Showing 39001 words to 42000 words out of 103342 words
Chapter 14 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
sai kowa
yayi duk sai suka ji dadi sai yanzu suka 'yarda da Ameerar ta gaskiya ce. Nan fa aka fara tafka
mahawara wasu na fadin a koma gida wasu na cewa Wallahi ba abunda zai mayar da su. Har
yanzu mai gadi Bai fito ba daga inda yake a Labe domin shi gaba daya kunya ma yake ji.
Kamar daga sama suka jiyo maganar alhaji. "Innallilahi Wa'inna illaihir raja'un, Mai zan gani
haka". Alhaji ne ya fadi haka lokacin da yake kokarin fitowa daga mota. "Me ya faru Asiya nake
ganin ko a Waje Cikin ku ba ko mai gyale?". Mama asiya da take a tsugunne dan tsabar gajiya
da tayi ta Dago. "Yo alhaji tunda m ma baka ganmu ba zannuwa ba Ai sai ka gode wa Allah.
Aljana ce fa Ta koro mu daga gida". Alhaji ya bata rai yace "Bana san zancen banza Aljana ko
dai tsoran ku. Oya kowa ya shiga mota". Yana fadar haka ya juya ya shiga gidan driver ba
yanda suka iya domin sun san halin Alhaji dole suka hakura suka shishiga. Sai da suka isa kof
Alhaji yata oda a nufinsa mai gadi ya zo ya bude. Sai ma lokacin suka tuno da mai gadi.
Fiddausi tace "Baba ai harda mai gadin muka gudu tare ma muka buya da shi". Tsaki alhaji yaja
kawai ya fito ya bude Gate din da kansa suka shiga. A falo suka tarar da Fatima tana kallon Tv
tana wasa da Babyn ta ba abunda ya dame ta._
_Su mama Asiya jaraba suka bita da shi wai wata kil ma itace aljanar. Alhaji na shigowa duk
sukayi tsi! "Gobe zanyi tafiya wajen wani aiki kuma zanyi kwana biyu can, Yanzu ma
shirye-shirye na taho in fara domin Tashin asuba zamuyi. Idan da mai matsala zata iya biyo ni ta
fada". Yana fadar haka ya kama hannun Fatima yaja ta suka nufi sama. Suna tafiya Mama
Asiya tace "Wai baku lura da wani abu kuwa". Gaba daya suka tambaya "Kamar me kenan?".
"Wannan yarinyar ni fa ban yarda da ita ba. Dama ban fada muku mayya bace ai inaga itace ta
zama Ameera dan ta tsorata mu domin gaba dayan mu mun tsora ta mun gudu amma ita kungo
a kanta". Wasu basu yarda ba amma dan mugun ta kawai sai suka amince da hakan. "Mama
asiya tace amma ku barni da ita ai gobe alhaji zai tafi zata ci uban......................._
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 49-50
NA. ✍KING BOY ISAH
✍ *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍
DEDICATED TO YOU BLOOD ME
*TRIPLE QUNEENS*
*QUEEN HAUWA HAUSY*
*BEAUTY QUEEN*
*QUEEN MARYAM 'YAR MAMAR MU*
☺ _→ABUNDA YAKE DAINA, ZANA FITAR NA HUCE TAKAI'CI, SOYAYYAR KU A RAI NA
ZANA FADA BAZAN BOYE BA←JINKU NAKE A CAN KARKASHIN ZUCIYAN. INA SANKU
SOSAI IRIN TOTALLY DIN NAN_
'YAN UKUN ZAMANI KENAN
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Wasu basu yarda ba amma dan mugun ta kawai sai suka amince da hakan. "Mama asiya tace
amma ku barni da ita ai gobe alhaji zai tafi zata ci ubanta…~
_»»Washe gari tun da asuba Alhaji yayi musu bankwana bayan ya bar musu duk abunda zasu
buka ta kafin dawowarsa. Mama Asiya kule take da Fatima hakan yasa tun da Asuba taje ta
taso ta ta zo ta fara saka ta Aikace-Aikace. Wai sai tayi mopping din gaba daya falo. Har wajen
karfe 7 Fatima na fama amma bata gama Ba, lokacin Duk matan gidan sun fito domin yin
girki. Juwaira da hauwa ne suka taho a jere. Lokacin Fatima na faman goge TV din da ke
makale jikin bango sai dadage take yi domin tsawanta bai karasa wa. Zuwaira ce ta lalabo ta
bayanta ta yi mata wani mugun Dundu kamar wacce ta sama sa'arta. Fatima kuka ta kwalla da
karfi. Da fara kukanta hauwa ta Wanka mata mari "Ke rufe mana baki dan uwarki ko in kara miki
yanzun nan". Fatima ba dan taso ta matse bakin ta da hannu kukan na dan fitowa a hankali.
