Showing 18001 words to 21000 words out of 103342 words
Chapter 7 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
taba. Tana taba yarinyar tajuyi hade da wani mugun razananen kara da ya
daki kunnan ta suman tsaye Asiya tayi a gurin..............,......```
TOFA MUJE ZUWA READERS. YANZU ZAMUGA GWANAYEN TSORO. AN FARA KENAN
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 21-22
NA. KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
IN DEDICATED TO ALL ZAMANI WRITERS. *ALLAH SARKI YAN UWANA UBAN GIJI ALLAH
YA ALBARKACI RAYUWAR MU. A KULLUM GURINA INGA ZAMANI BA'A BARMU A BAYA
BA. ALHMDULILAH KULLUM CIGABA MUKE. ALLAH YA KARA BASIRA, YAN UWANA
DOMIN NI KAMAR YAYYAI NA NA DAUKE KU. AUTAN KU NE KING NA AUTAR KU QUEEN.
ALLAH YA BARMU TARE YA KARA HADIN KAI. AMIN* ♥
.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
_Tana taba yarinyar tajuyi hade da wani mugun razananen kara da ya daki kunnan ta suman
tsaye Asiya tayi a gurin._
»» Aljanar a sufar shamsiya take, jikar Mama asiya hannaye biyu tasa da karfi ta shake wuyan
dogayen faracen hannunta masu shegen kaifi. Bakin shamsiya wani bakin abune mai kaure ya
fara zuba. Kuma idan ya zubo din a kan mama asiya yake sauka. Mama asiya in banda ihu da
neman ceto babu abunda take. Da dai taga ba ko alamun mutane a gida wanda zasu kawo
akaji.
Nan ta fara ihu tana kokarin kankare hannun Aljanar da ta makure mata wuya. Aljanar ce ta
bude idonu hade da dakawa Mama Asiya tsawa. Ai kuwa fitsari ya fara zubowa harda dan
guntun kashi da ya zubo. Fitsarin matseshi take amma zuba yake tsirrr! Duk jikin ta karkarwa
yake. Magana na rawa "Haba shamsiya dan allah ki sake ni karki kashe ni me nayi miki ne?,
nice fa mahaifiyar babanki". Mama asiya ce ke fadar haka. "Keeeee! Anji ke kika haifi
mahaifina to ke kika haife ni ne ni?, Shin a yanzu ni dake waye baba ma?". Muryar mai kamar
amsa kuwa aljanar ke magana da shi domin in tana yi dakin har wani jijiga yake yi. "Wallahi
kece, kwarai kece baba. Kece uwata ma. Kece ubana, kece yayana, kece yaya ta kece.....".
"Keee yimin shiru". Gum Mama asiya tayi ta tsaya da lissafin kafafunta sai rawar karkarwa take
fitsari kuwa duk sanda aljanar tayi mata tsawa sai ya subuce ya kwararo.
"Hahahhahahjahahhaha!
Aljanar ce ta dake kai sama tana wannan muguwar dariyar. Mama asiya ta dan shammace ta ta
ware iya karfin da hannuwa biyu ta tura ta. Can aljanar ta fadi gefe. Tubur-tubur abu ga mai jiki
ba gudun kirki, ta nufi hanyar Hawa sama, gaba daya wutar dakin ce ta dauke duf! Mama asiya
bata daina gudu ba saida ta hadu da bango kanta ta buda ji kake gum!! Ta kuma zube kasa
kamar an yarda buhun gero thom! Kanta ta dafe tana wash! Wash! Aljanar ta gani tazo dai-dai
saitin kanta da wata wuka wulshe-shiya a hannunta. "Hahaha- wato ni zaki tserewa ko?.
Wukuncin ki kisa ne". Da fadar haka ta daga takobin sama ta caka ma mama asiya a ciki.
Wani Mugun kara ta Saki ta tashi zaune tana nishi daya-daya tana laluba cikin ta jin ko da
gaske ne abunda ya faru. Karar da tayi ya tashi alhaji zumbur! Ya fara tambaya "lafiya-lafiya"?
Sai yanzu mama asiya ta fahimci cewa mafarki ne take ganin cikinta lafiya lau kuma haka kanta
bata jin wani radadi. Alhaji ni kam wallahi bazan yarda ba ashe yarinyar nan mayya ce da wuka
fa tazo zata kashe ni a mafarki, wallahi sai na dauki mataki a kanta, to ni kuwa me na tsare
mata ne take nema ta cinye kurwata danya". Duk surutun da take alhaji binta yake da tambaya.
