Showing 66001 words to 69000 words out of 103342 words
Chapter 23 - ALJANAR FATIMA Book Complete Hausa Novels by kingboy .pdf
mama Asiya ta Juya wanka wa
Abba mari hade da cewa. "Baka da hankali ko so kake yanzu ka jawo mana masifa, Me tayi
maka ne da zaka daki yar mutane daga zuwan ka". Abba cikin bacin rai kamar ya fashe da
kuka yace, "Mum yanzu a kan wannan Yar banzar Yarinyar ne kika daga hannu kika mare ni?
Abunda baki taba yi min ba. To Wallahi ta shiga uku tunda tasa aka mare ni ni kuwa a kullum
kuma duk haduwar da zamuyi sai na mare ta". Yana fadar haka ya tashi yana gunguni ya nufi
bangaren sa. Mama Asiya na kiranshi amma yake ko waigowa. Da sauri ta kama Fatima ta
dorata a kan kujerar da take kai. Da zanen jikin ta ta share mata hawayen fuskar ta ta shiga
lalashi. Ita kanta Fatima abun yayi mugun daure mata kai, Ta rasa dalilin yin hakan. Haka suma
su Zuwaira abun ya basu mamaki yanda Mama Asiya ta tsani Fatima yau kuma ita ce harda
lalashin ta._
_Ita kuwa ko kula da su batayi ba sai wani rawar jiki take gani Fatima sai kuka take tsoro take
Aljanar taci ubanta duk da dai ba ita ta mari fatin ba. Fatima kuka take tayi domin fuskar ta sai
zogi take. Da sauri Mama asiya ta kunto yar babyn Fatima ta mika mata "Yi shiru Fatima na, Ga
babyn ki ma na daukko miki kuma nayi mata wanka da kwaliyya kalli tayi kyau kuwa?". Fatima
sai a yanzu taga babyn nata. Dakatawa tayi da kukan ta wani wangale baki cike da farin ciki ta
karbi yar babyn nata tana jujawa. "Mama Asiya ke kika mata wannan kwaliyyar?. Amma tayi
kyau sosai". Itama mama Asiya cike da farin cikin ta rabu da alkakai tace, "Eh ni nayi mata
tashi ki kaita daki barci take ji". Fatima tace to Mama Asiya Ina akwatin kayan ta?". "Jeki kawai
yana dakina anjima zan kai miki". "To Fatima ta fada ta juya ta wuce dakin su cike da farin ciki.
Tana shiga dakin Mama Asiya tayi ajiyar zuciya. " Ita kuwa ko kula da su batayi ba sai wani
rawar jiki take gani Fatima sai kuka take tsoro take Aljanar taci ubanta duk da dai ba ita ta mari
fatin ba. Fatima kuka take tayi domin fuskar ta sai zogi take._
_Da sauri Mama asiya ta kunto yar babyn Fatima ta mika mata "Yi shiru Fatima na, Ga babyn ki
ma na daukko miki kuma nayi mata wanka da kwaliyya kalli tayi kyau kuwa?". Fatima sai a
yanzu taga babyn nata. Dakatawa tayi da kukan ta wani wangale baki cike da farin ciki ta karbi
yar babyn nata tana jujawa. "Mama Asiya ke kika mata wannan kwaliyyar?. Amma tayi kyau
sosai". Itama mama Asiya cike da farin cikin ta rabu da alkakai tace, "Eh ni nayi mata tashi ki
kaita daki barci take ji". Fatima tace to Mama Asiya Ina akwatin kayan ta?". "Jeki kawai yana
dakina anjima zan kai miki". "To Fatima ta fada ta juya ta wuce dakin su cike da farin ciki. Tana
shiga dakin Mama Asiya tayi ajiyar zuciya, Hade da wata doguwar mika tace, "In Allah yaso
falke sai kayan sa su tsunke a gindin kaba. Komai kayi hakuri kaga karshen sa". Da fadar haka
sai ganin wannan tsohuwar ta bayyana a gefan ta "Wannan maganar dawa kike?". Aljanar ta
tambaya. Mama Asiya na ganin ta ta wani wuntsila ta saman kujera ta fada kasa. Tana faduwa
ta tashi tayi daki a guje._
