Showing 90001 words to 93000 words out of 103342 words
Chapter 31 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
hanzari ta goce. Duka ya kara kai mata da kafa. Nan ma ta goce tana binshi da wani
shu'umin kallo tana murmushi. Mama Asiya da ta lura d Fatima da sauri ta zo ta janye danta
dan kar a sabauta mata shi. Shi kuwa tuni ya hau daukin zuciya sai huci yake. Yana hararen
Fatima da ita kuwa ko kula da shi batayi ba taje kusa da Fiddausi ta zauna tana shan tea. Tana
gamawa ta tashi zata fita waje. "Ke dan uwar ki dawo kije kiyi shirin makaranta". Cewar Abba.
Ficewa tayi ba tare da tace mushi komai ba. Abba yace_
_"Fatima ina tausaya miki. Dan Wallahi in na kamaki daga ni sai ke sai nayi miki fata-fata, Dan
yau naga kin tashi da wani sabon salon iskancin". "Ko?". Fatima ma juyo tace mishi. Kofin
shayin dake hannun shi ya wulla mata. Ba abunda ya bashi mamaki sai ganin da yayi kofin yayi
Kwana ya nufi wani wajen. Bayan ya gama shan shayin ya tashi ya nufi dakin shi domin yaje ya
huta. Yana shiga kafin ma ya bude kofa yaje kofar ta rufe kanta da karfki. Tsuru Abba ya tsaya
yana kallan Kan bad dinshi wani abu ne cikin Blanket dinshi Yana gurnani marar dadi yana
kuma mamotsawa._
_A hankali Abba ya nufi wajen hannun shi har karkarwa yake. Duk ya gama tsoracewa domin
shi bai bar kowa a dakin ba. Kuma baima taba jin gurnani kalar wannan ba. Zuciyoyin suka
shiga bashi shawara wata zuciyar na cewa ya bude yaga miyr wata zuciyar kuma na cewa ya
fita ya gayawa su Mama Asiya. Ta wani fannin kuma ceqa yake "inje in sanar da su kamar dai ni
din va namiji bane. Bari kawai in bude inga miye. Hannun na karkarwa sai ya kusa kama
bargon kawai sai yaja baya a tsorace. Kusan sau biyar yana yin haka. A na shida ne ya daure
ya kama bargon yaja da karfi. Ahhhhhhhhhhhhhh! Ya sakk ihu!............................?.....?......._
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA.
SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN
KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 101-102
© *KING BOY ISAH* ✍
. .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍ *®Z.W.A* .
. .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ta wani fannin kuma ceqa yake "inje in sanar da su kamar dai ni din va namiji bane. Bari kawai
in bude inga miye. Hannun na karkarwa sai ya kusa kama bargon kawai sai yaja baya a
tsorace. Kusan sau biyar yana yin haka. A na shida ne ya daure ya kama bargon yaja da karfi.
Ahhhhhhhhhhhhhh! Ya sakk ihu!.~
_*I*tama ihun ta kwada. Yana ganin Fatima ce sai ya bata rai hade da watsa mata harara. "Ke
uban me kike a nan dakin?. Wa yace ki shigo min daki?". Shiru tayi tana kallan shi ba tare da ta
bashi amsa ba. Dube-dube ya shiga yi yana neman abun da zai dake ta. Ganin ba bulala ko
wani mabugi a wajen ne yasa shi tsawa yana mata mugun kallo. "Oya tashi ki bar dakin nan ko
inyi kasa-kasa dake a nan wajen". "Bazan tafi ba din yau a nan xan wuni". "Ke ni kike gaya wa
wannan maganar?". Ya nufo wajen ta ya daga hannu zai mare ta yaji hannun ya tsaya cik! a
lankwashe. Hahahaha ta kwashe da dariya. Abba kuwa fama yake ya mike hannun shi amma
ina abun ya gagara. Ga Fatima sai Dariya take mai. Abun ya kara fusata shi nan take ya kara
daga dayan hannu da nufin ya wanka mata mari. nan ma hannun ya tsaya cik! Duk hannuwan
nashi biyu suka makale suka tsaya a lank'washe. Fatima da ganin hakan ta tashi ta fita daga
dakin a guje tana Dariya. Su mama Asiya lokacin sun gama cin abinci yara kuma duk sun tafi
makaranta. Sai su uku zaune a falo suna tadi._
_Fatima suka gani ta zo ta wuce a guje tana dariya. Zuwaira da Hauwa har yun kura zasu tsere
suma a tsorace sukaji Abba a daki sai kwalla kira yake. "Mama! Mama!". Da sauri suka nufi
dakin nashi a hanya sukayi kicibus. Hannuwan shi biyun duk a lankwashe. Ya rasa yanda zaiyi
har ya fara zubar hawaye. Su duk ukun tambayar shi suke me ya faru. Cikin kuka ya fada
musu duk abunda ya faru. Da jin haka mama Asiya tana jin haka tac "Kaico! Wai kai Abba me
yasa baka gane wa ne. Yarinyar nan tunda kaga ina raga mata ai ya kamata kasan cewa akwai
lauje cikin nadi. Aljanu ne suka shiga jikin Fatima. sau tari ina nuna maka ba ruwanka da ita
amma kaki yanzu gashi ka jawo mana bala'i. Dama yanzu nake so in zo in gaya maka cewa ka
fita harkar ta kar ta sabauta min kai. Ban sani ba ashe har ta faru ta kare". Ta kalli su Zuwaira
tukun taci gaba da magana. "Dan Allah yanzu miye abun yi?. Kunga ta mayar min da da
Masaki"._
_Jugum! Su Zuwaira sukayi suna nazari can Zuwaira tace, "Wannan abun ba wani abu ne ya
jawo shi ba sai rashin sani wanda kuwa kowa yasan cewa *YAFI DARE DUHU*. To amma
yanzu abun da ya dace shine muje mu roki Fatima ta taimaka ta mikar mishi da hannun shi.
