Showing 1 words to 3000 words out of 90573 words

Chapter 1 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8069

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43





*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*


MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423


PAGE 1

Ƙauyen Damagaran
Tsaye take tamkar wata soja, tana kallon Ma'u mai gyaɗa, cikin zallar rashin kunya da fitsara.
Cikin shiga ta riga da zani da ɗankwali duk daban, sai kuma ɗammara da ta sha da baƙin gyale.
Fuskarta ɗauke da kwalliya irin ta 'yan ƙauye, waɗanda suka amsa sunan su 'yan mata, kuma
suke ganiyar tashen ƙuruciya. Wata kalar hoda ta shafa a fuskarta, duk ta yi mata butsu-butsu.
Sai kuma gira aka ɗauke shi, tun da ga kan farkon girar, har zuwa kusa da idanunta, sannan
aka haɗe jagirar da kwallin da ta sanya a idanunta. Wasu irin bille guda biyu ta zane fuskarta da
shi, sannan aka ja baƙi a saman leɓenta. Silifas yake a ƙafarta duk ya tsiɗe, yayi datti, domin
duk wanda ya ga silifas ɗin, zai rantse ba a taɓa sanya masa ruwa an wanke ba. Ita a dole ta yi

kwalliya kuma ta yi kyau ta ƙure a daka, amma kana ganinta za ka tabbatar da ƙazamiya ce
sosai, irin ƙazaman nan, da an gansu za ka gane su, saboda in ta matso kusa da mutum, da
ƙyar zai iya shaƙar numfashi. Saboda ƙazantarta sam mutum ba zai iya gane fara ce ko baƙa
ba, sannan kyakkyawa ce ko mummuna. Duk wanda aka sanya ya fasalta ta;mummuna,
bagidajiya, ƙazamiya kuma mara tarbiya. Jimmalo jikar Tani kenan, wacce ta gagari kowa a
ƙauyen Badarawa. Sam babu wanda yake shan ruwa a hannunta, babba ko yaro, saboda ba ta
da kunya da haƙuri, uwa uba kuma ɗaurin gindin da ta samu a gurin Kanta Tani, wacce a halin
yanzu ita ce ta zame mata uwa da uba.

Tsawon lokacin da ta ɗauka, tana tsaye ba tare da ta jirga ba, jiran Ma'u mai gyaɗa take yi,
wacce ta bita har cikin gidanta ta ɗauko mata gyaɗa.

Bazawara ce irin masifaffun nan, domin jarabarta ya sanya ko sati uku ba ta yi ba, mijinta ya
sake ta. Tun daga wannan lokacin ta fara aure ana sakin ta, saboda tsananin masifarta. Ko a
ƙauyen mutane suna shakkarta, sai dai ta bambanta da Jimmalo, domin in har ba ka kula ta ba
sam ba za ta shiga sabgar ka ba, amma Jimmalo ita kowa takala take yi. Tun da ta gane ana
tsoron Ma'u a ƙauyen ita kuma ta ɗauka ɗamarar faɗa da ita. Duk lokacin da jarabarta ya tashi,
gidan Ma'u take wucewa ta je ta iban mata gyaɗa don ta takale ta.

Sosai ta girme ta domin ba sa'arta bace, amma saboda jarabarta da rashin kunyarta take
shakkarta. Jimmalo sam ba ta da haƙuri ga ta da nacin tsiya a faɗa, musamman in har ita aka
cuta. Ta rinƙa bibiyar mutum har sai ta rama abin da aka yi mata. Shekarun ta duka sha huɗu,
amma abubuwan da take yi ya girme shekarunta. Sai dai duk wannan halayen da take da shi,
tana da girman kai da nuna isa da kuma gadara, sannan ga shegen kafiya, akwai lokacin da
duk yadda mutum ya so ta kula shi ba za ta kula ba.

Da gudu ta shallake katangar gidan Ma'u mai gyaɗa tana dariya, ganin ta nufo ta da muciya.
Ma'u mai gyaɗa cikin tsananin ɓacin rai take kallonta.