_Umar tun ranar da wannan abun ya faru ya dai na bin layin gidan sa. Kullum sai dai yaje gidan
iyayen sa ya kwana. Yau kusan kwana biyu kenan sun tambaye har sun gaji amma yaki gaya
musu me ya ke hana shi kwana gida. Haka yauma sai da Inna ta tambaye shi Rafy Yace mata
lafiyan ta lau yaja mashin dinsa ya fita aiki. Misalin karfe daya na rana Safuratu Cikin sufar
Rafi'at Taje gidan su Umar Inna na ganin ta ta tarye ta cikin fara'a Rafy kuwa tun daga bakin
kofa tq fara kuka. Nan kuma Inna ta shiga jero tambayoyi "Aa Rafy lafiya zaki shigo lafiya kuma
ki kama kuka. Me yake damun ki?". Inna ta kama hannun ta tajata suka sama waje suka
zauna. Rafy tayi ajiyar zuciya bayan dan shiru da tayi Inna na tambaya. "Inna Umar ne gaba
daya ya fita lamarina tun Shekaran jiya waccan Umar baije gidan ba. Haka kuma bai fada min
inda zashi ba.... ....................... ............._
Al qura'an na gaji
☺I'm back My Fans aci gaba da gashi
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 75-76
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
DEDICATED TO ZAMANI. ABAR ALFAHARINA KUN ZAMA YAN UWANA. BANA
GAJIYA DA JIN ZANCEN KU KARKU BARI. KO BACIN RAI NAYI IN NA TUNO KU SAI INJI
FARIN CIKI ALLAH YA KARA MANA SAN JUNA DA HAKURI DA JUNA. ALLAH YA KARA
DAUKAKA YAN UWA NA
*KAMAR YANDA AKE YIWA AMARYA KAYAN DAKI. MUMA MAZA TA
KAMATA A RINGA WA ANGO WADANNAN ABUBUWAN SABO DA TSARO.*
KNIFE PROOF
TABARYA PROOF
MUCIYA PROOF
BULLET PROOF
HAKORI PROOF
MAGANIN TAURI
ACID PROOF
MAGANIN RUWAN ZAFI
KAI ALQURAN HAR ALLURA PROOF A HADA
*IRIN WANNAN KISA NA RASHIN IMANI. TO MAZA SAI A KULA A RINGA GOGE CHAT KO
TEXT IN ANYI DA BUDURWA.* *KUMA MAZAN AURE A BAR SAKACI DA WAYA HAR
UWAR GIDA TA DAUKA. KAI SAN SAMU MA KULLUM KA RINGA CHANGE SECURITY*
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Rafy tayi ajiyar zuciya bayan dan shiru da tayi Inna na tambaya. "Inna Umar ne gaba daya ya
fita lamarina tun Shekaran jiya waccan Umar baije gidan ba. Haka kuma bai fada min inda zashi
ba.~
_*R*af'iat taci gaba da magana. "Lokacin da zai tafi inna bai bar min kudin abinci ba. A kwana
biyun nan ni nake sayan abinci yan kudin hannuna duk sun kare. Da na dauka Umar garin ya
bari. Sai dazun wata makwabciyar mu take cewa ta ganshi a nan"._
_Inna ta rike baki hade da jijiga kai. "Ahhh! Ni RashidahYanzu Dama duk tambayar ki da nake a
gun Umar yana cewa lafiyan ki lau ashe karya yake yi". "Eh Wallahi Umma rabo na da shi tun
jiya". Inna ta bata rai sosai tace "Shikenan barni dashi zauna har ya dawo". Rafi'at tace "To"
na ta shiga taya Inna aiki har yamma tayi amma Umar bai ko leko ba. Umar yana yawon
acabar shi suka hadu da Mukhtar shima yana jan yar kurkurar shi. Nan suka tsaya suna
gaisawa Mukhtar yace "Abokina ya kwana biyu bana jin motsin ka ko dai Aljanar kace ke boye
ka a gida?". Umar ya hade gira yace "Kaga bana san wulakanci ya zaka ringa sako mana
maganar Aljana ana maganar kirki". Mukhtar yayi dariya yace "Ai kuwa dole in tambaye ka kai
da matar ka dan me bazan tambaye ka lafiyan ta ba?". Mtseeww Umar yaja tsaki kafin yace
"Ni fa wallahi in kana yi min maganar wannan Aljanar yanzu sai inja mashin dina inyi gaba".
