mare ki azzaluma kawai so kike ki kashe wannan yarinyar ne ko dan kinga
bata da mai rama mata ne". Safuratu dake gefe wadda su basa ganin ta tace, "Ga mai rama
mata nan kuwa". kukan kura Ameera tayi ta cakumi wuyan Fiddausi nan itama kuwa ta kamata
suka fara kunce da da naushin juna. Can Allah bawa Fiddausi sa'a ta wulla Ameeera da kadan
ta fada kan Asmart t goce tana dariya. Ameera a fusace ta taso ido cike da kwalla ta kara kama
Fiddausi. Su Nasmat kam gefe suka koma suna ta kyalkyala dariya suna kuma kara zugawa.
Karar dariyar su ce ta fito da mutanan gidan. Fitowar mama asiya tayi dai-dai da kwada Ameera
da kasa a karo na biyu. Da gudu ta rugo tubur-tubur tana zuwa kuwa ta nufi Fiddausi ta dauke
ta da mari.



Kaji 'yar iskan yarinya mutuniyar banza kawai, kashe ta zakiyi sanin kanki ne kin fita karfi amma
ki ke mata irin wannan kadi?". "Ai in ban kashe taba ita zata Fatima". Inji Fiddausi ta fadi tana
kara murtuke fuska. Mama asiya ta rike baki cike da mamaki "Innalilahi, Wai dama saboda
wannan mayyar yarinyar ne kike nema ki kashe 'yar uwarki. To Wallahi bari kiji daga yau Sai
yau kar in sake ganin kunyi fada da 'yar uwarki a kan Waccan tsinanar Fatimar ko kashe ta zata
yi ba ruwanki to ta mutu mana miye amfanin ta dama". Fiddausi hararen Ameera tayi da take
gefe ido ya kawo kwalla. "Chabb! Wallahi bazai yuyu ba. Taya ina kallo za'ayi zalunci a gaba na
Wallahi ko yanzu ta dake ta sai na rama mata. A'ah a kan me". "Haka kika ce, Haka kika ce.

Wai ni kam Fiddausi yaushe kika zama marar kunya fitsara ra haka ne. Wai yau har ni kike kallo
idona kina mayar min da magana san ranki?". Duk abunda ake Su Zuwaira gefe kallo kawai
suke ba wanda yayi magana a cikin su. Mama asiya ta kama hannu Ameera ta tura ta. "Je ki
daki Fatima muga a gaba na zata rama mata din ne?". Ameera kuwa ba kunya ta nufi gurin
Fatima da sauri da nufin Fatima ta wanke ta da mari da juyowar ta kuwa Fiddausi ta dauke ta
itama da mari mama asiya ce ta nufo ta da sauri da nufin ta dake ta. Da sauri zuwaira ta shiga
tsakanin su. "A'a Wallahi bazaki dakar min 'ya ba haka kawai. Ai idan ki zo bincike ya kamata ki
fara yi ba zartar da hukunci ba".




Mama Asiya tace "Au! Ni zaki wa gorin 'ya zuwaira, To naji malama bari inyi bincike kamar
yanda kike so. Amma fa in aka kama Fatima ce da laifi yau ba mai kwatar ta a gidan nan ni da
kaina zan ci uwarta". Ta kalli Ameera tace "Ke gaya mana me Fatima tayi miki, Duk da dai
nasan kece mai gaskiya amma tunda Su malama Bincikatu ansa mu ai dole muyi bincike". A
shagwabe Ameera ta fara magana "Mama wai fa habib ne ya kawo min Kaza da yegot Nazo na
zauna kafin in fara ci shine ya kira ni.To dan kar in barwa wadan can jarababun su cinye min
shine na tashi naje na kai karkashin gado ashe Fatima na jina shine tayi kamar barci take sai da
taga na fita ta dauki ta cinye min cinya biyu Yegot din ma ta kusa shanye wa bari kiga sauran da
ta bari". Tana fadar haka ta Nufi daki da sauri domin ta dauko. "To kinji ko?, Kinji ai ke mai
Fatima to kinji munafurcin da tayi ko har yanzu kina goyan bayanta?, Bari ta zo da kazar Ai
Kinga sai ki biyata tunda har kinda Karfin halin rama mata in an dake ai bazaki Rasa zuciyar
biya ba in tayi barna". Mama asiya ce ke kallan Fiddausi tana fadar haka. Fiddausi kam bata ce
komai ba amma a zuciyar ta tana shakkar maganganun Ameera. Asmart Rai a bace ta dan
matsa wajen kunnan Nasamat tace "Assha abu ya baci fada ya tsaya a kan mutane ni kuwa
Wallahi Aljanar na so taci uban Ameera". "Ke dai bari ai nima naji haushi Wallahi, Bomb din
nan bai tashi a dai-dai ba".




Ameera na bude kofa taga mage ta kama ledar Kazar da baki ta nufi ban daki da gudu. Ai kuwa
ta bita tana "Keeey! Keeey!". Tana wurwurga hannau alamun korarta take. Tuni magen ta
Shige Toilet din. "Wallahi sai na amso abuna ba bandaki ba ko cikin kashi zaki shiga. Shegiyar
mage ko daga ina ma oho". Ameera ke maganar yayin da ta nufi bandakin da sauri. Tana bude
kofar ta Zura kafa sai ji tayi kamar anja kafar ta fadi kasa sharaf!. Magen ce tazo tabi ta kanta
da gudu har yanzu da ledar a bakinta. "Wash! Wash!". Ameera ta fada ta kuma tashi cikin karfin
hali ta bi magen dake taga karkashin gadan Su Nasmat ta shiga. Zuwa tayi ta durkusa ta tura
kai Tana lekawa. Magen taji ta kama hancin ta. Wani mugun ihu! Ameerar tayi. Dan ji tayi
kamar zata cire mata hanci da sauri ta fiddo kanta tana laluba hancin ko jini ya fito. Sai da taga
babu tukun ta dan sama natsuwa. Kamar daga sama sai jin magen tayi ta duro a kanta ta fara
yakushin ta tana karta mata farce a ko'ina Ihu! Ta fara tana faman kaka be ta. Can Allah ya bata

sa'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login