"Wacece?, wai wace yarinyar". Budar bakin ta tace "Wace yarinya kuwa in ba wannan
mayar...". Ta dan dakata tana tunani in fa tace shamsiya abun bazaiyi tsari ba. "Wace"?.
"Wannan mayar 'yar taka ce Fatima, duk taimaka mata da nake a rayuwa wai ashe mayya ce ni
tazo zata kashe". Tsawa ya daka mata nan da nan ya murtuke fuska, "Asiya bana san iskanci
fa, bana san tambadar nan taki, kinje can kin tabo aljanunki sun motso shine zaki likawa
marainiya wato. To wallahi kar in sake ji". Gungune kawai tayi, Alhaji kuwa ya kwanta ya juya
baya abunsa. Mama asiya na zaune kamar ance ta kalli wajen mirror. Ihu! Ta kwalla ta
rukun-kume alhaji kamar wacce zata shige jikinsa. Yarinyar ta gani a cikin mirror tana kiranta.
Alhaji yana jinta ya kyale ta, can kuma saj yaji lema a jikinsa wanda yasan wannan ya wuce na
gumi.
Tashi yayi yana "Asiya wai miye a jikinki nake ji sharaf!". Har tashin da yayi a rike take gam da
shi idanunta a rufe. Wata mahaukaciyar dariya alhaji ya kwashe da ita, Irin wacce ya jima baiyi
ba harda kama ciki. Asiya ido a rufe taki budewa tunani take in ta bude zata sake ganin aljanar,
Jin dariyar alhajin taki ci taki karewa, yasata bude ido a hankali bata ko kalli wajen mirror ba.
"Alhaji ai dole kamin dariya wannan mayar 'yar taka so take sai ta kashe ni ta huta". "Asiya
kalli jikinki fitsari ne fa kika sharara duk kin bata gadon, Hahaha wai duk tsoran ne haka harda
fitsarin wando?".
Sai lokacin Asiya ta lura da jikinta sharkaf take ta jika kayan barci da fitsari. A kunyace ta tashi
da sauri ta nufi bandakin da ke cikin dakin domin tayi wanka. Bayan ta shiga ta juya baya tana
kokarin Cire riga sai ji tayi wata kalar muryar 'Yan yara tace "Yauwa Shannunki da Juwa". Da
gudu ta fito daga bayan dakin taje ta fada kan alhaji ta shishige mishi. Alhaji na niyar tashi yaje
ya canza kaya domin ta jika shi amma sam ta hana ta rufe idanu ko budewa batayi. A haka
suka kwanta har safe. Tun da safe taje dakin su fatima ta iske ta ta idar da sallah tana barci,
nan fa ta hau tikar ta wai tashin ta take a barci, kai da ka gani kasan mugunta ne
abun................
Ku danyi hakuri da wannan yaseen yau bana jin type din.
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 23-24
NA. KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
*DEDICATED TO YOU*
QUEEN HAUCY = *ILLAR BASHI*
BEAUTY QUEEN = *BADDEEYERH*
UMMU AFNANN = *FATIMAH*
ZUWAIRA MADADA = *MATA DA MIJI*
MARYAM 'YAR MAMA = *RAINAN KAUYE*
BEIBOH = *YASMEEN*
_DA KYAU JARUMAI NA ALLAH YA KARA BASIRA_
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~nan fa ta hau tikar ta wai tashin ta take a barci, kai da ka gani kasan mugunta ne abun.~
Fatima tace tayi sallah amma mama asiya bata barta ba saida tasakata kuka, "Shegiya mayya
wato shine jiya kika zo zaki cinye ni ko. Harda wani canza suffofi ko kin dauka bazan gano kece
ba". Faddausi ce ta farka jin kukan Fatima, "Mama asiya wallahi tayi sallah ita ta tayar dani ma".
Mama asiya tace to uwar iyayi ni ai ba bugwan sallah nake mata ba, wannan yarinyar da kike
gani mayyace ban taba sani ba sai jiya nima. A mafarki tazo min tana faman cinye ni, badan
Allah yasa kurwata jaruma bace". Fiddausi dai jinta kawai take yi tana mata kallan muguwa
azzaluma domin tasan duk maganganun Mama asiya ba gaskiya a ciki. Mama asiya ce ta
dankwashi kan Fatima hade da cewa "Yi mana shiru munahika mayya kawai, ai yau sai kinci
ubanki a gidan nan bara alhaji ya fita. Kuma yanzu ma ki biyo ni kitchen kina jina?". "Eh gani
nan zuwa'. Buzu-buzu mama asiya ta juya ta fita bata jima ba Fatima ta bita baya, Fiddausi
tabi bayan Fatima da kallo tace, "Kaico 'yar yarinyar da baki wuce a goya ba amma tun yanzu
kin fara shiga kitchen, Allah dai ya kawo miki mafita". "Ameen". Fiddausi taji ance maganar ta
fito daga saitin dan karamin gadan fatima ne, ganin ba kowa a gun tsoro ya kamata da sauri
taja blanket ta rufe tayi luff!. Kamar kullum yau ma fatima tasha wuya a kitchen bayan irin
Aikace-aikacen da tayi ga kuma Mama asiya daga anjima sai ta rankwashi kanta tace "Mayya
kawai allah yasa dai karki cinye mana 'ya'ya dan wallahi yarona daya in ya kamu da koda ciwan
kaine ke zan bincika".
