Showing 69001 words to 72000 words out of 103342 words

Chapter 24 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf

kingboy   

08 Jul 2025

5054

dakin ya iske Rafy zaune tana
zuba mishi abinci a plat "Babyna zo zauna in baka a baki". Yana murmushi ya karasa wajen ya
zauna. Kallan ta kawai yake yana kara jin santa a ranshi yana tuna rayuwar su ta baya. A baki
ta fara bashi abincin kamar yaro. Tana mishi hiraraki masu dadi. Har ya koshi, Tukun ta janye
abincin gefe. Shiru ta biyo baya Kafin Umar yace "My wife ban tambaye ki mana?". "Ina jinka
Uban 'ya'yana". Umar yace "Dan Allah ina kika samo wannan shinkafar gashi naga miyar harda
nama?". Dan murmushi tayi tace "Hmm mai gida kenan. Da kudina na saya kawai dan in
faranta maka. Domin nayi miss din dukan ka da zagi". A kunya ce ya sunkuyar da kai. (Kamar
wanda yaje kwartanci gidan surikan shi) Rafy tace "Dama ina so in maka wata tambaya in ba
damuwa babyna". "Ba damuwa inajinki" ya fada ba tare da ya dago kai ba. "In zaka tuna
lokacin da mukayi aure Mu masoya ne na azo a gani. Ko kadan bana san abunda zai bata
maka rai. Kullum cikin hidimar ka nake. A kanka har matsala muka samu da iyaye na. Amma
Umar wata biyu baya sai ka mayar da gidan nan kamar gidan kaso a guna. Zuciya ta da take
cike da farin ciki lokaci guda kasa kafa kayi facali da shi. Fuskar ka da ta zame min abar bege
wanda nake kallo ina jin dadi. Sai ka mayar da ita Abar tsoro, abun gudu. Jikina da ya kamata
ya sama kyakyawan kulawa daga gare ka. Amma sai ya zama abun duka. Umar mamaki na
shine lokaci daya canjin yazo. Meyasa?_





_Umar yaja dogon lumfashi yayi kasa da murya yace "Ba wani abu yasa ba sai ganin lokacin
idan na yarda mukaci gaba da zama a haka zaki rainani ki daina jin maganata. Hakan yasa..."
"Karya kake Umar ba wannan bane fada min gaskiya in ba haka ba yanz in wuji-jiga ka a anan

domin Ni ba Rafy dinka ta gaskiya bace". Cikin wata iriyar murya mai tsoratar wa Sufuratu tayi
mishi maganar cikin tsawa. Wani iska kamar doguwar guguwa ya zagaye inda take Sai gani
yayi ta canza hallitta zuwa wata dodanuwa mai ban tsoro. Mugun tsoro ne ya ziyarci Umar
lokaci guda domin har fitsari ya fara kubce masa. Da baya aya fara ja yana Mata magiya yana
cewa "Dan Allah kiyi hakuri Wallahi zan fada miki gaskiya. Zan fada zan fada". Aljanar cikin
murya ba dadi tace "Ka sani cewa in ka yarda kayi min karya na kuma bincika na gano haka
Wallahi sai ka gane kuren ka". Umar ya fara mata magana wanda bata fahimtar ma abunda
yake cewa domin rawar darin da yake saboda tsoro. Tace mishi ya kwantar da hankalin shi ba
abunda zata mishi muddun bai yi mata karya ba. Nan ya fara kora mata bayani._




_"Mukhatar dai babban abokina ne tun kafin in auri Rafy muke tare duk wasu abubuwana shi
yake ban shawara. To bayan auren mu da wata biyu muna zaman lafiya da matata sosai idan
na shigo wasa da dariya irin na masoya abun gwanin sha'awa. To wataran muna hira da
Mukhtar sai nake gaya mishi irin zaman mu ni da matata. Ina gama bashi labarin sai ya bushe
da dariya yace ashe ni banza ne marar wayo. Na tambaye shi dalili yace min ai wasan nan da
muke yi da Rafy shi zai jaho raini a tsakanin mu raini na har abada. Da na musa mishi amma
ya cika ni da zance har dai na yarda yace in gwada Murtuke wa. nuna mata wasa ya kare
amfanin abun da yake gaya min. Ni kuwa na amince a zuciya nace zan gwada in naga abun
baiyi min ba sai in dakata. To washe gari haka na tashi abu kadan idan tayi min sai in kyare ta
idan ta nuna wasa take min nan ma in hantare ta. A ranar dai na canza mata sosai kuma tun a
ranar ta fara jin tsoro na. Hakan yamin dadi nan na koma na fadawa Mukhtar sai yayi dariya
yace Sai ma na ringa hada mata da duka zata na min ladabi kamar babanta. To ni kuwa dake
na yarda da shi sosai dan ya fada min cewa shima haka yake wa matar shi.
Da yaga na nuna rashin amincewa washe gari yaja ni gidan nashi. Nan fa naga idan ya mata
magana har rawar jiki take. Haka duk abunda za'ayi bata ko iya daga kai ta kalle shi dan tsoro.
A gabana ya bata naira Dari yace ta sayo masara da kayan miya da nama tayi musu tuwo da
dare. Ko.gardama batayi ba ta amsa tana godiya kamar wacce ya bawa dubu. Nan na tambaye
shi nace ya dari zata isa a sayo masara nama da kayan miya. Nace ai ko kayan miya kadai
wanda za'a saya sunfi na dari. Yayi dariya yace ai ita zata cika a cikin kudinta. Dake naga tana
sana'a shiyasa ban ko musa ba. Kuma abun ya burge ni Kwadayin hakan yasa nima na hau
hanya. Wannan shine gaskiyar zance._





