Showing 15001 words to 18000 words out of 103342 words

Chapter 6 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5031

ni banga speaker a jikinta ba"
. fatima ta karbe abunta tace "Baba ai itama da baki take yi kamar mu baka gani bane?".




yace "eh ni ban gani ba, amma bari in na koma zan tambayi mai shagon inji ko tana magana.
Domin ni ta bani tsoro fa mamana". Haka dai yaci gaba da tuki cike da mamaki har suka karasa
gida. fatima ta sauka da gudu tana murna ta nufi cikin gida rungume da yar babynta a parlo ta
iske duk yan gidan yara nata rashin ji masu wasa nayi masu rigima ma hk. ai kuwa yan yaran
na ganin yar babyn suka yo kan fatima wannan ya karba wannan ya figa wai ko wane yaro sai
ya je gurin uwarsa ya kama kuka wai a kwace a bashi. can wasu yara marar ji guda biyu daya
ya kama wajen kan yar babyn daya kuma ya kama kafafun sai jayaya suke wannan yana so ya
karbe wannan ma yana so ya karbe fatima kuma sai kuka take zasu karya mata yar baby gashi
ba dama tayi mgn.



lokacin alhj ya shigo. "kai! kai! ku wane irin mararsa jin magana ne. zaku balla mata abu bata
kayanta maza". mika mata sukayi. ta karba ta nufi dakinta asiya ta harare ta tace a zuciyarta
"munahika ai alhajin zai tafi zaki ci ubanki". alhj yace "yanzu ku kuna gani a gabanku zasu
batawq yarinya abu a gabanku amma ko kuyi magana. haba asiya kece babba fa ko sauran
basuyi magana ba ai ya kamata ke kiyi mawa yaran magana". "uhm ai ni kullun a wajenka
marar adalci ce to amma yanzu kai ga adalci nan a fili ka nuna mana, tunda ga yara nan da
yawa a gida kuma duk yayanka ne amma ace ka ware fatima ita kadai ka saya mata abu.
wannan shine adalci ko?". Ran alhj ya bace har zaiyi mgn kuma sai ya fasa ya wuce up stairs.
yaje dakinsa ya dauko kudi yq fito yayi tafiyarsa.



su Zuwaira sukayi dariya sukace "aunty asiya kin min daidai ke kadai ce maganin alhj a gidan

nan". asiya tace "hmm ku kyale sa ai yau saina toya yar babyn nan muga ta tsiya sai inga me
zaiyi haba ya zai dinga fifita wacce kudabukar yarinyar a kan sauran yara bari inje gurinta". su
Zuwaira binta kawai sukayi da kallo. ta tashi buzun-buzun ta ta nufi dakin yara. fatima zaune
take a kan gadanta ta zaunar da yar babyn tana cin bisket itama tana tura mata a baki. tana ci
ci diyata daga bakin. kawai sai taga bakin ya bude. bata wani firgita ba sai ma dadi da taji. ta
tura mata bisket din tace "kin koshi.?



lokacin asiya ta karaso gurin ta kama yar babyn da hannu daya ta wullata jikin bango ta fado
tim! ta kuma wanke fatima da mari "shegiya yarinya me kike a nan tun dazu ina can ina jiranki
zan aike ki kin wani shigo daki kin zauna. dama nasan wannan yar babyn da kika samu ita zata
dinga hanaki aiki amma bari ynz in dauke tq in yayankata in toya muga ta tsiya". fatima ta fashe
da kuka tana bawa asiya hakuri karta yanka mata ya' abun mamaki fatima na fara kukan suka
jiyo kuka a baya. asiya ta juya baya. yar babyn ta gani a zaune tana kuka harda ruwan hawaye