"Shegiya kinibabba uwar iyayi, Yau shine zaki tarki wani goge-goge Na karya wato kinga alhaji
baya nan dan kinsan yau dakuwa zaki yi a gidan nan shiyasa kika fara aiki tun yanzu ko?". Inji
hauwa, Zuwaira tace "Dubi ma duk kin bata wa mutane waje da jurwayi Baki iya komai ba 'yar
iska kawai". Kama kunnan Fatima tayi ta murda. "Fada min Uwarwa ta saka ki mopping kika
bata mana Falo...". Maganar Mama Asiya suka ji wacce ta taso yanzu daga barci. "Ni na saka
ta domin Yau bata da hutu a gidan nan". Gaba daya suka juya a tare "Au! Aunty babba ke kika
saka ta ashe. Af! To ba laifi ai". Lokacin Mama Asiya ta karaso gurun tana murmushi mugun ta
tana kare wa Falon kallo. A zuciya tana cewa "Lalai yarinya kin aikatu". A fili kuwa wata
muguwar harara ta daka wa Fatima. "Muna fuka kin wani tsare ni da idanu kamar mayya kina
wani kukan karya, Maza wuce kitchen". Ta Make ta a kai da hannu. Fatima tana kuka Ta shiga
gaba suka bita baya su ukun sai zagin ta suke. Da aka shiga kitchen Fatima ta aikatu sosai.
Domin wani abun ma yafi karfin ta kawai saka ta suke. Su ukun ma sun wa aikin yawa amma
dan mugunta suka ki barin Fatima ta tafi ta huta. Yau dan wake suke yi da Tea ba'a dauki lokaci
ba aka karasa. Zuwaira ce tace wa Fatima ta Tsiyayo man gyada a galan. Duk da tasan Fatima
da kyar take iya karka ta galan din. Fatima ba gardama ta dauki mazubi taje ta fara Kokarin
bulbulowa. Wani mai ne dan kadan ya Zuba a kasan mama Asiya na juyowa ta gani. Sai ta hau
Fatima da duka da kuma masifa haka suma sauran._
_Fatima ta sha wuya gashi sun bige ta sun kuma wanata kuka. Hauwa ce tace, "Munafuka
wato kin zubar wa da mutane mai salon yayi saurin kare wa ubanki yazo ya kama mana jaraba
yace Ban nata sa muke yi ko. To Wallahi bari kiji Duk yau bake ba abinci a gidan nan". Mama
Asiya tace "yauwa kinyi min dai-dai Abunda nake shirin yi kenan. Dan ubanki tunda watan
azumi ya kusan kamawa ai dole ki fara koyan azumi. Dama azumi ba sahur yafi lada". Da fadar
haka suka bushe da dariyar mugun ta harda tafa hannuwa. Fatima kuwa kuka ta saka domin
tasan halin su in suka tashi mugun tarsu har fiye da haka yi mata suke. Aljana Safuratu dake
tsaye Tana kallan su duk abunda suke. Itama dariya tayi Tace "Tunda kuka yanke wannan
hukuncin. Nima na yanke irinsa a kanku. Ni da ku muga wanda zai cika, Ni nace kune bazaku ci
abinci ba sai gobe". Da fada Haka ta sake fashewa da dariya. Duk abunda take kuwa babu mai
jinta kuma babu mai ganinta. Mama asiya ce ta Juye dan waken a wata katuwar kulu wanda
tasan Fatima baza ta iya dauka ba. Amma tace dole sai ta dauka Ta kai dinner room, Fatima
ba gardama taje aka dora mata a kai tana kuka. Tun a nan ta fara Kokarin faduwa. Badan
Mama asiya tayi sauri rike wa ba da duk ya zube. Ai kuwa zagi suka bita da shi gaba dayan su.