"Wallahi Jimmalo, yau ni da ke ne a ƙauyen nan domin babu wanda ya isa, ya ci mini bashin
gyaɗata ya zauna lafiya, ballantana ki shigo har cikin gidana ki ina ina gani ki gudu.

Jimmalo dake kallonta tana dariyar ƙeta."Kin san cewar in har kika na ce sai kin karɓi kuɗin nan,
za ki ja wa kanku tashin hankali? Don na rantse yau ko Babanki Tanimu zai taso da ga ƙabari
ya yi mini fatalwa ba zan bayar da kuɗin nan ba."

"Ni kuma wallahi sai kin bani, Kuma daga yau sai na kawo ƙarshen shigo mini gida da kike yi ba
tare da izini ba." Ta ce tana gyara ɗanmarar da ta ji, tamkar wacce za ta yi dabbe.

"Gidan na ki ai ba aljanna bace, da sai mutum ya yi aikin lada za a barshi ya shiga. Gidan da
yake wari shadda ta cika kin ƙi kwashewa. Na ci na ƙarfi na ci na tsiya da dabbe. In kina da ƙarfi
ki zo ki ƙwata, kin san dai ki ba irin dolayen mazan da kike aure bane kina musu duka, domin
wallahi ɗaukar ki zan yi na tula da ƙasa." Ta ce tana murguɗa mata baki, tare da harararta.

Kallon kanta ta yi, jin abin da ta ce saboda Ma'u irin matan nanne masu jiki, yayin da Jimmalo
take siririya sai tsawo kamar rama.

"Ni za ki nuna wa Allah ki ƙwala da ƙasa?" Ta yi mata tambayar cikin takaici.

"Eh mana saboda ba irin mazan da kike aure bane. Ɗube ta ƙatuwa amma ta kasa zaman
aure."

"Don ubanki na fi ki saboda ni ina auruwa, ke kuwa tun da kika zama 'yan mata, babu karen da
ya zo gurinki. Ƙazamiya mai warin balaga."

Jin abin da ta ce kuma ta yanke ta da yawa, sai kawai ta ɗauki dutse ta ƙwala mata. Ta ci sa'a
kuwa ta same ta a ƙafa.

"Kan uba! Wallahi yau sai na biki ko cikin mamanki za ki koma, na ga uban da ya tsaya miki." Ta
ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka tare da kwasa da gudu.

Ganin haka itama ta ɗaga bujenta ta kwasa a gije. Gudu take yi sosai kamar wata 'yar
tsuntsuwa, don tsalle take bugawa dai ta shalle guri mai nisa.

Ba ta tsaya a ko'ina ba sai da ta ga ta kai ƙofar gidan, sannan ta tsaya tare da yi mata gwalo da
daƙuwa ta shige cikin gidan.

"Wallahi yau ko bayan Atine za ki shiga sai na biki, tun da ba ki da kunya, gabakiɗaya kin
addabi mutanen ƙauyen nan." Ta ce cikin fushi tare da shiga cikin gidan.

Da gudu ta shallake Baba Aitine da take tsaye a bakin ƙofa, tana ƙoƙarin ɗora bushashshen
tuwon da za ta shanya.

"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Don ubanki yau wane mara haƙurin kika tono kuma, har ya ja
aka yi mini asarar bushashshen tuwo?" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya.

Tura baki ta yi tana harararta, sai kuma ta kalli Ma'u mai gyaɗa da ta shigo ciki.

"Uhumh, da na na san sai ke jarababba mara haƙuri." Ta ce tana watsa mata mugun kallo
wacce take tsaye tana nishi kamar ta haɗiyi kwaɗo.

"Wannan mara haƙurin ne daga na ci bashin gyaɗa, na ce mata ranar da jakin baba ya yi ƙaho
zan ba ta, shi ne ta yi mini duka kuma ta biyo ni." Ta ƙarashe maganar tana ƙaƙalo hawayen
ƙarya.

