Showing 48001 words to 51000 words out of 103342 words

Chapter 17 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5059

suka tafi gida domin da kiyawa tayi wai
ita bazata je ba sai an dauko mata babyn ta. Sai da Fiddausi ta dake ta tukun. Su Nasmat
kuwa gaba daya ajin aka watse aka barsu zaune ba abunda suke sai leke wai jira suke malam
ya fito su bishi baya suyi ganin kwaf!._



_Nasmat tace "Asmart anya kuwa wannan ya fada tarkon da muka haka mishi?!". Asmart tayi
'yar dariya tace "Haba ke kuwa me kike ci na baka na zuba, Ki jira mana ni nasan bazata taba
kya...". Bata karashe maganar ba taga malam ya fita daga makarantar da sauri ta dauki jikar ta
ta nufi hanyar fita a ajin. "Yauwa taso, taso gashi can zai fita".Baya suka bishi ba tare da ya sani
ba daga Sunga zai waigo sai su labe. haka in suka ga ya tsaya wata majalissa sai su sama
waje su labe suna lekensa. Haka dai suka ci gaba da tafiya ba tare da ya gansu ba har ya isa
gida. Yana zuwa ya shige gida su kuwa a bakin kofa suka tsaya suna kace-nace. Malam na
shiga gidan ya fara jin kauri na tashi. "Masa'auda! Masa'auda!". Ya shiga kwalla wa matarsa
kira. Gyaran muryar tayi alamun tana ban daki. Da sauri ya nufi daki domin daga nan kaurin ke
tashi. Heater ya iske jone a socket An sata cikin ruwa. tayi daga gani ta dade a jone domin ta
kusan tsotse ruwan tayi daga sama kuwa tayi jawur har wayar ta fara narke wa. Cikin hanzari
malam ya kai hannun da niyar ya zare ta a jikin socket din, Ai kuwa yana kamawa abun ya
hade masa biyu ashe robar ta fara narke wa ga kuma shocking. Wani mugun ihu ya kwada yayo
waje a guje yana yarfa hannu yana fadin "Innalillahi!". Su Nasmat da suke kofa kamar jira
sukeyi suna jin ihun! Suka afka cikin gidan a guje. A tsakar gidan suka ja burki ganin malam
tsaye yana yarfa hannu yana kallansu. Lokacin Masa'uda matar malam ta fito daga ban daki da
sauri tana tambaya lafiya. Malam kuwa harara ya watsa wa su Nasmat "Kai uban me ya kawo
ku nan?". Kallan juna suka tukun suka juya suka kallesa kamar hadin baki suka ce. "Taimako
muka zo yi, (Emergency)". "Taimako to uban waya yace muku ana bukatar taimako a nan".
Asmart da sauri tace "Malam munzo wuce wa ne sai mukaji anyi ihu! Shine muka zo dan muga
me ke faruwa"._



_"Oh! To daga ina kuke yanzu ko kuna so kuce min da aka tashi daga makarantar ba gida kuka
tafi ba yawan ganta kuka fito?". Malam ya fada rai a bace. "Wallahi A'a malam ziyara muka je
mu". Malam ya zaro idanu "Ziyara gidan wa a nan layin?. Ba nan layin bane can ne gaba
kadan gidan wata kawar momyna ko a gida ka ansan zamu zo". Malam yace "To Shikenan naji
kuma Wallahi in gaya muku in na tambayi Fiddausi ko Ameera gobe suka ce min ba haka ba, to
jikin ku sai ya gaya muku maza ku wuce gida". Cike da haushi da takai'ci suka juya suka fita a
gidan. Tsabar bacin Rai sun dade suna tafiya amma Ko kala ba wanda yace Sai Tsaki kala-kala
da yake fitowa a bakunan su. Can asmart ta kalli Nasmat, rai a bace kamar tayi kuka tace "Ashe
dai dama Aljanar nan mu ta raina?, kinaga fa duk abunda malam yayi mata ko tsawa batayi
mishi ba". Nasmat tace "Ke dai bari abun ya kona min rai, Wai ace duk abunda mukayi munyi