Tunda durkusa wa wada ba gajiya wa bane in dai za'a sama biyan bukata". Gaba daya suka
aminta da shawarar Zuwaira. Kofar dakin su Fatima suka nufo tun daga nesa suka jin sautin
dariyar ta. Mama Asiya tace "A gaskiya gidan nan ba lafiya. Aljanun jikin fatima rikakkun
gardawa ne. In bamuyi a hankali ba duk sai sun babala mu. Kuma ya kama ta mu sanar da
alhaji ya tafi wannan shegen aikin nashi ga gida yana so ya fi karfin mu". Hauwa tace, "Gaskiya
ne amma ai naji yace ya ran Friday zai dawo". Zuwaira tura kofar tayi taji a rufe gam!
kwankwasa kofar ta shiga yi tana fadar "Fatima! Fatima!. Dan Allah ki bude mana. Ba dan halin
mu ba dan Allah". Shiru fatima taki bude wa. Sun dade a wajen kowa na tofa albarkacin bakin
sa na magiya. Abba ma cikin kuka yake rokon ta ta bude ta mikar mai da hannun shi. Domin
yaga wanki hulana neman kai shi dare. Fatima ta bude kofar cikin uniform dinta na islamiya rai
a bace tace,_
_"Ku gafa in wuce ko in hangiza ku gaba daya kuma ko mutum ya karyw ba abun da yasha
ruwana". Ta make kafada alamun ko Oho. Mama Asiya da Abba lokaci daya suka zube kan
gwiwoyin su suna magiya. Fatima ta kwashe da yar banzan Dariya. Wai yau su Mama Asiya ce
da durkusawa gaban Fati ana bada hakuri. Sai da Fatima tayi dariya mai isar ta cikin isa da iko
ta kalli asiya tace, "In kina so in mikar mai da hannu sai kinyi tsallan kwado". Tsuru! Suka
zazaro ido gaba dayan su. Hauwa da Zuwaira kamar su kwashe da dariya. Zuwaira da san
gulma ta wa Hauwa rada a kunne. "Yau zamu ga tsallan kwado a gun Asiya. Tubur-tuburtu
kenan". Wata muguwar dariya ce ta zo wa hauwa. Da kyar ta iya samu ta matse bakinta. Asiya
tayi misisi da ido ta marairaice, "Haba Fatima kiyi hakuri mana ni yanzu ina zan iya tsallan
kwado?". Fatima tayi hanyar wajen "Bakya so hannun danki ya mike ashe?"._
_Da sauri Asiya ta mike ta shiga gaban Fatima, "Yi hakuri dan Allah karki tafi ki bar Abba na a
cikin wannan yanayin". "To maza ina jiranki fara". Mama Asiya ta tsuguna. Juyawa tayi ta kalli
Su Zuwaira dariya suke mata sosai amma ciki-ciki ba yanda Fatima zata ji ba. tsalle mama
Asiya taso tayi amma ko rabuwa da kasa kafafunbatayi ba saboda nauyi da jikin ta yayi.
Hahhahhahah Fatima ta kwashe da dariya, "Malama kiyi sauri kiyi ina jira kinga dai na makara
makaranta". "To....To. Bari in kokarta". Tsalle mama Asiya tayi niyar yi a karo ma biyu. Akayi
rashin sa'a kuwa kafarta bata zo a dai-dai ba. Sai ji kake rigijif! Ta fadi._
_Fatima ta tuntsite da dariya. Haka ma su Zuwaira. Sai da Fatima tayi dariya har tana rike ciki.
