Showing 81001 words to 84000 words out of 103342 words

Chapter 28 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

Advertisement

kingboy   

08 Jul 2025

5146

da matar ka". Ba
gardama kuwa suka shiga suka kulle dakin._




_Alh. Dayyabu Ne a gaba Gefan shi Dan ladi sai kuma wasu garada su hudu Katti ne majiya
karfe ko wanne ka kalla fuskar shi zata gaya ma ba imani. Kursiyya tsakar gida ta zo ta yi tsaye
ta dan bubuda kafafu ta mayar da hannuwa baya. Irin tsayuwar guards. Alhji ba abunda yake in
banda zage-zage. Yana ganin mutumin da tsayuwar sa sai ya tsaya cik! Suma gaba ki daya
suka tsaya. Alhj._





_Ya kalle mutumin sama da kasa tukun ya bushe da dariya yace "Kai Amma Dan ladi ban taba
sanin kai mashiririci ne ba sai yau. Yanzu dan Allah a kan wannan dan Yarinyar ne ka taso mu
ni nama dauka wani jibeben gardi zan gani har na kwaso karti hudu. Hakan ma cewa kake wai
na kara wasu. Yo wannan karamin alhakin ko ni ai sai in tumurmusa shi". Dan ladi ya kara
matsawa kusa da alhji yayi ya mai rada a kunne. "Alhj bar ganin shi haka kashi daya ne da shi.
Da hannu daya fa ya dagani sama". Cikin fada da bacin rai alhaji yace. "Kai rufe min baki
matsoraci kawai bari kaga insa ayi min guduwa-guduwa da shi. Tiger Da Musa lion ku kamo
min yaran nan yau sai ya gaya min gidan na ubanshi ne da har zan sa a fitar da mutane ya ce a
mayar". Rufe bakinsa ke da wuya, Sai kuwa karti biyu suka nufi Safuratu ko wannen su a
murmurde yake fuskokin ba annuri. Safuratu Da ganin sun nufo ta sai ta ruga a guje ta shige
bandaki. Su tiger suka bita a guje suma. Da zuwa suka tarar da ba kowa a ban dakin sai wata
yarinya dake kallan su tana murmushi. Musa Lion ya chakumi rigar ta ta baya ya dage ta sama
da hannu daya. A haka suka fito sa ita. Alhaji tun kafin su karasa gurin sa yake cewa. "Kai bana
san iskancin banza fa. Ya nace ku kamo min wancan dan Yarinyar zaku kamo min wannan
karamar tsakuwar". Tiger ya bude baki maganar shi ita kadai ta isa ta tsorata mutum. "Alhaji ai
shine ya koma haka dq alamu yana da layar zana"._

_Alhaji yayi dariya. Hehehehehehe, "Au! Wato shine ya koma wannan Yarinyar nufinshi zamu
kyale shi ne". Alhaji ya matsa gaf da Safuratu dake rike a hannun tiger sosai alhaji ya matsa
kusa da ita yana mata wani irin kallan raini. har hancin shi na gogar nata. "Wato kana nufin da
ka koma wannan Yarinyar muyi hakuri mu kyale ka ko. To kuwa kayi kuskure domin da ka tarye
ni fada gwara ka taryi RUNDUNAR SADAUKAI. Domin ni nan da kake gani na nafi kububuwa
hadari. Sannan bani da imani ko miskala zarratun, Saboda rashin imanina cinnaka ake cemin
baka san na gida ba ciji Jariri in uwar ta motsa in galla ma..." Ai kafin ya rufe baki Safuratu ta
cije shi a hanci harda jini. Kafa tasa ta harbi tiger a ciki. Dan zafin da yaji baima san lokacin da
ya sake ta ba. Da gudu ta nufi wani bangare na gidan. Alhaji rike da hanci yace "Ku kamomin
wannan dan iskan ku cinye shi danye". Da fadar haka su duk hudun suka bi Safuratu da gudu.
Kamar biri haka ta kama gini makal-makal ta haye kan soro. Su tiger na zuwa sukayi tsaye suna
kallanta. Irin dutsen da ake dorawa a saman kwano gudun kar iska ya dauke ya yace kwano.
Shi Safuratu ta dauka ta daga sama alamun jefowa zatayi. Da ganin haka suka tsaya cik suna
kallanta. Dariya Safuratu kafin tace "In da mai so ya bakunci lahira a cikin ku ya karaso"._





