Showing 51001 words to 54000 words out of 103342 words

Chapter 18 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5049


"Shegiya Allah ya kara, dama ni wannan Aljanar ba santa nake ba, ni gaba daya ma na tsane
ta". Zuwaira tace "Au! Dama a kanta ne kike kuka ake ta rarashin ki amma kika ki ji, Ai ni dana
sani wallahi da duk da ina jin yunwa da sai na taso na fafala miki mari, mu wannan ai rahama
ne ma rabuwar mu da ita". Korar ta sukayi ta tafi daki tana kuka, Su Asmart suna canza kaya
suna sa na islamiyya ta shigo tana kuka. Nasmat na ganin ta ta nufo ta tana zazaginta. Wai ta
musu shiru, Fatima duk da ta so ta rike kukan amma yaki rukuwa. Nasmat dunkule hannu tayi
ta Dankwashi Fatima a kai, haba ai kuwa sai ta kara fashe wa da kuka, Fiddausi na ban daki jin
kukan Fatima yasa tayi sauri ta fito. "Keee! Keee! Wallahi in kika sake dukan ta sai naci
uwarki". Fiddausi tace lokaci da ta nufi inda suke. Maganar ce ta dakatar da Nasmat da tayi

niyar yiwa Fatima dundu. Nasmat tana gunguni ta koma gun Asmart dariya asmart tayi tace
"Nasmat mugunta ko wato dake Kinga *ALJANAR FATIMA* Bata nan". Nasmat tace "ai sai
na rama duk abunda tayi min"._


_"Asmart tace bari a dawo daga Islamiyya zata daku ai a waje na". Fiddausi ta tambayi Fatima
me take wa kuka Fatima ta fada mata mama asiya ce yace sai taje makaranta kuma kanta ke
ciwo. Fiddausi hannu ta dora a jikin Fatima taji da zafi, hakan yasa taje ta dauko mata magani
ta bata tashi tukun tace ta kwanta. Sunzo tafiya mama Asiya tace ala dole sai Fatima taje
makaranta, Sai da Fiddausi tayi yaki sosai tukun mama asiya ta barta. Ai kuwa suna fita mama
asiya ta koro Fatima waje. Wai ta koma cikin rana Mai zazabi baya san sanyi dan salan
mugunta. Aljanar Safuratu ce tafe cikin iska tun daga nesa ta hangi mama asiya sai jaraba take
wa Fatima tana dankwashin ta ita kuwa tana kuka hakan yasa ta kara
sauri....................................._




Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy














��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*

*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 61-62


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*


*NASAN NAYI MUKU LAIFI KUYI HAKURI DAN ALLAH MASOYA.*

� _JIYA KAM NAGA MASOYAN ALJANAR FATIMA. HAR KARFE GOMA MASSAGES BASU
DAI NA SHIGOWA WAYA TA BA. DUK MASU JIRAN POST NE._


_NA GODE MUKU MASOYAN WANNAN LITTAFIN NAWA, SANNAN IN BAKU HAKURI
BISA RASHIN POST DINA. WALLAHI INA CIKIN TYPING TUN KARFE 5 BIYAR BACCI YA
DAUKE NI BAN FARKA BA SAI WAJEN 9. TO BAKU KADAI NAWA LAIFI BA HAR DA
UBANGIJINA_

� I LUV OLL MY FANS. ANA MUGUN TARE �


*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Aljanar Safuratu ce tafe cikin iska tun daga nesa ta hangi mama asiya sai jaraba take wa
Fatima tana dankwashin ta ita kuwa tana kuka hakan yasa ta kara sauri.~