Abunda yayi mutukar tsorata Asiya kenan, da gudu taje ta shige karkashin gado, fatima na
ganin haka ta sauko tuni tama bar kukan ta fara dariya, mama asiya ta bata dariya. Zuwa tayi
ta dauka yar babyn tana lalashinta. "Yishiru-Yishiru diyata. Mama asiya ce ta taba min ke ko?"
Kunnuwan asiya sunji lokacin da yar babyn tace "Eh itace". Cikin wani karamin voice, "To yi shiri
bazata sake ba". Asiya a dan tsorace ta fito daga nesa tace "Au! Fatima dama yar tsanar taki
tana magana?". "Eh mama asiya ai tun a mota ta fara magana, babama ya dauka bata
magana". Asiya tace "to dan kawo ta mu gani". Amsa tayi ta duduba amma bataga speaker ba.
"Fatima ina speaker da wajen sa battery?". Mama ai da baki take magana kuma ba'a saka
mata battery, yanzu nayi mata wankq bata bushe ba".



Abuda ya fadowa asiya a rai shine. Hawayen da ta gani wato ruwan da fati tayi mata wanka ne.
Ai kuwa ta maka diyar da kasa tasa katuwar kafarta ta taka tabi ta samanta ta wuce tana
hararen Fatima hade da cewa. "Dauki yar iskar yar tsanar ki, ko dan wannan ai tama wuce yar
tsana a girm saidai ace *ALJANAR FATIMA*. Fatima bata tanka mataba da sauri taje ta dauki
yarta taci gaba da yin wasa da abunta.


A falo ta iske su Zuwaira suna nan inda suke basu tashi ba. Asiya tana dan dangeshi ta karasa
ta zauna ta saki wani gwabran nishi. Wanda yasa su Zuwaira saurin tambayar "Lafiya dai aunty
babba, fatan kin yayanka shegiyar yar tsanar nan..." Tarar nunfashinta tayi ta hanyar cewa, "Ina
fa 'yar tsana da ta tsoratani. Ashe wai tana magana, ban sani ba ina shiga dakin na karbe ta na
maka a bango juyawar da zanyi sai naganta tana kuka harda hawaye. Ai kafin kice me tuni na
shige karkashin gado na dauka ai aljana ce, washh! Wllh har yanzu gabana faduwa yake". Su

hauwa najin haka suka kwashe da dariya hararar da ta daka musu ita tasa su hadiye dariyar
dan dole. "Wai ina su asmart ne ko har yanzu basu dawo daga wajen kitsan ba". Asiya ta
tambaya. "Eh wllh kinga har yanzu basu dawo ba, Ni jirama nake su nasan su zasu lalata
wannan 'yar tsanar". Zuwaira ta bata amsa. "Ai kinji shiru gidan dake basa nan".


Su Nasmat kuwa na can gidan kitso gaba daya su hudun harda Fiddausi da ameera. Dake mai
kitsan tasan halinsu suna zuwa tace su zata fara yiwa su tafi abunsa.kafin a gamawa asmart
kitso saida nasmat ta Zubar da duk ruwan gidan, wai wanke kai take daga ta wanke sai ta
shinshina tace wari yake. su Fiddausi dama basuyi magana ba dake sunsan halin ta idan ma
sukayi mata magana baji zatayi ba. Da sauri mai kitsan ta burbura tayiwa asmart kitson Nasmat
duk ta jike kan, Amma a haka mai kitsan tace tazo a mata dake ya dansha iska. Haka itama
asmart tata barna kafin a gamawa nasmat saida tasa yara sunfi biyar kuka a ciki harda wanda
ta fasawa kai. Jini na zuba yaran tafi ya gayawa uwarsa. Asmart tazo ta kama nasmat kitsan ma
ba'a gama ba sauran layi biyu. Amma a haka suka gudu, basu zame ko'ina ba sai gidan aunty
Sakina yayar mamar su ce. (Wato mama asiya.)