"Tsinanna so tayi ta zubar kowa ya rasa, To Allah baiyi ba". Zuwaira ce ke fadar haka. Oya karbi
wannan saura kuma suma ki zubar, Wallahi da sai na daure ki a gidan nan na zane ki. Na kuma
sa kowa na gidan nan ya miki bulala Goma-Goma". Mama asiya ta fadi haka lokacin da ta
Dorawa Fatima wasu uwayen farantai da Cokula ta kai Dinning. Fatima da kyar ta kai su domin
sun mata Nauyi Haka ta dawo ta kuma jidar wasu kayan abincin. Sai da aka shirya komai tsabb!
Dan wake kusan cike da wani katuwan kula. Ga kuma tea da bread._
_Mama Asiya ce tace wa Fatima taje ta sako kayan islamiyar ta tazo ta tafi makaranta. To
kawai ta fada ta nufi dakin su tana shashekar kuka. Gaba dayan 'yan dakin barci suke sai
Asmart da Nasmat Da suke zaune suna tsara wani abun suna dariya da gani kasan ba abun
Arziki suke kitsawa ba. Suna ganin Fatima ta shigo suka taso daga inda suke da sauri suka
nufe ta ganin tana shirin kuka kuma fuskarta da gani ta sha uban kuka.Nasmat cike da iyayi ta
kama Fatima ta dora ta kan gado ta fara share mata hawaye, Tana fadin, "'yar kanwata waya
taba muna ke ne kika taho kina kuka?". Tana shashekar kuka tace "Ba su mama asiya bane
suka ta saka ni aiki kuma suka ce baza su bani abincin kari ba, Wai sai dai in tafi makaranta a
haka". Asmart cike da tausayawa Tace "Ayya 'yar kanwata yi hakuri bar kuka taso muje in miki
wanka Kuma in zaki tafi makarantar ma sai in baki Naira Hamsin ki karya". Cike da zumudi
Fatima ta Amsa "Toh Aunty Na na gode". Tashi tayi Asmart tayo mata wanka nan suka zi su
biyun suke yi mata kwalliya. Ko Fatima kanta da take yarinya abun ya bata mamaki, Sai dai
hankalin ta bai ka ta gano akwai wani abu a kasa ba. Asmart ce tace "Fatima daga yau mun
daina dukan ki. Kuma mun daina Zagin ki kinji?". Cike da farin ciki Fatima ta Rungumi Asmart
"Na gode aunty amma har 'yar baby nama kun dai na Dokanta ko?". Kamar hadin baki da sauri
suka ce "Eh daga yau baza mu kara ko taba ta ba". Suna fadar haka suka kalli juna dariya ce ta
kusan Kubuce musu jin Sunyi magana a tare. Nasmat ce ta datse dariyar ta kalli Fatima tace,
"Wai in tambaye ki, 'yar babyn ki ta iya Karatu?". 'Yar dariya Fatima tayi tace "Sai dai magana
ko in dauko ta kiji?". Da sauri Nasamt tace aa ba sai kin dauko ta ba, Abunda nake so dai shine
yau mu tafi da ita Islamiyya dan ta koyi karatu, Ai kina so kiji tana yi ko?". Eh fatima tace.
