Showing 21001 words to 24000 words out of 103342 words

Chapter 8 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5040

"Kai wai ba da ku nake magana ba?". Nan ma basu tanka
mishi ba. Abunda ya fusata malam Dalhat kenan, Ya nufo su da zureriyar dorina. Shaf! Shaf!
Kake jin karar dorinar da karfi yake dukan su. Bayan yayi wa ko wacce daga cikin su dorina
biyu, A ta ukun Nasmat ta Rike bulalar tare da mike wa tsaye. "Malam ya ishe ka haka". Asmart
ta fada ido cike da kwalla.



Cikin kuka-kuka Nasmat tace, "Ki kyale sa yaci gaba Wallahi ya sake dukana sai na mishi
abunda bai yi zato ba". Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar malam ya saki baki yana kallan
su, a zuciya yace, 'Ashe rashin kunyar nan ta su da ake fada har ya kai haka, Ni kuwa zanyi
maganin ku". Bulalar ya fizge da karfi ya fara zafga musu kan uwa da wa bi, da gudu suka fita
har suna bankade muta ne. Ko laidar Al'quranin ba wanda ya dauko a cikin su. Ko wacce
hawaye ne shabe-Shabe a fuskarta Asmart na cewa, "Wallahi bazan yarda ba dole sai na dauki
mata ki, chabb! Lalai wannan malamin bai sani ba ne". Nasmat ta ciji labe. "Hmm kyale sa
wasa yake damu". Cikin gari suka shiga yawo gida jen kawayen su, sai da suka Dai-Dai ci
lokacin tashi a Islamiyya yayi tukun suka koma gida.




Shigar su gidan suka tarar gaba ki daya mutanan gidan sun fito ana faman shiga motoci, da
sauri suka karasa suka tamabaya ina za'a je, Mama asiya tace, "'yan gantali har kun gama
iskancin kun dawo ko?, nasan dai ba makaranta kuka je ba, kunga Wallahi ku kiyayi rayuwa

gwara ku tsaya ku mayar da hankali kuyi karatu, Ni kai na yanzu haushi nake ji da bansan
komai ba a karatun Alqur'ani kuma kuma nasan ko Fatiha cikin ku da kyar in da wacce zata iya
kai wa dai-dai". Kallan juna sukayi hade da sosai kai Asmart tace, "Mama asiya ina zuwa?".
"Au! Har kun manta yau bikin Haleematu?". Wani irin tsalle Asmart tayi "Ashe yau ne". Kokarin
shiga mota ta farayi aka hanata, Akace sai taje ta canza kaya. Da gudu taje ta canzo Ko
kwalliya batayi ba tazo ta shiga mota. Nasmat kuwa tana guri A tsaye ta wani bata Rai. "Ke
bazaki je bane? Kowa na gidan zashi ko har yanzu 'yar banzar gabar nan ta rashin hankali kuna
yinta ke da Haleema?". Zuwaira ce tayi wa Nasmat magana. "Allah ya sawa ke inje gurin bikin
haleema, Ai ko mafarki nayi naje wajen sai na farka kuma in na farka sai nayi sadaka".
Juwaira bata ce mata komai ba t shiga mota. Motoci biyu ne cike. Har sun fara tafiya. Asmart ta
leko. "Yauwa nasmat ban gaya miki ba. Wannan tsinaniyar yarinyar tana can tana mana wasa
da kayan Makeup wai tana wa 'yar tsanarta kwalliya. Kije kici ubanta dan Allah". Tun asmart
bata karasa maganar ba Nasmat ta zungura da gudu ciki gidan.




Direct dakin su ta nufa, tana zuwa ta shako wuyan Fatima ta baya ta fara gallah mata mari.
Fatima kuwa ta hau kuka da ihu!, "Wato ke dan ubanki 'yar baby kike wa kwalliya da kayan mu
ko". Fatimar hakuri take bata amma taki ji sanda ta mata lilis! Kamar yanda ta fada yau 'yan
muguntar ne a kanta. Kunnan Fatima ta kama tana ja. Ba arziki Fatima ta ringa binta tana rike
kunnen dan karta ji mata ciwo. Sai da ta kai ta har kofar gida, mai gadi duk da yana tsoran
alhaji sai da ya bude kofa domin yasan Bala'in Nasmat Da Asmart. "Dan ubanki bazaki zauna a
gidan ba, kuma Wallahi in kika tafi wani waje na fito waje naga bakya nanto kema kin dan
sauran". Nasmat ta juya zata shige gidan Fatima ta riko kafarta "Aunty dan Allah ki bani baby
na to". Hararen ta tayi ta kuma sa kafa ta haure ta can Fatima ta fadi tana kuka. "Bara inje in
yan-yanka babyn dan ubanta itama ke da ganinta sai a lahira in 'yar Tsana na zuwa". Wani
kukan Fatima ta ci gaba da bada wa amma Nasmat bata saurare ta ba ta shige cikin gida ta bar
Fatima nan tana kuka.