Dake Mama asiya tabawa sauran kishiyoyin nata labari suma sai suka hau tsangwamar Fatima
da dukanta hade da bata aiki mai wahala, Wai suma kashedi suke mata karta kama musu nasu
yaran. Ita dai Fatima ba abunda take sai kuka sai in sunyi maganar karta kama musu yara tace
"Toh" al halin ita bata ma san miye wata maita ba. Sanda fatima tasha wuya sosai ta kuma yi
kuka ba adadi kafin a gama hada breakfast din. Bayan sun sako ta taje ta rungume 'yar
tsanarta tana kuka. "baby na kiyi hakuri na barki ke kadai. Wadan can mugayen ne suka ta
zalunta na". Yar baby ce ta kama kuka nan Fatima tasa ta a kafada tana jijiga ta tana bata
hakuri. "Momy bayi inje in yama miki". Wata siririyar murya ce ta fito daga 'yar tsanar. Fatima
bata ji tsoran komai ba. "A'a baby na kinga su manya ne ki kyale su. Allah zai saka mana, naji
malamin islamiyar mu yace, duk wanda aka zalunta allah zai saka masa". Yar babyn ce tace
"To na fasa zuwa". Yauwa yarinyata muje in miki brush da wanka tukun inzo in miki kwaliya
mai kyau". Tana gama fadin haka ta warci 'Yar babyn da hannu daya ta je ban daki. (Wai aka
ce 'Kuruci dangin hauka) bayan fatima ta ajiye ta tace. "Haaa, bakinki", nan take bakin 'yar
robber ya bude. Hakora ne reras! A jere fatima dake yarinya ce ba ruwanta batayi tunanin wani
abuba. Ta sa brush ta fara gurzar bakin. Tana farawa bakin ya fara jini. Fatima na ganin jini ta
daka da gurzar bakin ta zuba ruwa ta wanke mata tukun tace, "Gaskiya mai shagon da muka
sayo ki baya da mutun ci kuma kazami ne duba fa yanda ya bar miki hakori suka lalace baya
miki brush". Aljanar ce tace "Ko sau daya bai taba min ba". Nan dai fatima taci gaba da mata
wanka suna hira.
Kyauran ban dakin aka turo da karfi, Ameera ce ta shigo. "wai ke Fatima dan ubanki bana
hanaki magana a bandaki ba?. Ko baki san ba kyau ba?". "Yi hakuri aunty wanka nakewa
Baby na". "Kutumelesi kaji 'yar banzar yarinya wato barnar ruwa zaki tarkarwa mutane ko, To
daga yau sai yau kar in kara ganin kinwa wannan 'yar tsanar wanka kuma ma kawo ta nan,
yanzun nan zan kona shegiya kowa ma ya huta, Kawo ta nace magana fa nake miki". Fatima
kuka ta kamayi tana boye 'Yar babyn a bayanta tana fadin "Dan allah aunty ki bar min abuna ina
santa wallahi". Tsawa ameera ta daka mata wacce tasa saida ta firgita matsowa tayi kamar
zata mika mata kuma sai ta sulale da gudu ta ruga waje ai kuwa amira ta bita suka hau tsere.
Ameera ta kusan kamata kenan. Fatima tayi wata zilliya ta Bi ta karkashin ameerar ta wuce, sai
ji kake ameera Tum! Ameera tasha kasa. (SHI YASA BA'A SO BABBA YABI YARO, BA KYAU
DAN IN BA'A CI SA'A BA SAI KA FADI. AKWAI WANI UBA DA YABI DANSA DA GUDU. A LAYI
CIKIN JAMA'A YARAN YA KADA SA. YARO DA KAZA DUK KUSAN DAYA NE. WAYO AKE
MASA AYI CHARAF A KAMA. IN MA KABI DA GUDU TO KARKA YI GUDU MAI NISa.) Fatima
Direct dakin abbanta taje tana kuka yana ganinta ya bar abunda yake ya kamo hannunta.