_Dajin haka Safuratu ta bushe da wata irin mahaukaciyar dariya. Ta dade tanayi tukun ta da
kalle shi cikin dariya tace, "Amma Wallahi ka bani mamaki wannan ai shirme ne da rashin
hankali. Daga baka wannan banzar shawarar dan karta rai naka shikenan sai ka maisheta jaka
kata duka Wai ni kuwa kana santa kuwa?". "Da sauri Umar yace sosai ma ina santa Wallahi".

Safuratu ta watso mishi wata irin harara da idanuwan ta irin na dodannin wanda in ka kalle su
baka shirya ba sai ka sume tsabar tsoro. Da sauri Umar ya kauce kanshi. "Karya kake baka
santa Umar. Domin masoyin gaskiya haka kawai bazai ringa azabtar da masoyiyar sa ba.
Masoyi kullum burin sa shine yaga masoyin sa cikin farin ciki. Shin kai kuma kayi hakan?. Ai ko
kadan ba wanda zai yarda cewa kana san Rafy dan haka ni yanzu zanje in sama iyayen ta in
basu hakuri kai kuma maza rubuta mata takardar saki". Durum! Gaban Umar yayi mummunan
fada ji yayi kamar jiri na debar shi. Bai san ma yana san Rafy har haka ba. Tunanin irin
wulakanci da cin zarafin da yayi mata amma ta jure take zaune da shi haka yayi. Nan ya zube
gaban Safuratu magiya da roko ko wanne kala yazo bakin shi fada yake. Yana hadata da Allah
ta rufa mishi asiri karta rabashi da matar shi. Safuratu tace "wato ma da ita kaci gaba da
jibgarta kana cin zalin ta ko?. To bazai yuyu ba". Kuka Umar ya kama tun karfin shi yana
magiya Ita kanta ta tausaya mishi batayi zatan yana san matar tashi har haka ba. Abunda ta
lura dashi shine duk abunda yayi bayin kansa bane laifin Mukhtar ne._






_Cewa tayi "Umar bazan rabaka da matar kaba amma in kamin alkawarin bazaka sake mata
irin abubuwan da kake mata na wulakanci duka da sauran su a baya". Da sauri Muktar yace ya
amince. Safuratu taci gaba da cewa "Sannan kamin alkawarin zaka rabu da Mukhtar domin
Mukhtar munafuki ne duk abunda yake gaya ma ba gaskiya bane domin kamar mijin hajiya take
tsoran matar shi yake. Duk lokacin da kaje ka iske shi a waje to laifi ya mata ta koro shi wajen".
Umar zugun yayi zuciyar shi sam.bata amince da maganar da Safuratu tayi a kan Mukhtar na
tsoran matar shi ba. Safuratu tayi wata yar guntuwar dariya tace "Nasan bazaka yarda da
zancen da na fada maka ba. Domin ganin yanda matar tashi ke nuna maka idan kuka shiga
gidan nunawa take tsoran Mukhtar. take wanda kuma hakan wani plant ne shi Mukhtar din ya
hada. Duk wannan zabure-zaburen da yake mata da zarar ka fito a gidan sai ya biya ta kudi
dake kasan mayyar kudi ce. Amma abunda nake so dakai yanzu Bari inje in dawo ma da matar
ka gobe zan nuna ma a zahirin waye abokin ka". Kafin Umar ya daga baki Safuratu ta bace nan
ta barshi sai cicira ido yake. Ita kuwa can taje gidan kawun Rafy a sufar Umar ta dakko Rafy.
Da kawun nata yace ta bari sai da safe ta shirya amma taki yarda dake ita kant ta gaji da zaman
gidan duk da ba takura amma tafi san gidan mijin ta. Kuma tun da taga Umar tasan Safuratu ce
kuma tasan akwai wani abun. Tun a hanya Safuratu ta kwashe labarin duk yanda sukayi har
da labarin su sarkin bori ta bawa Rafy. Rafy tayi dariya sosai a zuciyar ta kuwa addu'a take
tana fargaba game da Umar. Tare suka shiga har cikin daki Umar ba karamin tsorata yayi ba
ganin Safuratu da sufar shi sak! Har kayan jikin sa ba banbanci. Da har ya tashi zai ruga ya boyi
Safuratu ta tsayar da shi. Rafy kuwa dariya ma abun ya bata. Domin ita yanzu bata ma tsoran
Safuratu ko kadan dan ta gane ba macuciya bace. Safuratu tace kaga malam ga matar ka nan
na dawo ma da ita ni na tafi sai da safe gobe ka shirya zamuje gidan Mukhtar ka gane wa idan
ka. Da fadar haka ta bace Battt!..............................._

