Showing 42001 words to 45000 words out of 103342 words

Chapter 15 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

Advertisement

kingboy   

08 Jul 2025

5147

kitchen". Watsewa akayi kowa yaje yayi shirin
makaranta. Su mama asiya kuwa mai gadi suka bawa Naira Dubu suka aike shi yaje ya soyo
musu Indomie da kwai. Asmart da nasmat a wajen mai shayi suka tarar da Fatima ita har ta
karya Tana zaune tana jiransu. Suma kudi suka bayar aka dafa musu indomie tukun suka nufi
makaranta._
*______________________*

_Zaune yake yana cin Garau-Garau Yana ci yan girgiza kai daka ganshi kasan yana jin dadin
abincin Sai da abincin ya rage baifi Cokali hudu ba ya kare, Mutumin ya Wani murtuke ya bata
rai!. "Rafi'at! Rafi'at! Rafy!". Kiran yake kwalla mata da karfi. Ba'a jima ba sai ga wata budurwa
ta fito ba laifi tana da kyau dai-dai gwargwado. Gaban shi ta durkushe "Mai gida gani". Mari ya
kwada mata wanda har sai da taga Taurari nan fa ta kwada ihu!. "To fa safiyar ai tayi, Ke dai
Rafy baki yi dacen miji ba ko kadan Wallahi". "Wai har yanzu Umar bai dai na dukan Rafy ba".
Makwabtan su ne ke wannan Hirar. "Ina fa malam ai kullum sai ya dake ta". "Ashsha! Kai
amma dai Allah ya shiryi Umar, gashi daga kayi masa magana sai ya hau ka da masifa yace Ai
ba matar ka bace". "Ai lamarin sa sai Addu'a, Rafy tana da hakuri"._

_"Cikin bacin Rai da masifa umar yace "Yanzu ke Dan Uwarki kinsan wake bai dawo ba shine
zaki kawo min abinci wato inci inshiga mutane Ina tusa ana kallona Ana dariya, Haka kike so
ko?". Ya fada yana kallanta. Cikin kuka tace "Mai gida dan Allah kayi hakuri Wallahi na dauka
ya dahu ne". Cokali ya dauka ya kara cika shi ya kai baki, Sai da ya kusan hade shi gaba daya
ya Furzo!. "Kan uba! Ai banji bama sai yanzu haka kika cika yaji a abincin ashe, Ashe so kike ki
kashe ni". Da sauri ya tashi ya nufi daki. Kamar tasan abunda yake shirin yi ta fara fadin "Mai
gida dan Allah kayi hakuri bazan kara ba Allah". Fadi take da karfi tana mai-maitawa. Da wani
Bakin Belt ya fito yana zuw kuwa ya fara Zane ta. Yana Fadin "Bari ni in illataki kafin ki kashe
ni". Ihu! Take tana bashi hakuri amma shi ko kadan baya da alamar Sasautawa balle ma ya
kyale ta. Da dai taga yana neman ya hallaka ta sai ta tashi ta ruga da gudu waje, Domin Tasan
ba wani wanda zai kawo dauki. Haka yake in yana bugon ta mace ta zo Kwatar ta har ita yake
hadawa ya daka. In kuwa namiji ne ya kore shi._