Mai gadin ganin yau gidan ba kowa kuma yana da 'yan uzuririka shima. Fitowa yayi har zai
wuce kuma sai ya tuna Fatima na kofa karta shiga, Katan kwado ya koma ya daukko ya zo ya
garkame gidan. Yayi tafiyarsa. Nasmat a fusace ta shiga ta daukko 'yar babyn ta nufi kitchen
da ita. Wuka ta dauka mai shegen kaifi ta fara dada rawa a jikin Robar amma ko kayan dake
jikin babyn sunki ko bancile. Canza wukar taje tayi a cewar ta ba kaifi ne. Fara da dara wukar
ta ke da wuya aka fara knock din kofar kitchen din da karfi abun kamar za'a balla. Ta dan
tsorata kuma sai ta jure. "Uban waye?". Shiru ba'ayi magana ba. Jin anyi shiru yasa taci gaba
da abunda take yi. Ganin wuka taki ta kama babyn ta dauko galan din kalanzir ta ajiye babyn a
kasa ta jike ta sharaf! Tukun ta dauko ashana. Zata kyasta kenan. Wani mugub karan buga
kofa ya kara dakar mata kunne. Ba tsoran koma Nasmat ta daka ashar, hade da cewa"wane

dan ku... Uba ne? Mai gadi nasan kai ne wallahi in na fito ni da kai ne". Bata rufe baki ba aka
kara bubugawa wannan karan harda murya ta mai gadi sak! Da yace "Ki buuuudeeee". Abun
ya fusata ta jin muryan mai gadi. Ashanar ta kyasta! Ta wula wa yar babyn nan take wuta ta
kama ta fara ci. Tana ganin haka farin ciki ya kamata tayi mugunta. Saura kai mai gadi ta fada
lokacin da ta nufi kofa rai! A bace domin har yanzu bugawa ake. Tana bude wa taga wayam,
bayan kuma yanzu-yanzu ko seconds 4 ba'ayi ba da bugawa. Kofar dakin su tafi an rufo garam.
Alamun wani ne ya shiga...............................


��� *Yau wata zata ci uban ta. Na tausaya mata.lolz*


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks




Autan writers nee king boy





��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 27-28


NA. ✍KING BOY ISAH


✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍

_*IN DEDICATED TO ALL ALJANAR FATIMA FAN'S. INA JINJINA MUKU NA YABA DA IRIN
KAUNAR DA KUKE WA BOOK DIN. SANNAN INA BAKU HAKURI MASU KORAFIN PAGE
YANA KADAN WALLAHI I'M BUSY. KUCI GABA DA HAKURI. IN DA JIRGIN SAMA YAJE
HAWAINIYA MA TAJE IN DAI ZA'A LALA BATA. LOLZ*_




*KARSHEN PAGEN BAYA*
Tana bude wa taga wayam, bayan kuma yanzu-yanzu ko seconds 4 ba'ayi ba da bugawa.
Kofar dakin su tafi an rufo garam. Alamun wani ne ya shiga..

»»Kofar dakin ta nufa cikin fushi tafe take da sauri rai a bace, tana zuwa kofar dakin tasa hannu
zata bude kenan wani makeken kadangare irin mai jan kan nan ya fado mata a kai. Wani
mugun ihu ta saka, ta fara tsalle-tsalle tana zagaye katan falon tana zazage-zazage da Kara
duk ta dauka yana jikinta ashe ya fado tun tuni. Ta dade tana yi sai da ta tabbatar baya jikin
nata tukun ta dan saki jikinta ta hau dube-dube. Bata hakura ba kofar ta sake tun kara da niyar
ta bude wannan karan ma kadangare ne karami ya fado mata wannan karan cikin riga ya shigar
mata. Nan ta fara ihu ta fadi kasa tana ta mirgine-mirgine. Kadan garen ya fita. Tashi tayi zaund
tana Raraba idanu. A zuciya tace "to wai me ma ya kawo kadangaru falo?".Kuma Wallahi sai
na shiga dakin". A fusace ta tashi sanda ta dai-dai ci kofar dakin tukun ta zura a guje. Ta
bankade kyauran ta fada karfin gudun nata ya rinjaye ta ta fadi sauran kadan da ta yi karo da
katanga.



