Showing 12001 words to 15000 words out of 103342 words

Chapter 5 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5041

ya jawo mata ta zama kamar jaba a gidan in aka cire Fiddausi,
maza da mata yara da manya baki daya ba mai ragawa fatima a gidan bata samun sauki da
farin ciki sai abbanta na gida.


Hakan yasa ma in baya nan sai ta shiga daki abunta wani lokacin tata barci wani tym din kuma
tata kuka abunta. idan ta tuno mahaifiyarta. A labarin da nake baku yanzu fatima takai shekara
9 da rabi a duniya ta iya yiwa kanta komai. Dan ko da tana karama bayi mata ake ba, Asiya da
dauda take barinta. Fatima na shan wuya sosai Domin har ta saba da wahalar da yan uwan
nata suke bata bama kamar Asmart, da Nasmat. Wadan nan biyu ba irin wuyar da basa bawa
fatima.


*Cigaban labarin*
Washe gari Fatima ce ta tashi daga barci ta kalli dan agogon dake ajiye a kan mirror dakin nasu
firgigit ta zabura ganin karfe 6:10 bata yi sallah ba. Sauran yan uwan nata mata da suke tare a
dakin ta kalla. Sai bacci suke abunsu. Fiddausi kawai ta tayar domin ita tace ta dinga tadata.
fatima sauran ta kalla ita ba abun ta tashe su ba tasha fada in bataci sa'a bama har duka. Tashi
tayi ta nufi ban daki a guje. Tayi alwala ta dawo ta tayar da sallah. Naji muku haushi sosai da
baku ji karatun yarinyar nan ba.

A hankali bayan tayi fatiha take jan suratul اغلا ةيش ghaashiya. Muryarta na fitowa a hankali.
Kamar kar karatun ya kare. Tayi zaman tahiya kafin ta karasa ta sallame. Tun kafin matar ta
karaso take kwalla uban kira. "Fatu! Fatutu!" Da karfi. Fatima najin haka ta kama sauri
allah-Allah take ta idar da sallah kafin matar ta shigo.



domin tasan halin mama asiya kwarai bata bata dadi kuma tafi kowa musguna mata a gidan.
Asiya dingishi take sakamakon double faduwa da tayi jiya. Banko dakin tayi.


Kamar wacce zata karya shi. Ta tsaya a gurin ta kama baki. "Iyye! Gaga 'yar banza wato sai
yanzu ma kike sallah baki tashi da asuba kinyi ba ko?. inji mama asiya. A zuciya kuwa tace
"yarinya kina kokari domin kuwa ni banma yi ba tukun". Daidai lokacin fatima ta idar da sallah ta
juyo ta dan risina tace, "mama asiya ina kwana". Dan ban kwana ba zaki ganni ne dan ubanki?.
Sunkuyar da kai kawai fatima tayi. "Munafuka Kaganta kamar wata salaha. To da ban kwana ba
zaki ganni ne?, Tambayarki nake, Maza-maza ki iske ni a kitchen.
Yau dake zamu hada kayan kari. Saura kuma ki ki zuwa da wuri ta kama kunnan fatima ta
murda. "Kinga kunnan nan to sai na cira shi. Ko in ba-ba-laki in yaso in bada kudin dori".



Faima sai da tayi dan kara domin zafin da taji na murda kunnan gashi har yanzu taki sakinta.
Asiya tace. "Bazaki bar yiwa mutane ihu ba sai kin tada mana yara. Maza ki iske ni a kitchen
kinji ko?". Gyda kai fatima tayi tace "naji gani nan zuwa mama". Mari ta wanka mata. "Wacece
mamarki din?, Allah ya suttura in haifi yarinya kamarki". Ta nuna wasu yan mata dake gefe a
gado suna ta sharar barci tace "kinga yarana can ba kamarki ba". Mtseww Ta ja tsaki ta fice.




