Showing 93001 words to 96000 words out of 103342 words
Chapter 32 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
nima dai ban yarda da wannan jawabin ba. Haba dai yo
ai ni ko a Tv ban taba gani ba. Kuma wallahi yanzu zan kuna TV din tayi abunda zatayi". Hauwa
tace, "To marar kunya wato duk da ina auren baban ku matsayina bai haura karyatawa kai tsaye
ba. To shikenan ni na barku lafiya. Ba dani ba raban fadan Zakuna. Wanda baiji bari ba yaji
hoho, Ni kunga tafiya ta". Hauwa na fadar haka ta haura sama abunda. Asmart tsaye tayi abun
nayi mata yawo a kwakwalwa. Tunani take ta Mayar da socket din ko ta fasa. Nasmat ganin
asmart ta kasa kunna tv yasa ta tashi ta nufi wajen "Dallah matsoraciya matsa ni in jona in ke
tsoro kike. Abunda dama wannan 'yar tsanar ce Aljanar kuma an toyata"._
_Asmart na jin haka tace "Kuma fa haka ne". Nan suka fara rige-rigen mayar da socket din.
Fiddausi na jinsu duk abunda suke ko uffan bata ce musu ba. Ta dukufa wajen karatun novel da
take a waya. Ameera kuwa game take a waya sai ihu! Take kamar zautacciya. Nasmat da
Asmart daga wannan taje saka socket din sai dayar ta ture ta. Wai kowa na fadin shi zai mayar.
Da suka dade suna haka sai kuma suka tsaya suka sasanta a kan a kama a saka a tare. Da
mayar da socket din da dauke war wutar dakin duk daya. Juye-juye suka shigayi. Fiddausi da
ameera su kansu sai da suka dakata da abun da suke. Gam! Gam! Gam! Windows din falon ne
suke rufe kansu da karfi. Duk da rana ce a lokacin amma sai falon ya zama duhu rudum, kamar
tsakar daren da ba farin wata. "Nasmat!, Fiddausi!, Ameera!. Kuna ina?"._
_Suma din gabaki daya a rikice suke sai kiraye-kirayen juna suke. Domin duhun yayi yawa ko
tafin hannun ka baka iya gani. Fiddausi ji tayi kawai anyi sama da ita ana ja kamar wacce iska
ke tafe da ita. Ihu! Take tun karfen ta hakan yasa su Nasmat suka kara rikicewa suma. Kofar
falo ta bude Fiddausi sai ji tayi an watso ta waje. Mai gadi ne yayo kanta yana tambaya
"Lafiya-lafiya me ke faruwa". "Aljanu ne". ta fada tana nuna mishi falo yayin da take kokarin
tashi. Tana tashi ta zangara a guje. Mai gadi ma da gudu ya koma daki ya garkame kanshi. Su
Asmart da sukaji ihun! Fiddausi ya lafa sai suka shiga kiranta. A hankali Asmart ke fadar "Aunty
Fiddausi! Aunty Fiddausi!". Shiru bata ji an amsa ba. A tafiyar da take tana lalube irin na makafi
sai taji hannuwanta sunci karo da mutum. Nan take ta fara lalubata tana kiran sunayen su.
"Nasmat ce?, Ko aunty Ameerah ce?. Fiddausi ce?. Yi magana mana". Shiru bata ji yarinyar
tayi magana ba. "Wai Fatima ce?". Ta kuma tambaya tana shafa fuskar. Tana zuwa saitin bakin
sai ji tayi an gallara mata cizo. Ahhhhhhhhh!. Ta saki ihu! Abunda ya kara dugunzuma su
Nasmat kenan suma suka rikice. Gudu suka ringa yi ba tare da sun san ina suka nufa ba.
Bango birki. Nasmat na tafe a cikin duhu taji tayi karo da mutum. Tunani ta Asmart ce. Cewa
tayi "Asmart wai duhun miye wannan?". Shiru bataji tayi magana ba._
_Lalube ta kamayi kuma sai taji ai yarinya ce taci karo da ita din. "Fatima! Fatima!". Wata irin
walkiya suka gani kamar an kawo nepa an dauke. Nan take suka kara dimaucewa.