"Yauwa yau da ita zamuje Islamiyya ta koyi karatu Daukko ta in goya miki". Cewar Asmart. Da
sauri Fatima ta dauko kayanta na islamiyya ta saka. Tukun ta daukko 'yar babyn A tsorace
suka goya mata ita._
_Suka saka mata hijab dake hijab din doguwa ce Ta rufe 'yar tsanar ba'a ko ganinta. "Karba
kudin, Kije wajen mai.shayin can kice ya baki tea Da bread kinji?. In kinci sai ki tsaya a gun ki
jira mu yanzu zamu shirya mu fito kinji?". Fatima tace to ta Nufi hanya ta fita. Da fitar ta su biyun
suka fara gagaba dariya. Harda rike ciki Dariyar ce ma ta tashi sauran 'yan uwansu da suke
barci. Asmaet ce ta dan tsakaita da dariyar ta kalli Nasmat tace "Kai sister amma kwanyar ki
naja ba lalai ba malam ya tsallake wannan target din gaskiya kin iya mugunta". Nasmat tace
"Kyale dan iska Nasan yanda ya tsani Diyar roba. Ko 'yar karama ce. Balle wannan katotuwar.
Nasan sai yayi boll da ita in ma bai ce zai toyata ba. Kinga kuwa ita Aljanar ba kyale sa zata yi
ba. Wata kil tun a gaban mu ta fara cin ubansa". Wafa dariyar suka dora da ita. Hauwa ce ta
shigo tayi musu magana tace su fito su ake jira ayi breakfast. To suka ce tukun suka tayar da
sauran. Suka je suka yo brush. A falo aka baje kowa yayi Ready Mama Asiya kawai ake jira ta
fito. Ba'a jima ba sai gata ta fito. Bayan ta zaun. Kamar yanda aka saba hauwa ce ta tashi da
niyar Zuzubawa kowa, Budewar da zatayi taga kular da ke cike da dan waken a wanke ko
alamar lema ma babu balle..............._
Domin samun farkon labarin shiga pagen mu kayi like.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
Shiga nan ka/ki yi like kai tsaye a page mu domin samun farkon lbrn
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee king boy
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 51-52
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
*DEDICATED TO YOU MAH BLOOD NASMAT ('YAR MUTAN ARKILLAH, AUNTY AMA. KU
KAM NA DABAN NE A GARE NI*
*SO AKAN CE HADI NA RABBAH, ZUCIYA KU TAKE YABAWA. NASMAT HAR DA AUNTY
AMA, IN BABU KU SAI DAI A DAKAH GUMBA* *BAYYANAR SO GA WANDA KAKE SO,
YA FI RIBA NI KU NA ZABA*
☺ _KOMAI DADI AI BAYYI ZAMA DA MASOYA BAH. SO YAY MIN RANA DAMA DA
BAZARKU NAKE TA RAWA KUMA INA._ ☺
_INAI MAKU FATAN ALKHAIRI. DUK ZAMANI WRITERS KU FITO_ ♂
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~A falo aka baje kowa yayi Ready Mama Asiya kawai ake jira ta fito. Ba'a jima ba sai gata ta
fito. Bayan ta zaun. Kamar yanda aka saba hauwa ce ta tashi da niyar Zuzubawa kowa,
Budewar da zatayi taga kular da ke cike da dan waken a wanke ko alamar lema ma babu
balle.~
_»Kular kamas da ita ko alamar dan wake babu, Domin a bushe ma take, Sakin baki hauwa
tayi tana kallan Su Mama asiya, Ganin kallon yayi yawa asiya tace "Ya dai hauwa lafiya kuwa,
Ki zuba mana dan wake mana kowa fa ke yake jira". Karkato mata kullar tayi suka ga kular
wayam, "Kutu.... Me zan gani haka?, To ina dan waken da yake kusan cike da Kula". Asiya ta