a banza malam sai ma kara mana duka da yayi. Amma fa kuma inaga Aljanar ta mutu ne?".
Da sauri Asmart ta kalli Nasmat "Haba dai, Dama aljanu suna mutuwa ne?". "Eh mana baki ji
malam adamu yace Idan suka rikida suka koma wani abu idan ka kashe abun shikenan ka
kashe su ba. Misali idan aljani ya koma maciji in kika kashe macijin shikenan Aljanin zai mutu,
To kinga kuma Wannan 'yar tsana ta koma kuma malam ya yayanka 'yar tsanar shikenan ta
mutu kenan"._




_Asmart najin haka tayi wani tsallan farin ciki da jin dadi. "Wayyo da kuwa naji dadi Wallahi,
Domin da Fatima ta shiga uku kullum da sai na sakata kuka sau uku. Kuma duk dukan da aka
mana a Islamiyya sai na rama a kanta". Hhhhhhhhhh Nasmat tayi dariya ta dora da cewa "Ke
dai bari mu isa gidan Ai ni kadai nasan abunda zanyi wa Fatima yanda Aljanar ta gasa ni itama
sai ta gasu". Suna hirar har suka karasa gidan. Yanayin da suka tarar da gidan yasa basu
nema Fatima bama kowa ta kansa yake. Domin Duk wanda ya shigo gidan ba damar fita sai
gida ya garkame in kaje da niyar budewa Kuwa kasha mari. Haka suka kwana a ranar su mama
asiya ba wanda yasa ko kwayar gero a baka._
_____________________


_Umar ne zaune gurin mai shayi ya saka a dafo mishi Indomie da kwai. Sai washe baki yake
ana hira. Bayan wani dan lokaci daban aka miko Mai indomie mai zafi a flat wacce aka lulube
da wainar kwai sai tururi Take kamshi na tashi. Karba yayi sai Hadiyar mugun yawu yake.
Cokali daya yayi ya kai na biyu ya lumshe ido domin dadin da yake ji na Wainar kwan. Kamar
daga sama yaji anyi ciki da Filet din indomie din duk ya warwatse masa a jiki. Da bude idansa
da fitowar "Kutumar uba!".Daga bakinsa Duk daya, ba kowa bane Rafy ce tayi kwallo da
Farantin indomie din takuma yi tsaye kerere tana hararen sa. "Ke dan iskanci da rainin wayo ni
kika biyo har nan kika zubarwa da Abinci?". "Eh an zubar din mugu macuci kawai". Ta bashi
amsa a hatsale Hannu ya daga ya kai mata mari cikin hanzari ta Duke. tana dagowa kuwa ta
wanka mishi mari Tass!!!....................._


Yaseen na gaji

*Turkash!!!*




Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy









��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 59-60


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*

*DEDICATED TO YOU*

❤ *FATIMA MUSA* ❤

❤ *AISHA LAWAL* ❤

❤ *KHADEEJAT ABDULLAHI* ❤

_HAKIKA KU MASOYAN ALJANAR NAN NE. ALLAH YA BARKU TARE YA BAR ZUMUNCI
A TSAKANIN KU_ �


❤ I LOVE U ALL MY FANS ❤
Da bazar ku nake Rawa. In baku sam! Bazan iya ba. ‍♂ Autan Zamani na gaishe ku

*KARSHEN PAGEN BAYA*

~"Ke dan iskanci da rainin wayo ni kika biyo har nan kika zubarwa da Abinci?". "Eh an zubar
din mugu macuci kawai". Ta bashi amsa a hatsale Hannu ya daga ya kai mata mari cikin
hanzari ta Duke. tana dagowa kuwa ta wanka mishi mari Tass!!!...~