Hahahahhaha gaba dayan dakin ya kwashi dariya, Zuwa can kuma sai wani ja haske ya cika
dakin gaba daya. Nan take suka ga junan su bayan sun hadu waje daya ne suka kuma jin wata
irin dariya kamar ta yara a bayansu. Ahhhhh! Suka fasa ihu a tare. Ba komai bane suka gani
sai kan Fatima na tafe q kan iska wuyan wani irin jini ne mai kauri ga danko yake zuba kasa. A
bakin ta kuwa wani danyan nama ne take ci duk jini na zuba. Ga kuma gashin kanta da ya
koma wasu murda-murda ba kyan gani sai motsin yake da kanshi kamar macizai. al'amarin duk
wanda yaga abun dole ya tsere in ba'aci sa'q bama mutum sai ya suma. Wannan kan na Fatima
mai shegen abun tsoro n ya nufi su Asmart su kuwa kamar wanda aka rike wa kafafu sun kasa
guduwa. Suna nan tsaye sai tsala ihu! Suke. Kan na zuwq saitin Ya wangare baki ya wani kara
fadi. Kamar zai hade su baki daya. Luuuw! Suka ringa zubewa sumammu. Kafin kiftawar ido
falo ya dawo yanda yake. Su Mama Asiya duk ihun da ake baya zuwa wajen su hakan ne ma
yasa basuji ba. Zuwaira ce ta sakko daukan wani abu. Tana ganin su Nasmat a shimfide ta rude
nan-da-nan ta fara kwallawa su Mama asiya kira. Suma da gudu suka sakko downstairs din
suna tambayar me akayi.Zuwaira ta nuna musu Asmart da yatsa. Ai da sauri hauwa ta dakko
ruwa mai sanyi aka fara yayafa musu._
_Duk wacce ta farfado sai ta kankame ta kusa da ita a firgice suna sambatu da ambatan sunan
Fatima. Mama Asiya da duk ta rude take tamabay me akayi. Hauwa tace, "Ni dai dazun na
barsu nan lokacin Asmart zata daki Fatima shine na dakatar da ita na fada musu cewa Fatima
nada aljanu. Shine har suke karyata ni. Sannan kuma Fatima ta zare socket tace duk wanda ya
mayar zatayi maganin sa". Hauwa ta kalle gurin socket din taga an mayar, "Af! Socket din suka
mayar ai yanzu gashi sun jawa kansu". Mama Asiya cikin masifa ta fara magana. "To Wallahi
bazai yuyu ba. Dole a dauki mataki Wallahi ko in bar gidan nan yau. Haba ya zan tsaya ina kallo
aljanun Fatima su kashe min yara. Bari in kira alhajin shima da yaje yayi zaman shi a kasar
mutane kamar can aka yanke mai cibi". Da sauri ta koma daki ta daukko wayar ta kira Alhaji. Ko
gaisawa basuyi ba ta fara binshi da masifa take gaya mishi duk abunda ke faru. Alhaji kuwa
wufantar da zancen yayi. Yake cewa. "Wato Asiya kuma ta nan zaki bullo wa Yarinyar nan ashe
har yanxu wannan zaluncin da kike wa Fatima baki daina ba. In banda karya da sharri ya zaki
ce wai Fatima ta addabi gida kaza-da-kaza?". Mama Asiya cikin masifa ta kara kai'mi. "Au!
Abun da zaka ce kenan. To Wallahi in haka ne zan tatara yarana in tafi da su gidan mu. Haba
ina dalili yaseen bazan yarda Aljanu su kashe min yara ba. Yanzu haka ga su Asmart nan rai
hannu Allah Aljanu sun dadake su duk sun ji musu ciwo". Daga can alhaji yayi magana da
alamun shima ya fusata. "To naji zaki iya tafiyar ki amma karki sake ki fitar min da yaro ko daya.