_Cik! Suka tsaya suna kallan ta domin kuwa sun san cewa duk wanda aka bugawa wannan
dutsen ba a kai ba ko a wani bangare na jiki ne ya banu. Ganin sunyi tsaye ba mai niyar zuwa
alhji yace, "Tiger dama abunda na daukko ku kuyi kenan?. Bana san iskancin banza fa". Cikin
maganar su irin ta yan daba yace "Wannan maganar rai ce fa ake, ahhee Bar gani na a haka
daga ta kwada min shi zaka ga na fara ah yane a nan gurin. Allah. Alhaji". Ran alhaji ne ya baci
nan ya fara tattare babbar riga "Bari ni inje tunda ku bazaku iya ba". Da sauri dan ladi ya rike
shi. "Aa alhaji karkaje wallahi Waccen daga gani ba imani zatayi ba". Safuratu ajiye dutsen tayi
ta kalli tiger suna hada ido sai kuwa idanun shi suka koma bakake wul! Ba ko alamar baki a ciki.
Da faruwar haka ta diro daga saman Soran. Musa lion da sauran biyun suka nufe ta a guje
kafin su karasa sai ganin Tiger sukayi ya shige gaban ta. Da ganin idanuwan shi suka gane ba
lafiya ba. "Ku tsaya". Tiger ya fada da karfe muryar kamar wanda yayi magana a Loudspeaker.
Cik suka tsaya. Abun mamaki duk wanda suka hada ido da tiger sai shima idanun su koma
baki kirin gaba dayan su haka.Alhaji da Dan ladi suna tsaye kallan ikon Allah kawai suke. Da
faruwar haka Safuratu tace "Kuje ku daukko min alhaji da yaran sa dan ladi ku kawo min shi
gaba na". Gaba daya su hudun suka juya suka nufi alhaji. Da gudu dan ladi ya juya da niyar ya
tsere ai kafin ya isa kofa tuni wani yasha gaban shi. A kafada aka sabo su alhaji aka dire a
gaban Safuratu. Alhaji na karkarwa yace...........,......................_

� *KAIKAYI YA KOMA KAN MASHEKIYA*



Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy






��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 91-92


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*


DEDICATED YOU MY SON *MUBASHSHIR*​


​HAPPY BIRTHDAY *MUBASHSHIR*​

?
Allah ya karo shekaru masu albarka

Happy 2+

?


*I'M HAPPY*

*HAPPY MAULIDIN NABIYYU SALLALAHU ALAIHI WASALLAM* ☺

*Bazamu taba mantawa dake ba ya masoyin Allah.*

*Bamu da kamar ka ya shugaban mu..*

*Mun san cewa duk irin so da kaunar da muke maka bazamu yi rabin san da kake mana ba ya
Habibullah*


*Mun gode wa Allah muna kara gode masa a kullum.da ya bamu kai ya Rasulillah.*


*Bamu da komai bamu da kowa sai kai manzan Allah. Ka cece mu ranar da ba mai ceto sai kai.
Ba dan matsayin mu ba dan girman Allah ya Rasullillah*


Makiyan ka sun tabe. Masoyan ka baza su taba tabe wa ba. Saka mu cikin masoyan ka.