"Da ma na san sai ita ai, sam ba ta da haƙuri sam, duk ƙauye nan ita ce kawai za ta biyo ki har

cikin gida, tun da ba ta da ido. Ai ko mutuwa na kunyar idon mahaifi. Haka kawai kin kashe
auren ki kin addabi jakalle ta."

"Kin san abin da ta yi mini ne? Don ta gaya miki ƙarya sai ki kama? Ina cikin ɗaurin gyaɗata
yarinyar nan, ta shiga har ɗakina ta iba gyaɗar ina jiran ta huce na ƙulla."

"Au Ashe ma ba bashi ta ci ba, Allah ya ba da kasuwa ta yi miki?" Kaka Tani ta furta cikin zallar
mamaki tana kallonta.

"Kuma ba ki ga gyaɗar ba kaɗan na iba, domin da na san ba za ta haƙura ba, sai na ibo mana
da yawa musha koko da safe da ita, amma ba ta iya suyan gyaɗata ba, duk ta ƙone ta yi baƙi."
Ta ƙarashe maganar tare da sakin ma kanta rankwashi.

"Ai da kin sani da kin ibo da yawa, tun da hakan bai hana ta biyo ki ba ." Ta ce tana kallonta.

"Yanzu abin da kike yi a Ƙauyen nan kuma kyautawa kuwa? Jikarki ta hana kowa saƙat kuma
ba za ki iya tsawata mata ba? A yadda kike ba ta tarbiya, sai dai ta mutu a ƙauye nan, babu
aure, domin babu wanda zai iya kwasar ma kansa bala'i."

"Au ke ma rashin tarbiyyar ya sanya ki gagara zama? Alhamdulillah tun da ba ita ta share fagen
ba." Kaka Tani ta furta mata cikin gatsali.

"Sai aka ce miki zan yi aure? Ai ni da aure sai dai in ana yi a ƙiyama, saboda ba zan ɗauki
wulakanci ba. Ke kanki kin san ɓalla mutum zan yi in har ya kawo mini raini."

"A'a Jimmalo, jikalle ta! Za ki aure kafin na mutu sai kin haifa yara na gani..."

"Allah Ubangiji ya kyauta! Ke ma kin san ba zan iya ɗaukar raini ba. Kina ganin Hamasiya da ta
yi aure mijinta ya zane ta? Na rantse da ace nice sai na fitar masa da haƙarƙari."

"Ni fa ba wannan maganar na zo ji ba, a biyani kuɗin gyaɗata ko jiki ya yi tsami." Ma'u ta
ƙarashe maganar tana jijjiga ƙugu.

"Na gaya miki ƙarfi ya ce daru ya hana." Ta ce cikin gatsali.

"Kina ganin rashin kunyar da jikarki take mini ko?"

"To so kike na daki marainiyar Allah? Yarinyar da aka mutu aka bar mini tana tsumma."

"Wallahi sai kin biyani kuɗin gyaɗata." Ta ce tare da cakumarta.

Ba tare da tunanin Ma'u mai gyaɗa ta girme ta ba, kawai ta daka tsalle ta wanka mata mari.

Ƙara ta saki cikin gigita ta fara dukanta. Taron dangi suka yi mata. Suka rinƙa dukanta tana ihu.
Jin ihu ta ya sanya maƙota suka rugo da gudu.

A lokacin sun yi mata liƙis sai huci suke yi sun haɗa zufa." Nan gaba karya miki ƙafafun zan yi,
kika ƙara gigin shgo mana gida."

Kowa ya kasa cewa komai, sai kallon Ma'u suke yi cikin tausaya wa, tare da ganin wutarta da ta
shigo musu har gida, domin ta san cewa ko a waje suka yi ba ƙyale ta za su yi. Duk garin waye
ba su takurawa ba.

"Wallahi sai na kai ƙarar ku gurin maigari, don ba zan haƙura ba."

"Ki kai ƙara gaba da nan. Birni za ki je ki kai mu ƙara gurin 'yan sanda, in kika tsaya iya nan ba
ki ci ba." Kaka Tani ta ce tana harararta.