Ke in ban isa inyi iko dake ba ai na isa inyi da yara na. Kuma in sha Allah wannan juma'ar zan
dawo sauran inga kuma ba dai-dai ba. Ko inji Fatima tace min zalumtar ta kuke. Wallahi da sai
na dau kwakwaran mataki wanda bazai miki dadi ba". Yana fadar haka ya kashe wayar._
_Tsaki mama Asiya taja, "Wato kai kana can ka bar mu da Aljana na neman sabautamu". Haka
dai gidan ya wuni cikin dar-dar, Fatima kam ta zama abar tsoro dan in tazo waje gaba daya sai
suyi tsit. Da dare da kyar suka yarda da su kwanta a dakinsu. Wajen karfe 11 na dare Fatima ta
tashi ta tafi sama mama Asiya na barci taji ana tashin ta. Tana farkawa kuwa taga Fatima.
"Fatima me akayi kike tayar dani tsakar daren nan?". Mama Asiya take maganar cike da tsoro.
"Murya na fitowa biyu-biyu Fatima tace, "A nan zan kwana dan haka ki tashi ki koma falo ki
kwanta". Mama Asiya na karkarwa ta tashi ta yayimi bargo ta fita a dakin. Tun kafin ta sakko
daga kan matakalar ta hangi mutum a zaune a falo mace ce kin bakaken kaya. Ta juya mata
baya........................................._
A dakace ni yaseen na gaji
DOMIN SAMUN FARKON LABARIN, DAMA WASU LABARAN MASU DADI DA MA'ANA.
SHIGA PAGEN MU KA/KIYI LIKE.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
SHIGA NAN KA/KI YI LIKE. DOMIN SAMUN FARKON LABARIN. DAMA WASU LITTAFAN
KING BOY ISAH.
https://m.facebook.com/bigboyisahfans/?ref=bookmarksbookmarks
Autan marubuta nee King Boy Isah
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 105-106
© *KING BOY ISAH* ✍
. .
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
. ✍ *®Z.W.A* .
. .
_*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_
_*Zaku iya samun littafan mu a Facebook*_
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
_*Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu*_
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*DEDICATED TO YOU*
QUEEN HAUCY
MINEERT
AMÆL
SALMAH
MINEERT
QUEEN MEIMIE
PHATEEMA
MARYAMU
MUHIEVER INDIA
❤ KUNA A RAINA KU DIN NA DABAN NE A HEAR DIN KIN. INA SANKU MASOYANA.
ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MUKU A DUK INDA KUKE.
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Mama Asiya na karkarwa ta tashi ta yayimi bargo ta fita a dakin. Tun kafin ta sakko daga kan
matakalar ta hangi mutum a zaune a falo mace ce kin bakaken kaya. Ta juya mata baya.~
_Cikin muryar tsoro mama Asiya ke magana. "Wacece?. Waye a nan?". Shiru bata amsa ba.
Kara matsawa tayi tsoran ta na dada karuwa. Sai tambya take amma anyi mata shiru. Nan ta
tsaya tana sake-saken ta juya ko kuwa ta karasa. Zuciyar ta ce ta bata shawarar cewa taje ta
gane wa idan ta waye a zaune. Gwara nan da can din wajen Fatima. Cikin Kwarin gwiwa ta nufi
wajen matar ta dan kauda tsoran ranta. "Waye-waye". Ta kara tambaya firgigit matar ta juyo
Hauwa ce, da alamu gyan-gyadi take. Mama Asiya na ganin Hauwa ce tace, "Hauwa wannan
wane irin kaniya ce. Kina ji ina miki magana kika share ni, Wallahi har kin bani tsoro". Hauwq na
murza ido tace, "Ni wallahi cikin barci ne ma naji kiran ki". Mama asiya tac, "To ke kuma wace
uwar ta dawo dake falo ga dakin ki can kin baro?". Hauwa ta waiga baya alamun marar gaskiya.