Nan ta bar fatima tana kuka. Ta zubda hawaye sosai tukun ta tashi taje da sauri ta shiga
bedroom tayi brush tukun ta canza kaya ta fito. Dugi-dugi ta nufi kitchen. Fatima tasha wuya
sosai a kitchen din dake gaba daya ake haduwa ayi girki a gidan. ba mai tausaya mata a cikin
matan baban nata duk su ukun miko wancan kulkula wannan wanke can gyara can. Ba mai
tausaya mata ko ganin kankantarta a cikin matan. Bayan an kamala ita suka dinga dorawa
kulolin abincin tana kaiwa dinner. Saida aka kamala komai tukun suka korata daki kuma suka
ce in ta shiga ta kwanta kmr mai barci kar ta yarda alhj ya gane cewa ta tashi balle ma ya gano
tayi aiki. Haka ta tafi tayi yanda sukace ta hau gadanta tayi shiru. Tana ajiyar zuciya. Su kuwa

kowacce. Sai ta shigo dakin ta tada ya-nata-ya-nata duk suka yi wanka sukayi brush tukun aka
nufi dinner. A nan kwance suka bar fatima. Tana jinsu duk abunda suke.
...................................................

Mujee zuwa.



Autan writers nee king boy












��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 15-16


NA. KING BOY ISAH



✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍




Abunda yake raina zana fitar na huce takaici, suyaya ku a raina zana fada bazan boye
ba.........

ALAMAR TAMBAYA TANA GA MAI YAWAITA TUNANI, MUSAM DA NASHI CIKIN
SOYAYYAR READERS NA. NA KWANA CIKIN TA NA RASA WANDA ZAI FIDDANI SAI KU
MASOYA NA WANDA KUKE DA KYAU NA KAMANNI, NA RIKE KAUNAR KU A RAINA TA
ZAUNA.. NAYI SHIRINA ZAN BAKU DUKA PAGEN GA�����
♥ BANI DA BAKIN GODE MUKU MASOYAN ALJANAR FATIMA, TUN YANZU KAFIN AJE
KO'INA MASSAGES DINKU SUN FARA RUTATOWA CIKIN WAYA TA. INA GANIN SAKONNIN
KU INA JIN DADI SOSAI, ALLAH YA BARMU TARE. DA MASU KIRANA INA GODIYA, KUNA A
HEART NA MUSAMMAN .♥
'YAN PHARIDAH KHAMSHI NOVELS

SAMEE KHAIRAH NOVELS

BIGBOY ISA NOVELS

BIGBOY ISAH FANS

ZAMANIWRITERSASSOCIATION
DA MA SAURAN SU....