_*K*afin Safuratu ta karaso wajen mama Asiya ta shige ciki, Tana ganin haka ta bace ta dawo
sufar Ameera, ta kofar gidan ta shigo taje gurin Fatima. "Ke wai miye tun jiya kike tayi wa
mutane kuka?". Fatima ta dago cikin kuka tace "Malam ne ya kwace min Babyna jiya ya
yayanka". Sai a lokacin Safuratu ta lura yar babyn a hannun Fatimar, Da sauri ta juya tana
fita daga gidan ta bace bata zame ko ina ba sai kofar mai shagon, inda aka sayo 'Yar babyn
shagon ta gani a kulle_
​ ________________

_A gidan Umar kuwa Safuratu na ganin Asuba ta kusa to sai tayi sauri ta dauke Rafy ta mayar
da ita gida ba tare da tama sani ba tana barci, Ita kuwa ta juye zuwa rafy din ta zo ta kwanta.
Da asuba Umar ya farka zaune yayi ya zuba wa Rafy da ke barci ido, Tunani yake a ranshi

wannan Rafy din ce ko kuwa, Da dabar ta yayi Rafy! Rafy! Tashi asuba tayi_




_Firgigit! Ta tashi a dan tsorace shi kanshi ma sai da ta tsorata shi. "Sannu mai gida lokacin
sallah yayi ko?". Ta fad murya a sanyaye daga jin haka a zuciyarsa yace "Wannan Rafy ce ba
Aljanar ba". Kai ya daga mata alamun eh, Ita kuwa ta saukko taje tayo alwala shima alwalar
yaje yayi yazo ya tada musu sallah. Bayan sun gama salar ma ya juyo y kalle ta yaga dai
alamar Rafy din ce. domin kamar yanda ta saba ko Ido bata iya hadawa da shi haka ma yanzu
Safuratu alamun tsoro take nuna mishi. Bayan ta gama adduo'i da sauri ta rissina cikin Ladabi
ta gaishe shi ya amsa. Ta shi tayi ta cire hijab din jikin ta koma kan gadan ta kwanta. Umar da
ganin haka ya murtuke fuska ya shiga zancen zuci. "Amma fa yarinyar nan in ita ce ta raina min
wayyo._



_Harda wani hayewa kan gado, Amma bari in gwada ta inga Aljanar ce ko kuwa". Da karfi ya
fara maganar "Rafy! Rafy! Saukko kasa malama kin wani je kin daare gado kamar na ubanki".
Da sauri ta tashi ta sauko a tsorace. Murmushi yayi yace Yauwa wannan Rafy dita ce. "Yauwa
ke abunda nake so kiyi min a yau zan zana miki yanzu kuma Wallahi in bakiyi daya daga ciki ba
har kika 'yar da na dawo,..Kema kin san sauran". "To mai gida ina jinka". Ya wulla mata
harara tukun ya fara lissafi da yatsun sa yana kirga mata aikin. "Na farko yanzu ki tashi kije ki
dafa min ruwan wanka, Kafin in fito ki dafa min abun break. Na uku kinga kayana can sun taru
sun kusan kala ashirin ki wanke min su ki goge, Na hudu kiyi min Taliya da farfesun kaza kinji
ni da kyau". Kuka ta fashe da shi, cikin kuka tace "Haba mai gida so kake yi ka kashe ni
wannan aikin ai sunyi yawa Wallahi bazan iya ba duk ni kadai a rana. Kum..." Tass! Taji saukan
mari a fuskan ta, "Kaji 'yar isakar 'yarinya to idan baki min ba wa zaiyi min wato a nufin ki in baki
ci da sha in barki gida mimike a kan gado kamar gasasar kaza ko?. To Wallahi ban lamunta ba,
oya maza tashi". Ball yake shirin yi da ita hakan yasa ta tashi ta fita a guje shi kuwa ya zauna a
bakin gado. Dariyar mugunta ya fara yi. Juyowar da zaiyi yaga Rafy tsaye tana kallansa.
Tsayawa yayi da dariya tukun yace "Ke me kika yi a nan maza wuce kije kiyi abunda nasa ki".
"Kai tashi maza je ka dafa min ruwan zafi ka kai min bayi, Kuma mintuna 15 kadai na baka".
Kamar daga sama yaji magana, juyawa yayi yaga lalai Rafy ce ke maganar, "Kanbuhun uba!.
Wato ina baki Umarni kema kina bani da Alamar dukan safe kike bukatar ki karya da shi yau".
Ta sowa yayi da hanzari zai dake ta ai kuwa ta rike hannun ta murda shi. Ihu ya kwalla Tukun ta
sake shi. "Oya wuce kayi abunda na saka ka kafin raina ya baci"."Rai nin wayo ma, ina mijin ki
ne zaki sa in miki wani ruwan zafi To Qur'an bazan yi ba. To ni in gaya miki a tarihin rayuwa ta
ban taba tsugunna wa gindin ba". "Au bazaka yi ba kenan!". "Eh bazan yi ba" ya fada a dan
tsorace domin ya gano ba Rafy bace._