Mukhtar yayi murmushi yace "Aa abun har yayi zafi haka?". Umar yacr "Ya ma wuce haka
domin in gaya ma Tun fitowar da mukayi da Yan borin nan ban sake lekawa gidan ba"._
_Mukhtar ya kece da dariya harda buka kafa. "Kaji matsalar ka fa. Sai mutum yazo ya gaya
maka matsalar shi amma ka ringa mishi dariya mtswww". Umar ya bata rai. Lokacin Mukhtar
ya dan tsagaita da dariya yace "Haba abokina karka ce haka mana. Abun ne ya bani dariya,
Amma kasan me Na samo mafita in dai zaka amince". Umar yace "Rike abunka bana so nasan
yanzu zakace ka samo wasu yan borin". Hhhhh Wata yar dariyar Mukhtar yayi tukun yace
"Haba ai koni yanzu ba ruwana da wasu yan bori. Wato naji labarin wani shahararren boka ne
wanda ya kware yayi matukar iya aiki.
Domin shi din aiki yake da Aljanu kuma walllahi na yarda da wanda ya fada min sosai, Sannan
kuma shi wannan bokan ba zuwa zamuyi mu daukko shi ba, Shi wannan daga munje mun fada
mishi shi da kanshi zai kirawo Aljanar ya daure ta yaci ubanta a gaban mu". Umar yaja dogwan
lunfashi da jin wannan dogon jawabi na abokinsa. Kasar zuciyar sa kuwa ta rabu biyu. Wani
barin na gaskata zancen wani na karyatawa. Zuwa can yace wa Mukhtar. "ka tabbata baza'a
sake samun matsala ba kuwa?. Gudu nake a je a kara yin irin na sarkin bori Duna". Muktar
yayi kasa da murya yace "Abokina ka yarda dani ni sam bani da gurin cutar da kai a rayuwa.
Duk Shawarar da kaji ta fito daga bakina to mai amfani ce". Umar yace "Na fahimta na gode
sosai abokina yanzu dai kaga Yamma tayi dan haka ka bari gobe mu shirya muje". Mukhtar
yace "To Allah ya kai mu amma ka tanadi yan karraffa". Dariya Umar yayi yace "Karka damu
abokina ai ni in dai za'a rabani da waccan Aljanar a dawo min da mata ta to ko nawane zan iya
kashe wa". "Su Umar an zama MIJIN ALJANA". Sukayi dariya gaba daya tukun sukayi ban
kwana Umar yaja mashin dinsa shima Mukhtar yaja Adai daitar sa kowa ya kama gaban shi.
Safuratu na gidan su Umar tana jira ya dawo har dare yayi tara ta kusa. Da har tace zata tafi
gida Inna ta hana tace dole sai ta jira Umar din ya dawo sun tafi tare._
_Wajejen karfe Tara Umar ya nufo gida domin yau aikin kawai yake ko abinci yakin saya yayi
wai tara kudin zuwa wajen boka yake. Tafe yake a kan mashin din yana yan wake-wake yana
jijiga kai. Da zuwa kofar gida yaje gaban shi yayi wani Dum! Ya fadi bai kula ba ya kutsa kai da
mashin dinsa ya shiga har yayi parking bai kula da mutanen dake zazaune suna kallan shi ba.