Ganin Safuratu ta bace nima nace bari in gwada bacewar. Batt!! .Lolz

*NA GAIDA SAFURATU. KIN KUSA SAITA NAN GIDAN SAURAN SU MAMA ASIYA*


Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION

Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks

Autan marubuta nee king boy







��

*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*

��

Page 79-80


© *KING BOY ISAH* ✍


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*


� DEDICATED TO ZAMANI WRITERS. JINKU NAKE KAMAR YAN UWA NA NA JINI.
ROKON ALLAH NAKE YA KARA DAUKAKA DA BASIRA. ALLAH YA TSARE MU SHARRIN
MAHASSADA. ALLAH YASA ALBARKA A WANNAN KUNGIYA TAMU.

Yanzu halin wasu bakin hanga.. »Baki na hanga...

Basu ganin wani yanada burga...

»Yanada burga...

Sai su bi daya biyu su zaga..
» biyar su zaga..

Munsan arzikin mune.. Zaya bimu...

Inadai lokacin mune za a jimu...

Kalmomi adansune Tubalin mu...

Harshe zamu tsarkake har ya kaimu....

Kyan lafazinka kwaliyar ka...

Inka biyata sai a dauka...

Sai makiyin ka ma yabika...

Ayita fada dashi a kanka...


Kada harshe ya kai ya barka...
» Yakai ya barka..

Yi tunanin amo ka saka...
»Amo ka saka...

Adabi shi ka gyara littafi
» ya gyara littaf...

Nazarin duniya misali....



*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Domin ita yanzu bata ma tsoran Safuratu ko kadan dan ta gane ba macuciya bace. Safuratu
tace kaga malam ga matar ka nan na dawo ma da ita ni na tafi sai da safe gobe ka shirya
zamuje gidan Mukhtar ka gane wa idan ka. Da fadar haka ta bace Battt!.~

_Washe gari da safe bayan su Umar sunyi wanka ya sayo musu abun kari sun karya ya sun
zauna suna hira sai gani sukayi Wata yar farar Yarinya ta bayyana a gaban su tana kallan su
tana murmushi. Tsorata sukayi dan Umar har zai tashi ya ruga. Yarinyar tace "Nice fa Safuratu

*ALJANAR FATIMA".* sai ta yaji haka tukun ya dawo ya zauna suna wa junan su dariya shi da
Rafy na tsorata da sukayi. Rafy tace "Kai dai Wallahi raggo ne kamar ba namiji ba. Ace mace
ma ta fika rashin tsoro". Umar yayi dariya yace "Ah! Ke kuwa ai da gaskiya ta wa zai tsaya
kallan ruwa kwado ya mai kafa". Hhhhh Rafy tayi dariya tace "Ai duk Safurat ta bani labarin ka
har da kokowa wajen mai shayi nayi dariya sosai. Ga kuma Sarkin bori mai cire Aljanu". Gaba
daya suka kwashe da dariya. Nan dai suka gaisa da Safuratu da take a sufar Yarinya. Tace "To
dan Allah Umar ko kai fa. Yanzu zaman a haka ba yafi dadi ba?. Kuna hirq da matar ka kuna
dariya. Amma da in ka shigo sai ka wani bata fuska kamar wanda aka kai gaban sarki bai karya
ba aka mai bulala dari". Dan murmushi Umar yayi hade da sosai keya yace "In sha Allah
hakan bazai sake faruwa ba. Wancan karon ma sharrin Mukhtar ne". Safuratu tace "Yauwa
haka ake so. Amma fa akwai mazan da suke haka wanda a waje_