Murya kasa-kasa tace "Wallahi Fatima ce ta bini daki ta koro ni wai in dawo falo ita zata kwanta
a dakin". Zagayawa mama Asiya tayi ta zauna._
_Cikin rada mama Asiya tace, "Taf! Di jam, Kika ce Fatima ce ta koro ki". "Eh Wallahi ita ce,
Yanzu haka tana can saman gado na tayi kwanciyar ta". "To Fatima aljanun nata ko har sun
fara raba ta gida biyu ne?. Domin yanzu ta koro ni fa daga daki na wai...". Sautin saukkowar da
suka ji daga stairs ne ysa mama Asiya bata karashe maganar da ta fara ba. Suka juya su biyun
suka zura wa wajen ido dan ganin wanda zai sakko. Ba kowa bane Zuwaira ce itama rike da
bargon ta a hannu kamar almajirin da ya fito rani. Mamaki ne ya kama ta ganin su Asiya a falo.
"Aunty Asiya, Me kuma kuke yi a falo". Zuwaira ke tambay. Asiya tace, "Ai ke ya kamata mu
tambayi me ya fito dake daga dakin ki da tsakar daran nan harda kwaso blanket". Zuwaira ta
juya baya tukun tayi kasa da murya tace, "Aljanun Fatima ne suka koro ni. Wai fa dan daukar
alhaki ina kwance abuna sai ji nayi ana tayar dani, Bayan na bude ido naga Fatima ce, Kar kuso
kuji cikin irin muryar da take magana. Da shi abar tsoro shine ta koro ni falo". Su mama asiya
suka ce ai sai kizo ki hau layi domin muma nan da kike gani ita ta koro mu". Zuwaira tace, "A
gaskiya ya kamata mu dauki mataki haba Aljanu ma ai suna da maganin". Asiya tace, "Rage
murya kar su jiki, Dan Wallahi yanzu zakiji ana gaura miki mari". Da sauri Zuwaira ta matse
bakin ta da hannaye. Bayan sun baje a falo. mama asiya tace, "Nasan matakin da zan dauka.
Ku bari gobe zan gaya muku"._
_Washe gari tun da asuba kafin su mama Asiya su tashi daga barci, Fatima taje ta debo ruwa a
waje mai shegen sanyi. Nan tazo ta fara kwara musu. Gaba daya a gigice suka ringa tashi.
Suna tashi suka ganta zaune kan 3Stars tana musu dariyar mugunta. Daga bisani ta bata rai
tace, "Maza ku tashi aje ayi sallah sannan a zo a shiga kitchen". Suna rawar dari suka tashi ko
wacce ta nufi dakin ta dan yin sallah. Fatima ta tashi ta shiga dakin su, Nasmat, Ameera da
sauran yaran sai barci suke abun su. Fiddausi ce kadai ta tarar kan sallaya tana karatu. Da
sauri Fatima ta koma ta kara debo ruwa ta zo ta dingi watsa musu tana tashin su suje suyi
sallah. Ameera watsa mata ruwan da akayi, abun yayi matukar bata mata rai. A fusace ta nufi
Fatima, Batayi wata-wata ba ta kwasa mata mari. Sannan ta dora da fada, Yayin da ita kuma
Fatima ta sadda kai kasa. "Ke Fatima bar ganin ana cewa wani kina da Aljanu. Wallahi ni ba
raga miki zan ba. Aljanun banza, Shikenan dan kina da Aljanu sai kita takura wa mutane. Miye
zaki wani watsa wa mutane ruwan sanyi da safiyar nan. Anki ayi sallahr". Firgigita Fatima ta
dago kai. Dagowar da tayi idanun ta sun koma kamar garwashi har wani tartsatsin wuta ke fita a
idan. Gabaki daya mutanan dakin sai da suka tsorata. Su Asmart kam kankame juna sukayi
hade da runtse idanu. Fiddausi kanta da take karatu abun ya firgitata. Nan take ta fara karatun
da karfi tana tofawa saitin Fatima. Fatima bata kula ba. Hannu ta mika saitin Ameera dake
baya-baya a tsorace kamar tayi kuka. Ameera sai ji tayi an shake mata wuya. An dage ta sama
ba tare da subga wanda ya daga tan ba. Sai da aka wul-wulata kafin aka mako ta kasa._
_Sa'arta daya kan katifa ta fado. Fatima cikin wata murya mai zaburar wa tace, "Maza kafin in
kirga goma kowa yaje yayi alwala,.....1....2..". Ai da gudu aka ringa rige-rigen shiga ban daki
dan yo alwala. Bayan sun yo alwalar sun fito kuma sai sukaga fatiman bata nan.