_Fitar ta tayi dai-dai da isowar su Fatima sai tin gidan. Haka ta fito tana kuka shi kuwa ya biyo
ta yana fadi "Oya zo wuce ki koma ciki, Ko kuwa Wallahi yau in farfasa miki jiki". Hakuri kawai
take bashi tana karawa. Dake tasan halinsa Ba dan ta so ba ta shige gidan a guje. Su Asmart
kuwa abun ne ya basu mamaki. Nasmat tace "Kuturun uba!. Lalai akwai masu hakuri yo ai ina
kamar wannan Wallahi mutumin nan bai isa ya dake ni in kyale sa ba, Wai dan yana aure na,
Haba kamar wani ubana". Dariya Asmart tayi. "Wai ke sai yau kika taba ganin wannan
azzalumin kenan. Ranar mu ai har ciki sai da muka shiga ni da Ameera ai kuwa ya biyo mu da
kadan y zabga min bulala". Gaba suka yi Aljana Safuratu kuwa tun da taji zancen su nasmat ta
fita daga Jikin 'yar tsana,Tace "wannan matar tana bukatar Taimako na, Kuma zan taimaka
mata. Cikin gidan ta shiga ta iske su ya zaunar da ita yana fadar, "Yi min shiru muna fuka.
Yanzu zan fita kuma ga naira Hamsin can a cikin aljihun rigar da na cire ki dauka ki auno
shinkafa kiyi Cefani ki dafa min Farar shinkafa da miyar tumatur (Jar miya). Cikin kuka tace
"Haba mai gida naira hamsin ai baza ta isa ko cefane ba". Tsawa ya daka mata hade da daga
hannun " Yi min shiru ko in make ki Shegiya ni hka na yi niyar badawa kuma dole kiyi min.
Kuma Wallahi idan na dawo na tarar bakiyi ba. Hmm kema kinsan sauran". Yana gama
fadar..........................._


*TABB! LALAI ANYI MUGU A NAN*


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy








mu kayi like.

Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn

https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy





��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 53-54


© *KING BOY ISAH* ✍



*YAU SAI INGA WANDA ZAICE NAYI MINTSILI, (KARAMI) PAGE* �

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*

_*WANNAN PAGEN DIN NAKU NE*_

✍ *ZAINUDEEN ZAIN* ✍

✍ *SANAH S. MATAZU* ✍

✍ *SANAH SHAHADA* ✍

✍ *RASH KARDAM* ✍


_Malamai kuma abokai a gare ni. Ubangiji Allah ya albarkaci Rayuwar ku, Yasa ku gama da

duniya lafiya. Ku Ukun Allah ya baku mazaje na gari wanda zasu zame muku rahama, wanda
zasu zare mayafin bakin cikin ku, su lulube ku da na farin ciki. Haka kai ma dan uwa
Zainudeen, Allah ya baka Salahar mace mai sanka dan Allah mai hakuri da juriya. wacce zata
Zame maka haske ta kore duhu a cikin rayuwarku._ � Ameen Allah ya amsa....

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Yi min shiru ko in make ki Shegiya ni hka na yi niyar badawa kuma dole kiyi min. Kuma Wallahi
idan na dawo na tarar bakiyi ba. Hmm kema kinsan sauran". Yana gama fadar.~

_≥»Yana gama fadar haka ya juya ya fice daga gidan. Safuratu tsaye tayi tana tunanin ta ina
zata fara ji da wannan matsala, Can kuma sai ta bace bat!. Rafy na zauna sai kuka take abun
duniya ya ishe ta ita kam yanzu bata ma san miye abun yi ba. Wata dattijuwa ce tayi salam
Rafy cikin Kuka-kuka ta amsa matar ce ta zo daf! Da ita ta sama waje ta zauna Rafy ba abunda
take sai binta da idanu wanda sunyi jawor dan tsabar kuka. Matar ce ta danyi gyaran murya
tukun ta kalli Rafy cike da tausayawa "Rafy Nasan kina cikin matsanan matsanan ciyar
damuwa, Naji labari kullum wannan mugun mijin naki sai ya dake to dan haka ne ma..." Da
sauri Rafy ta daga mata hannu "Dakata baiwar Allah naji na gode da tausayawa amma ba
ruwan ki wannan Kaddarar rayuwa ta ne, Dan haka dan Allah tashi ki tafi abunki". Matar ta dan
muskuta kadan tace, "Haba Rafy ki saurare ni mana ni taimakon ki zan...". CikinTsiwa Rafy tace
"Dakata malama nace bana bukata ki tashi ki tafi abunki, Wai ke din wace ce me ruwanki". Rafy
ganin matar na neman dauko wani sabon zance ta tashi ta kama hannunta ta jata har waje tana
cewa. "Naji na gode da shawara". Tana tura matar waje ta garkame gidan da sakata sama da
kasa. Juyowa tayi da wani kukan na Takai'ci A zuciya cewa take "Ba taimakon bane bana so.
Amma Nasan bazaki iya taimaka min da komai ba". Daga bayanta taji maganar matar tace
"Rafy kiyi hakuri amma fa ni bazan bar gidan nan ba sai na taimaka miki"._