BAN MANTA DA KUBA 'YAN WHATSAPP GROUPS INA GANIN SAKONNIN KU INA GODIYA.
ANA TARE, ANA TAREN TARE, ANA MUGUN TARE.LOLZ




FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----

*KARSHEN PAGEN BAYA*

~Su kuwa kowacce. Sai ta shigo dakin ta tada ya-nata-ya-nata duk suka yi wanka sukayi brush
tukun aka nufi dinner. A nan kwance suka bar fatima. Tana jinsu duk abunda suke.~

```»»Wajen cin abincin bangare-bangare ne wajen yara mata daban haka maza ma daban.
Bangaren uwaye kuma sunsa abincin gaba an zubawa kowa nasa saidai ba damar ci. Sai alhj
ya fito. Asiya tayi tsaki tace, "wai ace abincin ma sai an sawa mutane doka a kai, ji dallah yanda
ya bar mutane najin yunwa yaje yayi zamansa...". Shiru tayi sakamakon jin yara sun Fara hayaniya alamun shigowar alhj kenan. Idan ya shigo duk rashin jin yaro sai ya natsu domin
bashi da wasa. Bayan yaje ya zauna. Uwayan wato matansa. Suka fara gaishe sa tukun suma
yaran maza da mata masu dan wayo suka biyo layi daya bayan daya suna gaida shi. Yayi
mamaki da baiga fatima ba a cikin yan zuwa gaishe shi din ba. Da zai tambaya kuma sai ya
kyale.



Shi ya fara yin bismillah ya fara kai abincin baki tukun kowa ya fara ci. Dokar cin abincin kenan
sai ya fara cin indai yana gida tukun kow zaice. Fatima kuwa tana daki ga gajiya ga yunwa
kuma sun sata barcin dole. Saidai kwata-kwata barcin yaki zuwa domin yunwar dake kwakwalar
ta. Tana jin kwaram niyarsu ana cin abinci kamar ta fito sai dai kuma tana tsoran tayi laifi. Domin
tasan in ta saba musu to yau ta shiga uku ko abincin rana baza su bata ba. Haka suke mata
idan tayi musu wani laifin. Su sakata aiki mai tsanani kuma su sata azumin dole horo da yunwa.
Haka dai ta hakura ta kwanta tana kuka.



Bayan an gama cin abinci kowa ya kama gabansa dake yau weekend ba makarantar sai
islamiya. Alhj ya koma dakinsa amma sai ya kasa natsuwa da ya tino baiga fatima ba. Hakan
yasa ya fito ya tambayi matan "wai ina fatima ni ban ganta ba". Asiya tayi farat! Tace "uhmm alhj
kai da kasan halin yarinyar nan da shegiyar lalata. Tana can dakin yara tana barci nayi-nayi in
tashe ta tayi sallama amma taki tashi". Ta fadi hakan ne domin ta jawa fatima duka.




cikin fada yace "asiya wace irin banzar magana ne kika fada min kina nufin fatima bata tashi ba
har yanzu. me yasa kika zama muguwa maciya amana iyee! asiya. yarinyar nan fa marainiya ce
amanarta na baki. amma yanxu dan allah ace duk kin tashi yaranki sunyi wanka har sun karya
amma ita dake ba yarki bace shine zaki barta har wannan lokacin bata karya ba. yanzu karfe
9:30 fa". Ta wani marairaice "haba alhj in kuwa kace haka baka min adalci ba. yanzu duk irin

tatalin da nake wa wannan yarinyar kana so kace baka gani alhj. Ni ai a ganina rashin tashin ta
din ma da nayi duk a cikin gata ne. Na barta ne ta hutawa rant....".


Tsawa ya daka mata. "Ke dallah rufe min baki bana san wannan zakin bakin naki. Maza wuce ki
kira wo min ita". Murguda baki tayi ta tashi tana gunguni. Wai irin wannan ai sai yaja a rainata a
gaban kishiyoyinta ake mata wannan abun "Dama jiya ka targada ni dan mugunta". Alhj yace
"me kikace". Juyowa tayi. "Aa ni banyi magana ba". Ta wani gallo mishi harara. Ta nufi dakin
yara. Fatima najin turo kofarta tayi maza ta rufe idanunta kamar mai barci.







Asiya kuwa tazo ta kama tikarta "fati!-fati!, Tashe munafuka kinzo kin kwanta wato sai barci
kike.maza jeki kiyi brush ki zo wannan masifafan mutumin na kiranki". Fati bata ce komai ba ta