Da juyowar sa sukayi ido hudu da Ummansa da kuma Rafi'at. "Innahumin sulemanu wa'innahu
bissmillahi rahmanurrahim". ×3 Da sauri yake ambatar ayar zuwa can kuma ya durkushe a gun
ya fara cewa "Dan Allah dan annabi ki taimaki rayuwa ta, ki fita daga jikin mata ta. Kin hanani
zama a gidan mata ta. Na taho gidan mu nan ma kin biyo ni, Wai ya kike so inyi da raina ne?.
Me nayi miki". Da jin haka Rafi'at ta fashe da kuka tace Umma kinji fa ni yake cewa Aljana".
Cikin fushi Inna tace "Au! Umar wato duk abunda take fada ashe gaskiya ne?. Kai wanne irin
marar imani ne da zaka baro matar ka a gida kazo ka ringa kwana a nan?. Ba dan jaruma bace
ai da tun ranar zata biyo ka". Shi kam Umar gaba daya
Kanshi ya kulle yama rasa abun da zai ce._
_Inna taci gaba da cewa. "kalli yar baiwar Allah duk ta rarrame Ka baro ta da yunwa ashe duk
cewa da kake yi lafiyar ta lau karya kake ko gidan baka lekawa?". Umar dai baice komai ba
tunani yake shin wai Rafy din shi ce wannan ko kuwa Aljanar ce. Ita kuwa Rafy sai faman kuka
take. Inna ta dafa kafadar Rafy tace "yi shiru kinji share hawaye. Kai kuma maza ka tashi ka
koma gida da matar ka. Kuma in na sake ji ko na sake gani ranka sai yayi mugun baci". Umar
kamar yayi kuka ya fara magana "Inna dan Allah kiyi hakuri amma ni gaskiya bazan koma ba
Wallahi munafuka ce Aljana ce wannan ba Rafy ba". Rafy na jin haka ta kara Karfin kuka. Tana
cewa "Inna kina ji fa ni yake cewa aljana". Da sauri Inna ta rungume ta tana lalashi. Cikin fada
da masifa tace "Kai Umar tashi maza na gaya maka ku kama hanya ku tafi gida kai da matar ka
tun kafin rai ya baci bana san jin komai daga bakin ka. Dan iskanci Matar taka kake cewa
Aljana?". Har Umar zaiyi magana Inna ta taso ta nufo shi zata daka da gudu ya nufi waje. Rafy
tayi wa Inna sallama ta bishi. A jere suke tafe har gida ba wanda yace wa wani uffan daga cikin
su. Umar shi kam jikin shi sai rawa yake duk a tsorace yake. Suna shiga yaga gidan a gyare
tsaf! Ko ina ba wani datti. Sai da ma suka shiga dakin abun ya kara burge shi. Dakin sai uban
kamshi yake. Komai kuma gyare tsaf babu ko kyalle a yadda a kasa. Cikin wata irin murya mai
Dadi da sanyaya Zuciyar masoyi, Rafy tace "Sannu babyn na da gani kasha rana ka wahalar
min da kanka. Dan haka bari in hada ma ruwa kayi wanka tukun kazo in baka abinci kaci". Rafy
na fadar haka ta fita tsakar gida dan ta kai mishi ruwa ban daki. Umar suman tsaye yayi gaba
daya ji yake kamar ba shi ba. Har Rafy ta dawo bai ko motsa daga inda yake ba_
_Tana shiga ta kama hannun shi taja shi har bakin kofar ban dakin ta kara kashe murya tace.