Tace, Kin fadi jarabawa amma tun da dai kin sani dariya Abba mike hannun ka na dama". Tana
fadar haka ta juya ta wuce, Kamar wasa Abba ya mike hannun shi na dama yaka ya mike lafiya
lau kamar bai taba lankwashe wa ba. Yayi murna sosai sai dai kuma hannun hagun har yanzu
a lankwashe yake. Tun daga tsakar gida Fatima ke kwalawa Mai gadi kira yazo ya bude mata.
Da sauri ya fito yana ganin Fatimar ce yayi tsaki. "Wai ke wannan yarinyar yaushe kika koma
haka ne?. Ina tarbiyar ki take. Wato naga kwana biyun nan tashen rashin kunya kikeyi".
Gatsine da harara kawai take binshi da shi. Haushi abun ya bashi ya nufo ta zai daga. "Wallahi
kana dukana kayi ta aikin ka. Sanin kanka ne Alhaji baya san abunda zai taba ni kuma ran
Friday zai dawo". Yanq ji ta fadi haka sai jikin shi yayi sanyi. Tsaki yaja yaje ya bude mata
kofar._
_"Zo ki wuce jarababa kawai. Ke ma dai su Asmart sun koya miki wannan masifar ashe". Bata
tanka mishi ba dungwai-dungwai ta wuce har makaranta. Makaranta ta cika makil! Sai karatu
ake Fatima ba tare da wani fargaba ba ta shiga ajinsu. Malamin su na ganin ta ya fara binta da
harara. Ita kuwa ko a kwalarta. Domin yunkurin wucewa ta zauna ma take yi. Malam yace, "Ke
gidan ku, Ina zaki ko baki san kin makara bane?". "Ayi hakuri malam, na tsaya yin wani abu
ne". "Kaniyar ki. Zo nan". ba gardaa taje. Tana zuwa kuwa ya fara zafga mata bulala. Sai da
yayi mata uku. Yace "Oya maza wuce ki nema waje ki zauna". Tsaye tayi ta kafe shi da ido tana
hararen shi. Tsawa ya kara daka mata amma taki tafiya. Hakan yasa ya kara juyowa yaci gaba
da dukan ta abun yayi matukar tsorata malam yanda yasan Fatima da shegen kuka bulala daya
ko biyu yake mata ta fashe da kuka yau kuwa gata sai duka yake amma ta kafe shi da ido tana
harara ko kwalla babu. Sai da ya gaji da dukan dan kanshi ya barta yaje yaci gaba da darasi
yace, "In kinga dama ki kwana a nan tunda bazaki je ki zauna ba. Da fadar haka Fatima ta
wuce ta zauna. Abun ya daure wa Malam kai a zuciya yake saka "Anya kuwa wannan Fatima
ce?"._
_Basarwa yayi yaci gaba da darasi. "Yara yau zamu ga mai tsantsar hazaka daga cikin ku. Idan
baku manta ba kwanaki munyi bayanin taimama a cikin littafin ahdari. Sanan kuma mun kwana
biyu munayi wanda sai da na tabbatar kun hardace tukun na daina biya muku. Dan haka yanzu
ina bukatar Dalibin da zai tashi ya mai-maita mana. Kuma zan bawa duk wanda ya karanta min
dai-dai kyauta. Yara biyu ne suka tashi daya mace daya namiji sai duk sai sun fara sai su
kakare. Fatima ce ta mike. "Ni zan karanta kuma bana bukatar kyautar". Malam kallo kawai ya
bita da shi. Nan take ta fara_
_*"Tafiyar da bata sabon Allah ba. Da marar lafiya, (Wanda yaji ciwo ko kuma dai yaa jin
matsanan cin sanyi, Yana iya Taimama). Sallar farillah ko ta nafila. Mazaunin gida lafiyayye.
yana iya Taimama dan Gudun fital lokacin sallah. FARILLAN TAIMAMA: Niya da bigiri (waje)
mai tsarki. Shafar fuska, da shafar hannuwa zuwa dantse. Da bugun kasa na farko da
gagautawa. Shigar lokaci da sadar da ita zuwa sallah. BIGIRE: (WAJE) Wajen da ya hallata ayi
taimama a shi. Turbaya tubali. Da dutse da kankara da waje mai danshi da makamantan su.