sauko taje tayi brush ta dawo. Tazo gaban asiya tace nayi. Rigarta ta gyara mata ta kuma dan
go goge mata fuska kamar da gaske. Tace "idan kika yarda kika ce kinyi aiki kuma kika gayawa
alhj ni nace ki dawo daki ki kwanta to ni dake ne a gidan nan kinsan dai halina sarai".


Fatima tace "bazance ba aunty". Dankwashinta tayi a kai. "Kinci uwaki. Nice aunty wato bama
mama ba ko. Wuce muje". Fatima ta shiga gaba asiya na binta baya. Alhj kallo daya yayi wa
fatima ya gane tana jin yunwa. Bata karya ba. "Momyna". sunanda yake kiranta da shi kenan.
Kinci abinci kuwa. Girgiza kai tayi tace aa ynz na tashi a barci. Barci kuma?, wato bakiyi sallah
ba ko?. Bana ce ki dinga kula da sallah ba ki bar wasa da ita". "Dady nayi fa tun da wari nayi
sallah sannan na koma barcin". "That good haka nake san ji momyna".



Juyawa yayi ga matan nasa wanda duk sun Zuro musu ido ba abunda suke sai hararen fatima.
A cikin zuciyqrsu kuma tsanarta na kara fadada. "Wace tayi abinci?, Ina abincinta?". Ya
tambaya Zuwaira tace, "alhj wane abinci kuma ai gidan nan ba wani sauran abinci duk an cinye
tana can tana barci". Alhj yace "Yanzu Dan tsabar mugun hali yarinyar bata ci abinci ba shine
kukaki ajiye mata. Ko dan kunsan ba 'ya'yanku bane. Wato ita Marainiya batada uwa ko". Bai
tsaya jin abunda zasuce ba yaja hannun fatima yace "zo muje in saya miki abinci mamana".
Yaja hannunta suka fita.



Nan ya bar mata sai surutai suke yi. Har asiya na cewa "wai anya kuwa uwar yarinyar can ba

asiri tayiwa alhj ba kuma har yanzu bayan ta mutu yake tasiri a kan yarta ba.nifa abun ya fara
bani tsoro". Zuwaira tace "haba aunty barta mana ai gasuwa zatayi a gidan nan domin ko yar
aiki sai tafita jin dadi wllh. Yarinya karama sai kini bibin tsiya". Hauwa tace, ai wallah ni kadai
nasan muguntar da na shiryawa yarinyar nan, zaku gani da idanku". Yar guda sukayil a tare
suka hada hannu.



Mota suka hau alhj yaja saida suka je wata rumfar mai shayi tukun ya faka ya fito yajawo
hannunta suka shiga suka zauna yasa a soyo mata indomei da kwai da kuma zallar wainar
kwan da kofin shayi biyu. Kudi ya kashe musu dai sosai a gurin. Fatima saida taji cikinta ya cika
nat! Domin kuwa rabanta da ta sama isashen abinci tun waccan juma'ar da taje gidan su wata
kawarta ta wasa. Mota suka hau suka nufo gida tafiya ake fatima sai waige-waige take yi ta kalli
can ta kalli can. Tana kallan shaguna. "Dady tsaya-dady-tsaya". Bai shirya ba ya take birki. Ya
fara tambayarta "miye kika tsaida mu mamana?". "Dady danyi baya, Yi baya dady". Baiyi
gardama ba yayi baya da motar. Saida suka zo saitin wani shago tace ya tsaya. Da gudu ta
sauko taje tana kokarin dauko wata yar baby. Wacce suke a jere duk na sayarwa ne.


Mai shagon ne ya fito yana neman dukanta alhj ya dakatarda shi. Yace "mamana miye haka
kika zo zaki daukar musu abu na sayarwa ne fa ko baki sani ba?". "Na sani dady wannan nake
so ka saya min ina santa sosai kaga munyi kama da ita kuma ma dady kaga wannan tafi ta
nuratu kyau da girma". Dan Murmushi yayi kadan yace "ke kuwa me zakiyi da wannan katuwar
diyar robber ai tayi girma duba karama mn. Wannan tafa kusan kaiki tsayi". "Aa baba ni
wannan nake so". Alhj ya kalli mai shagon ya tambayi kudin diyar robar. Mai shago yace "dubu
bakwai". Alhj yace ina zuwa. Mota ya koma ya dauko kudi "kash! Ashe na baro kudin a gida".
Saura dubu uku ne a hannunsa. Ya dawo cikin yanayin damuwa gashi mutumin baisan shi ba.