_Juyawa tayi ta dauki Bulalar jiya ta nufe shi, Tun kafin ta karasa wajen shi ya farq ihu! Yana
bata hakuri. Batayi wata-wata bata fara zura mai bulala, shi kuwa ba abunda yake sai ihu!
Dake a daki ne ba'a ji sosai waje. Sai da ta mishi wajen bulala ashirin tukun tace "Yanzu zakayi
ko kuwa?" Da sauri yace "Eh Wallahi zanyi Allah zanyi ko ma abincin kike so zanyi miki, Amma
dan Allah ke wace ce" kaji dan rainin wayo Nice matar ka au! Dama duk abun da kake min
baka san kyale ka ne nake yi ba saboda san da nake yi ma?, To yanzu kuma naga ba wata
soyayya a tsakanin mu kullum sai dai ka dake ni, Hakan nema yasa nima sanka ya fita fit! A
raina yanzu in kaga ka dake ni to kyale ka nayi, Maza tashi kaje kayi min abunda na saka ka".
Cikin hanzari ya tashi ya fita yaje ya dora ruwan sai da yasha wuya tukun wutar ta huru.
Ruwan har yayi zafi ya kusan tafasa Rafy ta fito. "Yauwa uwar gida ruwan ya kusan tafasa ya
fada yana kallanta yana dan murmushi yak'e". Da sauri ta zo wajen sa ta kama hannun sa.
"Mai gida tashi mana miye kake haka, ina ce ni kasa in dafa maka ruwa, Ashanafa kawai naje
daukkowa shine kuma zaka zo ka fara dafa wa. Haba sahibina ai sai kaja min tsinuwar Allah
haba mai gidana koma daki abunka kar sanyi ya illata min kai". Tunda ta fara maganar ya saki
baki Galalah yana kallanta, Tunanuka iri-iri suke ziyartar kwalwar sa. Mike wa kawai yayi ya fara
tafiya ya nufi daki, Ya saka kafa daya cikin dakin kenan yaji ta shako rigar sa ta baya. "Munafuki
ina zaka ka wani nufi daki, Au! Wato ko dukan ne bai ishe ka ba kari kake so?. Maza malam
kaje ka karashe dafa min ruwan zafi na". Umar ji yayi kamar ya fashe da kuka dan bakin ciki,
Abu biyu yake tunani ko dai Aljana ce ko kuwa Aljanar ce ta shiga jikin matar sa. Sai da ya
tafasa ruwan duk tana tsaye kansa tana zafga mishi masifa, yaje ya surka ya kai mata ban daki.
Ta saka shi ya dafa musu tea kafin ta gama wanka. Ba yanda ya iya domin zuwa yanzu yayi
sanyi sosai mugun tsoran ta yake. Bayan ya dora tea din ne ya lura ba sugar sai da ya jira ta
fito ya sanar mata. Tace yaje sayo kamar jira yake dama ai kuwa ya tafi da sauri har ya kusan
zuwa kofar yaji ta ambaci sunansa. "Wallahi in ka wuce minti 15 sai na bika har inda kaje na
babalaka, ba daka tafi da sauri a nufin ka ka gudu ba". Kamar kuwa tasan niyar guduwa yake.
Maganar da tayi kuwa ta tuna mishi jiya hakan yasa jikin sa yayi sanyi. Fita yayi daga gidan
yana tafe a hankali ji yake duk duniyar tayi masa kunci baya jin wani dadi balle farin ciki._