Taimama bata halatta da suminti ko abun dafawa. Ko kan tabarma. Da itace da ciyayyi.*_
_*Anyi rangwami ga marar lafiya ya shafi bango in dai bai sama wanda zai samo mishi kasa
ba. SUNNONIN TA: Sabun ta bugun bigiri wajen shafar hannuwansa da shafar abunda ke
tsakani Ku'i biyu da dantsen sa. Da jerantawa. MUSATAHBBANTA: Yin bisimillah, Gabatar da
Zhirin Zura'i (Tsuntsuyar hannu). A bisa badinin sa. Farkon sa a bisa majinkircinsa. MASU
WARWARE TAIMAMA: Masu warware ta daya suke da masu warware alwala. Ba'a yin sallar
nafila biyu da taimam daya. Wanda yayi taimama domin yin Sallar farillah ya halatta a gare shin
yin farillah bayan ya gama. Ya halatta ka taba Alqurani dawafi, da Tilawa. Da sadar da ita kafin
fitar lokaci. Ya halatta ayi duk abunda aka ambata da taimama. Wanda yayi taimama yayi sallar
isha'i yayi sha'i da wuturi, ba tare da ya jinkirta ba. Wanda yayi taimama yana da janaba. Babu
makawa sai yayi niyar ta".*_
_Tana kaiwa nan ta koma ta zauna abunta. Malam kuwa tun da ta fara kallan ta kawai yake
yana kada kai da alamun mamaki. Bai san lokacin da bakin sa ya furta. "Attakabir" Ba. Yara
suka kwasa. ",Allahu akbar". Har aka tashi daga islamiyya malam na mamakin Fatima yau gaba
daya ta canza. Fatima tunda aka tashi daga makaranta ta tafi gidan Rafy. Rafy kuwa dake
tasan halin Safuratu sai tayi tunanin ko itace tayo sufar fatin. Nan sukata hira Fatima na taya ta
wasu aikin gida. Bayan la'asar Fatima ta koma gida. Yau ma kamar yanda ta sabawa mai gadi
haka tata buga get din da karfi. Wannan karan yana budewa ta bangaje shi ya fadi can gefe ta
wuc fuuuu! Abunta. Asmart Nasmat Ameerah da Fiddausi dake gefe tana karanta novel a
Facebook. Sune a falon. Suna kallon Mtv. Fatima na shigowa ta nemo remote ta rasa. Kawai sai
zare Socket din tayi. Asmart na ganin haka tayo kanta da masifa........................................._
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA.
SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN
KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 103-104
© *KING BOY ISAH* ✍
. .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍ *®Z.W.A* .
. .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
_*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
_*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*MASOYA AYI HAKURI DANI. WALLAHI KWANA BIYU INA BUSY NE BANA SAMUN TIME
DIN TYPE* *MASU CEWA JAN AJI NE. DUK SAI NA HADAKU DA ALJANU*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Asmart Nasmat Ameerah da Fiddausi dake gefe tana karanta novel a Facebook. Sune a falon.
Suna kallon Mtv. Fatima na shigowa ta nemo remote ta rasa. Kawai sai zare Socket din tayi.
Asmart na ganin haka tayo kanta da masifa.~
_"Ke Fatima bana san iskanci da tambada mayar mana da socket ko in lakada ki yanzun nan
Wallahi". "Baza'a mayar ba". Asmart da taga Fatimar bata da alamun mayar da socket din dai
ta nufo ta a fusace, Kafin ta karasa wajen ta. "Kai! kai! kai!._
_Rufa mana asiri in ba sokikr mu shiga uku ba yanzu". Hauwa ce ta fadi haka lokacin da ta fito
daga kitchen. Asmart dakata wa tayi tana kallan Hauwa'u. Fatima tace, "Duk wanda ya kunna tv
din nan yau ni da shi ne a cikin gidan nan". Da fadar haka ta juya ta wuce daki. Asmart tace,
"Me ke faru Aunty Hauwa?". Hauwa tace. "Wato ku duk baku san me ke faruwa a gidan nan ba
kenan?. Ai tun jiya Aljanu sun shiga jikin Fatima su suke sakata duk wani iskanci da take.
Kuma gasu da shegen karfi. Kai dazun ma Abba da yaje dukan ta Wallahi hannun shi tsayawa
yayi a lankwashe, Da kyar muka samu ta mikar mai da hannun daya, Dayan kuma taki mikar
mishi wai sai Aunty Asiya tayi tsallan kwadi". Hhhhhhhhhh Nasmat tayi dariya, "Lalai Aunty
Hauwa kin iya tatsuniya. Wai yanzu kina nufin daga naje dukan Fatima kawai dai hannuna ya
makale". Hauwa tace, "Kwarai in kuwa baki yarda ba gaki gata. Inda ba kasa nan ake
gardamar kokowa". Asmart tace, "Kai