Daki-daki.Fatima tabi ta tattaro su mama Asiya aka shiga kitchen domin hada abun kari. Tukun
taje dakin Abba ta tayar da shi shima yayi sallah. Har ya fara mata magiya a kan ta mikar mai
da dayan hannun shi, Ta daka mai tsawa hakan yasa ya kyale ta. Su mama Asiya sunji jiki sosai
yau a Kitchen, Domin kamar yanda suke wa Fatima. "Dake wannan kul-kula wancan kwashe
can gyara nan", A da. Haka itama Fatima yau ta ringa juyasu, kamar ta sama bayin ta. Haka
wajen cin abinci ta ringa bada doka. Domin ko katuwar loka taga mutum yayi sai ta kwala mishi
Cokali. Gaba dayan gidan kuwa tsoranta karuwa yake a gare su. Ana gama cin abinci Fatima
tace to masu zuwa islamiyya a tashi ayi shiru, Ku kuma matan gida a gyara gida shara
wanke-wanke da goge-goge. Tana fadar haka ta wuce daki. Yayin da suma masu zuwa
islamiyyar tuni sun fece sun bar wajen. Mama Asiya ta rike baki alamun mamaki "Oh! Duniya
kowa ya sama waje sai kiga ya baje kolin shi. Yanzu dai ga Fatima aljanu sun sata tana mana
iskancin yanda taga dama kamar mu yaranta ne"._
_"Ke dai bari wannan abun takaici. Ya muka iya haka zamuyi hakuri mu jure har Alh. Ya dawo
muga irin matakin da zai dauka". Cewar Zuwaira. Asiya ce ta katse mata hanzari ta hanyar
cewa. "Kai aradu bazamu jira har sai ya dawo ba. Yau fa laraba kuma shi yace sai ya kai juma'a
tukun zai zo, Dan haka yau zamuyi maganin abun ku dai bari wannan aljanar ta tafi makaranta
tukun". Nan suka fara share-share suna kakauda kayan da suka ci abincin. Ba'a jima ba sai ga
fiddausi da Fatima sun fito cikin uniform din islamiyya. Wani dan iskan kallo fatima ta jefa wa su
mama Asiya kafin tace, "Ai na dauka da bazakuyi abun da na saka ku ba"._
_Tana fadar haka bata ko jira sun tanka ba ta kama hannun Fiddausi suka fita. Ita dai Fiddausi
duk a tsorace take da Fatima gudu take cutar da ita. Bayan yara duk sun tafi makaranta su
mama asiya suka shirya mama asiya tace musu malami zasu je su samo yayi masu Ruqiya ya
fitar da aljanun. Gaba daya suka amince da haka. Ga motar alhaji amma suka fita a kasa.
Kasancewar a cikin su ba wacce ta iya mota. Suna tafe har sun kusan barin layin sukayi kicibus
da wata mata da alamu yar anguwar su ce, Tafe take tana rausaya kamar wata budurawa, Ba
hijab bane a jikin ta gyale ne ta dan yafa a kafada. Fuskar tasha hudar wacce zan iya ce muku
har taso tayi yawa. Cingum ne a bakin ta tana tauna lips din yasha jan baki. Da gani kasan yar
duniya ce. "Asiya Anguwa za'a fita, Da