"Mamana zo nan waya taba min ke tun da sanyin safiyar nan?
Cikin kuka Fatima tace "Dady wai aunty ameera ce zata toya min Babyna wai kuma tace kar in
kara mata wanka, yanzu ma da gudu ta biyo ni". Ran alhaji ne ya bace. Ya kama hannun
Fatima yace muje gunta. A falo suka isketa tana wash-wash.
Alhaji bai bi ta kan wash! Din da take ba ya bal-bale ta da fada hade da mata kashe karta kara
shiga sabgar Fatima. Su Asmart ba rabuwar arziki sukayi da Mama sakina ba. Bayan tusar da
suka ta banka mata da dare a daki kamar bodarai. Da asuba asmart ta tashi wai tea zata hada.
Madarar da suka zuba su biyu ta wuce ka'ida domin saida shayin yayi kauri kamar wani koko.
Sakina na ganin haka basu gama sha ba ma ta kora su gida. Da wuri suka je gidan lokacin ba'a
kai ga cin abinci ba. Tare da su aka ci sunci Sa'a ba wanda ya gayawa alhaji basu kwana a
gida ba. Bayan anci abinci an watse alhaji yayi musu salama ya tafi office. Nan fa mama asiya
ta kira Fatima suka mata dan banzan duka ita da sauran matan wai kashe ne karta cinye musu
yara Mama asiya kuma na cewa karta sake biyota mafarki. Waje suka korata can Fatima ta
koma bayan dakuna ta zaunar da 'Yar tsanar ta facing dinta tana kuka. Yar babyn itama kukan
ta fara. Abun ya bawa Fatima dariya itama kuma sai babyn tabar kuka ta fara dariya. Nan dai
sukata wasanni.
Su Nasmat da asmart makaranta suka taho basu ma ko tsaya jiran su Fiddausi ba da sauran
yara kamar da gaske suka yo sakko, alhalin kowa yasan ba karatun ba suke. A hanya Nasmat
ke cewa asmart
"Ni fa wallahi yau mugunta nake ji, Dan haka yau kan mai Tsautsayi". Dariya Asmart tayi
tace 'yar iskar karya kawai". Nasmat ta bata rai, "Ke ce dai 'yar iskar karya. Amma ni yau
muguntar ce kawai a kai na". "Yauwa yanzu zamu kure mai cika baki". Inji asmart "Ga wani
makaho can yana faman tsallaka rami jeki tunkuda shi in da gaske muguntar kike ji". Jakar
kur'anin ta tabawa asmart Riko ta nufi dan tshon da aniyar tunkuda shi rami...............
Ni kuwa nace Allah yasa aljani ne
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan writers nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 25-26
NA. ✍KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
_*IN DEDICATED TO 'YAN BOKO HARAM WA SOYAYYA TA.*_
*SHUGABAR TADA BOMB* FATIMA. (DAUGHTER)
*MAI BADA UMARNIN KAI HARIN* Hadiza hadi (Niger)
*'YAR KUNAR BAK'IN WAKE*
Zuwaira (madara)
_Kunci nasara kai harin da kukayi babban birni zuciya ta, inda kuka kashe mutum uku Biyu
kuma na nan suna zubar da jini. Shi yasa ma gaba dayan yau banda sukuni. Kuma yaseen
wuta Bal-Bal_
QUEEN HAUSY
I love you too much.
You kill me with you love
*KARSHEN PAGEN BAYA*
_Jakar kur'anin ta tabawa asmart Riko ta nufi dan tshon da aniyar tunkuda shi rami._
»»Irin tsofafin almajiran nan ne, yana yunkurin tsallaka wani rami ya kasa. Nasmat na zuwa
kamar wacce zata taimaka mishi dan har magana sai da tayi mishi. Sai da ta duba ko ina taga
ba mai kallan ta kawai ta ingiza shi cikin ramin, suka ruga a guje ita da asmart suna waigen sa
suna mishi dariya. "Wannan wane irin yara ne da mugun hali haka, yanzu ina fama da kai na ki
zo ki hankada ni rami salon in Karashe naka shewa ko, Jeki Allah ya isa. Allah zai hada ki da
gaman ki kema". Basu ce mishi komai ba gaba suka kara suna ta jan fada har suka isa
makaranta. Malamin na ganin su ya murtuke ya bata fuska, "Kai ku zo nan dan ubanku, yau sai
kun gaya min ubanwa ya daure muku gindi, yanzu karfe Goma zaku shigo aji". Gaba dayan su
gunguni sukayi, kamar ba su ya kira ba suka nufi bench suka zazauna. Kowa ta fiddo al'qura'ani
kamar da gaske karatun zasuyi.