"Sahibina ni fa ji nake kamar bazan iyayin hakuri in jure har ka fito ba domin idanuwa na Basa
iya jure rashin ka na dan lokaci kalilan. Badan wani boyayyen dalili ba dani zan shiga in ma
wankan babyna. Luuuu! Umar yaji kamar zai fadi dan dadin kalaman matar tashi. Wani
murmushin jin dadi ne ya kubuce mishi ba tare da yayi niyar yi ba. Bai san lokacin da yace
"Karki damu My onlyone yanzu zan fito nazo gare ki". Yana fadar haka ya shige ban dakin
wanka yake yana bangala dariya kama bashi ne mai tsoran Aljana ba. Farin ciki yama mantar
da shi cewa akwai Aljana a gidan. Allah-Allah yake ta fito daga wankan. Bai dau lokaci ba ya
fito sai zumudi yake ya nufi dakin. Yana daga labulan yaga Rafy tayi maza ta kauce kanta hade
da Rufe idanu da hannuwa. Abun ne ya kara burge shi nan take ya fara tuna rayuwar su ta
baya irin ta masoya da sukayi shi da Rafy. A hankali ya dinga takawa har yaje daf! Da ita tana
jun nunfashin shi a wuyan ta ta baya. "Haba Rafy tawa. Ya zaki nemi mayar dani kahon karfi
da yaji?. Idan kika hanani kallan fuskar ki idanu zusu makance. Juyo ki kalle ni Mana baby na".
"Dan Allah kai baka jin kunya na ne?". Rafy da ta juya baya ido rufe ta fadi haka. Umar yace
"Kunya kuma my ai tsakanin miji da mata ba kunya". Rafy tace "Kwarai haka ne annurin
zuciyata. Amma ai ya kama ta ko gajeran wando ne ka...". Ai kafin ta kai aya tuni Umar yayi
waje da gudu sakamakon Zumudin da yake na ya fito ashe ya ma manta ko Gajeran wando bai
sa ba Tsirara yake. Sai yanzu da ta fada ma ya lura hakan yasa yayi waje a
guje................................._
Umar abun ya kasu biyu. Kenan Muktar ya sake janka gun boka Ga Safuratu da
Salon So.
AUTAN MARUBUTA KING BOY NEEE
*^^^^^^^______^^^^^*
*ALJANAR FATIMA*
*^^^^^^_______^^^^^*
Page 77-78
© *KING BOY ISAH* ✍
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍ *®Z.W.A*
DEDICATED TO ZAMANI. ABAR ALFAHARINA
ZAMANI WRITERS BOOKS
*ZAMANAWA BOOKS*
Dan Allah tambaya nake yi nan *GIDAN MARAYU* ne?. Kunsan f ni *MARAINIYACE* Amma fa
hakan bai hanani *RAYUWAR 'YANCI* ba. Ko kunsan cewa *ABOKIN YAYA NA*.
*JA'JIRTACCE* Ne?.
Karkuyi mamakin ganina a guje *ALJANAR FATIMA* ce ta biyo ni, Tun daga *KURMIN DAJI*.
*ABU KAMAR WASA* Wai So na take. Kunsan kuma *SO MAKAHO NE*. Shiyasa Zan baku
*LABARINA*. Kamar yanda na bawa wasu *MATA DA MIJI*.In nayi haka Watakil na rabu da ita
*HAR ABADA*. Kunsan fa ni *RENON KAUYE CE* Hakan bai hanani zama *MARUBUCIYA*
Ba. Kunsan abun *HUKUNCIN ALLAH NE*. Allah nake gode wa da bayyi ni da *KAZAMIN
BURI* Ba. *HANYAR LIBIYA* Zaku nuna min. Domin can nake so inje Cigiyar *DEEJA DA
SANGAMI* , Sai dai ance min garin akwai wata *FATIMAH* Kuma wai *AHLIL KITAB*
ce.Bazadai kuji labarin *BABY KHAUSAR* a bakina ba. Kafin in tafi dai zan gaya muku cewa
*IDAN XURCIYA* ta gyaru to fa komai ya gyaru.
We love you Too much our following☺
*KARSHEN PAGEN BAYA*
~Ai kafin ta kai aya tuni Umar yayi waje da gudu sakamakon Zumudin da yake na ya fito ashe
ya ma manta ko Gajeran wando bai sa ba Tsirara yake. Sai yanzu da ta fada ma ya lura hakan
yasa yayi waje a guje.~
_*B*an daki ya koma ya sako kayan shi tukun ya dawo duk kunya ta cika shi. Lokacin da ya
dawo tun daga bakin kofa yake jin kamshin abinci. Yana shiga