karbi kular har shinshinawa tayi taji ko alamun dan wake ma babu. "Kutt! To alquran Wannan ba
kular da muka zuba dan wake ce ba. Haba kuji fa ko kamshin dan wake babu a ciki". "Tashin
hankali gobarar gemu, To waye zaiyi mana wannan aika-aika ina Fatima?". Zuwaira ke
maganar tana kallan su Nasmat da suma sunyi tsuru-tsuru sai kallan iyayen nasu suke. "Fatima
ai tun dazun ta tafi makaranta tace mana kunce yau baza ku bata abinci ba". Dajin haka gaba
daya hankalin Fiddausi ya tashi Ta bata rai "Haba mama yanzu kun kyauta kenan?. Ya zaku
kora yarinya da sanyin safiyar nan makaranta ba tare da ta karya ba. alhalin kuma kunsan ba'a
taso wa sai Karfe sha biyu ake tasowa". Gaba dayan su wani mugun kallo suke wa Fiddausin "
buhun ubanki Fiddausi ah! Kaji 'yar zamani, Yanzu mu zaki wa wa'azi To abinci dai in gaya miki
yau ko kwaya fatima bazata ci ba acikin gidan nan. Bama iya yanzu ba". Cewar Mama asiya,
Zuwaira tace 'Kyale 'Yar banza kamar yanda ta tafi da yunwa ke ma haka zaki tafi da ita tunda
kinga kular dan waken, Kuma ba mai sani in kuma shiga Kitchen"_
_Gaba daya su Mama asiya ma haka suka fada, "Dan haka kawai Hauwa raba burodin nan
kowa ya zuba tea yasha ya hakura". Tashi tayi ta jawo daya daga cikin maka-makan biredin
wajen guda takwas. Wuka tasa ta yanka tsakiyar biredin mamaki ne ya bayyana a fuskarta ta
tsaya tana kallan biredin Cikinsa yayi baki kirin wasu 'yan kananan kwaruka ne ma a ciki suke
yawo. "A'a jiya fa aka sayo wannan biredin bai kamata ace ya lalace yau ba". Asiya ce ta taso
daga kan kujerar da take a zaune "Lalacewa kuma kamar ya?". Hauwa ta mika mata biredin
tagan shi rube, "Ikon Allah, A inaga wannan shine marar kyau din bara muga". Wani ta dauko
ta yanka shima dai haka ba kyau. Gaba daya sai da suka fasa sauran bire din duk Sun lalace
daga ciki amma bayan Ko alamar lalacewa babu. Asiya ta hau jaraba. Tana zazagen Gidan
biredin. "Wannan ai rainin hankali ne, da zalunci. Ya zasu bawa mutane Rubaben Bread to
Wallahi sai na mayar musu anjima". Tsaki Ameera taja. "Mtseewww! Mun kusan makara ga
malamin mu bashi da mutunci bari mutum ko tea ne ma yasha". Tashi tayi ta dauki kofi ta
karkata wani filas nufin ta ta tsiyayi shayi. "Kan uba!". Abunda ta furta kenan. Gaba daya aka
juyo aka zuba mata na mujiya. "Wai ku yau kawai so kuke kuyi mana horo da yunwa kenan.
Nan ai ruwa ne zallah ko zafi ma babu". Hauwa tace "mu gani" Ta dauki kofin "lah! Wallahi da
gaske take ruwa ne zallah bayan kuma Ni da kai na na zuba tea a cikin nan"._
_Shiru su mama Asiya suka yi ido kawai suke bin Jama'ar gun da shi. "Mtseew To Wallahi ni
dai bazan kuma shiga kitchen a yanzu ba. Haba kamar wata jaka?". Cewar Mama Asiya.
Zuwaira tace "Wallahi ko ni bazan shiga ba". Fiddausi tace "To mu dai makaranta zamu tafi sai
a bamu kudin Break". Dari bi biyu mama asiya ta bisu da shi. Tace "Kowa yaje ya sayi abunda
zai ci mu dai ba wanda zai kara koma wa