_»»Dafe kunci yayi. "Ni kika mara?, Ni kika mara?". Ya maimata sau uku, "Eh an mare ka
azzalumi kawai ai irinku bama mari ya kamace su ba, Duka da bulala ne ya kamace ku..."
juyawa tayi ta kalli mutane dake wajen masu shan shayi da masu cin indomie wanda duk sun
zura mata ido, Tace "Munafukan banza dubeku dallah, ba kunya ba tsoran ido da yawa daga
cikin ku magidan ta ne, Sai ku baro matan ku da tuwan masara miyan kuka. Ku kuma kuzo nan
a fashe muku kwai shayi hadin kauri. Wai abinci mai kyau to ku da mata waye ne yafin bukatar
abinci mai kyau mai gina jiki da kara lafiya?. Su fa haihuwa suke. Kai Tirr! Da irin halin ku". Ta
juya ta kalli Umar "To kai malam zaka wuce mu tafi gida ne ko kuwa?". Abun ne yayi mugun
kona mishi rai yaga idan ya kalle ta mutanan wajen daga yau zasu raina shi in ba sa'a bama su
ringa ce mishi mijinta ce. Wawurar ta yayi da kokowa ai kuwa suka tayi tututur-tututur. Sun
dade suna yi amma Umar ko raba ta da kasa ya kasa yi. Haushi ma abun ya bata ai kuwa tq
daga umar ta nuna wa Allah tukun ta maka shi da kasa. Jin jama'a sun kwashi ihu! Yasa shi
yayi sauri ya mike._



_Yana kallanta cikin fushi yana huci "Ke dani zaki Wallahi karki kuskura kice zaki ja dani yanzu
sai in ka karya ki, Yanzun ma sa'a kika ci nayi tuntube kika shammace ni bar ganin mutane na
ihu! Wallahi zasu kai ki su baro ne kuma bari ki gani". Da karfi yake maganar ita kam Rafy a
tsaye take cik! Tana kallansa ko hijab dinta bata cire ba. 'Yar wayar sa da 'yan canjin sa ya kai
wa mai shayi ya ajiye masa tukun ya dawo fili. Ya tsaya yana mata surutai sai da ta
sakankance tukun ya durfafe ta cikin shammace. Kamar dazun haka ta kara yin hajijiya da shi
ta maka da kasa. Mutane da tune sun cika gurin suka bushe da dariya ana ihu! Tashi yayi ya ka
kabe Wandan sa. A zuciyarsa cewa yake, "Anya kuwa wannan Rafi't dina ce kuwa, Haba ai
karfin yayi yawa yaseen wannan ko kona za'ayi a nan bazan iya kayar da ita ba. Abunda yafi
kawai shine in fece". Jama'ar wajen ne suka fara ihu! Suna fadin "Raggk mace ta kada shi".
Umarvya kalli wasu daga ciki yace, "Aikin banza abunda ma ban shirya ba". Kamar dazun a
hankali ya ringa matsawa kusa da ita yana shirin kama kafafun ta ya kadata. Ita kuwa tsaye
take ba abunda take in ba kallansa ba. Wawura ya kai mata cikin rashin sa'a kuwa ta sake
Damke wuyansa kamar ta kama kaza haka ta fara wulwulawa da shi. Umar ihu! Ya farayi yana
neman taimako jama'ar wajen kuwa ba abunda suke in banda dariya. Wasu na cewa mai kashi
daya ce, Basu san *ALJANAR FATIMA* Bace. Sai da tayi juyi kusan hudu da shi tukun ta sake
shi ya fada kasa sharaf!._