Balle yace in ya fito zai kawo mishi. Ita kuwa fatima rike take da yar tsanar ta fara wasa da ita.



Ya dawo yace "malam na manta kudina ne a gida kaga saura dubu uku canjina kayi hakuri ka
rike wannan ka bamu yar robar in yaso idan na fito zan kawo maka". Mai shagon yace "ai ina
ban sanka ba bazan taba yarda ba. Kaga kawai in bazaka saya bane to".



Alhj ya kalli yar tasa yace fatima "kinga yanzu bani da canji zo muje gida in dauko kudi sai mu
dawo in saya miki". Fatima ta saka kuka ta kankame yar tsanar gam a kirjinta, wai ai ita baza'a
rabata da yar babyn ta ba. Alhj yayi-yayi da ita ta bari ya dawo amma taki. Ba yanda ya iya dole
wayarsa ya bawa mai shagon ya rike ya basu yar babyn kafin ya dauko mishi kudin. Haka kuwa
akayi. Mai shago ya karba yaje shago ya ajiye tukun ya dauko musu wata yar karamar akwati.
Ta kayan yar babyn ce. Suka karba fatima sai murna take ta dauki yar babyn wacce ta kusa

tsayinta tasa a mota suka tafi gida tunda suka taho a hanya yar babyn ta fara kwai-kwayan
fatima. In tayi dariya itama sai yar tsanar tayi, haka in ta bata rai! Sai yar tsanar ma ta tsuke
fuska. Fatima dady ta karaji nan tata mata abubuwa har gwallo in faty tayi yar tsanar sai ta rama
............................................... . .........```



Mujee zuwa.


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION




Autan writers nee king boy














��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 17-18

NA. KING BOY ISAH



✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍

� NA BAKU WANNAN PAGEN NE SABODA NAGA...

*TSABAR TSANTSAR TSANANIN TSAGWARAN, TSAYUWA DA TSAIDA TSABAGEN
TSAIDADE SO DA YA ZARCE NA TSINTSAYE SAMAN TSAMIYAR TSANGAYAR TSAUNI
TSANANIN SO DA KAUNA DA KUKE NUNA WA LITTAFAI NA.*

� *INA JI DAKU SABODA HAKA MA NA RUBUTA SUNAN KU A FARFAJIYAR FARAR
FAIFAR FATAR FARAR ZUCIYATA DAKE FAFADAR FADAR FADAMA MAI FANFUNAN DA KE
FIDA FURUCIN FITARWA MASU FUKAFUKAI DA FANKOKIN.....*

*SALMAH QUEEN*


*ZEANAV DAWISU*

_INA JI DAKU ALLAH YA BAR MIN KU KUNA SAHUN GABA CIKIN MASOYAN LITTAFAINA_


_SAM KALAMAN BAKINA SUNYI KADAN DA SU BAYYANA IRIN TSANTSAR FARIN CIKIN
DA NAKE JI YAYIN DA NAGA SAKONIN MASOYANA SUN SHIGO WAYATA._

FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
whatsapp's number
08096831009
----

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~In tayi dariya itama sai yar tsanar tayi, haka in ta bata rai! Sai yar tsanar ma ta tsuke fuska.
Fatima dady ta karaji nan tata mata abubuwa har gwallo in faty tayi yar tsanar sai ta rama~
```»»Tun a mota yar babyn ta fara magana. a cikin wata irin karamar murya. "Sunana safuratu
ina tayaki murna da sayana da kikayi". Fatima ta juya domin ganin mai magana bataga kowa
ba. tace "abba kaine kayi magana Yanzu?". yace "aa magana kikaji nayi". tace magana naji ko
yar babyna ce?. alhj murmushi yayi yace "'yar baby kuma ai ba irin mai magana bace bakiga
batada speaker ba...?. Kafin ya rufe baki wata siririyar murya ta kara magana, "Zan dinga saki
dariya, zan dinga baki labarai masu dadi, amma ni fa ba'a barina da yunwa, kuma ni kullum sai
anyi min wanka an canza min kaya anyi min make-up....." alhj tsurewa yayi domin yaji tabbas
yar babyn ce ke magana a tsorace ya fige yar robar yana dudubata wai ko zaiga speaker a
jikinta amma bai gani ba. ita kuwa fatima murna kawai take da jindadi yar babynta na magana.
alhj yace "fatima 'yar babynki ce fa mai maganar nan to amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login