Dole muyi murna da zuwan ka ya shugaba. Wanda basa murn bakin ciki ya kahe su ‍♂

*YA ALLAH KA KARAWA ANNABI DARAJA. AMIN*


*KARSHEN PAGEN BAYA*

_*"D*an Allah dan annabi kiyi min afuwa ki ceci rayuwa ta wallahi bansan ke din Aljana bace".
Safuratu ta harare shi. "To ai yanzu kasan ni Aljanar ce. Naga kamar ka kwaso wadan nan
kartin banzan ne domin suzo su tumurmusa ni dan na hana a watsar wa da nayin Allah kayan
su ko". Da sauri alh. Yace Aa wallahi sam ba da niyar haka na zo ba. Ni nazo ne ma in c na bar
musu gidan su rike. Amma dan Allah karki yi min komai". Kamal da kadija da sukaji shirun yayi
yawa basu ji ihun mutumin nan ba. Sai kamal ya taso ya leko. Yana ganin Yarinyar nan kuwa
kwalwarsa ta shiga aikin bincike yana kokarin tuna inda ya santa amma hakan ya gagara.
Khadija ya kari itama ta leka kamar dai shi. Itama taso ta san Yarinyar amma ta manta a ina._

_Safuratu tace "Aa ka rike gidan ka ai yanzu idan ka basu kyauta. Watakil wata mai tsayuwa
zaka zo kace su tashi ka fasa. Dan haka bari a biya ka kudin gidan ka". Bat! Safuratu ta bace.
Sai bayan kamar mintuna biyar ta bayyana rike da jaka. Ta mikawa alhj. Dayyabu hannu na
karkarwa ya karba. Tace ya daga ya gani. Ya daga kudi ne bandir-bandir na dubu-dubu.
Safuratu ta dauki biyu daga ciki tace. "Kudin nan Million daya da dubu dari ne. Ina ce dai sune
kudin da ka arawa kamala". Kai ya jijiga alamun eh. "Wannan dubu dari biyu da kaga na dauka
kuwa Khadijah zan bawa matar kamala domin ta sasayi duk abunda yaranka suka lalata mata
wajen fiddo kaya. Daga yau karka kuma kallan gidan nan balle ma kayi mafarkin zai zama
naka". Alhj. Duk a tsorace yake kamar kace arrr! Ya zurq aguje. Yaran shi kuwa sunyi tsaye
kem! Kamar wanda aka sasaka. "Kamala! 2×". Safuratu ta kwala mai kira. Da sauri ya amsa
suka fito tare da matarshi suma duk tsoro ya kamasu domin idanun su sun gane musu abunda
duk ya faru._




_Safuratu tace "Na biya wanna mutumin kudin shi da ya ara maka. Yanzu wannan 400k din
dake wajen ka kaja jari ke kuma ga wannan ki saya duk abunda suka lalata miki wajen fito da
kaya". Kamal da matar shi mamki suka cika da shi sai godiya suke. Kana kallan fuskokin su
kuwa zaka gane akwai alamar tambaya. Tsaya Safuratu ta dakawa alhji. Da yaran shi, tashi
yayi ya runtuma a guje haka suma yaran firgigit! Ko wannen su kamar wanda aka tayar daga
barci sukayi waje a guje. Safuratu ta mike tace "To ni zan tafi kuma sai wani lokacin. Cikin su ba
wanda yace uffan!. Har ta fara tafiya Kamal yace "Dan Allah ke din wace ce?". Jiyowa tayi
fuskar ta dauke da murmushi wanda shi ya kara fito da kamanin Yarinyar kwanaki nan take
suka gane ta. Safuratu tace "Ni ce Yarinyar da kuka taimaka kwanakin baya. Wannan
sakamakon alkhairi ne. Kunsan Allah ma yace . "Shin kyautatawa nada wata sakamako?,Face
Kyautatawa".RAHMAN 60 AYA:._