_Nan ma mutane suka fara kyalkyala dariya. Umar ya dan jima a zaune domin hajijiyar da tayi
da shi kansa ya dan fara juyawa. Mike wa yayi cikin fushi ya nanade kafar wandansa. Yana
mikewa ya kwasa a guje mutane kuwa suka ta mishi ihu! Yaji tsoran mace. Sai da ya danyi
nisa tukun ya tsaya ya juyo da karfi ya fara magana. "Ke ba dai ni kika wa haka a cikin jama'a
ba, Wallahi yau sai nayi maganin ki yau bazaki kwanar min a gida ba kuma Wallahi idan kika
shiga hannuna sai na dandana miki azabar da baki taba tunani ba. Yana fadar haka ya juya ya
nufi gida a guje bai ko tsaya karbar wayar sa da 'yan canjin sa ba na wajen mai shayi. Da
shigar sa gida ya saka kwado a kofar gidan ya kulle yana cewa. 'Yar iskan banza yau sai muga
a inda zaki kwana nasan dai gidan ku ko kinje koro ki zasuyi. Tun daga tsakar gida yaga
hasken fitila a daki a zuciyarsa yace, "Ashe ma a kunne ta bar fitilar ta fita masifa". Yana shiga
dakin yaga mace kwance sai dai ta juya baya. Baya iya ganin fuskarta, da alama barci take yi.
Tsaye yayi kofar dakin ya tsare ta da kallo kamar matar shi kamar kuma ba itaba. A hankali ya
fara matsawa sai da yaje gaf da ita yaga ashe ta dan lulube fuska da Wani gyale. A hankali
yasa hannu da niyar ya Cire yaga ko wace ce. Shi dai yasa a baya ya baro matar shi. Yana
taba gyalan Firgigit! Rafi'at ta tashi. "Mai gida ka dawo sannu da zuwa". Ta fada tana
mamakale wa dan tsoran shi kamar yanda ya saba. Da ya tsora ta kuma sai wani tunanin ya zo
mishi yace, "Haba kaga mata ta nan ga tsoro nan a fuskarta waccan Aljanar ce ba ko shakka".
Tsawa ya daka mata, "Dan ubanki bana hanaki kwantawa a kan gadan nan ba?". Da sauri ta
sauka tana bashi hakuri. Tsaye ya mike yana kallanta yana dariyar mugunta farin ciki yake ji.
Na ganinta domin yanzu zan rama duk abunda Aljana tayi min, Haka ya ayyana a Ranshi. Mari
ya galla mata dan tabbatar wa. Ai kuwa ta saki kara ta fara kuka tana bashi hakuri. Wani
murmushi yayi na mugunta domin yanzu a ganin sa ya tabbatar da matarsa ce ba aljanar._



_Murtuke fuska yayi ya kalle ta, "Wato in ma yi hakuri kike cewa ko, Da nayi niyar yi miki
babban hukunci amma tunda kin bani hakuri bulala 20 ce ba yawa". Ya juya ya nufi kofar fita a
dakin domin ya dauko bulala. Rafi'at abun tausayi har kafar shi take kamawa wajen bashi
hakurin amma sai dai ya fusge. Nan ya barta zaune a tsorace sai kuka take tana bashi hakuri.
Umar ya fita ya dauko bulalar katuwar Dorina ce mai baki biyu. Ya shigo da ita dakin, Ba
abunda ya daure mishi kai sai ganin Rafy a tsaye ta tsare shi da kallo fuskar nan tata babu
annuri. Shi da ya barta tana kuka yanzu kuwa ko hawaye babu a fuskanta. Da ganin haka ya
yarda bulalar domin ya kyaro Aljana ce. "Mai gida me zakayi da bulalar nan?". Rafy ta
tambaya cikin bacin rai!. A tsorace yace "Wallahi dama can din ne inda nake ajiye ta naga rana
an dakar ta shine na daukko zan canza mata wajen ajiya". Ok ta fada lokacin da ta nufe shi ta
durkusa ta dauki dorinar Umar karkarwa ya farayi dan a tunanin sa zane sa zatayi. Kamar yayi
waje da gudu kuma sai ya tuna gida a kulle yake da kwado. Sanda ta wulwula bulalar tukun ta
dorq mishi daya. Ihu! Ya kwada "wayyyo!!..". Da sauri tace "Haba sweetheart karka bada maza
mana. ni fa dama tambayar ka zanyi akwai zafi?". "Ehh A'aaa". Ya bada amsa biyu a jere,
yana sosa inda ta dake shi domin taji bulalar. Daga wa tayi da niyar kara mishi. Da sauri yace
"Akwai akwai zafin". Sannan ta wullar da bulalar gefe. Sweetheart to muje mu kwanta mana.