,
Matar yar lukuta wacce itama jikinta ya kai na mama asiya. Nan ta tashi tana musu sannu da
suwa. Bayan sun gaidata. Tace, "Asma'u uwayen rashin ji ziyara aka kawo min yanzu da
yamman nan?". Bayan sun kalli junane asmart tace "Eh mama asiya ce tace mu zo kuma ma a
nan zamu kwana". Sakina tace to madallah ai naji dadin zuwanku dama ga aiki nan kaca-kaca
ya min yawa a gida sai ku dan kama man muyi sauri mu gama kan magariba". Cikin daga
murya nasmat tace, "Kutumelesi kiji wannan matar wai mu tayata aiki". "Yaseen ni dai bazanyi
ba saidai ke ki tayata". Cewar Asmart "Kutt kinga malama yayar mamar ku ce ba yayar mamana
ba. Dan haka ko kwano daya bazan wanke mata ba". "Ke zaki tayata". "A'a wallahi ke dai".
Garda ma suka hauyi a tsakanin su ko wacce nacewa ita bazatayi aikin ba, abun har ya kaisu
ga kunce, ki'kir-ki'kir suka kama wai su da gaske fada zasuyi.....,.............```


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan writers nee king boy












��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 19-20


NA. KING BOY ISAH



✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍



IN DEDICATION TO YOU
*KHADIJA CANDY* *_ALLAH YA BAR ZUMUNCI, YASA KIFI HAKA NA GODE DA ADDUO'IN
DA KIKE MIN. KEMA KUMA ALLAH YA KARQ MIKIN DUMBIN BASIRA DA HIKIMA DA
FASAHA, ALLAH YA KARE MANA KE DAGA SHARRIN MAHASSADA DA YAN ADAWA DA
MAKIYA. ALLAH YA TSARE MANA KE DAGA SHARRIN DARE. SHARRIN RANA, FATAN
KOFOFIN ALKHAIRAI SU BUDE A RAYUWAR KI DUK NA SHARRIN SU GARKAME. AMIN
YA ALLAH.*_

_SAM KALAMAN BAKINA SUNYI KADAN DA SU BAYYANA IRIN TSANTSAR FARIN CIKIN
DA NAKE JI YAYIN DA NAGA SAKONIN MASOYANA SUN SHIGO WAYATA._

FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----


*KARSHEN PAGEN BAYA*

~Dan haka ko kwano daya bazan wanke mata ba". "Ke zaki tayata". "A'a wallahi ke dai". Garda
ma suka hauyi a tsakanin su ko wacce nacewa ita bazatayi aikin ba, abun har ya kaisu ga
kunce, ki'kir-ki'kir suka kama wai su da gaske fada zasuyi.~

```»»Aunty Sakina da ta saki baki tana kallansu ita kallansu take abun yaso ma ya bata dariya
kuma sai ta basar. Ta cire takalmin ta ta fara kwada musu da sauri suka saki juna. "Kaji yan
iskan yara daga zuwa zaku mayar min da gida kamar gidan dambe?, To wallahi bazan iya ba ku
tatara ku koma na gode allah ya baku ladan ziyara". Suna jin ta fadi haka sai suka shiga bata
hakuri Da rokonta a kan tayi hakuri ta barsu.


Bacin rai tanuna musu sosai ta murtuke fuska tace, wallahi kafin in futo daga dakin nan ku bar
gidan nan in kuwa ba haka ba wallahi sai jikin ku ya gaya muku". Tana gama fadar haka ta
shige dakin. Su kuwa kofar dakin sukaje duk su biyun sukayi Neldown kamar wasu mutanan
kirki.

Sanda tayi kamar mintuna biyar tukun ta fito daga dakin sun bata dariya a yanda ta sansu da
rashin ji yau sune roko harda durkusawa. Nan dai tace musu ta hakura amma fa aiki ba'a
janyewa'. Da sauri sukace "Mun yarda".

A can kuma gidan mai kitso uwar yaran da aka fasawa kai ce, tazo da wani danta saurayi dauke
da wata gora. Da ganin matar kasan jarababa ce, ko yanayin tafiyarta zai iya shedama ba da
alkhairi take tafe ba. "Wace yar kutu... Ce ta fasawa yarona kai, ku nuna min ita yanzu itama
insa a rotsa mata nata kan". Matar ce ta shigo gidan da wannan furucin lokacin da dan nata
kuma ya daga gorar yana shirin makawa duk wacce aka nunu. Da gudu Fiddausi da Ameera
suka Ruga dakin mai kitso. Tana shirin binsu Mai kitsan ta shiga gaba ta tare kofar dakin tana
"ki saurara basu bane ki saurare ni, kannansu ne basu ba". Tsayawa tayi tana jijiga. "To ai anzo
a dai-dai kenan yanzu in nasa aka fasawa daya daga cikin yayyen nasu kai, kinga ai anyi 1-1
ko". Aa dan allah ba haka za'ayi ba kinga nidai kitso suka zo min nan kuma sun tafi gida tun
lokacin da sukayi wannan ta'asar. So abunda yafi shine ki bisu can gidan Alhaji salim din".


"Kutumelesi dama yan gidan alhaji salim ne. Kai zo muje ba zama lafiya yau zasu san sun takali
wutar dafa kansu". Fuwww!! Ta wuce yaran na binta bayq da kulki a hannu. Tun daga get suka
fara rikici da mai gadi, yaki barinta tq wuce, sanda ta shsmmace shi tukun ta ingiza shi ya fadi
da sauri suka shiga. "Asiya! Asiya! Asiya!". Da duk illahirin karfin sautinta take kwalla wannan
uban kiran. Ta cire gelen dake makale a kafadarta ta daura a ku'gu.



Da sauri su asiya da sauran yan gidan suka fito suna tambaya "lafiya-lafiay". Cikin masifa da
tsiwa tace, "Ina fa lafiya ai tunda kuka ganni a haka kunsa ba lafiya ce ta kawo ni ba. Wannan
bala'eun 'yaran naku ne suka fasawa dana kai dan haka nazo ko dai a fiddosu insa a fasa musu
kai. Ko kuwa kuga tashin hankali". Nan ta fara jijiga tana cewa dan saurayin nan ya matso kusa
ya shirya. Asiya tace "Innalilahi yanzu su asmart bazasu barmu mu huta ba, Rikicin nasu ba iya
gida ya tsaya ba kenan. Kinga mariya zo muyi wata magana".



Mariya tace itafa ba inda zata sai an fiddo da su asmart ta rama wa yaranta tukun ta tafi daga
gidan nan domin har wani hauka-hauka take tana tsalle-tsalle lokacin da Asiyar kecewa suzo su
sasanta. Da kyar asiya taja hannunta bayan dakunan su. Basu fi mintuna biyu ba suka fito suna
washe hakora. Gaba dayan fishin da Mariya tayi ya zama tarihi ba abunda take sai godiya wa
hajiya. Sauran matan sunyi mamaki abun ya daure musu kai. Mariya tayi musu sallama tacewa
Dan saurayin "Kai zo mu tafi ai na yafe musu". "Haba mama Najeef fa aka fasa wa kai