Suman tsaye tayi a gurin. Dan ganin wani make ken maciji da ya fasa kai yana layi da kai.
Nasmat ta san tana matsawa a gurin sai ya sare ta. Karkarwa ta fara yi sai hawaye sharr! Kuka
wii! Wii cikin kukan da take tana ihu! "Wayyo mama na na mutu na lalace, dan Allah maciji kayi
min rai kayi min aikin gafara, Wallah bazan kara Fashin sallah ba, kuma Wallahi bazan kara
fashin zuwa makaran ta ba". Ihun take tana ta zuba Surutai! Da rantse-Rantse macijin ne ya
dan kara bude kai nan take yana zaro harshe yana mayarwa. Kara tsurewa tayi da taga macijin
yana kara matsowa a hankali. Tsoranta ne ya karu ta fara ihu! Tana karkarwa. Sululu macijin
yaje ya fara hawa kafarta. Tana jin haka sai fitsari Sharr! Gaba daya ta jika wajen. Sannan tayi
tsaye cik kamar gunki ta rufe ido. Har yanzu dai macijin hawa kanta yake. Jima kadan taji baya
nan. Bude ido tayi can ta hange shi ya shige ban daki su. Da gudu tayi waje ta zo dai dai falo
kenan wuta gaba daya ta dauke, dama nefa ce. Duk da rana ce amma bata iya ganin gabanta.
Juye-juye ta fara yi tama rasa ina zata nufa. Ji tayi an shafe ta ta baya an wuce. Wani razana
nan kara ta saki "Wayyo!" Cik kuma ta tsaya waje daya duk da bata gani amma tana jin motsi
kamar mutum ya nufo inda take. Abunda ya taho din tana jin karar tafiyan saura kadan ya kara
so gurin ta sai aka dawo da wuta. Wani gwabran nun fashi ta sauke nan ta du duba amma ba

komai a gun. Kan armchair ta zauna tana nunfashin wuya. "Wash! ni Nasmat yau naga bala'i
wannan katan maciji idan ya sare ni ai in ana Wuce lahira ma sai na wuce".




Sukur-sukurtu taji a baya da sauri ta juya Taga ba komai, hahhahahh! Dariya tayi da kanta
tukun tace, "Lalai yau na tsorata". Yar baby ta tuno da sauri ta tashi ta nufi kitchen domin gano
ko ta idasa kone wa?. Tana bude kyauran Kitchen din tayi tsaye hade da Zurawa guri daya ido,
mamaki ne karar ya bayyana a fuskarta. Ganin yar babyn gata nan a kwance inda ta yarda ta
amma ko alamar an jika ta da kalanzir babu balle ma Wuta. "Kai!, ban gane ba nafa kona
wannan abun kafin in fita. To ko bata jin wuta na?. To amma bari inga a gaba na zan kona ki yar
iska". Galan din gas ta dauko a wannan karon ta bul-bulawa yar babyn ta kyasta asha na ta
wulla mata. Nan take wuta ta kama bal-bal farin ciki ne ya lulube ta domin yau mugunta ce fal!
A ranta. "Kyal-kyal-kyal-kyal, hahahahahahaha, hihihihijijhehehehehrhr". Sautin wata iriyar
mahaukaciyar dariya ce da ke fitowa daga falo ya daki dodan kunnan Nasmat da ke tsaye itama
tana kallan yar babyn tana dariyar mugunta. Kofar ta bude a hankali ta Leka, fatima ta hanga
zaune kan kujera ita ce mai uwar dariyar nan. Nasmat na ganin ita ce sai ta bata rai ta Idasa
fitowa..




Ishar ta maka. "Fatima ku....banki". Shiru Fatima tayi ba tare da ta wai-wayo ba, Cikin sauri
Nasmat ta karasa gurin tana zuwa kuwa ta Falle Fatima da mari ta baya. Gugur-gugur kai ya
fadi kasa ya fara taya jini na fita a jiki. Gangar jikin ma Kasa ta fadi jini ya fara malala. Hannuwa
biyu Nasmat ta dora a kai ta maka wani uban kara, Ta nufi gurin gangar jikin fatima ta rugume ta
a kirji "Wayyo Allah na na shiga uku na lala ce, Fatima Wallahi ba kashe ki nayi niyar yi ba. Dan
Allah ki tashi yanzu in su momy suka zo me zan gaya musu, Yau na shiga uku". Kuka take
sosai ba kukan rashin Fatima sai kukan rashin abunda zata ce. "Ai da raina ban mutu ba Sake
ni". Gangar jikin Fatima ce ke magana. Shiru Nasmat tayi ta tsurawa Wuyan da har yanzu jini
ke zuba ido. Domin taji kamar daga nan taji magana sai dai bata tabbatar ba. "Ni ki sake ni
nace". Wata murya ce a shagwabe ta fadi hakan. Kafin a karasa maganar tuni Nasmat tayi wulli
da gangar jikin Fatima din tayi hanyar kitchen a guje kamar wacce zata tashi sama. Gangar jikin
tsaye ya tashi ya je ya daukko kan ya riko a hannuwa biyu A hakan Fatima ta nufo Nasmat da
ke can bakin kofar kitchn tana kokarin bude wa amma kofar ta ki bude wa. Fatimar tana fadin
"Aunty nasmat mayar min da kai na- mayar min da kai na". Kuka ne ya subuce wa Nasmat tana
tura kufa tana waigen baya tana fadin "Wayyo Allah momy na". Gangar jikin Fatima ya kusan
karasowa kenan kofa ta bude. Har Nasmat ta zura kafa zata fada kuma sai taja birki. Yar babyn
ta gani ta nufo ta tana kuka ga wuta na cin jikinta kuma hawayen jini ne ke fita a idanun ta.
"INNAHU MIN DAUDA WA, INNAHU MIN SULAIMANA, WA BAZAN KARABA NA TUBU KU
YAFE NI".Da karfi Nasmat din ke fadar haka tana karkarwa. Da dai taga wannan ba mafita
bac...........................