_"Kuyi hakuri wancan karon da na tafi ba tare da nayi muku sallama ba. Ni kaina naji dadin
zama daku. kuma zan so ci gaba da zama daku duk da ni ba mutum bace sai dai kuma
ayyukan gaba na baza su barni in zauna tare da ku ba shiyasa ma kawai na tafi a lokacin".
Hawaye ne ya fara zubowa Khadija. "Shin dan Allah yanzu ma tafiya zaki ki barmu?. Kinsan irin
Son da ake miki kuwa. Tun ranar da Kamal ya kawo ki gidan nan ya fada min cewa baki da
kowa kuma gaki kurma. Hakan yasa na kamu da tsantsar sanki da kaunar ki dan a lokacin sai
naji kamar an yaye min bakin cikin da nake ciki na rashin haihuwa. Kwatsam kuma a daren
ranar sai kika gudu kika barni. A ranar ga kamal nan wuni nayi ina kuka domin ji nayi kamar Na
haihu 'yar ta mutu ne". Tana zuwq nan ta fashe da kuka Kamal ya kwanto ta jikin shi yana
lalashi. Sosai ta bawa Safuratu tausayi domin itama sai da hawayen suka zubo mata. "Khadija
kiyi hakuri ki sani cewa aikin da na daukko babban aiki ne bazan iya tsayawa a nan gidan na

wasu kwqnaki ba domin in nayi hakan wasu da dama zasu shiga matsala. Zan dai riga zagayo
ku in na sama dama in sha Allah. Kuma zan na taya ku addu'a Allah ya baku haihuwa". Da
karashe fadar haka Safuratu ta bace._




_Bata bayyana a ko ina ba sai kofar shagon Muktar. Ta bayyana ne a cikin shigar wata tsohuwa
almajira fuskar ta duk a yaya mutse, Duk wanda yaga tsohuwar nan sai ya tausaya mata. Faced
din shagon matar ta nemi waje ta zauna. Ba abunda take sai kallan Muktar. Duk juyowqr da
zaiyi sai yaga sun hada ido da matar a zuciya yace "Waccen fa ina ga yunwa take ji. Kuma
yaseen ko mutuwa zakiyi bazan baki komai ba". An kwashi mintuna ya kara juyawa yaga dai
again shi take kallo abun ne ya bashi haushi a fusace ya fito daga shagon dan bala'i ko rufe wa
baiyi ba kanta yaje ya tsaya yana ta surfa masifa sai kace ya sama sa'ar shi. Ita dai ba abunda
tace sai idanu da ta kwalalo mishi ko kiftwa batayi. Daga karshe yace "Kinga malam in ma ke
mayya ce wallahi kurwata tafi karfen ki. Haba wannan kallo kamar naci ban biya ba". Ganin taki
tankawa ya juya ya koma shago. Abun haushi da takaici har yanzu bata daina kalla shi ba. A
zuciya tunanin abunda zai mata yake domin iya bacin rai ranshi ya gama baci. Wai tama rasa
wanda zata je ta tsare da kallo duk shagunan makwabtan shi sai shi. A fusace ya kara fita ya
koma wajen ta masifa har kamar ya dake ta yake. Mutane na ganin haka suka je suka bashi
hakuri hade da tada tsohuwar daga wajen. Can da yamma kuma sai gata hannun ta rike da
kwanan bara. "A bamu saraka a bamu ta annabi. Alllah ya baku mu samu. Ka bada Qalilan
rabbana ya maiyar da Kasirran"._