shikenan munzo a rama kice wai kin yafe". "Kai zanci ubanka fa wai bani nake maka magana
ba?". Yana dan gungunin sa ya bita suka fita. Sunje fita mai gadi ya leko ta kofa hade da cewa
"Jarababiya kawai allah ya isa turenin da kikayi". Da sauri ta juyo a fusce zatayo kansa "Me
kake cewa". Habawa ai da gudu ya shige dakin ya rufo.


Bayan su Asiya sun koma cikin falo Zuwaira tace "wai aunty dukan matar nan kikayi ne ko kusa
warning kikayi mata. Naga lokaci daya ta wani saukko". Yar dariya asiyar tayi hade da cewa,

"Hmm ba ko daya daga ciki kinsan fa in kikaga mutum na irin haka to in kika bincika harda
talauci a ciki, Naira 500N na bata kawai nace taje ayi mishi magani, Shine fa kinji harda su
godiya". Dariya sukayi gabaki daya Hauwa'u tace "Gwara da kikayi haka wllh dan da alhaji ya
zo ya tarar da ita. Bama su asmart ba mu kanmu bazamuji dadi ba". "Ashe dai kina ganewa
gashi yau a dakina yake kinsan yanda muke da shi dama. Ai shiyasa nayi saurin watsawa
Wutar nan ruwa".

************

Kwance take a daki ita kadai tana barci. Wata mahaukaciyar dariya mai gigitarwa ce ta daki
dodan kunnan ta. Bata shirya ba ta tashi zumbur! A tsorace, tana waige-waige "Alhaji! Alhaji!
Dubawa tayi gefan wajen wayam ba alhaji. Hahahahahaha! Dariyar mace ta jiyo kamar a
downstairs a dan tsorace ta tashi ta bude kyaure a hankula ta laleka bataga komai ba, hakan
yasa ta idasa fitowa. Da fitowarta Kofar dakin ta taji an banko da karfi kamar za'a balla, dan
kara tayi ta zabura kuma. Lokaci ta nema bude kofar amma sai taji kamar an Garkameta da
kwado. Abunda yayi mutukar girgizata kenan. A saman dakuna ne guda hudu dakinta ne a can
karshe sai na Zuwaira sai na Hindu wanda yanzu alhaji ya mayar nasa. Na karshen kuwa na
Hauwa'u ne. Dan lungun dakunan a haske yake fes da fararen Gululuka. Lokaci daya tada
wutar ta fara farfari. Kwayayen suna wata irin girgiza dariyar Yarinya ne ya biyo baya dariyar
marar dadin ji. Ahhh! Ahhh! Da karfe ta fara ihun itama. Ta durkushe a gurin ta sa hannaye ta
rurufe kunnuwanta. Hade da runtse idanu. Dif! Taji komai ya tsaya an bar dariyar haka kwayayin
sun daina girgiza da farfarin da suka. Mikewa tayi cikin kuka kuka ta fara tura kofa da karfi tana
fadin "na shiga uku ni Asiya me ya fito dani. Gashi sai tsorata ni ake yi".



Ta baya taji an tabata wata murya yara taji ance "Mama Aciya juyo cigan ni nayi kyau?". A
hankali ta fara juyowa dan ganin mai maganar a tsorace. Koda idanunta sukayi tozali da mai
maganar Aljanine yazo mata asuffar Iliyasu babban Dan hauwa. Kanshi a rabe yake gida biyu
hayaki ne ke fita da wani turiri a ko wanne bare. Aisiya na ganin haka jikinta ya fara bari ta hau
kyarma. Dariya taji ya farayi marar dadin saurare. Ya nufo gunta yana fadin "Nayi Ceau (kyau)
kuwa mama aciya(Asiya)?". ta kwada ihu! Ta zuba guje ta nufi Downstairs tsabar firgicewa Bata
iya kirga iya matatakalan da take tsallakewa. Sabanin 'da, da in zata sauka da Daya-Daya take
yi a hakan ma a hankali.



Tana saukowa tayi wata uwar tirjiya a falo nauyin jikinta da kadan ya rinjayeta ta fadi. Ba wani
abu yasa ta tsayawa ba. Sai ganin wata yarinya da ke zaune a Falon cikin wasu fararen kaya
masu dauke ido. Yarinyar ta juya bayane bata iya gane ko wacce ce. Hakan yasa ta fara
matsowa a hankula tana kiran sunayen yaran gidan wanda take tunanin ko daya daga ciki ne.
"Dan ubanki fatima me kike yi ne a nan?. Cikin wannan dare?". Shiru bataji amsa ba hakan ya
tabbatar mata da ba fatimar bace. A hankali take tafiya tana nufar wajen da yarinyar take. "Ba

fatim bace?. Shimsiya ce? Sa'adatu ce?. Ko dai salma ce?". Sunan jikokin ta take ta jerowa
wanda take tunanin ko sune. Lokacin ta karasa wajen mika hannu tayi tana karkarwa kamar ta
taba kamar karta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login