"Ni takaici ya hana ni cewa komai, so na yi na karya mata wuya, tun da har cikin gidanmu ta
shigo." Jimmalo ta furta tana zare ido.

"To ku wuce mana, kun zuba mana idanu munafukai kawai!" Kaka Tani ta daka ma mutanen
dake tsaye, a tsakar gida tsawan tana faɗin haka.

Da sauri suka fara fita sum-sum ba tare da sun furta komai ba.

"Munafukai kawai! Wallahi daidai muke da kowa a garin nan, tun da kuka nuna ba kwa sona da
jikata." Cewar Kaka Tani tana gyara ɗaurin ɗankwalinta.

"Ki sha kurumunki ki bar ni da su. Ni kawai na ishe su kakata, ba sai kin wahalar da kanki ba."

"Haka ne jikalle ta, amma ki kula kar wani ya illanta mini ke..."

"Ni! Har a garin nan akwai wanda zai iya dukana?" Ta yi mata tambayar, tare da zare ido cikin
mamaki ta dafe ƙirjinta.

"Na san babu wanda zai iya dukanki, amma ba na san asamu akasi, kin san ke kaɗai nake gani
na ke jin daɗi."

"Ki sha kurumunki kakata, don ni Jimmalo na zama gagara badau! Kuma na gagari kowa a
ƙauyen nan har maigari." Ta yi wa kanta kirari da hakan tana danƙwashi kanta.

"Kin ga Jimmalo, na gaya miki ya kamata ki kwance kanki na siyo miki fiya-fiya, ki sanya ma
ƙwarkwatan kanki."

Dariya ta yi tana ƙara rankwashi kanta da ƙarfi, saboda zafi har sai da ta ce,"Wash!" Tare da

cige leɓe.

"Aradu babu wata fiyafiyar da zan sanya, saboda ina jin daɗin kashe tana cewa ƙas!ƙas!!" Sai ta
ƙara kwashe da dariya tana dukan kan.

"Ya dai kamata gyara kanki."

Jin abin da ta ce, ya sanya ta ta shige cikin ɗakin ba tare da ta ce mata komai ba, domin idan
akwai abin da ta tsana ace mata ta gyara kanta. Tana da zafin kai, kuma ya haɗu da ƙazanta.

Ma'u cikin kuka ta ƙara da gurin gidan maigari. Kuka ta ƙara saki sannan ta kwashe komai ta
faɗa masa, sannan ta ƙarashe maganar tana faɗin,"Maigari ka yi mini tsakani da ita, wallahi na
gaji da rashin mutuncin da take mini, har gida take bina tana ci mini kayan sana'ata, kuma ba ni
da ikon na yi magana su haɗu su yi mini duka."
"Kai wallahi na gaji da ƙarar da ake kawo mini na mutanen nan! Ace mutane biyu sun gagari
ƙauye nan? Ko jiya sai da aka kawo mini ƙarar yarinyar nan, ta je ta zagi wani tsoho."

"Jimmalo ba ta da tarbiya kwata-kwata kakarta ba ta mata tarbiya mai kyau. Allah ko ni yarinyar
nan ina haƙonta, don dukan da ta yi wa ɗana Usmanu."

"Je ka yi mana kiransu." Ya faɗa cikin takaici jin abin da ya ce.

Miƙewa ya yi jikinsa na zikiri ya fice da sauri. Yana tafe yana addu'ar Allah ya sanya ayi mata
dukan tsiya.

"Assalamu alaikum," Ya kwaɗa sallama tare da jingina da garu.

"Waye yake damun mu da sallama kamar munci masa ba shi?" Ta fito tana tafiya cikin gadara.

Harara ya zabga mata yana yatsina fuska."Ai sai ki fito ki gani fitsarrarriya mara kunya."

"Ga ka Malam ka daina kirana da fitsarrarriya, don ba haka uwata da uban suka sanya mini ba.
Ta ce mishi cikin tsawan.