_Abokin sa Muhajeed ya tuna, "Yes". ya ambata direct ya nufi gidan Muhajeed din. Bayan yayi
sallama Muhajeed ya fito nan suka zauna ya kwashe labarin duk abunda yake faruwa a gidan
sa daga jiya zuwa yau ya fada wa Muhajeed. Dariya sosai Muhajeed yayi tukun yace "Kai
amma Wallahi ban taba sanin kai so ko ne ba sai yau, Haba dai nawan karka bada maza mana
Uhmm! Ace mace ta ringa buga ma irin wannan game din haba ai yanzu an wuce wannan
yayin". Dan bata rai Umar yayi yace "Abokina baka fahimta bane irin karfin da naji a jikinta ya
nuna ba ita kadai bace da aljanu a tare da ita". Mtseeeew "Aljanaun banza ni fa ban wani
'yar da da akwai wasu aljanu ba, Malam kawai jamfin mutane ne, Ni da mata ta ce ta tsuro min
da wannan iskancin Wallahi da tuni nayi maganin ta". Umar ya kada kai yace "Shin yanzu
idan na baka dama zaka iya zuwa ka Ladaftar min da ita?". Muhajeed yaji zancen mugunta da
sauri yace, "Kwarai kuwa abokina. idan ban mayar ma ita kamar mata ta ba daga yau mu raba
abotar nan". Umar yace "ok to
shikenan yi sauri tashi muje mintuna 15 dam ta bani". Muhajeed dariya ya tashi tana wa umar

wai ya zama mijin hajiya har tym.ake bashi. A zuciyar sa kuwa tunanin irin bugon da zaiwa
Rafy yake, Yana murmushi mugunta yana kara ganin wawancin abokin nasa._

_______________________

_Wajen karfe 11 tukun mai shagon ya bude. Safuratu a sufar alhaji salim taje ta tambayi irin 'yar
babyn ai kuwa taci sa'a saura daya irin ta Ta kuwa sayo. Fatima na zaune har wani gyangyadi
take daga zaune. Domin kanta sosai ciwo yake. Karar bude gida taji abunda yasa ta bude idan
ta ta zurawa kofar ido kenan dan ganin mai shigowa. Bisa mamaki taga 'yar tsanar ta ce ta
taho. Dungwai-dungwai Hannun ta rike da jakar kayanta. Wani ihun! Jin dadi Fatima tayi hade
da tashi da gudu ta tarye ta tana mata oyoyo. Daukar ta tayi tun dag nan take kwalla kira
"Mama Asiya! Mama Asiya! Babyn ta dawo". Haka take fada har ta karasa falo a iske su mama
Asiya suna kallo. Kan mama Asiya Fatima ta fada tana murna, da karfi mama Asiya ta tura ta
kasa suka yi daya-daya da babyn da dan akwatin. "Ji 'yar iskan yarinya karya ni zakiyi?".
Fatima dan bata rai tayi dan taji zafi daukko babyn tayi tace "Mama Asiya babyna ce ta dawo".
Sai yanzu ma suka lura da babyn "waya kawo miki ita malam din?," Kusan a tare suka yi
tambayar "Aa da kanta fazo". Inji Fatima Asiya tace "Zo Fatima". Tana zuwa kuwa ta zafga mata
mari, "Dan ubanki bana hanaki karya ba?". Kuka Fatima ta fara cikin kuka tace "Wallahi mama
ba karya nake ba". Gashin kan Fatima ta kama taja da karfi kamar zata cira shi. "Dan ubanki
Bana ce karki kara ce min Mama ba?". Hakuri Fatima ta shiga bata bata. Ita kuwa kamar kara
tunzurata take. Lafiyayun marika har biyu mama asiya ta wa Fatima. Hade da yin ball da ita ba
tausayi da ganin karamtar ta. Daukar 'yar babyn da Jakar tayi ta fita waje ta tulla su can saman
kwano. Ta dawo tace "Inga ubanda zai daukko miki". Ran Safuratu ya baci sosai, Bat ta bace ta
dawo falan ba tare da suna ganin ta ba. Muguwar harara kawai take bin Mama Asiya da shi
Allah-Allah take mama Asiya ta bar cikin falon.................................._