_Shiru Mukhtar yayi ba tare ya dago kai ya kalle ta ba. Kamar dazun sake maimaitawa tayi "A
bamu saraka a bamu ta annabi. Alllah ya baku mu samu. Ka bada Qalilan rabbana ya maiyar
da Kasirran". Dogan tsaki yaja. Tsohuwa bata tafi ba kara fada tayi "A bamu saraka a bamu ta
annabi. Alllah ya baku mu samu. Ka bada Qalilan rabbana ya maiyar da Kasirran". A fusace
Muktar ya dako "Anki a bada malam dallah ki ware ki ishi mutane". Kara murtuke fuska yayi
"Ke wai me zan miki ne tun dazun kin takura min haba malama ni kadai ne mutum a nan ne. Ko
kuma sadakar dole sai ni ne zan bayar..." Fada yake surfa mata kamar wanda ya sama diyar
shi. Kyalkyale wa tayi da dariyar mugunta. Hannu tasa ta kwaye rabin fatar fuskar ta. Abun da
yayi mutukar girgiza Muktar kenan nan take ya kama karkarwa ya zube a wajen yana bata
hakuri domin ya gane wace ce._




_Muryar ta ba dadi Tace "Wato dama abunda duk na gaya maka bai shiga kunnen ka ba ko.

Naga ma yanzu saura kadan ta rage ma ka fara dukan maryam yarinyar da na baka amana. Da
kudin ta fa kake ci kake sha. Amma naira hamsin ka kasa bata". Muktar yama rasa ya zayi
yasan dai yanzu bashi da wani abunda zai kare shi. Magiya hadata da Allah da annabi yake.
Safuratu ta daka mishi tsawa hade da cewa yanzu zan yi ma hukunci kuma irin shi zanci gaba
da yi ma muddun baka dai na abunda kake ba. Zan raba ka da duniyar mutane can zan kaika in
da bazaka ga kowa ba sai Dabbobi su kuwa sun fika rashin mutunci, kaga sai ku hadu kutayi in
baka ci sa'a bama Kora ko zaki wani ya cinye ka". Tana rufe baki bat! Suka bace yare muktar
sai ganin shi yayi a wani kurkurmin daji ba abunda kake ji sai kukan tsuntsaye ga kuma kukan
namun jeji. Wata murya da Muktar ya rasa daga ina take fitowa "Muktar wannan shine hukun
cin da ya dace da kai zan barka a nan kayi yan kwanaki nasan zaka kara daukan darasin
zaman duniya ka gane cewa rayuwa ba komai bace". Hannu muktar ya dora a kai ya fashe da
kuka "Dan Allah dan annabi kiyi hakuri wallahi na tuba bazan karaba karki min wannan
hukunncin". Shiru yaji ko uffan ba'a ce masa ba. Nan ya durkushe yana ta
kuka........................................_



‍♂ *MUKTAR DAGA YAU SAI ASAN MUTUNCIN DAN ADAM. KO YA YAKE BA ABUN A
WULAKANTA BANE. BAKA SAN KALAN BAIWAR DA ALLAH YA MASA BA*

Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy









��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 93-94


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*


*DEDICATED MY ASSOCIATION ZAMANI*

� ```FATAN ZAKUYI MIN AFUWA. MUNYI BIKI NE BANA SAMUN TYM DIN TYPE. AMMA
YANZU IN SHA ALLAH IDAN NA FARA SAI NAJE KARSHE```

INA ALFAHARI DAKU MASOYA NA ANA TARE

_Bayan ya gama kukan ya tashi ya hau zagaye dajin, Yayi yawo sosai amma ko alamar gida
balle mutum bai gani ba. Safuratu kuwa gida ta koma ta juye zuwa Muktar din. Haka taci gaba
da kula da harkokin sa har na tsawon sati guda. Muktar kuwa na can dajin wani lokacin ma
abincin da zaici wuya yake masa,_


_Loaci daya rayuwa ta juye mai barci sai dai ya sama wani dan kogun dutse ya shiga ya
kudundune. Haka kuma ruwa sai dai yaje wani dan gulbi da yaga ruwa na taruwa yasha. Yayi
kuka sosai kuma yayi nadamar abunda ya aikata. A zuciyarsa ya kudurci niyar cewa bazai sake
aikatawa Maryam makamancin wannan ba. Yayi kudirin zai rike ta da gaskiya kamar yarsa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login