AYI MIN AFUWA BUSY YASEEN



Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks




Autan writers nee king boy

















��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 29-30

NA. ✍KING BOY ISAH


✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍


PAGEN YAYI MIN DADI SHIYASA NA BAWA BEST FRIENDS NAWA.

Usaini atk 80k

Shamsuu Bin Yerhyer

Mustpha Rogo

Abdul King Article

Musa Umar Abdullahi

Shatu muhammed

Aisha adam

Ahmed tijjaniyu

*HAKIKA KU MASOYA NA NE NA GASKIYA, KUNA A SAHUN GABA CIKIN MASOYA NA. INA
GODIYA DA BIBIYAR LITTAFAI NA DA KUKE ALLAH YA BARMI YARE.*



Nasmat a guje ta bar wajen nan suka hau zagaye falo. Gangar jikin fatima dauke da kanta a
hannu jini na zuba tana bin nasmat di tana fadin "Auntu dan Allah ki tsaya ki samin kaina". Fadi
take tana maimatawa tana biye da nasmat din. Haka itama bangaren yar babyn bin Nasmat
take tana fadi "Aunty kashe min wuta wayyo! Wuta na cina". Gaba daya sun zagaye falon sun
mishi kaca-kaca da jinin da ke zuba. Nasmat abun ya zame mata biyu ga tsoro ga karfin
maganar tasu har cikin kwalwarta, Ta dai fahimci wannan so suke su Haukata ta. Allah ne ya
bata sa'a ta ta nufi kofar fita a falo tana kamawa kofar ta bude da sauri ta rufe kofar ta jingina da
kofar tana shasheka. Hamdala ta farayi a nufin ta ta rabu da su. "Aunty ki kashe min wutar".
Wani uban kara ta daka "waaaaaayyooooo Allah na" ta runtuma a guje tana kiran me gadi. 'Yar
babyn ta bita baya Nasmat dakin mai gadi ta leka shiru ba kowa. Nan taje ta fara kokarin Bude
kofa taji a garkame da kwado. Juyowa tayi ta zube a kan gwiwoyin ta tana bawa aljanar hakuri.

"Dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, daga yau bazan sake takurawa Fatima Allah wallahi tallahi
na rantsi da uwata da ubana ku....." "Kheeeeeeeee! Yi min shiru, muguwa kawai azzalumam".
Cikin wata iriyar murya mai karsashi da ban tsoro Aljanar ke magana. "Daga yau sai yau idan
har na sake ji ko gani kin wa Fatima ko harara, ki san da sani dan Wallahi sai na taba lafiyar
jikin ki, kina jina?". Da sauri "Eh naji *ALJANAR FATIMA* daga yau Wallahi na dai na". Wata
dariya 'yar tsanar tayi mai ban tsoro wanda kasa kanta girgiza take kamar jirgin dan kara zai
tashi. "Oya to dauke ni kije ki min wanka da kwalliya". Zaro ido Nasmat tayi ta kara make wa a
jikin gate din dan tsoro. "Keeee! Ba dake nake ba". Jiki na karkarwa Nasmat ta taso kamar bata
san tafiya hannun na karkarwa ta dauki 'yar tsanar ta wani mimike hannu kamar wacce ya dauki
abun kyama. "Au! Kyamata ma kike oya Rungume ni". Nasmat kamar ta fashe da kuka a
mugun tsora ce take. A haka taje tayi wa yar babyn wanka a tsorace Sai da 'yar babyn ta bata
wuya sosai a wajen wankan. Domin sai nasmat na mata wanka ta zuro hannu ta kama hancin
ta ja da karfi, ko kunne. Nasmat sai dai yi kara kawai. Bayan gama wankan aljanar tasa
Nasmat ta zo tayi mata kwalliya ta dauko akwatin ta tasaka mata kaya masu kyau.



"Yanzu abunda nake so shine ki dauke ni ki kaiwa Fatima kice mata dama wanka ne zaki mini,
karki yarda kice mata nayi miki wani abun kina jina". Da sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login