‍♂� *YAU WASU ZASU DAKU, MAMA ASIYA, MUJAHEED*

*KAICO FATIMA*



Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy

��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 63-64


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*

*KIN CANCAN Ce SHI. NA BAKI PAGEN DUK DADIN SA. KE KADAI. (ROUKIE BABY)*

��� *LABARI NA*���


✍ *Writing by*
ROOKIE BABY

JINJINAR BAN GIRMA GARE KI RUKKAYA. DAYA KIKE TAMKAR DA DUBU. INA
GWANIN WANI GA TAWA GWANAR BA GWANAR A GUN FADA BA KO ZAGI. JINI NA MIJIN
FAMA. HADARI SA GABANKA INDA KAKE SO.GIWA KIKA BAKI WAI WAYE IN KUN NAUSA.
GWANKI MAI RANGWANGWAN. ZAKI SA MAZA GUDU. KABEWAR KAN KABARI BAKIN
CIKKN MAI TAUSHE. MURUCIN KAN DUTSE. MAHASSADAN KI A YAU SUNE FADAWAN
KI. LA'ILAHA ILLALAHU".�.

_Hakika kinyi rawar gani kin kawo abunda ake so labari ne mai dadi cike da ma'ana labarin
da zai sa matasan mu su hankalta musamman ma mata. Labarin da akayi amfani da salo mai
burgewa wajen jan hankalin mai karatu. Idan na fara karanta page ya kare kamar in daka
wayar da kasa nake ji._ *Godiya muke yi yar uwa Allah ya kara basira zakin hannu. Allah ya
kara hada kawunan mu. All Zamani Writers. Wuta kawai kuke ina biye da ku ina barbada
Fetur*

� Autan ku ne. *King boy*

*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ta dawo tace "Inga ubanda zai daukko miki". Ran Safuratu ya baci sosai, Bat ta bace ta dawo
falan ba tare da suna ganin ta ba. Muguwar harara kawai take bin Mama Asiya da shi
Allah-Allah take mama Asiya ta bar cikin falon.~


_»» *S*u Umar hanya suka biyo sai sauri suke Muhajeed har ya matsu aje gidan dan hannun
shi kaikayi yake, Abun da basu sani ba duk abunda suke yi Aljana Safuratu na gurin tana jinsu.
Mujaheed yayi mugun bata haushi, A ranta tace yanzu fa da Rafy ce da sai y same ta ya Zane
baiwar Allah. Lokacin su Umar suka karasa gidan, dake ba bulala kusa Umar da kanshi ya
dauki wani itace dan dogo ya mikawa Mujaheed. Shi kanshi Mujaheed yaga Girman iccen,
Amma dan mugunta sai bai ce yayi girma ba. Umar ya bashi Izinin shiga. Kamar wani uban ta
haka ya fada dakin. Dake dakin da dan duhu Rafy ta kunna fitila yana shiga ya iske ta a bakin
gado cikin shiga ta bakar doguwar riga. "Munafuka algunguma, Tazo yayi wani mukus kamar
wata salaha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login