"Zagina za ki yi?" Ya yi mata tambayar cikin zallar mamaki.

"In ta kama mai zai hana? Don wallahi bana tsoron uban kuwa, kuma dama duk babban da bai
ja girman shi ba, ai sai yaro ya yi wasa da girman a ƙasa."

Mamaki ya cika shi ganin yadda take zare idanu, kamar tana magana da sa'anta.

"Ke kan Jimmalo, albasa ba ta yi halin ruwa ba, saboda kowa ya san iyayenki suna da mutunci.

Allah ya ɗibe miki albarka. Kamata tsoho da ni fuska duk gemu kike zagi?"

"Ni fa Malam ka kama girmanka." Ta furta tare da ɗaga masa hannu.

"Ba komai za ki haɗu da gamonki. Sai ki je in kin ga dama maigari yana neman ki da kakarki."

Jin abin da ya ce, ba tare da ta tsorata ba ta kama ƙunkunai. "Zaginsa za ki yi kenan?"

"In ji maƙura sai na gaya maka." Ta faɗi da ƙarfi tana zabga masa harara.

"Allah ya kawo mana guguwar da za ta kwashe ki ki bar garin nan, domin a ranar sai mun zuba
ruwa a ƙasa mu sha."

"Tun da ga annoba ta tafi ba, to ina nan zama daram-dam a cikin ƙauyen nan." Ta ce tare da jan
tsuka ta shige ciki.

"Da ikon Allah sai kin bar ƙauyen nan, muna nan muna jan miki yasin da tabaraka. Yarinyar sai
ka ce jujal duk tabi ta addabi mutane." Ya ce yana tafiya.

"Kaka Tani, kin ji maigari yana kiranmu." Ta yi maganar cikin shagwaɓa.

"To sai me? Kiran maigari kiran Allah ne. Ma za ɗauki mini mayafi mu je, in ta kama ai ko
agabansa zan yi faɗa da kowa a kanki."

Murmushi ta yi, jin abin da ta ce tana kallonta."Shi ya sa na ke so ki kakata."

"Ni ma ina son ki Jimmalo takwarata."

A hanya suna tafe suna hira, tamkar ba laifi suka aikata ba har suka isa.

Cikin gadara ta tsaya a bakin ƙofa tana aikawa Ma'u mai gyaɗa harara.

"Za ki shigo ki zauna mara kunya." Cewar wani a cikin zauren.

"A ka yi mata a hankali, kar ka tsorata mini jikata." Kaka Tani ta furta tana kallon sa.

"Na gaji da ƙarar ku da ake kawo mana kullum. Jikarki tana aikata ba daidai ba, amma soyayyar
da kike mata ya rufe mata idanu."

"Ka san ita mai ta aikata maigari? Matar nan fa har gida ta biyo jikata zata buga. Ni kuma da
yake bani da hankali sai na tsaya ina kallonta? Wannan dalilin ya sanya na ɗauki matakin da
kowa ce uwa za ta ɗauka, saboda ba zan iya gani ba ta dukan mini jikata."

"Wallahi maigari, yarinyar nan har gida ta shiga ta ibar mini gyada ina ina ƙullawa."

"Innalillahi! Amma baki da mutunci ƙarya za ki yi mini. Ba shi na siya kuma na ce zan biya."

"Ke!" Ya daka mata tsawan jin abin da ta ce.

"Sam ba kyau girmama manya ko?"

Tura baki ta yi tare da kallon gefe ba ta ce masa komai ba.

"Tun da bashi kika siya ki biya ta kuɗinta."

"Zan biya ina samu, dama ba ce ba sha nono uwa ba." Ta yi maganar a hankali, tana tura
ɗankwali gaba tare da sakin ma kanta ranƙwashi.

"To ki ba ta kuɗinta."

"Za ta biya inta samu, saboda bamu da shi, kuma yanxu ko gwamnati ana binta ba shi."

"Kin ga Tani? Wallahi in har ba ki rinƙa wa jikarki faɗa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login