_Zakaga suna ta bude baki suna wangale hakora kamar wanda aka wa alkawarin Hajji bana.
Haka in suna hira suta zuba sai kace Anyiwa waziri aku gorin labari. Amma da zarar sun zo
gida shikenan sai kaga sun daure fuska maganar ma sai kaga dakyar suke wa matan kamar
wanda aka makure akace suyi dole. Kai wani fa hirar arziki ma bata hada shi da matar shi,
balle wasa da Dariya. Wani abu kadan da matar shi tayi masa sai hantara in bata ci sa'a ba
harda duka. Kamar dogari a fadar sarki haka suke wa matan da kinyi kuskure kadan. Haba wai
su me yasa basa fahimta ne aure fa ana yinshi ne dan cika Umar nin ma'aiki sannan ba'a ce ka
auri wacce baka so ba. Wai wasu kamar dai kai yanda ka zaunu a shawarar Mukhtar. Wai suna
yin duk hakan ne dan kar matan su raina su. Haba muma matan muna da hankali fa shikenan
dan ina wasa da mijina sai in raina shi a kan me?. Raf'iat ko kina ganin zaki iya raina Umar dan
wasan da kuke yi". Safuratu ta mayar da kallan ta zuwa ga Rafy shima Umar haka. Rafy tace
"Haba-haba ko da wasa Wallahi bazan rainashi ba. Duk abunda kuwa zan mishi cikin wasa ne
irin na masoya domin ni tun a waje lokacin ina budurwa na tsara zamana a gidan miji kamar
yanda ko wacce mace take tsara nata. Tsarina zan Girmamashi zan kuma maida shi abokin
wasa na duk da kuwa nasan cewa shugaba na ne. Amma a nawa tunanin wasa tsakanin
ma'aurata na kara dankon soyayya a tsakani. Amma fa ba mugun wasa ba wasa dai irin na
masoya. Kamar yanda Addini ya Halarta mana._





_Sannan wasan yana taka muhimmiyar rawa ta bangaren Fushi. Wani abun idan nayi mishi
daga naga alamun yayi fushi sai in mayar da abun wasa. Haka wani lokacin ko mun fara cacar
baki mun fara fada sanadin wasa da muka sabayi sai kiga abun ya juye ya koma wasa. To ni dai
gaskiya bana tunanin zan wasan da muke zaisa in raina shi ko da yaushe zan bawa mijina
girmanshi in lokacin wasa ne ayi. In kuwa ba lokacinshi bane a bari". Raf! Raf! Raf! Safuratu
ta fara tabi tana kallan Rafy tana murmushi. Shima Umar tafa mata yake. Safuratu tace

"gaskiya kin burge ni kuma ni banga kuskure a maganar ki ba. Umar bari muje gidan Mukhtar
yau zaka sha mamaki. Karbi wannan abun ka hadiye". Hani farin abu kamar magani ne ta mika
masa ba gardama ya karba ya afa baki. Yana hadiyewa ya bace wa Rafy bata ganin shi. A rude
ta mike "Innalillahi, Ina Umar din". Umar yana zaune agun yana kallanta amma ita bata ganin
shi. Umar da baima san ya bace ba'a ganin shi ba ya kalli Rafy da duk ta rude tana cewa
Safuratu ina yake. "Rafy miye haka gani nan a gaban ki ki ringa cewa wai ina nake". Rafy kam
bata ji maganar shi ba._





_Dariya Safuratu tayi Ta kalli Umar tace "Ai yanzu ba wanda zai ganka kuma ba wanda zaiji
maganar ka daga Allah sai ni. Yanzu haka ka bace Rafy bata ganin ka. Maganar da kayi yanzu
ma bata ji ba". Mamaki ne ya kama Umar. Safuratu tace wa Rafy "Ke ma kwantar da hankalin ki
ga Umar dinki nan ba sace shi nayi ba. Yanzu zamu tafi gidan Mukhtar ne da shi to har ciki
zamu shiga dan haka bazasu gan mu ba. Mun tafi sai mun dawo". Da fadar haka sai suka bace
ita da Umar din sai gasu sun bayyana a gidan Mukhtar. Da bullowar su suka ji Murja a daki sai
masifa take surfawa Umar hakan yasa Rafy tace su karasa cikin daki. Umar kam duk a tsorace
yake dan gani yake kamar Mukhtar zai ganshi. Sai da suka suka shiga dakin ya tabbatar da
cewa ba'a ganin shi Nan sukayi tsatsaye suna kallan su Mukhtar din. Mukhtar ne zaune gefan
gado Murja matar shi a gefan shi ta rike kugu cikin daga murya da kakatu tace "Kai malam tun
dazun magana nake maka amma kayi shiru kamar ina magana da dutse. Kasan dai cewa gidan
nan ko kwayar hatsi bama da shi balle kace ayi dan banzan kokon nan da ka saba cewa ayi a
karya da shi._





_Dan Wallahi yau bazan karya da koko ba. Duk kayana na saide-saide mun cinye su baka bani
kudina ba. Gashi yanzu ina so inje kasuwa inyo sari amma ba kudi a hannuna duk suna gunka.
Dan haka tattaro min gaba daya kudina rankatakaf! Ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login