To ya fada da sauri yaje ya haye gado. Itama taje ta hau ta wani shishige mishi. shi kuwa duk a
tsorace yake a haka har barci ya kwashe shi. Tana ganin haka ta bace cikin abunda baiyi Minti
daya ba taje ta dauko Real Rafy ta hada su hade da cewa karta kuskura taji tsoran shi....._
__________________

_Fatima tunda tajw gida ta shiga daki ba abunda take sai kuka sai da tayi mai isar ta tukun barci
yayi gaba da ita. Kamar yanda ta saba kullum idan ta tashi zata fitsari da babyn ta take zuwa
dake a gado daya suke kwana. Yau kuwa tana farkawa taga ba yar baby ta tuna abunda ya faru
jiya sai kuwa ta hau kuka. Ameera ce ta farka a lokacin, Sai da taci uban Fatima tukun Fatima
tayi shiru. Washe gari tun da asuba Mama Asiya ta fito daga dakinta tafiyar kamar marar lafiya
domin yunwa taci-taci. A falo ta zube a kasa ita kam tama rasa abunyi har jiri take gani. Tashi
tayi ta nufi kitchen kamar ance ta bude store ta bude. Komai nasu ya dawo abun ne taga kamar
gizo yake mata, hakan yasa ta murjw idanu. Haba gaba daya yunwar da wani rashin karsashi
tafiya sukayi a lokacin. Kira ta fara kwallawa su Zuwaira. Ko wacce na dakinta suma ba barcin
suke ba yunwa ce taci ubansu. Shiru suka mata Alhalin kuma suna jinta. "Hauwa Zuwaira ku
fito kuga ikon Allah abincin mu ya dawo". Haba kafin ta rufe baki tagan su kowa ta fito a
sukwane. Kitchen din suka koma suna gani kuwa suka fara murna Zuwaira kam duk da tana jin
yunwa har da rawa. Indomie suka zuba a tukunya wajen guda 10. Tun kafin ta Dahu mama
Asiya taci Indomie danya leda biyu. Cin hauka sukayi wa indomie din domin ko bari ta huce
basuyi ba. Sai da kowa ya cika cikin sa mama asiya kam tayi zari da yawa dan har sai da tayi
amai._




_Da safe bayan kowa ya karya akayi shirin islamiyya domin ba boko an bada hutu, Fatima
tace bata da lafiya kanta ke ciwo mama Asiya tace "Munafuka wato makarantar ce bakya san
zuwa shiyasa kika azawa kanki ciwan karya ko?. To Alqur'an sai kinje maza wuce ki sako
Uniform dinki". Fatima kuka ta fashe da shi ta nufi daki tana cicila kafa. Mama asiya ta juya ta
kalle ta. Ta kama baki alamaun mamaki. "Iyeeee! Fatima ni kika wa wannan rashin kunyar dan
na taimake ki nace ki tafi makaranta ko, oya zo nan dan ubanki dawo". Fatima ta dawo tana
kuka ta durkusa a gaban mama asiya, "jiya dama naji kin shigo kina kuka ana ta lalashin ki miye
kike wa kuka?". Zuwaira ta tambaya. Cikin kuka Fatima tace "Ba malamin mu na islamiyya
bane ya kwace min Babyn na ya yanka min ba". Da jin haka mama Asiya ta bushe da dariya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login