_Rafy na juwa taga Wannan matar ce sai ta kwada ihu! Ta ruga daki a guje nan ma ta rufo
dakin._
*__________________*

_Su mama Asiya ne zaune a falo har wajen goma da rabi basu karya ba suna jiran Mai gadi har
yanzu bai dawo ba. Mtseeww Mama Asiya tayi tsaki, "Wannan mai gadin sai naci ubansa in
yazo Wallahi. Haba wannan ai iskanci ne. Ya zai barmu ko kari babu ya tafi uzurinsa". Tana rufe
baki sai gashi ya shigo da sallamar sa. Mama Asiya kular take kallo tana mata fassarori Iri-iri
kamar da abu ciki kamar babu. Yana karasowa ya ajiye kular a kasa ta saki sauti Kwangal!
Daga ji kasan ba komai a ciki, Gaba daya binsa suke da mugun kallo, Jira suke kawai yace bai
samo ba su bal-bale shi da masifa. "Hajiya Wallahi matsala aka samu wajen Mai shaye Biyar
naje Duk inda naje sai in samu indomie din ta kare". Zuwaira tace "Kuturun uba!, Amma wallahu
kayi mugun rai na mana wayo Akwai mai shayin da za'a je gunsa A rasa Indomie ne?"._

_Haba kyale shi Zuwaira, Inaga dai Wa'adin zamansa a gidan nan ne ya cika. Amma in ba
iskanci da rainin wayo ba ya za'ayi ace kamar mu mu aike ka ka dawo mana da kula wai babu".
Mai gadi ganin Aikin sa ya fara tangal-tangal yasa shi fara bada hakuri. Yana cewa "Dan Allah
kuyi hakuri karku min sanadin aiki na Wallahi in kuna ma so yanzu sai inje in sayo in dafa
muku". "Kutumelesi Dallah tashi ka bace mana karka fusata ni yanzu in sallame ka a aiki, Dan
ma ka raina mana wayo mune zaka yiwa girki?". Tashi yayi ya fita da sauri ya barsu nan suna
tsaki. Hauwa ta kalle su "Ni fa Wallahi bazan iya wannan abun ba, wannan ai cutar kai ce kawai
ku tashi muje mu dafa ko indomie ce". Zuwaira tace "Sai dai in ke zaki yi taimako ki dafo min ki
kawo min. Amma ni tunda nace bazan shiga kitchen ba to bazan shiga ba sai rana tayi". Mama
asiya tace "Wallahi ko ni bazan shiga ba sai dai ki taimaka ki daho ki kawo mana". Mikewa
Hauwa tayi zumbur! "Kuturun kare, To alqur'an ba wacce zanje inyi aiki in dafa abu in kawo
mata tana nan ta Mimike kafafu a falo tana shakar AC". Mama Asiya ta tashi tana nuna Hauwa
da yatsa "Ke karki kuskura, Wallahi karki kuskura ki zage ni". "Ni kam ban zagi wata ba amma
dai maganar abinci nace bazan daho in kawowa wani ba". Tana fadar haka ta wuce ta nufi
kitchen._





_Inda suke ajiye kayan abinci ta shiga. Tsaye tayi tana kallan dan Sito (store ) Taga wayam ko
Kangon buhu babu balle ma asama mai wani abu a ciki. Haka ma kwalilikan indomie babu ko
daya. Tsawa tayi cik! A wajen tama rasa abunyi. "Aunty Asiya!, Aunty Asiya!". Tun daga can
take kwalla kira Asiya na jinta amma tayi kunnan uwar shegu, ta kyale ta. Sai da ta gaji da
kwalla kiran tukun ta fito ta gayawa su mama Asiya abunda ke faruwa. Tubur-tubur ta tashi da
sauri ita da zuwairar suka nufi kitchen din hauwa na biye da su. Tsaye sukayi suna kallan Store
din suna kallan juna._
*_______________*
_Rafy na daki duk tsoro ya kamata kallan kofar kawai take. Mace ta gani ta ratso ta cikin kofar,
Wani mugun kara tayi a tsorace ta haye kan gado ta wani kudun-dune cikin blanket. "Sunana
Safuratu ni aljana ce amma ba muguwa bace ni. Dan ni nama tsani mugu, Naga mijin ki kuwa
mugu ne shiyasa ma nazo dan in taimake ki. Dan haka ki saki jikin ki karkiji tsoro na". A hankali
ta dago tana hada ido da Matar kuma sai ta kara shigar da kanta cikin bargon. Tana magana
cikin tsoro, "Dan Allah kiyi hakuri ki tafi na gode amma mijina ba mugu bane dazun ma laifi nayi
masa shiyasa ma ya dake n...." Kafin ta rufe baki Aljanar ta daka mata Tsawa wanda sai da ya
rikita ta gaba daya. "Bana san iskanci fa, Wato dan kinga ina lalabaki shine kike min wannan
kafiyar Yanzun nan zan mayar dake kaza kuma in kashe mijin naki in baki bani hadin kai nayi
abunda ya kawo ni Salun alun ba". Dajin haka Rafy tayi sauri ta fito. "Dan Allah kiyi hakuri karki
mai dani kaza Wallahi zanyi duk yanda kika ce Aljana". Aljanar ta dan matsa kusa da ita ta

zauna. Rafy duk a tsorace take. "To da dai yafi, Kuma ina so ki saki jikin ki ki kaddara a ranki
Kamar da mace 'yar uwarki kike magana Ba Aljana ba. Yanzu fara bani tarihin rayuwar Auren
ku shin baya sanki ne Yake miki irin wannaj duka ko kuwa?". Hawaye ne yq fara Go slow daya
bayan daya a idanunta kafin tayi magana cikin kuka._




*A social net muka hadu da Umar har soyayyar mu ta zama ta zahiri Domin dan anguwar mu
ne ban sani ba sai daga baya. muna san juna sosai. Nida umar matsalan da aka samu shine
Iyayena masu kudi ne Shi kuwa umar Okada yake da shi yake ciyar da iyayesa ma. Bayan nayi
candy sai baba na yace aure zaiyi min kuma auren gida. Wato da dan yayan shi zai hada ni. Ni
kuwa na nuna rashin amincewa ta nace umar nake so. Yayan baban nawa dake shi ya kawo
shawarar a hadani da dan nasa da yaji nace umar nake so sai ya hakura ya janye. Yace ba
laifina bane tunda ba'a tambaye ni wanda nake so ba. Mahaifina kuwa gaba daya ya kasa
fahimta. Daga karshe ma cewa yayi zaiyi min Aure da Umar din kuma zai min duk abunda uba
kewa 'yarsa amma idan wata matsala ta biyo baya kar in ko nufi hanyar gidansa. Haka na
amince domin ji nake bazan iya rayuwa da kowa wanne namiji in ba Umar ba. Haka aka daura
auren mahaifina duk a fusace yake dani ko hudubar kirki baiyi min ba. Wannan gidan umar ya
kama mana haya muna zaune lafiya lau ba wata matsala kullum sai farantawa juna rai. na
tsawan wata biyu, A cikin wata na uku umar ya bullo da wani sabon tsari wanda gaba daya ban
sanshi da shi ba. Yau wata na biyu kenan Kusan kullum sai umar ya dake ni. Ba fira mai dadi
irin ta ma'aurata. Na kai kararsa gurin iyayensa Suka kira shi a gabana suka mishi tatas, Suka
mai fada sosai a nan yace bazai kara ba. Ranar da muka dawo gida Kashe ni ne kawai umar
baiyi ba. Gida kuwa sau daya naje da suna yaji Babana ya koro ni yace ma karya kara ganin
kafata a gidansa duk abunda ya faru dani ba ruwansa wai ni naja wa kai na. Ranar da Umar
yake jin mugunta yasan bani da kudi kuma yasan babu mai bani haka zai dauki Kudi kalilan
kamar yanda yayi yau. Yace in mishi wani abincin mai tsada wanda yasan kudin da ya bani
bazasu yi ba. Idan ya dawo ya iske banyi ba haka zai same ni yata maka kamar jaka. Nayi
kuka na zubda hawaye a kullum kuma addu'a nake Allah ya kawo min mafita Ni kam ba kudi
nake so ba. Farin ciki da soyayyar da Umar ke min a da su nake bukata su dawo.*




_Safuratu tayi ajiyar zuciya tukun ta dafa Rafy tace, "Allah sarki haka rayuwar take, wani sai
kayi masa tuwan shinkafa idan ya tashi sai kaga ya biya ka da bak'in kanzo. Ina so in miki
Albishir da cewa Allah ya amsa addu'ar ki. In sha Allah zan mayar miki da mijin ki kamar da zan
sai ta shi. Amma fa sai kin bani hadin kai". Rafy ta kalle ta cikin kuka, "Me zaki mishi, dan Allah
karki taba lafiyarsa Wallahi ina sanshi duk abunda yake min ban taba fatan rabuwa da shi ba. Ni
kam fata na a gare shi Allah ya shirya min shi". Dan murmushi Safuratu tayi, "Karki damu ba
abunda zai same shi nayi miki alkawari, Misali yanzu idan umar zaiyi tafiya na kwana biyu haka,

Zai iya kai ki gidan ku yq musu bayani kuma su amince?". Rafy girgiza kai tayi alamun aa. "Sai
dai gidan Yayan babana". Aljanar tace "Ok dauko hijab dinki mu tafi can". Tana fadar haka ta
tashi ta fito waje. Ita kuwa Rafy ta yi sauri ta dauko hijab da fitowar ta maimakon ta tarar da
Safuratu sai Umar ta iske tsaye cikin manyan kaya ya wani bata rai!. Durkusawa tayi tana
karkarwa dan tsabar tsoransa da take ji. "Me gida sannu da zuwa, yaushe ka dawo". Cikin fada
yace ban sani ba ina abincin da nace kiyi". In-ina ta farayi "Um um, dama-dama.." Harara ya
wurga mata. "Dama me?, Shin yanzu da kika sako hijab ina zakije?". Kuka ta fara tana fadin
Wallahi ba "Inda zani". Dariya Umar din ya fara yi ita kuwa ta saki baki tana kallansa cikr da
mamaki domin rabun ta da ganin umar na dariya Tun baya da wata biyu. "Matsoraciya ashe
haka kike mugun tsoran Umar din. To ba Umar bane wannan *ALJANAR FATIMA* ce, Nice nayi
sufarsa nayi kyau kuwa?"._




_"Eh kwarai mai gida kayi kyau". Ta fada da sauri Aljanar ta fahimci har yanzu Rafy bata yarda
ba shiyasa ma tayi mata Muryanta, Sai a lokacin Rafy ta yarda ta mike tsaye. "Yanzu zuwa
zamuyi in kai ki gidan yayan babanki ince masa zan danyi tafiya ne na kwana biyu, Kuma ba
dadi a barki a gida ke daya shiyasa ma na kaiki ce, Ni kuma sai in koma sufarki in dawo nan in
saita Umar tukun. Kina ganin yayan babankun zai yarda kuwa?". "Eh zai yarda". Inji Rafy "Ok

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login